Ticker

6/recent/ticker-posts

Adashen Mata A Garin Gusau (2)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Adashen Mata A Garin Gusau (2)

NA

AMINA ABUBAKAR

 

Kudi

BABI NA ƊAYA

1.0 GABATARWA

Wannan babi mai suna Gabatarwa, a cikinsa za a yi tsokaci a kan manufar bincike, sai dalilin gudanar da bincike da kuma bayani a kan muhallin bincike. Bugu da ƙari, za a yi bayani a kan hanyoyin da aka bi wajen gudanar da bincike. Idan aka nutsa a cikin babin za a yi bayani a kan muhimmancin bincike, da kuma hujjar ci gaba da bincike. Haka kuma za a duba ayyukan da suka gabata. Daga ƙarshe kammalawa.

 

1.1 MANUFAR BINCIKE

Kamar kowane irin bincike, a kan buƙaci a nemo wasu muhimman abubuwa da ba a san su ba tun farko, ko kuma an san su amma ba a fito da su domin nazari ba, don haka za a gano irin waɗannan keɓaɓɓun abubuwa da ke cikin adashen mata, kuma a yi nazarin su.

 

Hausawa kan ce “Banza ba ta kai zomo kasuwa”. Domin haka, duk abin da za a yi sai da dalilin yin sa, kasancewar haka ya sa ɗaya daga cikin manufofin binciken nan shi ne fito da ainihin yadda mata suke gudanar da adashe musamman a garin Gusau. Bugu da ƙari, za a yi tsokaci a kan irin alfanun da ake samu a yayin gudanar da adashe. Daga bisani za a kalli illolin da ke tattare ga adashe.

 

1.2 DALILIN GUDANAR DA BINCIKE 

Dalilin da ke sa a gudanar da bincike suna ɗauke da manufofi daban-daban kamar yadda ake aiwatar da shi binciken. Saboda haka dalillan da suka sa aka gudanar da wannan bincike suna da yawa, amma ga wasu kamar haka:

a.      Domin masu nazari a cikin ɗakunan karatu da kuma masu nazari a kan harshen Hausa

b.      Domin neman shaidar kammala karatun digiri na farko a Jami’ar tarayya ta Gusau a fannin da aka zaɓa na “adashen Mata a Garin Gusau”.

c.       Zaburar da masana da masu bincike a kan al’ada, domin karkato da hankalinsu zuwa ga fannin sana’ar adashe, domin haɓɓaka bincike a wannan ɓangare.

d.     Don samar da ingantaccen bayani a kan adashe a harshen Hausa domin Hausawa da masu sha’awar al’adun Hausawa.

 

1.3 MAHALLIN BINCIKE

Adashe wani rukuni ne babba daga cikin jerin sana’o’in Hausawa, saboda da yawa wasu sun ɗauke shi a matsayin sana’a. Don haka wannan bincike zai kewaya a cikin garin Gusau musamman manyan gundumumin dake cikin garin. Saboda haka, wannan bincike zai tsaya ne a gundumomi kamar haka:

a.      Gundumar Tudun Wada

b.      Gundumar Sabon Gari

c.       Gundumar Mayana

d.     Gundumar Galadima

e.      Gundumar Madawaki

Wannan bincike na “Adashen Mata a Garin Gusau”, zai tsaya ne kawai a cikin waɗannan gundumomi, za a nemi mutane a yi fira da su ta hanyar da suke gudanar da adashe.

 

A ƙarshe binciken zai bayyana ma’anar adashe da kuma ire-iren adashe. Bugu da ƙari, zai bayyana su wa ke gudanar da adashe, tare da yin bayani a kan yadda ake kwasar adashe, binciken zai kalli muhimmancin adashe, daga bisani za a dubi illolinsa.

