Ticker

6/recent/ticker-posts

Kirarin Fitattun Wasu Garuruwan Zamfara Jiya Da Yau (4)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Kirarin Fitattun Wasu Garuruwan Zamfara Jiya Da Yau (4)

Na

BILYA UMA 

Zamfara

BABI NA UKU

KIRARIN FITATUN GARURUWAN ZAMFARA JIYA DA YAU

TAƘAITACCEN TARIHIN ƘASAR ZAMFARA

3.0 SHINFIƊA

Ainihin tarihin ƙasar Zamfara wanda aka sani tun daga kaka da  kakanni ba a rubuce yake ba, tarihi ya nuna bayan lokaci mai tsawo kafin samuwar rubutu Darman Dutsi da Sarkin Zamfaran Anka sunce: Asalinsu daga Gabas suke kamar sauran al’ummar ƙasar nan da suka biyo ta ƙasar Barno da Kano. Ga yanzu kamar a wancan lokacin da wurin ke da maguzawa ne mahalban Zamfarawa kuma taubasan juna ne tsakanin su da kanawa wato abukkan wasan juna suke. Wannan alaƙa ta su ta ƙullu ne saboda wasu dalilai da zamu gani can gaba. ‘Yan asalin wannan ƙasa ta Zamfara da suka fara zama a wannan yanki sun kai misalin su saba’in a tsakanin mazansu da matansu tare da iyayensu sun fito ne daga ƙasar Gabas. Sun kuma fara zama ne a wani yankin ƙasar Zamfara suka sama garin suna “Dutse” a nan cikin yankin “Zurmi” ta jihar Zamfara a yanzu. Sunyi shekaru har bakwai ba su da sarki ko shugaba wanda zai yi jagorancinsu a garin “Dutse” a samu mai bada umurnin yin wani abu ko a bari.

Bayan shekarun aka fara naɗa sarki a garin Dutse matsayin shugaba mai ba da umurni na farko, sai aka sama sarautar suna “Dakka” a matsayin mai shugabancin garin a farko. Bayan shi an samu masu mulkin garin har guda huɗu wani bayan  wani. Sun kuma bada suna shugabanci kafin wata “mace” tayi nata lokaci don ta yi mulki ne a bayansu da daɗewa don ta zarar ƙwarai ana kiran ta ’yar goje- Algoja. Ga sunayen mutanen da suka yi shugabancin farko – farko a garin “Dutse” kamar haka:

1.      Jatau

2.      Jimir Dakka

3.      Kakaikotai,

4.      Dudufani,

Dukkansu an ce samudawa ne masu ƙarfi ƙwarai da gaske su na nuna ƙwazonsu da jaruntakarsu zuwa ga al’ummarsu.   

Garuruwan da suka kafa a  farkon ƙasar Zamfara su ne:

1.      Zurmi

2.      Kanoma

3.      Bunguɗu

4.      Maradun

5.      Hargum

6.      Kasara

7.      Birnin Gada

8.      Roni

9.      Dhuwar

10.  Mafara

11.  Kyawa

12.  Sabon Gari

13.  Cika ziki Mawadaci

14.  Renuwa

15.  Damari

16.  Gummi

17.  Bini

18.  Bingi

19.  Jata

Akwai yankin da yake tsohon wuri ne sai dai ba a ambace shi ba don duk ya tsofi ma sauran garuruwan da aka zana sunayensu shine wurin zamansu na farko daga baya ya koma yankin ƙasar Katsina.

Ƙasar Zamfara ta yi iyaka da wasu garuruwan da Al’majiran mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo suke kamarsu: Burmi a garin Bakura ta yi iyaka da wasu kamar: Matazgi a inda Mallam Muhammadu Tukur yake da Mafara, a inda Mallam  Dambo a Birnin Gada cikin yankin Bunguɗu. Mutanen da ƙasar ta Zamfara yawancin su musulmai ne masu bin addini da kaɗaita Allah ba tarayya da wani ba, daga cikin su akwai masu bin addinin “Tsafi” na gargajiya wanda suka gada tun   daga kaka da kakanni tun kafin yawaitar musulunci a Nahiyar mu ta “Afrika ƙasar baƙaƙen fata” wato gabanin jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo kenan.

