Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwatanci Tsakanin Tsakanin Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ da ‘Waƙar Lalura’

Sani, A-U. & Abdullahi, M. (2016). Kwatanci Tsakanin Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ da Waƙar ‘Lalura’. In Yahya, A. B. Journal of Hausa Poetry Studies Vol. 1, No. 3. PP 10-22. Sakkwato, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.

Kwatanci Tsakanin Tsakanin Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ da ‘Waƙar Lalura’

Abu-UbaidaSANI
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau

Da

Mansur Abdullahi
Department of Hausa Studies
College of Education, Ikere-Ekiti
Phone No: 08034402746

wakoki

1.0 Gabatarwa

            Babban yunƙurin aikin nan shi ne fito da bambanci da kuma kamanceceniya da ke tsakanin Waƙar Lalura da kuma Tabban Haƙiƙan. Aikin ya kawo taƙaitaccen tarihin marubucin waƙoƙin na asali (Shehu Usmanu Ɗanfodiyo). Baya ga haka, aikin ya kawo taƙaitaccen tarihin Isa Ɗan Shehu da kuma Nana Asma’u a matsayin masu hannu wajen fassara waƙoƙin daga Fillanci zuwa Hausa, tare kuma da yi musu tahamisi. Wato Shehu Usman a matsayin wanda ya wallafa waƙoƙin biyu, Nana Asma’u ta fassara Tabban Haƙiƙan sannan Isan Kware ya yi mata tahamisi. A ɗaya ɓangaren kuma, Isan Kware ne ya fassara waƙar Lalura daga Fillanci zuwa Hausa, sannan ya yi mata Tahamisi.[1]

            Aikin ya shafi waƙa ne, sannan rubutacciyar waƙa ba waƙar baka ba. Masana da dama sun ba da ma’anar waƙa kamar haka:

Waƙa wani furuci ne (lafazi ko saƙo) cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaitattun kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi. (Ɗangambo, a cikin Habibu, 2001).

            Haƙiƙa waƙoƙi suna taka muhimmiyar rawa wurin faɗakarwa tare da wa’azantarwa ga al’umma. Ba za a taɓa mantawa da gudummuwar rubutattun waƙoƙi ba a lokacin jihadin jaddada addinin Musulunci ƙarƙashin jagoranci Shehu Usmanu Ɗanfodiyo (Yahya, 1987; Zurmi, 2006).

1.2 Rubutacciyar Waƙa

            Masana da dama sun kawo ma’anar rubutacciyar waƙa. Wasu masanan a rubuce-rubucensu suna bambancewa tsakanin waƙa, da rubutacciyar waƙa da kuma waƙar baka. Wasu kuma suna kawo ma’anar waƙar ne kawai a dunƙule ba tare da bambancewa ko rabewa ba.[2] Habibu, 2001 ya rawaito Yahya yana cewa:

Rubutacciyar waƙa magana ce mai ƙunshe da saƙo a rubuce, da ta shafi zaɓen kalmomi da tsara su cikin tsarin da ba lallai sai sun dace da maganar yau da kullun ba. Wannan tsari yana buƙatar karin sauti da amsa-amo. (Yahya a cikin Habibu, 2001)

1.1.1 Taƙaitaccen Tarihin Rubutacciyar Waƙa

          Masana da marubuta da dama sun kawo tarihin samuwar rubutattun waƙoƙi a ayyukan rubuce-rubuce daban-daban da suka yi[3]. Sai dai wannan aikin zai kawo tarihin ne a taƙaice.

          Masana suna ƙiyasi ne kawai na lokacin da aka fara samar da rubutattun waƙoƙin Hausa. Babban linzamin wannan ƙiyasi shi ne, kasancewar ba a fara samun rubutattun waƙoƙin Hausa ba sai da Hausawa suka koyi karatu da rubutu. Wannan ya faru ne bayan sun karɓi addinin Musulunci. Wannan ne ya sa rubutattun waƙoƙin farko suka fi mayar da hankali kan faɗakarwar addini da ilmantarwa da kuma wa’azantarwa, da ma sauran jigogi da suka shafi addinin Musulunci (Habibu, 2001).

            Duk da akwai masana da suke ganin cewa addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa tun kafin ƙarni na goma sha huɗu,[4] ba a samu wata hujja da take nuna samuwar rubutattun waƙoƙi a wancan lokaci ba. Hasali ma an samu ɓurɓushin rubutattun waƙoƙin da suka fi daɗewa ne waɗanda aka yi a ƙarni na goma sha bakwai. Waɗannan ɓurɓushin waƙoƙi da aka ƙiyasta samuwarsu za su iya kasancewa tun a ƙarni na goma sha bakwai (17). Waƙoƙin sun haɗa da, Shi’ir Hausa da Jamuya na wani malami mai suna Shekh Ahmad Tila. Sai dai ba a tantance ko wane ne malamin ba. Bayan waɗannan akwai wasu waƙoƙi na Wali Ɗan Marina da kuma Wali Ɗan Masani, waɗanda aka tabbatar sun samu tun ƙarni na goma sha bakwai (17) (Habibu, 2001).