 

1.4 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

Kowane aiki yana da hanyar da ake bi domin aiwatar da shi, kamar yadda Hausawa kan ce “Kowace ƙwarya da abokiyar ɓurminta”. Kamar yadda yake a bayyane, cewa kowane irin bincike za a gabatar ko gudanar musamman ma na ilimi ba zai kammalu ba ba tare da an bi hanyoyi da dabarun gudanar da shi ba. Saboda haka, kafin a kammala wannan bincike, za a yi amfani da hanyoyin da suka dace tare da dabaru daban-daban domin ganin haƙa ta cimma ruwa. A yayin gudanar da wannan bincike za a ziyarci ɗakunan karatu da cibiyoyin ilmi daban-daban domin samun bayanai daga ayyukan masana daban-daban a kan a bin da ake nazari. Abubuwan da za a bincika sun haɗa da:

-          Nazarin littafan da aka wallafa a kan al’ada

-          Tattaunawa ta musamman da mata da suke da masaniya a kan adashe, domin neman ƙarin bayani da shawarwari.

A taƙaice, waɗannan su ne hanyoyi da dabarun da za a bi a yayin aiwatar da wannan bincike.

 

1.5 MUHIMMANCIN BINCIKE

Muhimmanci kalma ce mai auna darajar abu ko ƙimar sa, kamar yadda masana suka faɗi cewa “bincike tsani ne na ƙara fahimtar matsayin abu da irin muhimmancinsa da kuma ci gabansa ga rayuwar al’ummar Hausawa” Funtuwa (2012).

 

Kamar yadda masana al’ada suka bayyana ta da cewa “hanya ce da ta shafi rayuwar Ɗan’adam tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa”. Wato ke nan sana’ar adashe wata abu ce mai muhimmancin gaske musamman ta hanyar samar da tattalin arziki ga al’umma. Saboda haka, adashe yana ɗaya daga cikin abubuwan da suka ba da gudummuwa wajen bunƙasa al’adu da sana’o’in gargajiya.

 

1.6 HUJJAR CI GABA DA BINCIKE

Ba shakka masana da dama sun yi rubuce-rubuce a kan sana’o’in Hausawa, adashe na ɗaya daga cikinsu. Haka kuma ɗalibbai da dama sun rubuta kundaye a kan sana’o’in Hausawa daban-daban. Amma duk da haka wannan ba zai hana mu kalli adashen mata a garin Gusau mu bayar da ta mu gudummuwa.

 

 

 

1.7 BITAR AYUKKAN DA SUKA GABATA

Al’adun Hausawa sun daɗe ana rubuta su da nazari a kansu. saboda an taskace sassan al’ada daban-daban ta rubutawa da wallafawa. Masana da manazarta da marubuta da yawa sun yi ayyuka da dama da suka shafi sana’o’in Hausawa na gargajiya, da ma yadda ake kallonsu a aladance. Dalilin haka ne ya sa gabanin a za tubalin wannan aiki aka yi ɗan ƙoƙarin bitar ayyukan da suka gabaci wannan bincike, masu dangantaka da irin wannan aiki gwargwadon hali.

 

Ayukkan da aka duba a lokacin gudanar da bitar sun haɗa da wallafaffun littafai, da ƙungiyoyin haɗin guiwa, da kundayen bincike. Ga jerin ayyukan da aka duba kamar haka:

 

1.7.1 ƘUNGIYOYIN HAƊIN GUIWA

Magaji U. (2018), ya bayyana yanayin adashe na ƙungiyar taimakon kai da kai. (Royal Cooperatiɓe). A rahotonsa na shekara shekara inda ya zayyano ƙa’idojin adashe da kuma alfanunsa ga membobin ƙungiyar ta hanyar kawo ci gaban da ake samu na samun ƙaruwar yawan mambobin. Wannan adashe ma’aikata ce kan bayar da wani kaso na daga cikin albashin da yake ɗauka a duk wata. Shi ma wani kalar nau’in adashe na zamani. Saboda haka, wannan aiki yana da alaƙa da adashen mata a garin Gusau. Sai dai na mu ya tsaya ne a garin Gusau kawai.

