Ticker

6/recent/ticker-posts

Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (1)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a sashen koyar da harsuna da al’adu tsangayar fasaha da ilimi, jami’ar tarayya, gusau don neman digiri na farko

Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (1)

NA

HIZBULLAHI ƊANLAMI

birkila

SADAUKARWA

            Na sadaukar da wannan bincike, mai taken Birkila/Mesin a garin kwatarkwashi ga mahaifina Alhaji Ɗanlami Abubakar Kurah da mahaifiyata Faɗimatu Muhammad Kwatarkwashi (mai unguwar Saɓawa). A bisa ɗawainiyarsu gare ni, tun ina ƙarami har zuwa yau.

            Da malamaina tun daga kan makarantar allo, da islamiya da firamare, zuwa sakandare da kuma kwalejin ilmi har zuwa Jami’a. Da ma duk wani nazari da ci gaban harshen Hausa.

GODIYA

            Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah a kan ni’imominsa na bayyane da na ɓoye, da da yanzu. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga babban ɗan babban farin jakada Annabi Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa, da mabiyansu managarta har zuwa ranar ƙarshe.

            Bayan haka, aikin bincike aiki ne, wanda yake da wahalar gaske a ce mutum ya kammala shi ba tare da taimakon wasu ba. Saboda haka, ya zama dole in miƙa godiyata ga dukkan waɗanda suka ba ni gudunmuwar ganin wannan aiki ya cimma nasarar kammalarsa.

            Tushiya mafarin dawa; Tilas in fara miƙa godiyata ga mahaifana a bisa ɗawainiyar da suka yi da ni, ta tarbiya da neman ilmi da addu’o’in fatan alheri tun daga haihuwa har zuwa yau.

            Hausawa kan ce “Daga wawa sai mahaukaci ke mance mafari”. To dole ne in miƙa  gwaggwaɓar godiya maras adadi da jinjina da yabawa ga malamina tun daga C.O.E  Maru, har zuwa Jami’a wato Dr. Aliyu Rabi’u Ɗangulbi, a bisa juriyar duba wannan aiki tun daga farkonsa har zuwa kammalarsa, tare da gyara da shawarwari da nasihohi irin na ɗa da mahaifi don ganin  wannan bincike  haƙarsa ta cimma ruwa, ina roƙon Allah mai girma da buwaya da ya ƙara ɗaukaka kuma cikin ƙanƙanin lokaci mu zo bukin zamowa shehin malami (Professor), amin.

Bayan wannan kuma ya zama dole in miƙa godiyata tare da jinjina da fatar alheri ga malamaina waɗanda da bazarsu ce na taka rawa a fagen neman ilmi, ta hanyar shawarwri, fatan alheri na yau da kullum, kamar: Farfesa Aliyu Muhammad Bunza da farfesa Magaji Tsoho Yakawada da farfesa Balarabe Abdullahi da farfesa Aliyu Musa Kano da Dr. Adamu Rabi’u Bakura da Dr. Musa Fadama Gummi da Dr. Nazir Ibrahim Abbas da malam Isah S/Fada da malam Musa Abdullahi Zaria da Malam Shafi’u Adamu Tazame da malam Ɗahiru Hussaini Sankalawa da kuma Dr. Sani Aliyu Soba (FCET) Gusau, da Mubarak (typer FCET) Gusau.

Saboda ajizancina ina ba da haƙuri ga duk wanda ba a ambaci sunansa ba a wannan fage, ya yi haƙuri.

Na gode !!!

Post a Comment

0 Comments