            Daga ƙarni na sha takwas zuwa na sha tara kuma, (musamman lokacin jihadi), marubuta da dama sun rubuta waƙoƙi domin faɗakarwa da kuma kiran al’umma (Birnin-Tudu, 2002)[5].

1.2 Tarihin Mawallafan Tabban Haƙiƙan da Waƙar Lalura

            Dalilin da aka ce ‘mawallafa’ ba ‘mawallafi’ ba shi ne kasancewar sa hannun wasu daban bayan asalin marubucin waƙoƙin, ma’ana fassararta da kuma yi mata tahamisi. Aikin zai kawo tarihinsu a taƙaice domin ya zama tubalin ginin bayanai game da waƙoƙin biyu.

1.2.1 Shehu Usmanu Ɗanfodiyo

          Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya fito ne daga tsatson Fulani. Sun yo hijira zuwa ƙasar Hausa ne daga Futa Toro. An haife shi a shekarar 1754 a Maratta ta ƙasar Gobir. Sai dai ya tashi ne a Ɗegel a sakamakon hijirar da iyayensa suka yi daga Maratta zuwa Ɗegel. Sannan a Ɗegel ne ya fara koyarwa da kuma wa’azi, wanda hakan ne ya kai shi ga martabar da ya samu a rayuwa (Yahya, 1987).

            Shehu ya fara karatu ne a wurin babansa. Bayan nan kuma ya yi a wurin baffansa mai suna Shekh Jibril Umar. Bayan wani lokaci kuma sai shi da sahabbansa suka fara tafiya ƙauyukan Gobir da Zamfara da kuma Kabi domin koyarwa da kuma kira zuwa ga Musulunci. Ya wallafa littattafai da dama sannan ya rubuta waƙoƙi. Abubuwan da ba za a taɓa mantawa ba game da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, sun haɗa da ɗimbin rubuce-rubucensa da kuma kasancewarsa jagoran jihadin ɗaukaka addinin Musulunci (Yahya, 1987; Birnin-Tudu, 2002).

            Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya rasu a shekarar 1817, lokacin yana da shekaru sittin da uku a duniya. Ya rasu ne a Sakkwato shekaru biyu da komawrsa nan (Sakkwato) daga Sifawa (Yahya, 1987).

1.2.2 Nana Asma’u

          Nana Asma’u ita ce ɗiyar da ta fi sanuwa a cikin ‘ya’yan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. An haife ta a shekarar 1792 a Ɗegel, wato bayan dawowar Shehu daga Zamfara inda ya yi wa’azin tsawon shekaru biyar. Ta auri Usman Giɗaɗo wanda aka fi sani da Waziri Giɗaɗo. Nana Asma’u ta rubuta waƙoƙi da dama, sannan ta fassara wasu zuwa harshen Hausa, waɗanda Shehu Ɗanfodiyo ya rubuta. Ɗaya daga cikin waƙoƙin da ta fassara ita ce Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ ta Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Daga cikin waƙoƙin da ta rubuta akwai Kiran Amada da Gwadaben Gaskiya da waɗansu daban-daban da ta rubuta cikin harshen Hausa da Fillanci (Yahya, 1987).

Bayan rubutun waƙoƙinta, ɗaya daga cikin abubuwan da za a tuna Nana Asma’u da shi, shi ne kasancewarta jagorar ‘Yan Taru. Wato ƙungiyar fafutukar ilimantar da mata. wadda ta yi ƙoƙarin haɗa kan mata tare da ilmantar da su. Nana Asma’u ta rasu a shekarar 1817 (Yahya, 1987).

1.2.3 Isa Ɗan Shehu

          An haifi Isa Ɗan Shehu a shekarar 1870, wato watanni kaɗan bayan rasuwar mahaifinsa (Shehu Usmanu Ɗanfodiyo). Yarsa (Nana Asma’u) ita ce ta riƙe shi har zuwa girmansa. Wasu masana suna ganin cewa, wannan ne ya sanya masa sha’awar rubuta waƙa, saboda Nana Asma’u marubuciyar waƙa ce (Muhammad, 1986; Yahya, 1987).

            Isan Kware shi ne ɗan auta a wurin Shehu. Ana masa laƙabi da Isan Kware ne saboda naɗa shi da aka yi Sarkin Yamman Kware. Wanda ya naɗa shi, shi ne Sultan na wancan lokaci, wato Muhammadu Bello. Isah ya fassara waƙoƙin Shehu da ma na Nana Asma’u da dama zuwa Hausa. Baya ga haka, ya yi tahamisin waƙoƙi da dama, ɗaya daga ciki ita ce ‘Tabban Haƙiƙan’ ta Shehu Ɗanfodiyo (Yahya, 1987).