Ƙasar Zamfara tana da mallammai ƙwarai na addinin musulunci suna kuma yawatawa don bada ilmin a ƙasa-ƙasa da yankin garuruwa, kamar su “Mallam Bawa” wanda ya yi wata waƙa a matsayin shi na mallamin addinin gabanin jihadin Shehu Usmnan Ɗanfodiyo.

Saboda yanayin ƙasar Zamfara ta samu kanta a lokacin jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo don kasan cewarsu akwai masu bin “Tsafin” gargajiya na gado wato kaka da kakannin su ne maguzawa.

A kan haka sai da aka yaƙi wani ɓangaren ƙasar Zamfara saboda suna da garuruwa  daban-daban da suka watsu suna gudanar da rayuwarsu kamar yadda suke so.

3.1 Gusau

1. Gusau ta Sambo ƙanwar Daji daga gareki sai ai Ɗamara.

An yi wa Gusau wannan kirari saboda a lokacin da aka kafa ta tana a cikin surƙuƙin daji ne kafin ta bunƙasa har ma ta cika ta tumbatsa. Wasu kuma suna ganin Sakkwatawa da sauran waɗansu mutane idan sun zo za su tafi wajen Katsina ko kano ko Borno ko Bauchi ko Zariya da sauransu a Gusau ne ake yada zango a shirya wa tafiyar sosai, daga nan ne kuma ake haɗa su da ‘yan rakkiya don namun daji da ‘yan fashi. To, saboda haka ne wasu suke yi wa Gusau kirari da ƙanwarda tun da tana maƙwabtaka da daji.

2. Gusau ta Sambo dandin Hausa kowaz zo Gusau abinai shi gusa.

Gusau ta samu wannan kirari a zamanin sarkin Katsinan Gusau malam Muhammad Mai Akwai (1929-1943) lokacin da sarakunan Gusau suka yi mulki tun daga malam Albdulƙadir har zuwa sarkin Katsina Umaru Malam ba su bar mutane su sake da aikata bidi’a da masha’a ba. An nuna a lokacin Umaru Malam ko kuwa mai Karfi mutum bazai yiba balle kiɗa, Umaru Malam duk ya hana don koyi da mutanen da suka wuce. Amma a lokacin Muhammadu mai akwai sai ya bar masu shagulgula da masha’a da kiɗe-kiɗe suka yi ta annashuwa a Gusau, wannan ya ƙara jawo malalowar baƙi a Gusau. Haka kuma aka yi muwafaƙa da lokacin zuwan jirgin ƙasa Gusau da ƙauran Namoda don haka, sai Gusau ta cika da ayyukan jin daɗi da sauran harkokin walwala. To ta nan ne ta samu wannan kirarai.

3. Gusau ta Sambo ƙali mali ta sambo ko kara kuɗɗina.

A taƙaice ana nufin wannan kirari Gusau ta ƙunshi abubuwa da yawa, ilimi da kuɗi da sana’o’i iri-iri, mutum ko kara yake sayarwa zai sami kuɗin da zai ci abinci harma ya yi arziƙi. Wannan kirari ya nuna irin shaharar da Gusau ta yi wajen kasuwanci da tashi tsaye haiƙan da yin sana’o;i kuma ga kasancewar Gusawa mutane ne waɗanda ba su raina kaɗan.

4. Gusau ta Sambo kwarya mai kashe Akushi, Takarda mai kashe Turnmin lailai.

Shi kuma wannan kirari ya ƙunshi yabo da zuga mutanen Gusau. Mutane ne masu yaji da juriya da dauriya waɗanda ba a iya cinye su da yaƙi. Akwai misalin wani yaƙi da aka taɓa kawowa Gusau wanda Sarkin Katsinan Maraɗi Ɗan Baskore ya zo da shi. A wannan yaƙi Gusau ta nuna haƙiƙanin  jarumtaka duk da rashin yawansu in da suka kama wajen mutum 300 a matsayin bayi suka kashe na kashewa, wasu ko suka gudu.

