Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Gargajiya A Garin Kwatarkwashi (3)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Auren Gargajiya A Garin Kwatarkwashi (3)

NA

NURA SANI KOTORKOSHI

Raka amarya

BABI NA BIYU

2.0 GABATARWA

Masana da manazarta sun yi ayyuka masu ɗimbin yawa a lokutta daban-daban masu alaƙa da wannan aiki nawa. Saboda haka, a wannan babi za a duba ayyukan da suka gabat masu alaƙa da wannan aiki. Daga cikin ayyukan da za’a duba a kwai kundayen bincike, bugaggun littattafai da kuma mujallu da muƙalu.

 

2.1 KUNDAYEN BINCIKE

Akwai kundayen bincike da dama masu alaƙa da wannan aiki nawa. Akwai kundayen bincike kamar haka:

 

Al-hassan da wasu (1982). A cikin littafinsu waɗannan marubuta sun tsara nasu littafi ne a kan al’adun Hausawa, inda suka sanya littafin a cikin tsarin kanun batutuwa kamar haka:

 

Duniyar Hausawa da aure da haihuwa da Tarbiyya da sana’o’i da sarautu da muƙami da kuma ana Bukin duniya. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar aure. Bambancin dake tsakanin nawa aiki da nasu shi ne, nasu aikin yana magana a kan ƙasar Hausa baki ɗaya, ya yin da nawa aikin mai taken; Auren Gargajiya a Garin Kwatarkwashi.

 

Rabi’atu da wasu (2009). Manazartan sun gudanar da aikinsu ne a kan ma’anar kayan adon ɗakin Hausawa na gargajiya da tarihin samuwarsu da hanyoyin samar da su da nau’o’insu da muhimamncinsu ga rayuwar Hausawa, wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar auren gargajiya.

 

Bambancin dake akwai tsakanin nawa aikin da nasu shi ne, nasu aikin yana bayani game da nazari a kan kayan adon ɗakin Hausawa na Gargajiya. In da ni kuma nawa aikin yake magana a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi.

 

Abdullahi da Wani (2011) a cikin littafinsu sun yi bayani a kan ƙasar Kwatarkwashi. Dangantakar aikinsu da wannan bincike shi ne wannan bincike anyi shi ne a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi

 

Dashi (2009). Ya yi bayani a kan “Kan gida da ire-irensa a ƙasar Kwatarkwashi. Dangantakar aikinsa da wannan bincike shi ne wannan bincike ana yinsa ne a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi.

 

Bala (2012). Ya yi bayani a kan tasirin zamani a auren Maguzawan Kwatarkwashi. Dangantakar aikinsa da wannan ana bayani ne a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi. A nan shi kuwa ya yi bayani ne a kan tasirin zamani a auren Maguzuwan Kwatarkwashi.

Abdullahi (2008). Ya yi bayani a kan tsafe-tsafe a Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi. A wannan bincike kuma ana magana ne a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi.

Shi kuwa Balarabe (2019) a Laccarsa ta aji. Masanin ya yi bayani a kan yadda Hausawa suke gudanar da auratayya a tsakaninsu da kuma al’adodi da kasha-kashen al’adodin da kuma hanyoyin samar da kayayyakin Bahaushe na gargajiya da muhallin Hausawa da tufafin Hausawa da kayan sufurin Hausawa da yadda suke aiwatar da sana’o’insu da kuma ire-iren addinansu na gargajya. Dangantakar aikinsa da nawa aikin shi ne nawa yana bayani ne a kan auren gargajiya.

 

Aliyu, (2010). Manazarcin ya yi ƙoƙari wajen bayyana ma’anar zumunci, zumunci a jiya, zumunci a yau, da ire-iren zumunci, sai dai bai taɓo ɓangaren al’adun aure a ƙasar Kwatarkwashi ba. Wannan aiki yana da alaƙa da wannan aiki ta fuskar al’adu; Bambancin dake tsakanin wannan aiki shi ne, na shi aiki na magana ne a kan zumunci a jiya da yau, ya yin da wannan aiki ke magana a kan aure.

 

Sulaiman da wasu (2010). Marubutan sun yi ƙoƙri wajen bayyana ma’anar zamantakewa a birni da ƙuaye, zamantakewa a jiya da zamantakewa a yau da sauransu, sai dai ba su yi magana a kan al’adun aure ba. Wannan aikin nasu yana da alaƙa da wannan aiki ta fuskar al’adu.

Bambancin dake tsakanin nasu aiki da wannan shi ne, nasu aiki yana magana ne a kan zamantakewa a ƙasar Hausa gaba ɗaya, yayin da wannan aiki ya keɓanta ne a kan al’adun aure a garin Kwatarkwashi.