 

 

1.7.2 MUJALLU DA MAƘALU

Zabi da Aliyu (2016) a cikin maƙalarsu mai taken “Tasiri da barazanar zamani a kan sana’ar noma, wadda suka gabatar a cikin mujallar Argungu Journal of Language Studies, Marubutan sun yi magana ne a kan Hausawa da sana’ar noma a ƙasar Hausa, da ma’anar tattalin arziki da bunƙasar tattalin arzikin Bahaushe da sauran su. Wannan aiki nasu yana da alaƙa da wannan ta fuskar sana’o’in Hausawa da al’adunsu. Bambancin da ke tsakanin wannan aiki da nasu shi ne, nasu yana magana a kan ƙasar Hausa baki ɗaya, yayin da wannan yake magana a kan adashen mata a garin Gusau.

 

Muhammad (2016) a maƙalarsa mai taken “Gudummuwar ƙira wajen samar da kayayyakin Hausawa na gargajiya” Wadda ya gabatar a cikin mujallar Argungu Journal of Language studies. Marubucin ya yi bayani a kan su wane ne Hausawa da ƙasar Hausa? Sai sana’o’in Hausa na gargajiya da ita kanta sana’ar ƙira da muhimmancinta da sauransu. Wannan maƙala tana da alaƙa da wannan aiki ta fuskar sana’a, sai dai bambancin da ke tsakanin maƙalar da wannan aiki shi ne, aikinsa ya ta’allaƙa ne a kan sana’ar ƙira kawai, yayin da wannan aiki yake magana a kan adashen mata a garin Gusau.

 

1.7.3 KUNDAYEN BINCIKE:

Bagudo, F.A (2010) “In Ba ku ba Ƙasa: Gudummawar Matan Sakkwato Wajen Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasa” A inda manazarcin ya yi bayanin gudunmawar mata wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, saboda sun yi tarayya wajen bayani a kan tattalin arziki, wanda wannan yana ɗaya daga cikin farfajiyar wannan aiki.

 

Amina A. (2001), “Sana’o’in Gargajiya na Hausa, Bunƙasarsu da Taɓarbarewar su”. A inda manazarciyar ta yi bayanin sana’o’in Hausawa na gargajiya da bunƙasarsu. Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, saboda sun yi tarayya wajen bayani a kan sana’o’in gargajiya, wanda wannan aiki yana ɗaya daga cikin abin da zai duba.

 

Umar M.B (1980) “Tattalin Arzikin Hausa jiya da yau". A inda manazarcin ya yi bayani a kan tattalin arzikin Hausawa. Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, saboda sun yi tarayya wajen bayani a kan tattalin arziki. Wanda wannan aiki yana ɗaya daga cikin ruhin aikin.

 

Safiya S.M (1985) “Sana’o’in Matan Hausawa”. A inda manazarciya ta yi bayanin sana’o’in Hausawa. Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, saboda sun yi tarayya wajen bayani a kan sana’o’in Hausawa, wanda wanann aiki yana ɗaya daga cikin irin sana’o’in da tayi magana a kai.

Ibrahim Idris (2011) “Muhimmancin Adashe ga Rayuwar Al’umma” A inda manazarcin ya yi bayani a kan muhimmancin adashe. Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, saboda sun yi tarayya wajen bayani a kan muhimamncin adashe, wanda wannan aiki yana ɗaya daga cikin farfajiyar wannan aiki da ake gudanarwa.

 

Kado, A. (1986) “Saƙa Sana’ar Auduga a Ƙasar Hausawa, Tasirinta da Muhimmancinta ga Al’ummar a Kan Saƙa Sana’ar Auduga a Ƙasar Hausa”. Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, saboda sun yi tarayya wajen bayani a kan tasirin sana’a da muhimamncinta ga al’umma, a ya yin da za mu dubi adashen mata a garin Gusau.

 

1.8 KAMMALAWA

A nan za a taƙaita abubuwan da aka yi bayaninsu a baya, wato abin da bincike ya tattauna, ko mu ce abin da kanun bincike ya yi magana a kai wato “Adashen mata a garin Gusau”.

 

An kawo manufar bincike da dalilin bincike da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da bincike waɗanda suka haɗa da nazartar littafai da kundaye da muƙalu da kuma hira da masana fannin adashe, an kuma kawo farfajiyar bincike da muhimmancin bincike, daga ƙarshe kammalawa.

Post a Comment

0 Comments