Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwalliyar Matan Garin Gusau (3)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Kwalliyar Matan Garin Gusau (3)

NA

ƊAYYABA MUSTAPHA IBRAHIM

Kwalliya

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0 GABATARWA

Bitar ayyukan da suka gabata waiwaye ne akan wasu ayyuka da a ka yi rubutu a kansu masu alaƙa da wannan aikin. Masu bincike da dama sun yi bincike akan wani abu daga cikin abubuwa masu alaƙa da kwalliyar mata, saboda haka yana da kyau muduba irin waɗannan bincike. Wannan babi na biyu babi ne wanda zamu yi waiwaye akan ayyukan da suka gabata na masu bincike daga kundayen bincike na ɗaya har zuwa na uku sai littafai, da jaridu, da mujallu, da sauran takardu domin samun dammar yin nazari yadda ya da ce da kuma gano binciken da za’a gudanar da faɗaɗa shi.

2.1 KUNDAYEN BINCIKE

Kundayen bincike kundaye ne da masu bincike suke rubutawa idan sun kammala karatun su na gaba da sakandare ta ɓangaren da suka nazarta don bunƙasa ilimi da samar da wasu abubuwa sababbi ko ƙara haske a wannan fanni, haka kuma domin fito da wasu muhimman al-adu da rayuwar al-umma da abubuwan rayuwa yau da kullum. Waɗanda suke a ɓoye, afito da su sarari domin ɗalibai masu tasowa.

Za a duba waɗannan kundaye da masu bincike suka yi rubutu a kansu masu alaƙa da wannan aiki.

2.1.1 KUNDAYEN BINCIKE NA UKU

A cikin kundayen bincike na uku akwai masu bincike da suka yi rubutu mai alaƙa da wannan aikin kamar su:

Magaji (2002) a bincikensa ya yi bayani a kan al-adun Hausawa na gargajiya musamman a ƙasar Katsina, ya yi bayanin al-adun aure dana haihuwa da kuma na mutuwa, sai bukukuwa irin su wargin ɗiya da Dudu da Tambari a ƙasar Katsina. Wannan mai bincike ya yi ƙoƙari kwarai da gaske wajen bayyana yadda bikin tambari yake, inda ya kawo bayani kan yadda ƙasaitacciyar mace take yi, sai dai bai kawo bayanin irin kwalliyar da ita matar (Tambara) da ƙawayenta (Tambarori) dama sauran matan da suke halartar bikin suke yi a wannan muhimmiyar rana.

 

Wannan bincike ya tallafawa wannan aiki ta hanyar ƙara sanin wasu daga cikin tufafi da wasu al-adun mata Hausawa waɗanda suka shafi kwalliyar mata, amma duk da haka sun sha bamban ganin cewa binciken ya kalli al-ada ne wadda ta danganci bukukuwa, inda shi kuma wannan aiki ya dubi kwalliyar matan garin Gusau.

 

Shi kuwa Mu’azu (2005) ya yi bayanin Hausawa da dangantakarsu da daki a ciki ya yi bayanin al-adun Hausawa ya kuma bayyana yadda suka sani hanyar rubutunsu da karatunsu kuma ya dubi jirwayen baƙin al’adu na nesa da suka haɗa da na larabawa da turwa da kuma indiyawa. A cikin an tsakuro wasu al-adu kamar ƙunshi da yanayin sutura da yin fari da kyautar faranni da sauransu. Wannan ya ƙunshi nason baƙin al-adu na maƙwabta akan na Hausawa waɗanda suka haɗa da yarbawa da Fulani da barebari da kuma nufawa.

Wannan bincike ya bada gudummawa muhimmiya ga wannan aikin ta hanyar nuna yadda aka sami ƙunshi da sutura ta wasu al-adu amma a cikin ƙagaggun labaran soyayya. Don haka aikin ya bambanta da wannan aiki da za a duba kan kwalliyar matan garin Gusau.

2.1.2 KUNDAYEN BINCIKE NA BIYU

Haka kuma an samo kundayen bincike na biyu na masu bincike waɗand ake da alaƙa da wannan aiki da dama kamar su;

Kafin – Hausawa (1983) a bincikensa ya yi bincike akan ire-iren bukukuwan Hausawa na gargajiya kamar irinsu bikin sallah da naɗin sarauta. Ya ɗauki kowane biki ya yi bayanin yadda ake yinsa da lokacin da ake gudanar da shi tare da masu aiwatar da shi wato, maza ne ko mata ne zalla, ko kuma Haɗaka ne, akwai bukukuwa guda biyu da suka shafi kwalliyar mata Hausawa ta gargajiya. Waɗannan bukukuwa kuwa su ne, ƙunshi da cin fure. Inda ya yi bayanin yadda ake yinsu.

