Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Adashen Mata
A Garin Gusau (6)
NA
AMINA
ABUBAKAR
BABI NA BIYAR
KAMMALAWA
5.0 GABATARWA:
A wannan babi
za a naɗi dukkan
abubuwan da aka binciko a kan wannan aiki tare da yin nazarin kowane babi ɗaya bayan ɗaya domin
kawo su a taƙaice, wato a ƙarƙashin
taƙaitawa. Hakazalika, a nan ne za a kammala
wannan aiki gaba ɗaya.
Bugu da ƙari,
cikin babin ne za a ga shawarwarin da aka bayar ga ‘yan uwa ɗalibai, da
manazarta da masu sha’awar wannan harshe na Hausa, haka kuma da irin sakamakon
binciken da aka samu wajen gudanar da wannan bincike. A ƙarshe ne za a
yi bayanin kammalawa tare da manazarta.
5.1 SAKAMAKON
BINCIKE:
Kamar yadda
muka sani cewa komai na duniya yana da sakamako, ga dukkan abin da bawa zai
gudanar a rayuwar yau da kullum to lallai ne sai ya samu sakamakon abun nan,
mai kyau ne ko marar kyau, to wannan bincike shi ma akwai wasu abubuwa da aka
gano ta dalilin sa, waɗannan abubuwan sun haɗa da:
1. A ƙarƙashin
wannan bincike mun gano dalilan da suke sa a gudanar da bincike, tare da gano
muhallin bincike ga malamai har zuwa ga ɗaliban ilimi.
2. A ƙarƙashin
wannan bincike mun gano irin muhimmancin da sana’a take da shi a cikin rayuwar
al’umma, a inda muka ga cewa muhimmancin sana’a yana raya al’adun gargajiya,
misali idan aka dauƙi sana’ar sassaƙa
da dukanci za a tarar tana raya tare da adana wasu al’adun Hausawa na
gargajiya.
3. A ƙarƙashin
wannan bincike mun gano ma’anar adashe daga bakin wasu masana da kuma Shehunan
malamai, a inda muka samo ma’anoni daban-daban.
4. A ƙarƙashin
wannan bincike mungano ire-iren adashen gargajiya wanda muke da shi da kuma
yadda ake gudanar da shi a cikin al’ummar Hausawa.
5. A ƙarƙashin
wannan bincike mun gano su wa ke gudanar da adashe, a inda muka ga cewa mata su
ne waɗanda suka fi
gudanar da adashe, da kuma ‘yan kasuwa, kamar irin su masu sayar da fata, masu
kanikanci, ‘yan kasuwa da sauransu.
6. Duk a cikin
wannan bincike mun ga yadda ake gudanar da adashe a garin Gusau, haka kuma mun
gano wace ce uwar Dutsi.
7. Wannan
bincike ya sa mun gano yadda ake zubin adashe da kuma hanyoyin da ake bi wajen
zubin da ranakun zibi ga ma su adashe. Bugu da ƙari mun ga
yadda ake kwasar adashe, da kuma kuɗin da ake baiwa uwar adashe.
8. Daga ƙarshe
mun ga irin muhimmancin da adashe yake da shi, da irin alfanun da ake samu ga
masu yin sa, haka kuma mun ga irin illolin dake ƙunshe cikin
adashe.
A nan mun ga irin sakamakon da aka
samu ta dalilin wannan bincike, domin an gano abubuwa da yawa a cikin wannan
bincike.
5.3
SHAWARWARI:
To, a nan
shawarwarin da za a ba da, ba su wuce na malamai da ɗalibai masu
nazarin harshen Hausa da masu magana da harshen. Shawara ta farko ita ce,
malamai da ɗaliban harshe
su ci gaba da irin wannan nazarin saboda muhimmancinsa, ta irin wannan bincike
ne za a gane bakin abubuwan da suka shigo.
