Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Gargajiya A Garin Kwatarkwashi (1)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Auren Gargajiya A Garin Kwatarkwashi (1)

NA

NURA SANI KOTORKOSHI

Soyayya

SADAUKARWA

Ni Nura Sani Kotorkoshi na sadaukar da wannan littafin kundin digiri na farko da na yi a Sashen Harsuna da Al’adun na Jami’ar Tarayya, Gusau. Na Kuma sadaukar da shi ne ga mahaifina Mal. Sani Amada Kwatarkwashi, wanda shi ne ya ɗauki nauyin karatuna tun daga Firamare zuwa Sakandare har in da Allah ya kai ni a yanzu. Don haka ina mai roƙon Allah dare da rana da cewa Allah ya saka mashi da mafificin alheri ya kuma sa su gama lafiya da duniya, ya sa su Al-Jannah Firdausi amin.


GODOYA

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin bayi, mahaliccin sammai da ƙassai da ya bani ikon gudanar da wannan karatu har ya zuwa wannan mataki. Haka ma yabo da jinjina ga Annabinmu Muhammad ɗan Abdullahi, cikamakon Annabawa da dukkan ahalinsa da sahabbansa.

 

Ina godiya ga iyayena maza da mata da suka bani tarbiyya tun daga haihuwata har ya zuwa wannan mataki, Allah ya saka masu da Al-Jannah Firdausi amin.

 

Tarin godiya mai yawa ga malamaina na sashen Hausa a ƙarƙashin shugaban sashen farfesa Aliyu Muhammad Bunza, su ma Allah ya saka masu da alheri baki ɗaya. Ba zani manta da abokan karatuna ba, Saboda shawarwari da suke bani a lokacin gudanar da wannan aiki nawa, nagode ƙwarai.

 

Haka kuma ina godiya ga dukkan al’ummar musulmi da duk wani wanda ya bayar da gudunmuwarsa wajen gudanar da wannan aiki. Allah ya sa aikin ya amfani al’umma amin.

TSAKURE

Wannan kundi na bincike ya ƙunshi “Auren Gargajiya a Garin Kwatarkwashi” da kuma tarihin masarautar Kwatarkwashi. Wannan aikin bincike ya bayyana ma’anar aure. Haka kuma ya duba ire-iren aure. A ƙarƙashin wannan aiki an bayyana auren gargajiya a Kwatarkwashi da kuma irin al’adun aure lokaci da bayan mutuwarsa a tsakanin Kwatarkwasawa.

Post a Comment

0 Comments