Kirarin Fitattun Wasu Garuruwan Zamfara Jiya Da Yau (5)

    Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

    Kirarin Fitattun Wasu Garuruwan Zamfara Jiya Da Yau (5)

    Na

    BILYA UMAR

    Zamfara

    BABI NA HUƊU

    KIRARIN FITATTUNN GARURUWAN ZAMFARA TA AREWA

    4.1 Ƙaura

    Ƙauran Namdoda mai kamar yau sallah. Anayi wa garin Ƙaura wannan kirari ne dalili ƙaura na nufin hijira (migration) Na moda wani almajiri ne na Shehu Usmanu Ɗanfodiyo wanda ya yi hijira ya zo anan garin ya kafa sansaninsa wannan ne dalilin  da ya sa ake kiran garin ƙaurar namoda mai kamar yau sallah kuma idan akayi la’akari da yanda mutanen garin suke za a ga a ko da yaushe sun fito fes-fes kuma suna ta hada hada kowa na harkar gabansa za ka ga kamar ranar sallah to bisa wannan dalilan ne ake yiwa garin Ƙaura wannan kirari.

    1. Ɗan Isa

    Ɗan Isa garin isa. Garin ya samu wannan kirarrin  ne dalili garin ya samu cigaba ne na cika da ya yi da jama’a wanda ake ganin cewa duk inda gari ke ganin ya kai ko ya isa haka shi ma garin Ɗan isa ya kai a bisa wannan dalili ne ake yi wa garin kirari da garin Isa.

    2. kuryar madaro

    Kuryar madaro masu arziƙin gado. Wanann garin ya samu wannan kirrai ne bisa dalilin cewa a duk lokacin da wani ɗan garin na kuryar madaro yake wani kasuwanci sai ya samu kariyar arziƙi to mutanen garin zasu yi  ƙoƙarin su bashi wani jari don ya cigaba da sana’arsa domin arziƙin sa da ya kucce masa ya dawo masa kuma tun kaka da kakanni suke yi wa junansu haka wannan ne dalilin da ya sa ake yiwa garin wannan kirari na masu arziƙin gado.

     

    3. Kasuwar Daji.

    Kasuwar Daji ta Arɗo maicika har daji. Wannan gari  ya samu wannan kirari ne dalili Arɗo shi ne sarkin garin na farko garin yana da wata babbar Kasuwa waddad ke ci duk ranar Assabar dalilin cikar da kasuwar ke yi ne matuƙa da jama’a masu cin kasuwa Baƙi tun daga Ikko da Shagamu suna kawo goro da sauran su ranar kasuwar kusan duk ƙauyukkan da suke maƙwabtaka da garin suna cika da jama’a masu cin kasuwa idan aka yi la’akari da irin cikar da kasuwar ke yi shi ya haifar da wannan kirari da ake yiwa garin. 

    4. Dogon Kaɗe

    Dogon Kaɗe kinawa kowa amma fa ban da Ɓarawo kowat tahoki sai ya kwanta.

    Dogon kaɗe garinsu ta Allah.

    Garin ya samu wannan kirari ne dalili kuwa mutanen garin suna da haba haba da baƙo duk wanda ya zo baƙunci sukan tarbe shi dai dai gwargwado wannan ne dalilin da ya sa duk wanda ya je garin zaiji garin yayi masa.

    Ammam mutanen garin wanda basu so shi ne ɓarawo mutanen dogon kaɗe ba su son ɓarawo ko kaɗan duk wani baƙo suna bashi wurin kwana idan dai ba ɓarawo ba. Wannan ne dalilin kirarin Dogon Kaɗe.

    5. Modomawa

    Modomawa garin mamuda. Dalili Mamuda yana daga cikin sarakunan da suka yi sarautar garin Modomawa. Wannan ne dalili.

