Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau
Kirarin Fitattun Wasu Garuruwan Zamfara Jiya Da Yau (2)
Na
BILYA UMAR
BABI NA ƊAYA
GABATARWA
Taken wannan aiki shi ne “Kirarin fitattun wasu garuruwan Zamfara jiya da
yau” kamar yadda aka sani kowa ya zo a zangon ƙarshe na kammala karatun sa na
digirin farko a kowace jami’a a kwai wata gudummuwar da ake bayarwa a sashen da mutum yake karatu.
Ma’ana yakan rubuta wani kundi a matsayin cikon wani bagire na karatunsa.
Bisa wannan dalilin ne aka ƙudurci aiwatar da wannan nazari domin bayar da gudunmuwa
ga sashen da ake karatu, wato sashen koyar da Harsunan Najeriya ko ma na Afrika na Jami’ar Tarayya ta garin
Gusau da ke jihar Zamfara. Wannan bincike za’a yi shi ne a kan kirarin fitattun
garuruwan Zamfara jiya da yau jin hakan zai fito muna da yadda suke da dalilin
samar da su.
1.1 MANUFAR BINCIKE
Manufar wannan bincike shi ne domin zaƙulo irin gudummuwar da kirari ke
bayarwa wajen bunƙasa Harshen Hausa da raya adabin
Hausawa. Sakamakon haka zai iya kasancewa wata hanya ta bayar da wata gudummuwa
wajen bunƙasa Harshen Hausa da adabin Hausawa da al’adunsu ta gano muhimman abubuwan
da ke tattare da wannan kirare-kiraren garuruawan Zamfara.
1.2 BITAR AYUKKAN DA SUKA GABATA
Bincike ya nuna cewa an gudanar da ayyuka da dama da suka shafi fannonin
adabin baka daban-daban musamman abin da
ya shafi kirari a cikin waƙoƙi ko sana’o’in Hausawa. Daga cikin ayyukkan da suke da alaƙa da wannan bincike
akwai:
Ingawa A. Da wasu, (1948) a cikin littafinsa mai suna Zaman mutum da
sana’arsa, sun kawo kirarin abubuwa kamar mutane da dabbobi da garuruwa da ƙwari da abubuwa masu rai
da marasa rai da yadda ake yi masu kirari da kuma sana’o’i kamar saƙa da dai sauransu.
Dangantakar wannan littafi nasu da wannan bincike ita ce ta fuskar amfani
da kirari musamman harma da na garuruwa. Saidai sun bambanta, domin a nan, za’a
faɗaɗa ta hanyar nazarin kirarin fitattun garuruwan Zamfara
musamman na jiya da na yau.
Ames, D. W. Da wasu (1971) a cikin littafinsa mai suna A Drum langauge
of hausa youth, sun taɓo wani abu daga kirari da yadda ake yinsa. Dangantakar wannan littafi da
wannan kundi da za a gabatar shi ne ta fuskar kirari, sai dai a nan an kawo
kirarin fitattun garuruwan Zamfara ne musammana na jiya da kuma na yau.
Umar, M. B (1978) a wata maƙala da ya gabatar mai suna “Kirari da ma’anarsa”, ya kawo
ma’anar kirari da masu yin kirari da ire-iren kirari da yadda ya kasu zuwa
gida-gida da yadda ya ke fitowa a take ko kuma a cikin karin magana. Wannan maƙala na da alaƙa da wannan bincike da
za a gabatar domin duk sun taɓo kirarin sai dai kuma bai kawo abin da ya shafi kirarin garuruwa ba.
Ɗangambo A. (1979) a tasa
maƙalar mai suna “The use of kirari and take in Hausa oral praise song”
Nagerian magazine No. 129. A wannan maƙala ya nuna cewa, kirari da take abu guda ne, sannan ya
kawo abubuwan da ake yiwa kirari kamar garuruwa da sauransu, wannan maƙala tasa na da alaƙa ta ƙud da ƙud da wannan kudi da za
a gabatar duk da wannan alaƙa da suke da ita da wannan kundi ta ƙud da ƙud, sun bambannta , domin a nan za a
yi kirarin garuruwan jihar Zamfar ne na jiya da yau.
