Ticker

6/recent/ticker-posts

Kirarin Fitattun Wasu Garuruwan Zamfara Jiya Da Yau (6)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Kirarin Fitattun Wasu Garuruwan Zamfara Jiya Da Yau (6)

Na

BILYA UMAR

Zamfara 

BABI NA BIYAR

KIRARUWAN FITATTUN GARURUWAN ZAMFARA TA YAMMA

5.1 Anka

Anka ta Ɗan baƙo mai wuyar kai yaƙi mai gida kusa ga ruwa kowaggaya ɗan baro ya hwaɗi.

Garin Anka ya samu wannan kirari falili Ɗan baƙo sarkin Anka ne a farko mai wuyar kai yaki idan a a kayi la’akari da yanayin garin za a ga ruwa sun kewaye garin a duk lokacin da malora suka so su shigo garin a duk lokacin da malora suka so su shigo garin sai su kasa  dalilin waɗannan ruwan da ke kewaye da garin wannan dalilin ne ya sa Anka take da wuyar kai yaƙi, mai gida kusa ga ruwa a baya kusan duk gidajen garin suna kusa da ruwa ne dalilin haka  garin na Anka yanada yawan gadoji domin ruwa su samu hanyar wucewa ko wagga ɗan baro ya hwaɗi su ba a sayar da ruwa ga baro basu da matsalar ruwa balle har ɗan baro ya riƙa saida ruwa a garin. Wannan ne dalilin yi wa garin Anka wanann kirari.

1. Wuya

Wuya garin Wuya ga rani daɗi. Garin Wuya manoma ne rani da damuna amma sunfi samun alheri ga noman su na rani dalili noman damina noma ne na gama gari amma noman rani nomansa na ɗai ɗai kun jama’a ne wannan ya sa mutanen yankin sunfi samun kuɗi ga rani. Wannan dalilin ne ya sa suke yi wa garin kirari da garin Wuya ga rani daɗi. Saboda sauran lokuttan mutanen garin na wahala amma idan sukayi noman rani kuma suna jin daɗi.

2. Bagega

Bagega ta Ɗan mazuru gandun dawa kowan noma dame ɗari raggo na kowammutu dawa takkashe shi. Garin Bagega ya samu wannan kirari ne dalili Ɗan mazuru shi ne uban ƙasar Bagega na farko gandun dawa dalilin yawan noman dawa da sukeyi ne yasa ake cewa gandun dawa kowan noma dami ɗari raggo na a garin Bagega. Idan mutum ya noma dawa don ya sami dame ɗari bai yi ƙoƙari ba wato shi ba zarumi bane. Saboda yawan noman dawa da sukayi shi ne dalilin da ya sa suka ta’allaƙa cewa duk wanda ya mutu dawa takkashe shi wasu kuma suka ce ba mutuwa ta har abada ba a’a mutuwa dai ta kasawa mutum ya zamanto ya kasa noma yana kallo anayi amma shi bai iyawa na yawan noman dawar ya kashe shi wannan ne dalili.

3. Bawar Daji

Bawar daji Garin mai kura mai Giwa mai damisa a bayan  ɗaki. Dalilin wannan kirari a baya a garin anyi wani bagarde kuma maharbi wanda shi ne wanda ya kafa garin Bawar daji a lokacin garin dokar daji ne babu komai in ba namun  daji ba tun babu kowa, har ya hayayyafa a wurin har wurin tun yana daji ya zama gari har garin ya zamo ya fara bunƙasa yana da ire-iren waɗannan namun daji wannan dalilin ya sa ake yi wa garin kirari da Bawar Daji garin mai kura mai  giwa mai damisa a bayan ɗaki.

5. Tungar Kudaku

Tungar kudaku ta Garba mai kukuma.

5.2 Bakura

Bakura ɓurmi gidan ɗan kwai.