Wannan mai bincike ya taɓa kaɗan daga cikin nau’o’in kwalliyar mata Hausawa ta gargajiya. Saboda haka aikin ya taimakawa wannan aiki, amma sun bambanta, kasancewar aikin ya kalli bukukuwa da wasu kayan kwalliyar mata kawai, saboda haka wannan aiki nada alaƙa da binciken da za a gudanar kan kwalliyar matan garin Gusau kacokan bawai iya kayan kwalliyar ba kawai harda yadda ake yinta.

Haka kuma Mashi (2000) ta yi ƙoƙarin zaƙulo tasirin da zamananci ya yi a kan rayuwar Hausawa a cikin kundin ta ta nuna yadda rayuwar Hausawa take gudana kafin zuwan Turawa ƙasar Hausa sannan taci gaba da bayyana yadda rayuwar Hausawa ta cuɗanya da wasu al-adun Turawa, a ɓangaren al-adun aure da haihuwa da kuma mutuwa.

 

A sakamakon binciken ta nuna cewa a sanadiyyar cuɗanya ne a tsakanin Hausawa da turawa ne aka samu wasu kayayyaki, sutura da abinci da kayan kwalliya da sauran abubuwan amfani na yau da kullum.

A taƙaice wannan nazari ya bayyana tasirin zamananci a kan a bin da ya shafi tarbiyya da abinci da sutura wadda mata Hausawa suke yin kwalliya da ita da kuma al-adun aure da na haihuwa da na mutuwa, don haka wannan aiki ya bambanta da wannan da aka gudanar, amma duk da haka ya ƙara wa aikin inganci wajen samun wasu ƙarin suturu da muhimman bayanai.

Shi ma Mahmud (1996) ya yi ƙoƙari ƙwarai wajen yin bayanai a kan ire-iren mata tare da nau’o’in buƙatun da suke kaisu wajen malaman tsibbu. Haka kuma ya yi bayanai kan masu bayar da magungunan Hausawa na gargajiya da yanayen yanayen kowannensu da kuma yadda mai magani yake bayarwa da su. Daga ƙarshe ya duba hanyoyin waraka, wato hanyoyin da mata suke bi domin magance matsalolinsu ba tare da sunje wajen malaman tsibbo ba. Sannan ta bayyana illolin malaman tsibbu wannan binciken ta yi shi ne a kan abubuwan da suka shafi mata sai dai babu wani abu a ciki daya shafi kwalliyar mata.

Wannan aiki ya taimaka wa wannan aiki wajen gano yadda mata suke gudanar da abubuwan da suka shafe su, amma sun bambanta matuƙa dangane da inda kowa ne bincike ya karkata.

Haka ma, Sallau (2000) ya yi bayanai masu muhimmanci a kan sana’ar wanzanci, ya yi bayanin rabe-rabe wanzamai da ire-iren kayayyakin da suke amfani da su wajen aiwatar da sana’ar wanzanci. Sannan ya ƙara da bayyana ire-iren ayyukan wanzamai da amfaninsu ga al’ummar ƙasar Hausa wanda ya haɗa da irin magunguna da suke bayarwa. Har wa yau ya yi bayani mai gamsarwa a kan tsaga da ire-irenta da kuma tsagar da mata suke yi domin yin kwalliya. Daga ƙarshe ya naɗa a cikin naso da shawarwari kan yadda za a inganta sana’ar wanzanci ƙasar Hausa.

Akwai bambanci sosai tsakanin aikin da wannan binciken da aka gudanar, amma duk da haka aikin ya tallafa wa wannan bincike wajen gano ire-iren tsagar da mata Hausawa suke yi domin yin kwalliya. Sannan wannan bincike ya kalli kwalliyar matan garin Gusau, ba wanzanci a matsayin al-ada ba.