Tarihi haka ne ƙwarya ta kashe akushi, kuma takarda ta kashe turmin lailai komai kazo da shi Gusau ta tserema.

Wasu daga cikin kirare-kiraren Gusau kuma sun haɗa da :

·         Gusau ta malam Sambo, in da naka Gusau (guso) in babu naka Gusau (gus) in ko da sharri ka zo to gurgusa ka gushe in ka ƙi jin bar, hoho zaka ji ka gushe.

·         Gusau gusa an  nahwa, ta sambo dangalin mutanen Hausa.

·         Gusau ta Sambo gurugusa kayi naka, ka gurgusa kaba wani naka.

·         Gusau ta Sambo ɗangari mai sha’awa kwazzo shi yau da niyyar shi wuce sai ya nemi ɗan wuri ya zauna.

·         Gusau ta Sambo ba’a kai maki yaƙi, ta Sambo garkuwar mutanen Sambo.

·         Gusau ta Sambo noma yaƙi inda babu mishkili ba  huntu.

·         Gusau ta Sambo tsangayar malammai, gidan Malam Gwani da Malam Buda.

·         Gusau ta Sambo ɗinɗimar alƙarya, mai kasuwa da filin idi, ta Sambo kanon mutanen yamma.

·         Gusau ta Malam Sambo garin sarakunan musulunci inda ɗan talakka ke zaman shi shi wala da sauaransu.

1. Wanke – Wanke tsiya garin mai ƙurau

2. Wonaka – Ta kogo ceɗiya baki ƙaya

Dalilin  da ya sa ake yiw wonaka wannan wannan kirari shi kogo uban ƙasarsu ne suna kiran uban ƙasar su da kogo ne.

Ceɗiyar kuwa garin mafi yawan itatuwansu ceɗiya ce suna da yawan itace na ceɗiya kuma ita ceɗiya ansan batada ƙaya ceɗiya icce ne wanda baya da ƙaya wannan  shine dalilin wannan kirari na Wonaka.

3. Mada- Ba ruwa sai manya ko manya sai an yasa.

4. Rijiya – Garin sha’aya ɗan gari da Sarki uku

5. Magami- garin mai tarko

3.2 Tsafe 

Tsafe garin ‘yan doto garewa kashin shanu yaro taka sannu.

Garin Tsafe ya samu wannan kirarine dalili kuwa  Doton Sunan wani Dutse ne da ke cikin garin Tsafe wanda a baya duk wanda za a naɗa  sarkin garin Tsafe a wurin wannan Dutsen ake zuwa a naɗa mutum sarki duk sarkin da za a naɗa wannan lokaci dole ne sai an je wurin wannan dutsen mai suna Doto sannan za a naɗa shi sarki wannan ne dalilin da ya sa  ake cewa Tsafe garin ‘yan Doto.

Garewa kuwa da ake kiran su shi kuma yanki ne da ya haɗa da tun daga Bakori ya zagayo har zuwa ƙanƙara ya tafi har zuwa Wasagu dukkansu waɗannan yankuna ana kiransu garewa ne.

Kashin shanu kuwa abu ne da yake da santsi ma’ana sulɓi wanda idan mutum  ya ci karo dashi to dole ne yabi sannu dalili kuwa idan mutum bai bi sannu ba zai ɓatashi ko ya kada shi.

Yaro taka sannu mutanen garin Tsafe mutane ne masu zafin gaske ma’ana masu saurin fushi idan baƙo ya shigo garin to dole ne ya bisu sannu wannan shi ne dalilin da ake cewa garin na Tsafe yaro taka sannu.

