Ticker

6/recent/ticker-posts

Kirarin Fitattun Wasu Garuruwan Zamfara Jiya Da Yau (1)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Kirarin Fitattun Wasu Garuruwan Zamfara Jiya Da Yau (1)

Na

BILYA UMAR

Zamfara

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki ga mahaifiyata Hajiya Fadimatu Yahaya Dogara da mahaifina Malan Umar Shehu Dan Ajuwa.

GODIYA

Dukkan Yabo da Godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikkai Masanin abin da ke ɓoye da bayyane mai sanar da bayinsa abin da basu sani ba. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W)

            Bayan haka ina mika godiyata ga Dakta Abdullahi .S. Gulbi Wanda ya ɗauki ɗawainiyar duba wannan aiki tare da bani shawarwari waɗanda suka taimaka mani don ganin wannan aiki ya samu kammala, Allah ya saka masa da alheri. Haka kuma ina miƙa godiyata ga dukkan malaman sashen Hausa na jami’ar Tarayya ta Gusau Ubangiji Allah ya saka masu da mafificin  alherin sa Amin.

Haka kuma ina miƙa godiya ta musamman ga babana malamina kuma shugaban sashe wato Prof. Aliyu Muhammad Bunza wand ya bamu gudunmuwa tun daga kan tarbiya ilmantarwa da fatan Allah ya saka masa da Alheri Amin.

Harwa yau ba zan manta da irin shawarwari da gudunmuwar da Dr. Yakubu Gobir da Dr. Musa Fadama da Mal. Salisu Sadi da Malam S. Fada da malam Musa Abdullahi da Malam Aliyu Ɗan gulbi suka bani ba, ina fatan Allah ya saka masu da Alherinsa Amin.

            Bayan haka ina matukar nuna farin cikina da Allah ya nufe ni da kawowa wannan mastayin da nake a halin yanzu. Har wa yau zan yi amfani da Wannan dama domin isar da godiyata ga iyayena  da yayana da Matata da Ƙanne na akan irin ga garumar gudummuwar da suka ba ni har cinmma rubuta wannan kundi nawa na digirin Farko

Bayan haka ba zan manta da gudummuwar da ‘yan uwana da masoyana da abokana arziƙi suka bani ba a lokacin gudanar da wannan bincike. Kamar Yusuf Bala Dogara da Surajo Musa Yaro da Shamsu Umar da Imrana Umar da Muhammad Umar da Abdulwahid Umar da Isma’il Aminu da Halilu Ibrahim Dogara da Hamza Ibrahim Dogara da Abdulwahab Abdurrahman da Abdurrahman Abdurrahman da sauranasu.

Daga ƙarshe ina miƙa godiya ga duk wanda ya bada gudummuwa don ganin wannan aiki ya kammala Allah ya saka ma kowa da alheri Amin.

Post a Comment

0 Comments