     

     

    4.2 Zurmi

    Zurmi zurum da wawa garin Ɗanjeka. Ana yi wa garin Zurmi wannan kirari ne bisa dalili a duk lokacin da baƙo zai yi hulɗa da mutumin Zurmi dole ne ya kiyaye idan bai kiyaye ba zai zurma da shi ma’ana zai durmuyar da mutum wannan ne daliin da ake yi wa garin kirari da Zurum da wawa. Garin ɗan jeka kuwa sunna da suke yiwa sarkin su kenan ɗan jeka.

    1. Moriki

    Moriki kaɗan mai albarka. Dalilin wannan kirari garin Moriki bai da faɗin ƙasa amma Allah ya albarkaci garin da noma da kuma samun amfanin gona mai yawan gaske wannan ne dalilin da ya sa ake yiwa garin wannan kirari da kaɗan mai albarka.

    2. Birane

    Birane Birnin kuka. Dalili Allah ya azurta garin Birane da yawan itacen kuka kusan garin ba su da wasu itace da suka fi yawa irin itacen kuka ta  haka ne aka yi amfani wurin yi wa garin kirari da birnin kuka.

    3. Dauran

    Dauran ta Ɗancida. Dalili Ɗancida shine mai garin Dauran na farko ma’ana shine sarki na farko a garin Dauran.

    4. Birnin tsaba

    Birnin tsaba garin su maduga. Dalili maduga ya na nufin shugaba wata shugaba ce ta mata da aka yi a baya a ƙasar Birnin tsaba wadda wannan lokaci ita ce jagorar mata ta wannan lokacin dalilin wannan ne ya sa ake yi wa garin kirari da Birnin tsaba garin su maduga. An yi amfani da sunan nata wurin aiwatar da kirarin.

    5. Kwashabawa

    Kwashabawa garin su A’i ‘yar da tsanya.

    4.3 Shinkafi

    Shinkafi ta magaji kin  fi murnar baƙo.

    Shinkafi kwata magama ta magaji mai cika har tabki.

    Shinkafi ta magaji garin shinkafa.

    Dalilin yi wa garin shinkafi wannan kirari magaji sarki ne kinfi murnar baƙo dalilin shigowar da baƙi ke yi cin kasuwa ya jawo wa garin cigaba soasai ta  fuskar kasuwancin su garin Shinkafa kuma ana noman shinkafa sosai a ƙasar wannan ne yasa ake yiwa garin kirari da garin shinkafa.

    1. Kurya Dambo

    Kurya Dambo ta makaru. Makaru wani sarki ne da akayi a garin kurya Dambo wanda ankayi amfani wajen yiwa garin kirari da sunan sa.

    2. Galadi

    Galadi cibiyar fadawa kuci kuba wasu su ci.

    3. Shanawa

    Shanwa ta mai dabo.

    4. Ajiya

    Ajiya-Ajiyar Allah gani nan bari nan don dole.

    5. Zangeru

    Zangeru garin Ɗan Mammana.

    4.4 Birnin Magaji

    Birnin magaji gani nan bari nan dukiyar alawa.

    Dalili alawa fulani ne bawa jan gwarzo ya yi musu wannan kirari lokacin da ya je wurin yi musu rabon gado.

    1. Nasarawar Godal

    Godal mai kura

    2. Shamushalle

    Shama babban tabki.

    3. Yalle

    Yalle koran yunwa in kun ƙoshi mai gari kuka ɓaci.

    4. Jabande

    Jabande garin jarummai ɗan gari na yamma da dulbi. An yi wa garin wanann kirari ne dalili gari ne da keda ‘yan tauri sosai. Wannan ne dalilin da yasa ake ma garin kirari da garin jarummai.

    4.5 NAƊEWA

    Babban abin buri ga kowane ɗalibi mai nazari shi ne ya samu nasarar bincikensa. Haka kuma ya samu karɓuwa ga ɗalibbai ‘yan uwansa matsayin wani asusun ilimi da za’a yi nazari a kai ga biyan buƙatu. Ina fatan Allah ta’ala ya sanyawa wannan bincike da aka gabatar albarka.        

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.