Magaji, A. (1980-29) a kundinsa na neman digiri na ɗaya mai taken “ Kirarin dabbobi ya kawo ma’anar kirari,
da nau’o’in kirari, sannan ya kawo bambancin da ke tsakanin take da kirari da
kuma bambancin zambo da kirari da yadda kirari yake fitowa a cikin waƙa.
Alaƙar wannan bincike da kundin sa shi ne ta wajen kirarai. Bambancin su kuwa
shi ne wannan bincike ya ƙunshi kirarin garuruwa ne musamman na Zamfara wanda shi
bai kawo haka ba.
Abubakar A. (1980) (39-41) a kundinsa na samun digiri na ɗaya mai suna “Kirarin maza da mata” ya bayyana kalmomin
da ake amfani da su wajen yin kirari
kamar kwarjini ko ƙarfi, ko girma, ko ƙanƙanta, ko ban tsoro, ko abin ƙi, ko ƙasaita, ko shahara, ko kuma alfarma. Wannan bincike na da
alaƙa da kundin nasa ta amfani da kirari, kamar yadda za a duba kirari a nan.
Abubakar A. (1980) a nasa kundin na digiri na ɗaya mai taken “Dangantakar take da kirari” ya kawo jerin
kalmomin da ake amfani da su wajen yin kirari da take da kuma kalmomi waɗanda ake yin amfani dasu domin koɗa ko kushe wani ko dabbobi ko wata sana’a. Ya kawo
kamanci da siffantawa da ƙasƙantarwa a cikin kirari. Haka kuma ya ci gaba da kawo
dangantakar da take da kirari kamar kamanci da kambamawa da siffantawa da
dangantawa.
Wannan kundin nasa yana da alaƙa da wannan binciken ta fuskar yin kirari, sai daiduk da
haka shi dangantakar take ne da kirari, wanda a wannan binciken iza a kawo
kirarin garuruwan Zamafara ne.
Umar, H. D (1982, 33-39) a cikin kundinsa na neman digiri na ɗaya mai suna “Kirarin sarautu da sana’o’i da unguwannin
Zariya”, yayi bayanin kirari da yadda
zubin magana da yadda tsarinsa yake da kuma siffantawa d a mutuntarwa
wanda akan yi da nufin washi. Ya ƙara da cewa “akwai kyawawan lafazi a cikin kirari wanda
in ba a Hausa ba babu inda zaka saame su idan ba wajen lafazin kirari ba.
Alaƙar aikin nasa da wannan bincike shi ne yadda yayi nazarin kirari , sai dai
sun bambanta domin yayi nasa ne akan kirari zalla. Shi kuwa wannan kundi ya haɗa ne da kirarin garuruwa na Zamfara.
Zaruk, R. M da wani (1982) a littafinsu mai suna “kirarin duniya 222”
sunyi magana ne a kan kirarin duniya guda ɗari biyu da ishirin da biyu kuma sun kawo ma’anar kirari,
da bambancin kirari da karin magana da habaici da kuma take. Haka kuma sun kawo
misalan kirarin abubuwa da dama.
Wannan littafi nasu yana da dangantaka da wannan binciike da za a gabatar
ta fuskar kirari. Haka kuma sun bambanta
wannan kundi domin sun yi nasu ne akan kirarin duniya zalla a nan kuwa
za a kawo kirarin garuruwan Zamfar ne jiya da yau.
Kafin Hausa, A. (1985) a cikin kundinsa na samun digiri na biyu, (M. A) mai
suna “Kirari a Hausa: Matsayinsa da yanayinsa” ya bayyana muhimman abubuwa da
suka shafi kirari kamar asalin kalmar kirari da ma’anar kirari da ire-irensa da
ma’abota kirari ya kuma kasa kirari kashi-kashi
ta hanyar amfani da abinda akewa kirari. Misali:
Kirarin abinci da mutane da dabbobi da kayan marmari da
dai saura da dama. Ga yadda ya kawo kirarin abinci irin su tuwo:
1.
Tuwo abincin kullum,
tuwalle mai jiki duk tsoka
2.
Tuwalle nama ba ƙashi
Kundin nasa yana da alaƙa da wannan bincike sakamakon kirarin da ke cikinsa sai
dai bambancinsu shi ne wannan ya taƙaita ne ga kirarin garuruwan Zamfara.