Suleiman (1990) ya yi cikakken bayani kan ma’anar tsaga da masu yin tsaga da kuma waɗanda a ke yi wa tsagar. Haka kuma ya yi bayani kayayyakin da ake amfani da su wajen yin tsaga. Sannan kuma ya kawo ire-iren tsagar da mata suke yi a ɓangarorin jikinsu daban-daban domin yin kwalliya a ƙasar Hausa.

Wannan nazari ya kalli tsagar gargajiya ne kawai kuma a ƙasar Kano, inda wannan aikin ya kalli kwalliyar matan garin Gusau, ciki hard a tsaga. Saboda ita ma tsagar mata suna yin ta ne domin kwalliya. Dan haka wannan nazari ya tallafa wa wannan aiki ainun, amma sun sha bamban sosai da nawa aikin.

 

2.1.3 KUNDAYEN BINCIKE NA ƊAYA

A cikin kundayen bincike na ɗaya akwai kundaye da masu bincike suka yi rubutu masu alaƙa da wannan aikin da dama kamar su;

Nadabo da Wani (1989) sun yi ƙoƙari sosai wajen bayyana ire-iren kwalliyar Hausawa gaba ɗaya, wato kwalliyar maza da mata da kuma ta yara. A ɓangaren maza sun yi bayanin wasu daga cikin ire-iren kwalliyar da suke yi ranar sallah, da kuma irin kwalliyar da ta da ce idan za a tafi kasuwa. Dangane da mata kuwa, sun yi bayani kaɗan daga cikin tufafinsu tare da kayan kyalli da kuma na shafe-shafe. A ɓangaren yara ma sun kawo bayanai kan kwalliyar tufafinsu. A cikin wannan bincike nasu, sun sassaƙa hotuna a duk inda ya dace, kuma sun sanyasu ne kamar yadda suke a jikin mutane.

Wannan bincike na da ya shafi kwalliya baki ɗaya wanda idan aka kwatanta batun nazarin tsakanin bincike da wannan aikin, bambancin a bayyane yake, tun da shi binciken ya duba kwalliya ma’ana da nau’o’inta a tsakanin maza da mata da kuma yara, amma wannan aikin ya duba kwalliyar mata ne kuma na garin Gusau.

Shi Yakasai (1992) ya yi bayani kan tufafin Hausawa na gargajiya, inda ya tsara su zuwa na maza da na mata. A ɓangaren tufafin maza, ya yi bayani tun daga kan ire-iren manyan riguna na musamman da huluna da kuma takalma. A ɓangaren mata kuma ya yi bayani zannuwa da rigunan mata da sauran su, ya yi bayani kan tufafi tare da nuna su cikin hoto

 

Nazarin ya shafi tufafin Hausawa maza da mata, kuma ya yi ƙoƙari wajen fito da ire-irensu da muhimmancin kowace ga rayuwar Hausawa. Don haka, nazarin yaba da haske ainun wajen gano kwalliyar mata Hausawa ta tufafi, amma sun bambanta saboda wannan binciken ya duba kwalliyar matan garin Gusau, amma kuma ya taimaka wajen samun wasu tufafi na mata.

 

Musa (1981) ya yi cikakken bincike a kan yadda ake aiwatar da sana’ar ƙira a birnin Kano da kuma bayyana unguwannin da ake yin ƙirar kamar su zango da Ƙofar Wambai ya kuma kawo bayanin yadda ake ƙera wasu daga cikin kayan kyalli na kwalliyar mata Hausawa waɗanda maƙera farfaru suke ƙerawa a Kano.

 

Binciken haƙiƙa ya shafi wani ɓangare da wannan aiki ya kalla, wato kayan ƙyalli waɗanda mata suke yin kwalliya da su. Don haka binciken ya tallafa wa wannan aiki ta fuskar gano wasu kayan kwalliya na mata Hausawa, amma duk da haka sun bambanta kasancewar wannan aiki ya kalli kwalliyar matan garin Gusau.

 

Aliyu (1983) ya yi bayanin tarihin sana’ar dukanci ya kuma kawo bayanin fata da yadda ake sarrafa ta, tare da ire-iren kayan aikin dukanci da kuma dangantakar sana’ar da sauran sana’o’in Hausawa na gargajiya. Daga ƙarshe kuma ya bayyana sana’ar da matsalolinta da kuma yadda za a inganta ta ya kuma zayyana ire-iren kayayyakin dukanci da mata suke amfani da su a matsayin kayan kwalliya kamar jakunkuna da takalma da sauransu.

