Ticker

6/recent/ticker-posts

Yajin Aiki

Waƙar "Yajin Aiki" ta Murtala Uba Mohammed. Fasihin ya taɓo muhimman bautuwa dangane da yajin aikin ASUU wadda ta shafe tsawon kimanin watanni takwas.

yajin aikin asuu

Yajin aikin ƙasarmu
Wa zan zarga cikinmu
Shugabanni ko ko ASUU?

Godiya na yi wa Allah
Al-Alimu mafi Jamala
Shi ne tushe na ilmu.

Nai yabo a gun Aminu
Ya fi kowa kyan bayanu
Ya fi kowa ba da ilmu

Zan batu ne kan ƙasarmu
Yajin aiki garin mu
Jimi’o’i mun rufe mu.

Ga watanni sun yi nisa
An bar mu muna ta wasa
Mun bar nema na ilmu

Lokacin mu muna asara
Hali na abin mu lura
Ga takaici ya rufe mu.

Duniya kuma na ta moving
Mu muna nan sai sleeping
An yi nisa can a ilmu.

Can ana rocket da robot
Can ana AI da CT
Tuni har an sha gabanmu.

Mun tsaya waje guda ne
Mun rigingine kan gado ne
Tuni an tafi an baro mu.

Ga shi mun rufe dari ilmun
Za mu kuna cikin juhulun
Mun rufe ilimi garin mu.

Ga shi har an yo takwas ma
Wata zai doshi goma
Mun garke gida na ilmu.

Kuma duk mun kulle baki
Ba mai cewa ci kan ki
Dukka mun yi shiru abinmu.

Kuma duk mun sa idanu
Kai ƙasar nan sai a sannu
Tamkar mu an washe mu.

Ga ASUU ta na ta raji
Ga gwamnati na ta gunji
Jama’a mun kau da kai mu.

Laifin waye cikin mu?
ASUU manyan malaman mu?
Ko ko gwamnati ce, uwarmu?

ASUU dai ta zo da hujja
Shekara tara tai tana ja
“Nema haƙƙi, ku bamu.”

Tun two thousand da nine ne
ASUU tai yarjeniya ne
Da mutan villa ƙasar mu.

An yi yarjejeniya ne
Hannu suka rattaba ne
Na batun kula da ilmu

Cewa ilmi gaban mu
Za a inganta shi gun mu
Za a kyautata jami’armu.

Za a kyautata duk classes
Za a kalli gini da hostels
Library za mu samu.

Laboratory a gyra
Yin hakan zai sa mu cara
Duniyar yau za a ji mu.

Sai gwamnati yau ta kasa
Kun ga ai ta zo da wasa!
Ta ci haƙƙin malamanmu.

Albashi babu ƙari
Bayan kuma an yi tsari
Za a kalli ma-ba-da ilmu.

Farfesa ba hamasa
Albashi bai isarsa
Kai rashin kirki gare mu.

Ilmi baya gaban su
Tun da har dai ba ɗiyan su
Sun daina kula da ilmu.

Cinkoso jami’armu
Cincirundo ɗakunanmu
Ci da ƙarfi ga ɗalibanmu.

Ga classes babu ko seats
Babu toilets ko a hostels
Ba ruwa kuma jami’armu.

Babu ci gaba library
Babu ITCs da tsari
Sai takaici jami’armu.

Shugabanni sun biris ne
Sun gani kuma sunka kanne
Sun ƙi ƙwalla ko su damu.

Tun da dai ‘ya’yan talak ne
Ba ‘ya’yan wane wane
Ba su kishin jami’armu..

Sai su je foreign ɗiyansu
Sui karatu can abunsu
Ko da an rufe jami’armu.  

Sai su kai ‘ya’yansu Landon
Amsterdam ko China, Beijing
Ba su kallon na mu ilmu.

Wanda bai da ruwa a tsari
Ya zai inganta tsari
Matsayi na shuwagabanmu. 

Har da dai an zargi ASUU
Da rashin aiki wasun su
Da corruption jami’armu

Visiting lecture gare su
Wasu sun bar ɗalibansu
Sun daina kula da ilmu

Har da dai laifi akwai shi
Gwano wari jikin shi
Da akwai aibu gare mu.

Amma government ta jawo
Tun da dai ita ce ta kawo
Jami’a birjik ƙasarmu.

Amma kuma babu teachers
Sai ya ja visiting ya zam case
Hanyar bayar da ilmu.

Har ya ja in babu shi yau
Za a kulle jami’a yau
Babu hanyar ba da ilmu.

Tun da babu profs a shashi
Tillas a rufe a bar shi
Malami ke ba da ilmu. 

Kuma gwamnati ke da dama
Visiting sai ta ga dama
Ita ke da wuƙa ta ilmu.

Ga hukumar jami’o’i
Ita ce iko ta ce ‘i’
Haƙinta kula da ilmu.

ASUU ko ita ƙungiya ta
Haƙinta take ta fata
Burinta a gyra ilmu.

Yajin aiki larura
Babu mai so nai mu lura
Mun fi ƙaunar ba da ilmu.

Fata Allah Hakimu
Wanda ke sama Al-Alimu
Ya siturta ƙasarmu ta mu.

Duba mai rauni cikinmu
Rabbi kalli digwui-dugwunmu
Allah ka ji tausayin mu.

Ba mu leaders masu son mu
Masu burin cigaban mu
Masu son nazari da ilmu.

Taimakawa jami’armu
Har da ma su furamarenmu
Ba mu inganci a ilmu

Nan za ni tsaya da birki
Murtala na zaɓi aiki
Yajin aiki ya bar mu.

Murtala Uba Mohammed
Sashen Jogorafi
Jami’ar Bayero ta Kano

Post a Comment

0 Comments