Zaruk. R. M da wasu, (1988) a cikin littafin sa mai suna Sabuwar hanyar
Nazarin Hausa. Sun kawo ma’anar kirari da kuma yadda kirari yake kamar waƙa-waƙa, magana-magana. Shi ba
waƙa ba shi kuma ba magana ba ce kara zube,. Babu shakka, wannan littafi yana
da alaƙa da wannan bincike da za a gabatar ta fuskar kirari, domin a nan ma
kirarin fitatun garuruwan Zamfara ne za a nazarta.
Yahaya I. Y da wasu (1992) a cikin littafin
su mai suna Darussan Hausa sun kawo ma’anar kirari da karin
magana da masu yin kirari da yadda kirari ya kasu zuwa gida gida da yadda
ake samunsa a cikin zambo sun bambanta
take da zambo, tare da kwatanta zambo da kirari.
Dangantakar wannan littafi da wannan kundi shi ne yadda suka taɓo kirari sai dai a nan za a yi nazarin kirarin garuruwan
Zamfara ne.
Bargery. G. P (1993) a wani littafinsa mai suna Kirari, ya kawo
ma’anar kirari da yadda aka kasashi kashi-kashi da yadda ake yin kirari da
sigogin sa da yadda yake fitowa a cikin waƙa.
Haka kuma ya kawo ire-iren kalmomin da ake amfani da su wajen kambamawa da
mutuntarwa da alamtarwa da siffantarwa. Waɗanda ake samu a cikin kirari. Ganin ya yi nazarin kirari
yasa aikin yake da alaƙa da wanda za a yi.
Dikko, I. (1994) a cikin kundinsa na neman digiri na biyu mai taken
“Kirarin mutane” ya yi bayanin ma’anar kirari a cikin adabin Hausa, ya bayyana
cewa kirari na iya fitowa a kowa ne ɓangare na adabin Hausawa, wato ko a waƙa ko wasan kwaikwayo ko kuma a
rubutun zube. Ya nuna cewar, kirari yana fitowa a kirarin magana da kuma yadda
ake aro kirari daga karin magana.
Wannan kundin nasa nada alaƙa da wannan bincike da za a gabatar domin ya taɓo kirari, sai dai bambancin su shi ne ya yi nasa ne a kan
kirari n mutane kaɗai. Shi kuwa wannan binciken kirari ne na garuruwan jihar Zamfara.
Yahaya, I. Y (1995) a cikin wata maƙalarsa mai suna “Kirarin sarakuna da na Garuruwa”, ya
kawo ma’anar kalmar kirari da kirarin sarakuna da na garuruwa da kuma bambancin
da ke tsakanin kirarin sarakuna da na garuruwa.
Ya kawo abubuwa kamar su kwalliya da kambamawa da dabbanfarwa da
siffantarwa duk a cikin kirari… wannan maƙala tasa tana da alaƙa ƙud da ƙud da wannan bincike don ya taɓo kirarin garuruwa sai dai bana jihar Zamfara ba.
Ɗan’ Iya N. (1997) a
cikin kundinsa mai suna “Adon Harshe cikin rubutaccen adabin Hausa”, ya kawo
ma’anar kirari da yadda adon Harshe yake fitowa a cikin kirari da kuma
dangantakar adon da kirari.
Alaƙar wannan kundi da wannan bincike ita ce, ta fuskar yin kirari domin shi
m,a ya yi nasa ne a kan kirari. Sai dai wannan bincike za a yi shi ne a kan
kirarin garuruwan Zamfara na jiya da yau.
Adama Abdullahi (1998) a kundinta na digiri na ɗaya mai suna “Kirarin dabbobi”, ta kawo kirari na dabbobi
iri-iri da kuma yadda ake yiwa kowace dabba kirari. Haka kuma sun bambanta,
saboda ta yi nata ne a kan kirarin dabbibi shi kuwa wannan bincike za a yi shi
ne a akan kirarin fitattun garuruwan Zamfara na jiya da yau.
Aminu, M. L (2002) a kundinsa na
neman digiri na uku mai suna “The Hausa metaphysical world ɓiew”, ya yi bayaninsa kan
ma’anar kirari da al’amuran da
suka shafi bukukuwa da sinadarin take da zambo. Haka kuma akwai azancin magana
da tsoratarwa da kuma razanarwa da kamabamawa.
Dangantakar kundinsa da wannan binciken ita ce domin ya yi nazarin kirari.