 

Nazarin an gudanar da shi a kan sana’ar dukanci wadda tana ɗaya daga cikin sana’o’in da suka samar da kayan kwalliya na mata Hausawa musamman ɓangaren takalma da jakunkuna. Don haka nazarin da wannan aikin suna da alaƙa, amma duk da haka sun bambanta dangane da taken da kowanne ya nazarta.

Lawal (1985) ya yi bayani akan asalin sana’ar rini da wuraren da ake yenta, sannan an kawo bayani akan marina da kayayyakin da ake amfani da su wajen yin rini, kamar irinsu baba da kasu da ruwa da shuni da muciya da sauransu. Haka kuma binciken ya fito da siga da kuma fa’idojin rini, kamar ƙawata tufafi. Dagan an ya fito da al-adu da ɗabi’un marina, kamar ɓangaren sarrafa harshe. Haka zalika, ya yi bayani kan mabuga da dan gantakarta da marina, da kuma gudumuwar da sana’ar take bayarwa wajen bunƙasa tattalin arziki a ƙasar Hausa.

 

Wannan bincike ya nuna nau’o’in rini da ake yi wa tufafin mata Hausawa domin ado. Don haka ya taimaka wajen inganta wannan aiki, amma sun bambanta saboda wannan binciken ya kalli yadda kwalliyar matan garin Gusau, inda shi kuwa binciken ya kalli rini da nau’o’insa.

 

Kado (1986) ya yi bayani kan asalin sana’ar saƙa da nau’o’inta da matsayinta a sana’o’in Hausawa. Sannan ya yi bayanin kayayyakin da ake amfani da su wajen gudanar da ita, kamar su akwasu da buda da akillabi da gwangwala da kwalba da ƙugiya da kuma ƙoshiya, da sauransu. Haka kuma bincike ya yi bayani a kan masaƙu da yadda ake saƙa, da kuma ire-iren abubuwan da suke saƙawa. Haka kuma, binciken ya fito da ire-iren kayan mata na kwalliya da ake saƙawa misali, gansaki da bunu da sauransu.

 

Binciken ya yi ƙoƙarin gano ire-iren tufafin da ake saƙawa domin amfanin mata da maza. Binciken ya taimaka wa wannan bincike ta hanyar gano ire-iren tufafin kwalliyar mata Hausawa, amma sun sha bamban ta fuskar taken da kowanne ya gabatar da nazarinsa.

 

Dayo (2002) ya yi ƙoƙarin fito da ire-iren bambance- bambance da ya ke tsakanin tufafin Hausawa na gargajiya da kuma na Yarbawa ta fuskar bayanin nau’insu da yadda suka bambanta. Daga nan ya kawo bayani kan kamanceceniya tsakanin tufafin maza da kuma na mata. Haka kuma bincike ya yi bayanin ire-iren tufafin da ake yiwa mata zane ko ado a matsayin kwalliya.

 

Binciken ya yi ƙoƙarin kwatanta tufafin Hausawa da na Yarbawa. Don haka binciken ya tallafawa wannan aiki ta fuskar irin tufafin da Yarbawa suka kawo wa Hausawa, musamman mata. Duk da haka wannan binciken ya sha bamban da wannan aiki, musamman idan muka kalli batun ko wane bincike.

 

Sanda (2004) ya yi bayanin asalin sana’o’in Hausawa da ire-irensu, mai bincike tafi mayar da hankali a kan sana’ar kitso da bayyana asalinta, da kuma yadda ake, sannan da kuma wuraren da ake yenta. Daga nan an bayyana kayayyakin da ake amfani da su wajen yin kitso da ire-irensa da kuma bayanin kitson Hausawa na gargajiya da kuma na zamani. Har wa yau, binciken ya kawo hanyoyin tanadin gashin mata da gyara shi ya yi kyau kuma ya ƙayatar.

 

Nazarin ya bayyana yadda mata suke tsaftace gashin kansu ta hanyar yin kitso ko gyaran gashi. Don haka wannan bincike ya haskaka wa wannan binciken fitilar da aka gano ire-iren kitson mata na da kuma baƙi, amma nazarin ya bambanta da wannan aikin da aka gudanar.