Bakura garin mai kura inda kura ka kuka da rana. Dalilin wannan kirari na Bakura ɓurmi sunan Sarauta ne shi ne sunan sarkin Bakura na farko wanda ya fara sarauta garin na ɗaya. Dalilin da ya sa ake kiransa da Ɗan kwai, Ɗiya uku ya haifa duka maza na farko sunansa  Amadu bahillace da Muhamadu Tauɗe da kuma Ima waɗannan su ne ɗiya da sarkin Bakura na farko ya haifa kuma duka su uku ɗin sun yi sarauta garin. Wannan ne dalilin da ya sa ake yi wa garin kirari da burmi gidan ɗan ƙwai.

Haka kuma a baya kamin garin ya bunƙasa an yi lokacin  da garin yake da kuraye sosai lokacin da garin yana daji a wannan lokacin za’aji kura da rana kata tana kuka a lokacin garin na daji babu jama’a namun daji ba su matsa gaba ba. Wanann dalilin ne ya sa ake cewa inda kura ka kuka da rana.

1. Rini

Rini garin Ɗan kaka arhaki dame tsadar ki ‘yan ƙanannan mata . Dalili Ɗan kaka sarki ne Rini na farko arhaki dame hatsi basu da tsada musamman ga kaka idan amfanin gona ya kai. Abi mai tsada a wannan lokacin musamman garin kaka ta kama shi ne mutum ya ce zai wanki budurwa ma’ana zai armi budurwa ba kananan kuɗi zai kashe ba kamin ya armeta dalili kuwa ganin kaka ta kai a wannan lokacin dame bai da tsada amma armen budurwa na da tsada shi ne dalilin wannan kirari.

2. Damri

Damri garin ibo marayar gwabro.

3. Mafara

·         Mafara garin farar shinkafa.

·         Mafara garken haɗe.

·         Mafara galma uwar rufi ko baku son mutum baku faɗi.

Dalili idan akayi la’akari da irin shinkafar da ake nomawa a garin Mafara za’aga ta sha bamban da ta maƙwabtanata za’a ga irin yanda ta Mafara take fara tas saɓanin ta wani wuri za’a ganta da wasu kaloli ba fara tas ba. Wannan ne dalili.

Garken haɗe fulani Bahaushe. Maguzawa na wancan lokacin haɗe dalilin yawan baƙi da ake yi a garin zaka iya samun ɗan Kano ko ɗan Katsina ko Bauci dadai sauransu a garin wannan dalilin ya sa fulani ke yi wa garin kirari da mafara garken  haɗe.

1. Kagara

·         Kagara garin gara ta bagarde.

·         Kagara garin gara inda gara ka cin mutum gashi tsaye.

Dalili garin Kagara suna fama da yawan gara sosai idan aka yi la’akari da irin yanayin garar da ke garin ba ‘ana nufin tana cin mutum bane da gaske a’a tana dai cin dukiyar mutum idan ta ci dukiyar mutum ai ta ci mutum ta nan ne masu iya magana sukayi amfani da irin nasu salon magana suka yi wa garin kirari da inda gara kacin mutum gashi tsaye.

2. Matuzgi

Matuzgi garin Ɗan binta Mamman Tukur waliyin Allah.

Mamman Tukur daya ɗaga cikin almajiran Shehu ne, waɗanda su ne suka yi gwagwrmaya don Allah.

3. Jangebe

Jangebe  kanon baƙin daji lahadi ga arna fashi.

4. Gwaram

Gwaram Ɗan gari mai daɗi shahararka ɗau galmarka.

5. Morai

Morai gidan iya.

5.4 Maradun

·         Maradun gadon ƙaya kun  buwayi maza faɗa.

·         Maradun  garin na gwabrau hwaƙo mai daɗin hitsari ga wanda ya iya.

1. Gorannamaye

Gorannamaye kowa sarki inda mai lage ka sarauta mai riga na kallo.

2. Dosara ta Amadu  Namijin Gari

5.5 Bukkuyum

·         Bukkuyum garin ta gijinga masu garin kiɗa ba don kiɗa ba da kin watse.

·         Bukkuyum garin ta gajinga baku noman dawa.

·         Bukkuyum garin ta gajinga masu garin tuwo miya  abbabu.

·         Bukkuyum garin ta gijinga gabas ga zauma yamma ga masu dutsi garin ɗan jibo.