Haka kuma,
yana da matuƙar muhimmanci hukumar makaranta ta sanya
wannan bincike a cikin tsarin bincike da ake rubuta maƙala a kansa,
idan muka yi la’akari da muhimmancinsa. Domin ya taɓo ɓangarori na
rayuwar Bahaushe tamkar dai muna iya cewa adashe wata hanya ce da ake amfani da
ita wajen cimma wani buri da mutum yake son cimma, waɗanda suka
shafi abubuwan buƙatar rayuwa na amfani da kuma abubuwan
sana’a, waɗanda suka haɗa da faɗaɗa jari idan
ya yi ƙasa, da kuma ƙaro kayan
sana’a domin kasuwanci ya ƙara bunƙasa,
da sauran abubuwa makamantan waɗannan.
Bayan nan
kuma, gwamnati ita ma ya kamata ta sanya wannan adashe a cikin manhaja ga ɗalibai tun
daga firamare har zuwa jami’a, a cikin darussan da ake karantar da ɗalibai kamar
yadda ake karantar da Karin magana, da habaici da tatsuniya da waƙa
da adabi, shi ma adashe ya kamata a ce ana karantar da shi domin muhimmancinsa
da alfanun da ake samu a cikin sa, da kuma irin taimakon da yake ba da wa ga
rayuwar Bahaushe da kuma al’ummomi daban-daban masu gudanar da shi.
Daga ƙarshe
kuma ya zama dole ɗalibai masu nazarin harshen Hausa a matakai
daban-daban kama daga masu neman takardar shaidar malanta wato (NCE) da masu
karatun digiri na 1 da 2 da 3, su tsunduma a sha’anin bincike a kan adashe, ta
hanyar rubuta kundayensu na kammala karatu a kan wannan sha’ani na yadda ake
gudanar da adashe a Bahaushiyar al’ada.
5.4
KAMMALAWA
A babi na
farko wannan aiki ko bincike an yi cikakken bayani ne game da manufar wannan
bincike, da dalilin gudanar da bincike, da muhimmancin bincike, haka kuma, an
yi bayani a kan hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan bincike, da kuma
muhallin da wannan bincike ya ƙunsa, haka
kuma an yi bayani a kan hujjar ci gaba da wannan bincike. A ƙarshen
babin an yi bayani a kan bitar ayyukkan da suka gabata, sai kuma bayanin
kammalawa.
Babi na biyu
wato an yi tsokaci a kan taƙitaccen
tarihin garin Gusau, inda muka yi bayani a kan yadda garin Gusau yake a taƙaice,
da kuma ire-iren sana’o’in da mutanen Gusau suke yi a gargajiya, waɗanda suka
gada tun daga kaka da kakkanni, haka kuma a cikin babin an yi bayani a kan
muhimmancin sana’a, misali irin su bunƙasa tattalin
arziki, samar da abin masarufi, samar da aikin yi, haifar da wasu sana’o’i,
samar da magunguna na musamman, raya al’adun gargajiya, tare da yin bayaninsu ɗaya bayan ɗaya. Daga ƙarshe
babin, an yi bayani na kammalawa.
Babi na uku
kuwa shi ne babin da aka yi magana a kan ma’anar adashe. Inda muka yi bayani a
kan irin yadda masana suka yi bayani a kan ma’anar adashe, da kuma hasashensu a
kan tarihin samuwar adashe, kazalika duk a cikin babin, an yi magana a kan su
wa ke gudanar da adashe, tare da rabe-raben adashe, inda daga ƙarshe
aka kammala babin.
Babi na huɗu an tattauna
a kan muhimmancin abubuwa kamar haka; adashe a garin Gusau, uwar dutsi, zubin
adashe, kwasar adashe. Haka kuma, mun yi tsokaci a kan muhimmancin adashe ga
al’umma, da irin alfanun da ake samu a cikin adashe, haka kuma duk a cikin
babin mun yi duba zuwa ga illolin dake ƙunshe cikin
adashe tare da yin bayani. Daga ƙarshe muka yi
bayanin kammalawa.
Babi na
biyar, mai suna kammalawa, wato kammala aikin ne gaba ɗaya, an kawo
sakamakon bincike, shawarwari da kammalawa, daga ƙarshe baki ɗaya
manazarta.
MANAZARTA
Tuntuɓi Amsoshi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.