1. Bilbis : Garin gaskiya garin da kura ta ka ma akuya ta maida ɗan gaskiyar mutanne Bilbis.

Ana yiwa garin Bilbis wannan  kirari ne dalilin mutanen garin mutane ne masu gaskiya da riƙon amana duk yanda ka bawa mutumen Bilbis amanar wani abu to tabbas zaka samu abunda ka bashi ajiya yanda ka bashi shi. Wannan shi ya  sa kurama da ta kama akuyar mutanne Bilbis ta kasa cinye akuyar ta maida don gaskiyar mutanen garin Bilbis.

2. Keta- Keta ƙasar Allah, mutanen garin Keta mutane ne masu tawakkali da Allah masu maida al’amarinsu ga Allah wannan dalilin ne ya sa ake cewa garin ƙasar Allah.

3. ‘Yan ware- Kwata garin ɗan dutse kwaɗo da baya cizon kowa.

Mutanen garin ‘yan ware mutane ne da ba su cin amanar kowa ba su zaluntar kowa wannan ne dalilin da ya sa aka yi wa garin ‘yan ware wannan kirari.

4. ‘Yan kuzo -  Ta Malami mai da Ɗan wani naki

5. ‘Yan Doto: ‘Yan Doto bata ratsuwa a yi suna.

 

3.3 Maru

Maru garin dogo jar ƙasa garin Banaga jicce garin maƙetata shigo da Raƙumi fito da akala.

Ana yi wa garin Maru wannan kirari ne dalilin shi ne idan aka yi la’akari da irin ƙasar garin Maru za a ga ja ce ba irin ta garin Gusau ba misali. Garin Banaga shi kuwa wannan sunan da ake yi wa Sarkin  garin ke nan sunan sarautar garin kenan su basu amfani da sarki sai dai banaga.

Garin maƙetata da ake cewa mutanen garin Maru ba ana nufin suna da ƙetatr mutane ba a a, a zamanin da ya gabata idan mahara suka kawo ma garin Maru hari akwai wasu itace da suke dasu na kuka guda uku da zarar mahara sun shigo garin na Maru sai mutanen garin na Maru su dunguma sai su yi wurin waɗannan itace na kuka da suke da su lokacin da su maharan suka cimma su wurin waɗannan itace na kuka da zarar suka nufaci itace za su yi kamar wata runduna ta tunkarosu wadda tafi ta su to daga wannan lokacin sai su maharan su gudu. An ce waɗannan maharan ne ake nufi a lokacin da za su shiga garin za su shiga ne tare gaɓa ɗai amma a lokacin da suka tinkari waɗannan itace na kuka suka ji kamar runduna ta tunkarosu mai makon su fita tare yada suka shigo to sai su watse su fita ɗai ɗai wannan shi ne dalilin da aka bayar dangane da shigo da Raƙumi fito da akala.

1. Bingi

·         Bingi ɗan gari mai dawa

·         Bingi ba’a cinki da gaye

Ana yi w a garin Bingi wannan kirari ne dalili kuwa suna yawan noma dawa ƙasarsu ta noma tana da kyau musamman idan aka noma dawa. Haka kuma Bingi ba a cin ki da gaye shi kuwa ya shirya ma’ana ya sa kaya masu kyau idan yaje cin kasuwa a garin Bingi to kafin a gama cin kasuwar waɗannan kaya sun ɓaci dole sai mutum ya canja su.

2. Ɗan Gulbi

Ɗan gulbi garin su na rikwado

3. Ɗan Kurmi

Ɗan kurmi garin ɗan Ba’u garin da ba’a haihuwar ɗa raggo.

4. Kanoma

Kanoma ɗan gari bisa dutse

Kanoma ana yi wa garin wannan kirari ne dalilin da idan aka dibi garin Kanoma gari ne da ke saman dutse wanda duk aka ambaci garin Kanoma sai an ambaci dutse ana kiransa Kanoma gari bisa dutse.

5. Mayanci – Garin ɗan Ali kowa sarki Ɗan Ali shi ne sarki na farko a garin Mayanci. Kowa sarki kuwa mutanne garin suna da jin kai ne kamar ‘yan sarauta.