Dalilin kirari na garin Bukkuyum gijinga kamar yada tarihi ya bayyana ba’a samu haƙiƙanin cikakkiyar dalilin da ake kiran garin ta gijinga ba gabas ga zauma idan aka dubi garin zauma garin na Bukkuyum yana gabas da garin zauma kuma masu Bukkuyum na yamma ga garin na masu wannan ne dalilin da ake kiranta gabas ga zauma yamma ga masu.

Dutsi Garin Ɗan Jibo

 Ɗan Jibo wani sarki ne da aka yi a Bukkuyum amma ba shi ne sarki na farko ba Ɗan Ali shi ne sarkin Bukkuyum na farko amma kuma tarihi abunda ya nuna cewa Ɗan Jibo shi ne ya sara garin na Bukkuyum. Wannan ne cikakken tarihin wannan kirari na garin Bukkuyum.

1. Zauma

Zauma da kuje ta Ɗan ƙauyaye kowa sarkai zaum ɗan gari bisa duutse na yamma ga gulbi.

Idan aka yi la’akari da yanayin garin zauma za a ga yana saman dutsi ne ba bisa ƙasa ya ke shinhiɗe ba. Haka kuma gulbin garin yana gabas da garin yana yamma da gulbin. Ƙayaye kuwa uban ƙasar Zauma ne sunan sarauta ne ƙayaye kowa sarki garin Zauma mutanen garin na da jin ƙai ma’ana suna da jin kansu kowa jin kansa yakeyi kamar sarki waɗannan dalilin ne aka samu a wurinwannan bincike.

2. Zarummai

Zarummai Ankar yaƙi

3. Adabka

Adabka ta goje mai kamar ran sallah.

Dalilin wannan kirari Goje sarki ne na garin mai kamar ran sallah kuwa garin a duk lokacin da baƙo ya shiga garin yanayinda mutanen garin suke ciki na anna shawa da raha da walwala yanayin mutane’n garin da irin suturar da suke sanyawa za a ga kamar ranar sallah ne wannan ne dalilin da ya sa ake musu wannan kirarin.

4. Ɗan Gurunfa

Ɗan gurumfa karkare ta Maradun ba don haki ba da kinfi Kano ko yanzu ma dami kano taffiki.

5. Gwashi

Gwashi garin magaji garin da ba a ɗaukar kowa.

Dalili shi magaji sarkine. Ba a ɗaukar kowa garin a baya an taɓa zargin garin da ɓacewar wasu fatake sai akayi ta tunanin anan garin ne suka bata bisa wannan dalili ne sarkin garin ya bada bayanin cewa a garin ba’a ɗaukar kowa ta wannan dalilin ne ake yiwa garin kirari da garin da ba’a ɗaukar kowa.

5.6 Gumi

·         Gumi gumama ta Ali gandun ƙwarya dogon burni garin mai saje.

·         Gumi gumma ta Ali mai kamar ran sallah.

Ali sarkin garin Gumi ne. Gandun ƙwarya idan aka dubi irin yadda ake noman ƙwarya a garin za’a ga duk yankin ba a kaisu noman ƙwarya ba. Ba Komai ake nomawa ba kamar ta, wannan dalilin ne ya sa a ke yi wa garin kirari da gandun ƙwarya

1. Gyalenge

Gyalenge ta Marafa kowa sarki mai kamar kano ga bardokawo badon kiɗa ba da kin watse. Mutanen Bardoki a nan ne suke shaƙatawa da cin kasuwa.

2. Gayari

Gayari ba ku cin kajinku sai an yi gobara ku ci mushe.

Gayari garin gairar mai farar arake ta sarkin dutse. Suna noman rake sosai a jiya da yau.

3. Birnin Tudu

Birnin Tudu madinar Tauri.

4. Iyaka

Iyakar ƙasa ta sarkin Gulbi, gari ne dake kan iyakar Gummi da Anka a can da kafin kafa Bukkuyum.