 

2.2 BUGAGGUN LITTAFAI

Dangane da bugaggun littafai da wannan nazari ya yi bincike a kansu. Sun shafi littafai ne waɗanda masana sukayi bitar su da amincewa da shi wajen gudanar da bincike na ilimi. Amma duk da haka akwai karancin rubuce-rubuce na littafai a ɓangaren da ya shafi al-ada ta kwalliyar mata Hausawa. Wasu daga cikin littafan wannan binciken ya kai hannu a kansu sun haɗa da:

 

Madauki da Wasu (1968) a cikin littafin an yi bayani filla – filla a kan muhimman al-adun Hausawa na gargajiya tare da wasanni da kuma adabinsu, haka kuma an yi bayani a kan sana’o’in Hausawa na gargajiya da yadda ake aiwatar da su, littafin ya kawo bayani akan kaɗan daga cikin irin kayan ƙyalli kamar zobba da mundaye.

 

Haka kuma a ɓangaren kayan sawa ya yi bayani kan zannuwan da masaƙa suke sakawa irin su baƙin saƙi da muddakare da tsaniya da sauransu. Waɗannan su ne abubuwan da aka yi bayaninsu a cikin littafin, kuma sun shafi wani nau’in kwalliyar matan Hausawa na gargajiya.

 

Wannan littafi ya ƙoƙarta wajen bayyana al-adun Hausawa sannan an kawo ire-iren kayayyakin Hausawa na kwalliya na asali. Don haka littafin ya tallafawa wannan bincike ƙwarai da gaske, amma sun sha bamban danane da gundarin take da kuma abubuwa da kowanne ke ƙunshe da shi.

 

Adam (1978) ya yi bayani a kan asalin Hausawa da kuma ƙasashen Hausawa. Daga nan ya kawo bayani a kan cinikayya tsakanin Hausawa da wasu ƙasashe da suke maƙwabtaka da su, irin mutanen su haɗa da gwanja da sauransu. Ya kuma ƙara da abubuwan da suka shafi cinikayya da sauran abubuwan da suka shafi al’ada sai kuma ya bayyana dangantakar da take tsakanin Hausawa da wasu ƙabilu maƙwabta. A ƙarshe ya yi bayani a kan tufafin Hausawa na gargajiya da ire-iren tufafin Hausawa na gargajiya waɗanda suka haɗa da na maza da na mata. A nan ne kawai ya yi bayani kan batun da ya shafi kwalliyar mata Hausawa ta gargajiya.

 

Wannan littafi ya fito da wasu tufafin Hausawa da ire-irensu, wannan littafi ya tallafawa wannan aikin da wasu yan bayanai, amma duk da haka sun bambanta.

 

Madabo (1978) ya yi bayani mai gamsarwa kan sana’o’in kimanin goma sha huɗu. Sannan ya ɗauki masu yin ta, tare da abubuwan da ake samarwa da kuma irin amfanin kowace sana’a ya yi ƙoƙarin bayyana irin maganganun hikima da ke cikinta. Haka kuma ya yi bayani akan abubuwan da suka shafi ado da kwalliyar mata Hausawa na gargajiya. Misali, ya ɗauki ko wace sana’a ya yi bayanin kan irin abubuwan da ake samu daga sana’ar wanda na kwalliyar ake samu daga sana’ar ƙira, kamar yari da munduwa da warwaro da sauransu.

 

Daga cikin sana’ar saƙa kuma, ya kawo bayani kan farin Kano da bunu da gwanda da saƙa da bakurɗe waɗanda dukkaninsu zannuwa ne na mata. Dangane da dukanci kuwa, ya yi maganar takalma, sakadale da silifa. A sana’ar rini ma ya bayyana yadda ake rina zannuwa da rigunan mata.

 

Dangane da ciniki kuwa, ya yi bayanin kasuwar Kurmi da wurare da ake sayar da abubuwan wato layukan da ake sayar da kayayyakin sana’o’in a cikin kasuwa.

 

A sashen dillalai ana samun zannuwan mata da dutsen wuya da murjani da tsakiya da ‘yan kwalaye. A ɓangaren ‘yan koli kuma akwai ramar kitso da kwalli da koya da sauransu. A wajen ‘yan fatu, ana samun jaka da takalmi da kuma tuntun (abin zama) wanda ake amfani da shi wajen gyaran gida. ‘Yan haja kuma ana samun gyale da atamfa, a sana’ar ɗinki kuwa suna ɗinka rigunan mata, haka ma ɓangaren kitso, inda ya yi cikakken bayani a kan kitso da masu yinsa da kuma kayayyakin yin kitso. Daga nan ya kawo ire-iren kitso da kuma al’adun makitsa.

