Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Sarautar Fawa
A Garin Gusau (6)
NA
ABDULRASHID
S. PAWA
Phone Number: 08132326047
Email: abdulrashidspawa@gmail.com
BABI NA BIYAR
KAMMALAWA
5.0 GABATARWA
Wannan babi
zai yi magana a kan kammala wannan aikin binciken, tare da jawabin kammalawa da
taƙaitawa da kuma shawarwari domin ganin an ƙara
kawo wasu hanyoyin cigaban sarautar fawa a garin Gusau.
Haka kuma
wannan babi zai yi magana a kan sakamakon da aka samu a wannan binciken da aka
gudanar, daga ƙarshe wannan babi zai kawo manazartan da aka
aiwatar da wannan bincike domin samun bayanai.
5.1 JAWABIN
KAMMALAWA
Dukkan wasu muhimman
bayanai da aka samu a wannan bincike sun samu asali ne ta tsarin shirya kundin
bincike, wanda duk wani bincike da za a shirya shi to tilas ne ya bi wannan
tsarin domin samun bincike mai nagarta.
Haka kuma tun
farkon wannan bincike kafin a gudanar da shi sai da aka samu dalilan da zai sa
a yi wannan bincike tare da samin farfajiyar shi da hanyoyin gudanar da shi da
muhimmancin shi da matsalolin shi da kuma tambayoyi da za a gabatar a kan binciken.
Bayan haka an
yi waiwaye a kan wasu ayyuka da suka gabaci wannan bincike, domin sanin inda
aka kwana da suka haÉ—a da Kundaye da Jaridu da kuma bugaggun
littafai.
Wannan
bincike ya kawo taƙaitaccen tarihin
Gusau da sana’o’inta, domin a san tushen mutanen garin da kuma irin sana’o’insu
da kuma ire-iren sarautun sana’o’in su.
Haka kuma
wannan bincike ya yi rawar gani wajen kawo taƙaitaccen
tarihin sarautar fawa a garn Gusau domin wannan shi ne bincike na farko da aka
taɓa yi a kan
wannan sarautar. Bugu da ƙari, wannan
bincike ya kawo muhimman abubuwa da suka ƙunshi
sarautar da suka haÉ—a da ma’anar sarautar fawa, da sarautunta, da
masu tsarin sarautar da kuma hanyoyin da aka bi wajen zaɓen Sarkin
Fawa, haka kuma wannan bincike ya yi bayani a kan masu zaɓen Sarkin
Fawa tare da gudummawar sarautar da magungunan da take samarwa, tare da
shugabancin Sarkin Fawa da al’adun sarautar fawa da ire-iren su.
Daga ƙarshen
wannan bincike ya kawo sunayen sarakunan fawa na garin Gusau, da kuma jawabin
kammalawa da taƙaitawa tare da shawarwari da kuma sakamakon
binciken da aka gudanar tare da manazarta, da kuma mutanen da aka tattauna da
su domin samun bayanai daga garesu.
5.2 TAƘAITAWA
Wannan
bincike ya taƙaita ne a kan duk wasu ayyuka da suka gabata,
waÉ—anda suke da
alaƙa da wannan bincike. Haka kuma, wannan
bincike ya taƙaita ne a kan taƙaitaccen
tarihin garin Gusau, da mutanen da ke ciki tare da ire-iren sana’o’in da suke
yi da suka haɗa da Noma, Ƙira,
Fawa, Wanzanci da Su (kamun kifi), tare da ire – iren sarautun sana’o’in
gargajiya na garin Gusau, kamar Sarkin Noma, Sarkin Ƙira, Sarkin
Fawa, Sarkin Aska da kuma Sarkin Ruwa.
Bayan haka,
wannan bincike ya taƙaita ne a kan taƙaitaccen
tarihin sarautar fawa a garin Gusau da kuma duk wasu abubuwa masu muhimmanci da
suke da alaƙa da sarautar kamar irin ƙananan
sarautun da ke ƙarƙashinta da
suka haÉ—a da Wakilin
Fawa, Ajiyan Fawa, da kuma Sarkin Zango (Sarkin Kara). Haka kuma wannan bincike
ya taƙaita ne a kan duk wata gudummawa da kuma
magungunan da sarautar fawa ke samarwa tare da al’adun sarautar da ire-iren
al’adunta. Haka kuma wannan bincike ya taÆ™aita ne ga
sarautar fawa a garin Gusau da kuma sarakunan fawa na garin Gusau. Daga ƙarshe
duk wasu shawarwari da aka bayar da kuma sakamakon da aka samu a wannan
binciken duk sun taƙaita ne a kan
sarautar fawa a garin Gusau.