Duk da wannan dangantaka, sun bambanta domin a anan za a faɗaɗa, saboda za a yi nazarin kirarin fitattun, saboda za a yi nazarin kirarin fitattun garuruwan Zamfara ne na jiya da yau.
Nasiru, M. (2007) a kundinsa na digiri na farko ma suna “Kirarin samari da
‘yan mata”, ya kawo ma’anar kirari da
asalin sa a ƙasar Haus a da ma’abota kirari da kuma bambancin da ke tskanibn kirari da
karin magana. Har ila yau, ya kawo muhimmancin kirari da rabe-raben sa da kuma
wurin yin kirari da kirarin samari da ‘yan mata.
Dangantakar wannan kundi da wannan binciken ita ce ta fuskar yin kirari sai
dai duk da haka, sun bambanta saboda ya yi nasa ne akan kirarin samari da ‘yan
mata ne kawai, shi kuwa wannan binciken za a yi shi ne a kan kirarin fitatun
garuruwan Zamfara na jiya da yau.
Zarruk R. M. Al-Hassan B. Y (2001-5051) a cikin wani
littafi nasa mai suna Kafin Hausawa A A sun kawo ma’anar kirari da kuma sigogin
kirari da ire-iren kirari inda suka kawo misalin wasu kirare – kirare kamar
haka:
1.
Giwa bukkar daji
2.
Jalla, iƙira, babbar Hausa
Inda suka kawo misalai da dama dangane da abin da ya shafi kirari. Duk da
haka dangantakar su da wannan bincike shi ne ta kirari da aka kawo.
Ibrahim Garba (1997), “Take da kirari a waƙoƙin baka na maza” kundin digiri na
farko a sashen Harsunan Najeriya Jami’ar
Usman Ɗan fodiyo Sakkwato.
A wannan kundi anyi maganar abunda
ya shafi take da kuma kirari dangantakar wannan kundi nasa da
wannan bincike shi ne ta fuskar yanda aka taɓo kirari wannan shi ne dangantakar wannan kundi da wannan
aiki, sai dai har wa yau a wannan bincike ana magana ne akan kirarin fitattun
garuruwan Zamfara jiya da kuma yau ne.
Jibrin Aliyu (2002) “Kirarin fadar sarkin Gwambe” kundin digiri na farko
sashen kotyar da harsuna da al’adun afrika jami’ar tarayya A.B.U Zariya.
Dangantakar wannan kundi nasa da kuma binciken da akeyi da kirari ne nasa
binciken ya yi sa ne kacokan akan kirari wannan bincike za a yi shi ne akan
kirarin fitattun garuruwan Zamfara ne na jiya da yau.
Mustapha Bala (2000) a cikin kundinsa na neman digiri na farko mai suna
kirari a kan sana’o’in Hausawa. Sashen koyar da harsuna da al’adu na Afrika
Jami’ar Tarayya da ke Zariya.
A wannan kundin nasa ya gabatar da shi ne akan kirar in sana’o’in Hausawa.
Dangantakar wannan kundi nasa da kuma wannan bincike da ake gabatarwa ita ce ta fuskar kirari wanda a wannan na
garuruwa ne na Zamfara.
Gusau, S. M (2000), “Kirari a waƙoƙin Makaɗan Hausa “. Maƙalar da ke cikin Hausa studies Ɓol II. 2 Sakkwato, sashen
Harsunan Najeriya Jami’ar Usmanu Ɗan fodiyo. Ya kawo kirari, a wannan muƙala tasa wadda
dangantakar wannan da wannan bincike kirarin da aka kawo sai dai a wannan
bincike za a yi aiki ne akan kirarin fitattun garuruwan Zamfara ne.
A. U Karin Hausa (1981), “Ma’ana da amfanin kirari a Hausa” muƙalar da ke cikin studies
in Hausa Langauge, literature and Culture, Ɓol. II, Kano. CNHN Jami’ar Bayaro.
A wannan muƙala da aka gabatar ita ma anyi magana akan kirari ne wanda shi ne ya
danganta binciken da ake gudanarwa. Bambancin da ke akwai a tsakani a wannan
bincike ana magana akan kirarin garururwan Zamfara na jiya da na yau fitattu.
Umar, K. T (1996), “Rubutattun waƙoƙin ƙarni na ashirin kirari da zuga” Kundin digiri na farko sashen Harsunan
Najeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato. A wannan kundi anyi magana ne a kan
kirari da zuga.