2.2 BUGAGGUN LITTATTAFAI

Akwai bugaggun littattafai da dama masu alaƙa da wannan aikin nawa. Daga ciki akwai littafin Alhassan da Wasu (1981) a cikin littafin. Marubutan sun yi ƙoƙarin kawo bayani game da aure da kashe-kashensa. Aikin yana da alaƙa da nawa aikin domin ya shafi aure a ƙasar Hausa. Bambanci da ke tsakanin nasu aikin da nawa aikin shi ne, nawa yana magana ne kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi.

 

Yakasai (2002) a littafinsa. Marubucin ya yi ƙoƙari wajen bayyana aure a da da kuma yanayin zaman aure a yanzu, tare da ire-irensa, sai dai bai taɓo wasu ɓangarori na al’adu ba. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar aure da kuma yanayin zaman aure. Bambancin da ke tsakanin wannan aiki da nawa aiki shi ne, nawa aiki yana magana ne a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi, yayin da nasa aikin ke magana a kan aure da kuma yanayin zaman aure.

NTI (2013) a wani littafi da ta rubuta, ta taɓo zaman Hausawa kamar iyali da tsarin sarautu, sai dai ba tayi magana a kan auren gargajiya ba. Wannan aikin yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar al’adun. Bambancin dake tsakaninsu shi ne, nawa aikin na magana ne a kan auren gargajiya, ya yin da nata aikin ke magana a kan tsarin zaman Hausawa na iyali da sarautu baki ɗaya.

 

Gusau (2012) a littafinsa. Marubcuin ya yi ƙoƙari ƙwarai da gaske, don haka kuma ya taɓo wasu Bukukuwa da al’adun Hausawa, sai dai bai taɓo auren Gargajiya ba. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar al’adu. Bambancin da ke tsakanin nawa aikin da nasa aikin kuwa shi ne; nasa aikin na magana ne a kan Bukukuwan Hausawa baki ɗaya. Yayin da nawa aikin kuwa ya keɓanta ne a kan auren gargajiya.

 

B.U.K (1981), a littafinsa. Ya yi ƙoƙarin bayayna ma’anar aure da muhimmancinsa da shugabanci a gida. Wannan aiki yana da alaƙa da wannan aikin ta fuskar aure. Bambancin dake tsakaninsa da nawa aikin shi ne; Nawa aikin bai tsaya kan aure da muhimmancinsa kaɗai ba, ya taɓo ire-iren aure da al’adun aure kamin gudanar da shi, ya yin da nata aikin ya tsaya ne a kan rayuwar Hausawa ne kawai:

 

C.N.H.N (1981), a wannan littafinta ta yi ƙoƙarin bayyana ma’anar aure da muhimmancinsa da shugabanci a gida, wannan aikin yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar al’ada. Bambancin da ke tsakaninsa da wannan aiki shi ne; su sun yi magana ne a kan rayuwar, HAUSAWA jimlace, a wannan kuwa ana nazari ne a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi. 

 

Yahaya da wasu (2001) a littafinsu, marubutan sun yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wajen kawo zamantakewa tsakanin maƙwabta da shugabanni. Wannan aiki yana da alaƙa da wannan aiki ta fuskar al’adu. Bambancin da ke tsakaninsu shi ne, wannan aiki yana magana ne a kan al’adun aure a garin Kwatarkwashi, ya yin da nasu aiki yake magana a kan zamantakewa al’umma.

 

2.3 MUJALLU DA MAƘALU

Akwai mujallu da maƙalu da dama masu alaƙa da wannan aiki kamar haka.

 

Dalijan (2016), a maƙalarsa. Marubucin ya yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wajen bayani a kan zamantakewar Hausawa ta fuskar iyali da tasirin iyali ga Hausawa da zamantakewar Hausawa a zaman gandu. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar aure. Bambancin dake tsakaninsu shi ne. wannan aikin yana magana ne a kan zamantakewar Hausawa gaba ɗaya yayin da wannan aikin ke magana a kan auren gargajiya.

 

Sadiya (2018), a maƙalarta marubuciyar tayi bayani a kan Bukin auren Hausawa a yau, wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar Bukin auren Hausawa a yau. Bambancin dake tsakaninsu shi ne wannan aikin yana magana ne a kan bukin auren Hausawa a yau, yayin da nawa aikin ke bayani a kan auren gargajiya.

 

Joɗi (2010) a wata maƙala ya yi bayani a kan bukin aure tsakanin Kwatarkwasawa ya kawo yadda suke aiwatar da Bukin aurensu.

 

2.4 KAMMALAWA

An kammala wannan ba bi ne, domin fito da abubuwan da aka tattauna a kai a cikin wannan babi kamar haka; an yi bayani a kan bitar ayyukan da suka gabata, sannan kuma aka duba kundayen bincike. Haka kuma an duba bugaggun littattafai. Bayan nan daga ƙarshe an duba mujallu da maƙalu, duk a cikin wannan babi.

Post a Comment

0 Comments