5.3
SHAWARWARI
“Gyara
kayanka bai zama sauke mu raba”
-
Shawara ga mutanen garin Gusau da su ci gaba
da riƙe kambunsu na son baƙi, da
girmamasu da kuma son dangi da halin gaskiya da riƙon amana, da
yakana da riƙon addini da dai duk sauran halaye da aka san
Gusauwa da su tun farko. Haka kuma su riÆ™e sana’o’insu
da darajja domin sana’a maganin zaman banza ce.
-
Shawara ga masu riƙe da sarautun
sana’o’in gargajiya da su riÆ™a amana ta
shugabancin da suke a kai na jagorancin masu sana’o’in gargajiya, kuma su Æ™ara
fito da wasu hanyoyin cigaba a kan wannan sana’ar da suke jagoranta.
-
Shawara ga masu sana’ar fawa, wato mahauta da
su riÆ™e sana’arsu da muhimmanci, domin sana’ar fawa
ta samo asali ne daga mutanen ƙwarai, don
haka su riÆ™e gaskiya da amana, kuma su inganta sana’arsu
ta hanyar zamananci domin komai yana tafiya da zamani ne.
-
Shawara ga Sarkin Fawa shugaban mahauta masu
sana’ar fawa, da ya fito da wasu hanyoyi da za a Æ™ara inganta
sana’ar fawa, haka kuma ya Æ™ara inganta
al’adun sarautar fawa, domin al’adu ne masu muhimmanci ba ma ga sarautar fawa
ba har ma ga al’adun rayuwarsu Hausawa, domin su na daga cikin al’adun Hausawa
waÉ—anda suka
gada tun kaka da kakanni.
-
Shawara ga É—alibai masu
nazarin harshen Hausa da su ƙara azama
wajen bincike a kan al’adun Hausawa, domin al’adu ne masu matuÆ™ar
muhimmanci, domin su ne madubin dubawa da za’a kalla a gano mai ya faru a jiya
da kuma yau.
Daga ƙarshe,
ina shawartar É—alibai da su
zurfafa bincike a kan al’adun sarautar fawa domin Æ™ara fito da
wasu muhimman bayanai masu amfani da ke ƙunshe a cikin
wannan sarautar da ma sauran sarautun sana’o’in gargajiya da suke da faÉ—in gaske,
“ruwa na Æ™asa sai ga wanda bai tona ba”.
5.4 SAKAMAKON
BINCIKE
“Kowane
al’lazi na da na shi amanu”
Wannan
bincike ya samo wasu muhimman sakamako da suke da matuƙar amfani da
suka haÉ—a da:
·
Kawo taƙaitaccen
tarihin garin Gusau domin a amfana da muhimman bayanan da ke ƙunshe
a ciki.
·
Bayani a kan mutanen garin Gusau da
sana’o’insu, domin a san su ko waÉ—anne irin mutane ne, kuma yaya
sana’o’in su suke
·
Bayani a kan ire-iren sarautun sana’o’in
gargajiya a garin Gusau.
·
Bayani a kan sarauta da amfaninta da kuma
matsalolinta da ke tattare a cikinta.
·
Kawo tarihin sarautar fawa a garin Gusau,
domin wannan bincike shi ne na farko da ya kawo tarihinta da tsarinta da
sarautunta da ma’anarta da gudumawarta da al’adunta sarakunanta da dai sauran
abubuwa da suke da alaƙa da wannan sarautar.
·
Fito da wasu al’adu da suke da muhimanci ga
sarautar fawa da kuma wadataccen bayani a kansu, da kuma kawo sunayen sarakunan
fawa da shekarun da su ka yi sarautar fawa a garin Gusau.
5.5
KAMMALAWA
“Komai ya yi
farko yana da Æ™arshe”
Wannan babi
kusan shi ne babi na ƙarshe a cikin wannan
kundin bincike da aka gudanar a kan “Sarautar fawa a garin Gusau”. Wannan babi
ya yi magana a kan jawabin kammalawa da taƙaitawa da
kuma shawarwari tare da sakamakon bincike da aka gudanar. Haka kuma wannan babi
ya kammala wannan aikin binciken, sannan ya kawo manazarta da aka yi amfani da
ita domin samun wasu bayanai.
MANAZARTA
Tuntuɓi masu gudanarwa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.