Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Gargajiya A Garin Kwatarkwashi (2)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Auren Gargajiya A Garin Kwatarkwashi (2)

NA

NURA SANI KOTORKOSHI

Kayan aure

BABI NA ƊAYA

1.0 GABATARWA

Wannan aiki nawa mai taken “Auren Gargajiya a Garin Kwatarkwashi”, aiki ne da zai binciko irin yadda al’ummar garin Kwatarkwashi ke aiwatar da aurace-auracensu; domin samun sauƙin gudanar da wannan aiki da sauƙaƙawa ga masu karatu a ka kasa wannan aiki a kan babi- babi har gida biyar kamar haka.

 

Babi na ɗaya ya ƙunshi gabatarwa, dalilin gudanar da bincike, manufar bincike, farfajiyar bincike, hanyoyin gudanar da bincike da kuma muhimmancin bincike.

 

A babi na biyu kuwa, binciken zai yi tsokaci a kan ayyukan da suka gabata masu alaƙa da wannan aiki, tun daga kundayen bincike har zuwa bugaggun littattafai dai mujallu da muƙalu.

 

Babi na uku zai yi magana ne akan taƙaitaccen tarihin masarautar kwatarkwashi da ma’anar kalmar Kwatarkwashi da kafuwar garin Kwatarkwashi da addinin gargajiya da sana’o’i da zanen suna da kuma kaciya, sannan sai kammalawa.

 

Shi kuwa babi na huɗu zai yi magana ne akan ma’anar aure da ire-iren aure da auren gargajiya a Kwatarkwashi da zaman lalle da ɗaurin aure da al’adun aure kafin gudanar da buki da al’adun aure lokaci da bayan mutuwarsa a tsakanin Kwatarkwashi. Babi na biyar kuma na ƙarshe zai yi jawabin kammalawa da shawarwari da manazarta.

 

1.1 DALILIN GUDANAR DA BINCIKE

Idan aka ce dalili to ana nufin asali ko mafarin duk abin da mutum ke aiwatarwa, domin kuwa duk wani abu ko ma’amala da ba ta da dalili to bata da ma’ana ko amfani. Saboda haka wannan bincike yana da dalilan da aka hango har aka yi sha’awar aiwatar da shi.

 

Dalilan da suka sa a gudanar da wannan bincike sun haɗa da bayyana yadda auren gargajiya yake gudana a garin Kwatarkwashi. Wani dalili shi ne domin a ƙara zaƙolo muhimman bayanai da suka shafi auratayya da kuma irin kashe-kashen aure.

 

Wani kuma dalilin bincike shi ne domin ya zama ci gaba a kan wasu ayyuka da suka gabaci wannan.

 

Haka kuma wannan bincike zai taimaka wajen fahimtar al’adun aure musamman a garin Kwatarkwashi da kewaye.

 

Har wa yau wannan bincike zai taimaka wa ɗalibbai da masu nazari kan wannan fanni domin su sami abin karantawa domin cigabansu.

 

1.2 MANUFAR BINCIKE

Manufar bincike shi ne ayi ƙoƙari domin afito da abubuwan da ya sa wanda ke bincike ya nuna wa al’umma wanda ba’a sani ba musamman yadda Kwatarkwasawa suke aiwatar da irin al’adunsu na auratayya duk dai da cewa za’a samu kundayen da suka yi bayani a kan aure ko wani abu da ya shafi wani bayani mai magana akan auratayya.

 

1.3 FARFAJIYAR BINCIKE

Wannan aiki na gudanar da shi ne a fannin al’adun Hausawa na gargajiya, sannan kuma na keɓanceshi a kan irin yadda Kwatarkwasawa suke aiwatar da auratayyansu a gargajiyance.

 

Kuma ina fatar wannan aiki zai yi amfani ga manazarta a sashen harsunan Nijeriya musamman masu karatun (B.A Hausa) a sashen harsuna da al’adu ga duk wanda zai yi nazari a kan auren gargajiya.  Kuma ina roƙon Allah yasa mai amfani ne ga na bayanmu a tsakanin ƙannenmu da ɗiyanmu da ma jikokinmu da su amfana da shi, amin.

 

1.4 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

Hanyoyin gudanar da bincike, hanyoyi ne daban-daban da manazarci ko mai aikin bincike ke bi, wajen samun bayanai da suka dace da abin da suke nazari.

Akwai hanyoyin samun bayanai da yawa da manazarci ke bi wajen samun bayanai. A wannan binciken za a a hanyoyi kamar haka:

Nazartar kundayen bincike da bugaggun littattafai da mujallu da muƙalu masu alaƙa da abin da ake nazari akai. Domin tattaro bayanan da suka dace. Sannan kuma na yi hira da mutanen garin Kwatarkwashi kama daga tsofaffin Malamai, maza da mata da dai sauransu.

 

1.5 MUHIMMANCIN BINCIKE

Muhimmanci na nufin amfani da abu, duk wani abu da ɗan Adam zai aiwatar a rayuwarsa to yana da muhimmanci musamman aikin bincike.

 

Domin kuwa aikin bincike aiki ne mai muhimmanci ga ɗalibai masu karatu a makarantun gaba da sakandare.

 

Bincike abu ne mai muhimmanci domin shi ke ba da dammar gano matsala da niyar samun waraka a kan matsalar.

 

Wannan ya nuna cewa bincike abu ne mai muhimmanci ga ɗalibai, domin kuwa ya kan taimaka masu ta waɗnnan hanyoyi kamar haka:

·         Yana taimakawa ɗalibai su samu ƙwarewa a fannin da suke nazari a kai

·         Yana taimaka masu wajen gudanar da bincike na kansu

·         Yana baiwa ɗalibai damar zurfafa tunani da kuma yawaitar bincike don samun haske ga abin da suke nazari a kai

·         Yana ba ɗalibai dammar tsayawa da kansu wajen magance matsaloli da za su iya fuskanta a nan gaba

·         Yana basu damar ƙwarewa, musamman ta hanyar cuɗanya da mutane masu halaye da ɗabi’u daban-daban a cikin al’umma

·         Aikin bincike na ba dalibai damar fara tunanin wallafe-wallafen littattafai domin su bada tasu gudummuwa wajen ci gaban ilimi ga al’umma.

 

Kazalika, shi wannan aiki na bincike yana da muhimmanci ga reni domin kasancewarsa ɗaya daga cikin sharuɗɗan dake bada dammar samun takardar shaidar kammala digiri na farko a jami’ar tarayya Gusau. 

 

1.6 KAMMALAWA

An kamala wannan Babi ne, tare da yin bayanin abubuwan da wannan babi ya ƙunsa kamar haka; anyi tsokaci a kan gabatarwa da dalilin gudanar da bincike da kuma manufar bincike da farfajiyar bincike da kuma hanyoyin gudanar da bincike, kai da kuma muhimmancin bincike, duk a cikin wannan babi na ɗaya.

Post a Comment

0 Comments