 

Wannan littafi ya yi ƙoƙari wajen kawo wasu sana’o’in Hausawa daban-daban waɗanda suke da jigo a wajen samar da kayan kwalliya na mata. Don haka wannan littafi ya tallafawa wannan aikin da aka gudanar, amma sun sha bamban ta ɓangaren taken batun da aka nazarta.

 

Mahmud (1985) ya yi ƙoƙarin yin bayanin wasu sana’o’in Hausawa kamar su Noma da Gini da Ƙira da Saƙa da Kasuwanci da kuma Malanta. A cikin wannan littafi, marubucin ya kawo ire-iren tufafin Hausawa, tare da kawo tufafin mata kamar su kallabi da fatari da bante da zani da mayafi da gyale da taguwa da kanfai da dunhu da sauransu.

 

Daga nan ya kawo tufafin maza da suka haɗa da walki da tako da wando da taguwa da jamfa da kaftani da babbar riga da sauransu. Haka nan littafin ya kawo ire-iren hulunan maza kamar ɗankwara da bakwala da sauransu, daga nan ya kawo ire-iren takalma kamar su faɗe da sambatsai da wutsiyar shirwa da sauransu.

 

A cikin wannan littafi, marubucin ya bayyana abubuwa da dama waɗanda haƙiƙa sun ƙarawa wannan bincike haske kan fannonin kwalliyar mata ta gargajiya da kuma irin sana’oin da suke samar da kayan kwalliya don mata Hausawa. Wannan littafi ya bambanta da binciken da aka gudanar domin shi binciken ya kalli kwalliyar mata ne gaba ɗaya har da kitso da ƙunshi.

 

Fagge (2007) ya yi cikakken nazari kan yadda mata suke ƙawata jikinsu musamman hannaye da ƙafafuwa ta hanyar yi masu ƙunshi wannan littafi ya bayarda ƙarfi wajen nuna hotunan ƙunshi daban-daban sannan ya fito da nau’o’in ƙunshin mata na zamani iri- iri, daga cikin ire-iren ƙunshi sun haɗa da fulawa wanda ake yi da dayis ko lalle ko muhallabiya da kuma turare.

A irin wannan ƙunshin ana amfani da abu mai tsini ta yadda za a dinga dangwala ana zana irin fulawar da ake so a kafafuwa ko hannaye ya yi ƙoƙari sosai wajen kawo bayani kan ƙunshi da nau’o’insa kimanin guda arba’in.

 

Wannan littafi ya yi ƙoƙari wajen kawo nau’o’in ƙunshin mata Hausawa suke yi yauda kullum, Littafin ya bambanta da wannan aiki domin wannan aikin ya kalli kwalliyar matan garin Gusau.

Haka ma sagagi (2013) ya yi bayani inda ya kawo bayanai kan muhimmancin ado da kwalliya a musulunci wanda ya shafi halittar sama da ta ƙasa da kuma ta ruwa da tufafi. Sannan ya yi bayani kan tabbacin halaccin ado da kwalliya ta hanyar kawo hujjoji daga cikin ƙur’ani da hadisan Manzon Allah (SAW), sai kuma ya yi bayani a kan illolin wasu daga cikin kayan ado da na kwalliya, sannan kuma ya kawo dunƙulallun matsaloli, sannan ya yi bayani kan musanya mafi alheri, sai kuma ya kammala littafin nasa.

 

Wannan littafi ya taimaka wa wannan littafi wajen samun wasu cikakkun hujjoji dangane da nuna muhimmancin kwalliya, a wajen mata a addininmu wanda hakan ya taimaka wa al-adun kwalliyar matan Hausawa, amma duk da haka sun bambanta da wannan aiki ta la’akari da al-ƙiblar da kowane ya fuskanta.

 

2.3 MUƘALU

Daga cikin maƙalu da kuma sauran takardu da aka gabatar waɗanda suka shafi wani fanni na farfajiyar wannan bincike sun haɗa da:

 

Ibrahim (1987) ya yi cikakken bayani a kan littafin arzikin ƙasar Hausa na gargajiya da yadda ya samu bunƙasa tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. A cikin wannan muƙala anyi ƙoƙarin fito da yadda tattalin arzikin ƙasar Hausa zai farfaɗo ta hanyar rungumar hanyoyin samar da kayayyaki na gargajiya kamar yadda masu sana’o’in gargajiya suke samarwa.