3.4 Bunguɗu

Bunguɗu galma uwar rufi ko baku son mutum ba shi sani. Ana yi wa garin Bunguɗu wannan kirari saboda mutanen garin Bunguɗu fulani ne su kuwa fulani mutane ne masu kunya da kawaici ba kasafai mutum zai iya fahimtar inda fulani suka dosa ba don mutum ba zai iya fahimtar suna son sa ba ko basu son sa ba saboda ɗabi’ar da su ke da ita ta kunya da kawaici wannan ne dalilin da ya sa ake yi wa garin Bunguɗu wanann kirari.

1. Rawayya

Rawayya ta rashi mai ruwa ban ɗaki ta rashi garin ƙa’ida.

Ana yiwa garin Rawayya wannan kirari ne dalili kuwa a baya garin yana fama da ruwa musamman idan damina ta kama garin zai zamanto ko ina yana yoyon ruwa kamar fadama  duk inda mutum zai sa ƙafarsa ruwa ne wannan ne dalilin da ya sa ake yiwa garin Rawayya wannan kirari.

2. Nahuce

Nahuce garin ɗan gesha,.

Nahuce ta samu wannan kirari dalili kuwa shi ne idan  aka yi la’akari da yadda wasu sauran garuruwa ke danganta kirarin garin su ga wani jigo da suke da shi haka su ma Nahuce sun danganta nasu kirarin garin da sunan wani jigo da suke da shi mai suna ɗan gesha wannan ne dalilin da ake yi ma Nahuce wannan kirarin.

3. Kwatar Kwashi

Kwatarkwashi sutse da ganuwa ga maiki ga hazbiya.

Ana yi wa garin Kwatar kwashi wannan kirari ne musamman idan aka dubi sigar garin za a ga kusan duk dutse ya mamaye garin. Haka kuma a saman wannan dutse ne ake samun maiki  wanda kusan a nan babu wani wuri inda ake samun maiki idan ba saman wannan dutse na Kwatar kwashi ba wanda a baya lokacin da maguzawan Kwatar kwashi na cikin tsabar maguzancinsu idan ana son a gane saurayin da ya isa aure za a sa shi ya hau wannan dutse domin ya ɗau ɗan ɗan maiki idan har ya hau a saman wannan dutse ya ɗauko ɗan maiki kuma ya sauko da shi to tabbas ya isa aure idan kuma ya kasa to lallai bai isa aure ba. Ita kuwa hasbiya ita ma ana samunta ne a saman wannan dutse na Kwatar kwashi wannan ne dalilin yi wa garin Kwatar kwashi wannan kirari.

4. Furfuri

Furfuri garin ɗan jeka kuma wasu kan kira shi da suna Furfuri garin mayu.

Dalilin da ya sa ake kiran garin Furufuri da garin Ɗan jeka shi ne sunan uban ƙasar jeka sai aka yi amfani da wannan dama aka riƙa yi wa garin kirari da sunan uban ƙasar nasu.

Wasu kuwa na kiran garin mayu ba ni da tabbas na garin akwai mayu ko babu.

Dalili kuwa ban taɓa ganin maye ba a garin na Furfuri amman an ce wai suna da yawan mayu ne shi ne dalilin da ya sa ake yi wa garin kirari da Furufri garin Mayu. Allah masani.

 

5. Karakkai

Karakkai kara maƙarar cuta

Ana yi wa karakkai wannan kirari ne kamar yadda aka samu labari wajen wannan bincike mutanen garin Karakkai mutane ne masu yawan noma kamar Gero da Dawa da Masara to waɗannan duk hatsi ne kuma suna yin kara. Amfanin gona ne da ke da kara to waɗannan karan tunda ta nan ne ake samun hatsi su kuwa hatsi suna maganin cuta ko wace irin cuta ce itace cutar yunwa to sai akayi amfani da wannan damar ake yi wa garin na Karakkai wannan kirari na kara makarar cuta.


Post a Comment

0 Comments