Dangantakar wannan kundi da binciken da ake gudanarwa shi ne ta kirari shi
ne abunda ya danganta wannan kundi da kuma binciken da ake kanyi ya shafi
kirarin garuruwan Zamfara ne na jiya da na yau kuma fitattu.
1.3 HUJJAR CIGABA DA BINCKE
Hausawa na cewa “Ruwa baya tsami banza” ko kuma “Idan
kaga kare na sunsuna takalmi to ɗauka zai yi”. Wannan haka yake, domin ba ayi tunanin rubuta wannan kundi ba
sai da wasu dalilai na musamman da za a iya kallo a matsayin cikon wannan aiki
da aka sanya a gaba.
(1)
Don gano wasu hanyoyi da
masana suka bi don zaƙulo ilimi mai amfani da zai taimakawa masu nazari a kan kirarin fitattun
garuruwan Zamfara na jiya da yau.
(2)
Don samun damar kammala
karatun digiri na farko a ƙarƙashin sashen koyar da Harsunan Najeriya na Jami’ar
Tarayya ta Gusau.
(3)
Domin nuna wa mutane
muhimmancin kirari a Harshen Hausa da hikimomin da suke cikinsa, musamman wajen
ƙwarewa da hikimomi na zantukkan
Harshen Hausa, da iya magana da kuma nishaɗi da ake samu a cikinsa da kuma yadda ake sarrafa harshe
da gwaninta da shi don isar da saƙo ga masu saurare, da isar da saƙonni iri-iri daban daban waɗannan kaɗan ne daga cikin dalilan da suka sanya cigaba da wannan bincike. Ke nan
domin farfaɗo da al’adu da ɗabi’un Hausawa na adabinsu domin yana daga cikin wannan
aiki inda ake cewa “Kowa yabar gida gida ya barshi”.
1.4 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE
Hanyoyin da aka bi wajen guadanar da wannan binciken sune waɗanda masana ilimi suka amince da su kuma wanda aka yi
amfani da su.
Masu iya magana sun ce, “Idan baka san gari ba to ka saurari daka”, kuma
sun ce “bin na gaba bin Allah”. Hanya ta farko da za yin amfani da ita wajen
gudanar da wannan bincike ita ce neman bayanai daga wajen masu ruwa da tsaki
game da tarihin garuruwan Zamfara.
Haka kuma akwai malamai masana da kuma manazarta waɗanda suka naƙanci wannan fanni.
Hanya ta biyu ita ce zan yi nazarin waɗansu ayukka da suka gabata na masana daban-daban. Ayukkan
da zan duba masu nasaba ne ko kuma masu
wata alaƙa ko dangantaka da wanannan aikin wannan zai iya zamowa wani jagora wajen gina wannan bincike
zan karanta littafai da muƙaloli da aka gabatar a wurare daban-daban waɗanda suka shafi bunƙasar kirari domin kammala wannan bincike cikin nasara.
Zan tattara kirarin da za a nazar ta ta hanyar yin hira da masarautu da
suke waɗannan garuruwa na Zamfara.
1.5 MUHIMMANCIN BINCIKE
Duk wani ilimi ya samu ne ta hanyar bincike, kuma wannan bincike zai
taimaka wa ɗalibbai da masu niyya a fagen ilimi,
musamman waɗanda suke bincike da nazarin harshen
Hausa a matakin farko na digiri ta wajen samar da muhimman bayanai waɗanda suke da dangantaka a sigar da aka ba su a fannin
kirarin garuruwan Zamfara.
Nazarin zai taimaka wajen hana salwantar adabin kuma zai sa a adana shi
domin wanda zai zo bincike daga baya.
Wannan bincike zai yi bayani akan kirari Fitattun garuruwan jihar Zamfara
na jiya da yau tare da fatan samun cikakkiyar nasaraa a wannan bincike don ganin
kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
KAMMALAWA
A wannan babi na farko anyi ɗan ta’aliƙi game da abinda ya shafi gabatarwa da manufar bincike da bitar ayukkan da
suka gabata da hujjar ci gaba da bincike da hanyoyin gudanar da bincike da kuma
muhimmancin bincike da wannan ne aka
kammala wannan manhaja ta babi na farko tare da fatan samnun cikakkiyar nasara ga wannan bincike.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.