 

Bincike ya taimaka wa wannan aikin wajen samar da hanyoyin da za a iya farfaɗo da sana’oin gargajiya na Hausawa waɗanda suke samar da kayayyakin da ake amfani da su musamman wajen yin kwalliya cikinsu har da kayan kwalliyar sana’o’in gargajiya na Hausawa wajen farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya ya bambanta da wannan bincike, ganin shi wannan binciken ya kalli kwalliayar matan garin Gusau.

 

Usman (2006) ya yi bayani mai gamsarwa kuma cikakke kan asalin Yarbawa da suke zaune a Gusau tare da bayyana wuraren zamansu na asali da rabe-rabensu da kuma irin dangantakar da take tsakanin su da Hausawan garin Gusau. Ya ci gaba da bayyana halin zamantakewarsu da musayar al-adu waɗanda suka shafi ɓangaren al-adu kwalliya musamman na mata Hausawa.

 

Wannan takarda ta yi ƙoƙarin fito da irin cuɗanyar da aka samu tsakanin Hausawa da Yarbawa musamman a garin Gusau. Saoda haka akwai bambanci ta fuskar taken batun da aka nazarta.

 

Ibrahim (2004) wannan takarda ta ƙunshi cikakken bayani kan garin Kano wanda yana ɗaya daga cikin manyan garuruwan ƙasar Hausa, da mazauninsa na asali da kuma irin baƙin da suke cikinsa kamar Azbinawa da Tokon kawo da Larabawa da Nufawa da sauransu, sannan takardar ta cigaba da nuna samuwar wasu muhimman abubuwa a ƙasar Hausa, musamman Kano, wato maɗaba’ai da masaƙu da sauransu inda nan ne ake saƙa irin tufafin da ake kwalliya da su.

 

Wannan takarda ta yi ƙoƙarin fito da tarihin da ya shafi Kano da kuma irin mazauna garin Kano, wato ɓaƙi kamar, Yarbawa, da Azbinawa da Larabawa da Turawa da sauransu, waɗanda suke zaune a ɓangarori daban-daban. Dan haka binciken ya taimaka ainun wajen ƙaro ingancin wannan aikin, amma sun bambanta sosai.

 

2.4 JARIDU

Akwai jaridu daban-daban da aka yi magana a kan nau’o’in kwalliya waɗanda suke da alaƙa da wannan aiki kamar su:

 

Esther (2015) ta yi bayanin kitso da nau’o’in sa inda ta kawo nau’o’in Kitso da ake yi da atacimen kala- kala kamar su shiku, shade, kalaba, Ghana wibin da sauransu.

 

Wannan Jarida ta taimaka wajen gano irin kitson da mata ke yi na atacimen kala-kala, amma ya sha bamban, saboda wannan jarida kan kitson mata kawai ta kalla inda wannan aiki ya kalli kwalliyar mata gaba ɗaya.

 

Merry(2016) ta yi bayani a kan kwalliyar gyaran gashi na mata, inda tai bayani kan nau’o’in gyaran gashi da mata suke yi irin su; Sitimin, Sitirecin, diraya da sauransu. Sannan kuma ta yi bayani irin amfaninshi ga gashin mata, wannan abu ya taimaka ma wannan aiki, amma kuma suna da bambanci sosai

Huriya (2019) ta yi bayani a kan kwalliyar fuska ta mata, inda ta kawo nau’o’in kayan da ake amfani da su wajen kwalliyar fuska da amfaninsu. Wannan ya taimaka ma wannan aiki wajen samun kayan kwalliyar fuska ta mata, amma suna da bambanci sosai, saboda ita iya kwalliyar fuska ta tsaya shi kuma wannan aiki ya yi magana kan kwalliya ta mata gaba ɗaya.

 

2.5 KAMMALAWA

A cikin wannan babi na biyu an duba bitar ayyukan da suka gabata, inda aka duba gabatarwa, kundayen bincike na ɗaya har zuwa na uku, sannan kuma an duba littafai da mujallu da sauran takardu inda aka ga abin da masu bincike suka ce dangane da abubuwa masu alaƙa da kwalliyar mata.

Post a Comment

0 Comments