5. Ɗaki Takwas

 Ɗaki Takwas garin ‘yan banza idan kaga ɗan ƙwarai baƙo ne. Saboda an yi lokacin da garin yake sharkiratar karuwai.

5.5 SAKAMAKON BINCIKE

Zaɓen fagen bincike ra’ayin mai bincike ne, bisa ga irin horon da ya samu da yadda ala’arsa take da fagen bincike. Haka kuma wannan binciken an gudanar da shi ne domin daɗa ƙara fito da adabin Hausawa da al’adunsu a sarari domin mai nazari ya san inda aka sa gaba. Haka kuma a wannan bincike an kawo taƙaitaccen tarihin ƙasar zamfara jiya da yau, da kuma kirarin wasu fitattun garurusw da ke ƙarƙashinta domin a ƙara fito da ƙasar Zamfara a fili domin masu sha’awar wannan fage su sami abin dubawa. Idan haka ne kuwa sakamakon wannan bincike shine bunƙasa adabi da al’adun Hausawa ta fuskar fito da kirarin wasu fitatun garuruwan Zamfara na jiya da yau da fatan wannan kundi da aka gabatar ya kasance jagora ga Ɗalibai ‘yan uwa da masu nazari dama mai sha’awa akan wannan sashe.  

5.6 KAMMALAWA

Duk abin da yake da farko yana da ɗarshe, ion banda ikon Allah, inji masu fashin baƙin magana. Allah (S.W.T) ya bada ikon kawo ƙarshen wannan  aiki mai taken “Kirarin fitattun  garuruwan Zamfara ta tsakiya da Zamfara ta arewa da kuma Zamfara ta Yamma” ina fatan  wannan aiki da Allahu ya bada iko aka gabatar tare da taimakon malamai na ina fatar ya kasance jagora ga masu so su yi nazari a kan abinda ya shafi kirarin garuruwan Zamfara baki ɗaya. Haka kuma ina fatar wanann kundi ya kasance tamkar wani ma’adani ko wani abin ciyar da harshen  Hausa da adabin Hausawa gaba tare da fatan kwalliya za ta biya kuɗin sabulu.

Kamar yadda ya gabata wannan aiki da aka gabatar wanda ya ƙunshi babi babi har guda biyar inda babi na ɗaya yake ɗauke da gabatarwa da manufar bincike, da bitar ayukkan da suka gabata da hujjar cigaba da bincike da hanyoyin gudanar da bincike.

A babi na biyu an yi magana ne dangane da wasu ra’ayoyi na masana a kan abinda ya shafi ma’anar kirari ta nuna irin yadda kowanen su ya fassara ma’anar kirari. Haka kuma a cikin wannan babi an yi magana kan asalin kirari wato inda ya fito da mafarin samunsa, sannan kuma aka yi magana a akan rabe-raben kirari inda aka kalli kirari gida biyui kirarin kai da kuma kirarin wani. A cikin babi na uku an kawo kirarin fitattun garuruwan Zamfara ta tsakiya.

A babi na huɗu ko an kawo  kirarin fitattun garuruwan Zamfara ta arewa.

Haka kuma a cikin babi na biyar inda aka kawo kirarin fitatun garuruwan Zamfara ta yamma wanda idan aka dubi irin  yadda aka yi ƙoƙarin kawo waɗannan kirare kirare za a ga cewa kowane bakin wuta da nsahi hayaƙi tare da fatan Allah ta ala ya sanya wa wannan aiki albarka ya kuma sa wannan aiki da aka gabatar ya amfanar da ‘yan uwa ɗalibbai da sauran masu nazari a kan adabi musamman dangane da abin da ya shafi kirarin garuruwan Zamfara.

Ina fatan Allah ya sa wannan aiki ya kasance mai amfani ga jama’a musamman masu nazari da sha’awar harshen Hausa ya zamanto madubi a garesu.

Haka kuma ina fatar wanna aiki ya zamanto matashiya ga cigaba da zurfafa bincike a kan adabin da ya shafi kirari domin dibin hikima da fasaha da balaga da ke ciki.

MANAZARTA

Tuntuɓi Amsoshi.

Post a Comment

0 Comments