Ticker

6/recent/ticker-posts

Zamfarci Da Rabe-Rabensa (6)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Zamfarci Da Rabe-Rabensa (6)

NA

AHMAD MUHAMMAD KABIR

Zamfara

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0 SHIMFIƊA

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai kowa mai komai ubangijin duKkan halittu, wanda yakasance tun kafin kasancewa ta kasance.

 

Salati da ɗaukaka su ƙara tabbata a kan shugabanmu Annabi Muhammad (SAW), da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

 

A cikin wannan babi na ƙarshe, wato babi na biyar za a gabatar da jawabin taƙaitawa sannan kuma ya zo muna da shawarwari zuwa ga ‘yan’uwa ɗalibai da masu nazarin irin wannan aiki nan gaba. Haka zalika za a yi ta’arifin wasu kalmomi da aka yi amfani da su a cikin wannan aiki daga ƙarshe sai naɗewa.

 

5.1 TAƘAITAWA  

Kamar dai yadda mai karatu ya gani a shimfiɗa cewa akwai abubuwa da dama da aka ambata a cikin wannan bincike, hakan baya nuna cewa an ambaci dukan abin da ya shafi karin harshen Zamfarci da kuma rabe-raben karin harshen Zamfarci ba, a a an dai ambaci wasu ‘yan abubuwa muhimmai waɗanda ake ganin ya kamata a ambace su.

 

Da farko a cikin babi na ɗaya an gabatarwa mai karatu ko mai nazari dalilan da suka sanya a gudanar da wannan aiki, haɗi da muhallin da aka yi wannan binciken tare da hanyoyin da aka bi domin gudanar da binciken. Bugu da ƙari an yi bayanin muhimmancin bincike da kuma matsalolin da aka fuskanta ya yin gudanar da wannan aiki.

 

A babi na biyu an yi bayanin ayukkan da aka duba waɗanda suka yi alaƙa da wannan bincike, an yi bitar wasu daga cikin rubutattun littafai, muƙalu da kuma kundayen bincike, haɗi da gudummuwar aiki ga ilimi. Daɗin daɗawa an yi bayanin yadda tsarin gabatar da aikin ya kasance. Daga ƙarshe sai naɗewa.

 

Harwayau a cikin babi na uku binciken ya kawo ma’anar harshe, da kuma kare-karen harshen Hausa, wani abin burgewa an yi bayanin karin harshen gabas da kuma karin harshen yamma sai kuma naɗewa.

 

Ba a nan kawai aka tsaya ba a cikin babi na huɗu an kawo tarihin Zamfara, inda a ciki har da taswirar ƙasar Zamfara aka gabatar, sannan kuma karin harshen Zamfarci ya biyo baya da kuma rabe-rabensa, sannan aka yi bayanin Daidaitacciyar Hausa. Haka zalika aka gabatar da kalmomin Zamfarci da kuma na Daidaitacciyar Hausa daga ƙarshe aka naɗe.

 

5.2 SHAWARWARI

Kasancewar duk wani aiki da mutum ya gabatar ko ya gudanar akwai buƙatar shawara daga gare shi domin cin gajiyar wannan shawarwarin ga al’umma. Saboda haka, ina ba duk wanda zai yi nazari a wannan fanni shawara cewa, in dai ya ci karo da wannan kundin kuma in har binciken nasa yana da alaƙa da wannan, da su yi ƙoƙarin ɗorawa daga inda wannan bincike ya tsaya, kar su ce su kwashe kaɗai, wannan baya taimakawa nazari. Kamar yadda aka zaƙulo wannan taken na “Zamfarci da rabe-rabensa aka yi ƙoƙari har aka tattaro bayanan da suka gina wannan kundin, ya zama abin karatu ko nazari ga ‘yan uwa ɗalibai, to lallai su ma ya zama wajibi su dage don su samar da wani abu mai amfani, ga al’umma ba wai su kwashe abin da suka wani ya yi ba.

 

5.3 TA’ARIFIN WASU KALMOMI  

1.      Alaye – Iyalan gidan Annabi

2.      Bagire – Wuri

3.      Bincike – Nazari

4.      Bisnewa – Rufewa

5.      Fantamawa – Warwatsuwa

6.      Galaba – Nasara

7.      Gudana – Faruwa

8.      Haɓaka – Ci-gaba

9.      Habɓasa /Wuɓɓasa – Ƙoƙari

10.  Husuma – Rigima

11.  Tagguwa – Riga

12.  Kire – Kira

13.  Huriyarsu – ‘Yanci

14.  Karakaina – Kaiwa-da – Kamowa

15.  Sargafewa – Ratayewa

16.  Suɓulewa – Kuɓucewa

17.  Surmuƙewa – Yamutsawa

18.  Warwatsuwa – Rarrabuwa

19.  Zaƙulowa – Samowa / Fitowa

20.  Waɗan – Mutane

21.  Canka – Zaɓi

22.  Mussai – Musshe/ Marar rai

23.  Surutu – Magana/ Batu

 

5.4 NAƊEWA

Wannan babi na biyar kuma babi na ƙarshe ya fara da gabatarwa da shimfiɗa, bayan nan ya yi bayanin kundin gaba ɗaya, amma a taƙaice sannan ya kawo shawarwari kuma ya yi ta’arifin wasu kalmomin da aka yi amfani da su a cikin kundin baki ɗaya, daga ƙarshe ya zo da naɗewa.

MANAZARTA

Tuntuɓi masu gudanarwa.

Post a Comment

0 Comments