            Yahya (1987) ya ce, akwai kokonto game da taƙamaimai ranar rasuwarsa. Sai dai ya ce, Ɗangambo ya rawaito Junaidu yana cewa, Isan Kware ya rasu ne a shekarar zuwa 1970. Sai dai wasu masana sunan ganin bai kai wannan lokaci ba.

1.3 Tsokaci Kan Tabban Haƙiƙan da Waƙar Lalura

          Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ ce ta fara samuwa kafin ‘Waƙar Lalura’. Ɗanfodiyo ya rubuta waƙar ne da Fillanci. Bayan wani lokaci sai Nana Asma’u ta fassara ta zuwa harshen Hausa. Daga ƙarshe kuma Isan Kware ya yi mata tahamisi. Waƙar ta kasance mai tsauri sosai, kusan babu sassauci a cikinta ko kaɗan. Za a iya lura da hakan yayin da aka dubi baitocin waƙar, wato yadda suke tabbatar da shiga wuta ga masu aikata wasu zunubai (waɗanda aka zayyano a cikin waƙar) ba tare da kawo uzuri ba (Birniwa, 2016). Ga misalin ɗaya daga cikin irin waɗanan baitoci:

Masu cin kura kasuwa duk akwai su,

Wansu keri su kai su samo bukinsu,

Wansu na nan ina faɗa ma kamassu,

Masu cin dukiya ta baital wasunsu,

            Su wuta kan ci gobe tabban haƙiƙan.

 

          A ɗaya ɓangaren kuma, Ɗanfodiyo ya rubuta ‘Waƙar Lalura’ ne sakamakon koke da sahabbansa suka yi game da tsauri na waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’. Saboda haka ne Ɗanfodiyo ya yi takwararta (Waƙar Lalura). A ciki ya nuna cewa, akwai lalura game da duka hukuncin da ya shafi kowane laifi. Misali, a baitin sama da aka kawo, an yi nunin hukuncin wuta ga masu cin dukiyar da ba ta halarta ba gare su, kai tsaye ba tare da sassauci ba. Akwai takwaran wannan baiti a ‘Waƙar lalura inda aka nuna akwai sassaucin hukunci idan dai akwai lalura. Ga misali daga cikin waƙar:

Ka jiya min abinga dut na faɗa ma,

Kada ka bar ko guda karanta ka kama,

Shaihu yac ce riƙe batun mai karama,

Dukiyaj jangali da gado ku koma,

            Har ta yaƙi wuta halam shi larura.

 

1.4 Kamanceceniya Tsakanin ‘Tabban Haƙiƙan’ da ‘Waƙar Lalura’

          Akwai kamanceceniya tsakanin ‘Tabban Haƙiƙan’ da kuma ‘Waƙar Lalura’. Wannan kamanceceniya ta shafi sigogin waƙoƙin biyu, da zubi da tsarinsu da ma tarihin rubuta su. Saboda haka, za  a iya raba waɗannan kamaceceniya ta fuskoki kamar haka:

1.4.1 Tarihin Rubutun Waƙoƙin

          Haƙiƙa idan aka bi tarihin waƙoƙin biyu za a tarar cewa suna da tushe ɗaya. Dalili kuwa shi ne, dukkaninsu biyu, marubucinsu shi ne Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. An bayyana hakan a cikin baitocin waƙoƙin biyu na kammalawa. Ga yanda abin yake:

A waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ an ce:

Shehu na yaf fa waƙi waƙa ta asali,

Nana Hausance taf fa maishe ta badali,

Isa tahmisi yay yi kau ya halili,

Ya yi Hausance kun ji shi ko dalili,

            Wa’azu na don ku ji shi tabban haƙiƙan.

 

A takwararta ma an tabbatar da Shehu ne ya rubuta ta, misali:

Shehu asalinta Isa na bi ma baya,

Don fa lada ta samu har dud da shirya,

Niy yi Hausance don darajjassu manya,

Nan da can in gane shi in samu tariya,

            Don darajassu sun bi sunna larura.

 

1.4.1.1 Fassara

          Fassarar da aka yi wa duka waƙoƙin biyu shi ma yana mazaunin wata kamanceceniya a tsakaninsu. Dukkannin waƙoƙin biyu, Shehu ya rubuta su ne da Fillanci, sai daga baya aka fassara su zuwa Hausa. A cikin waƙoƙin akwai baitoci da ke tabbatar da fassara waƙoƙin aka yi. Idan aka duba misalin da aka bayar a sama na ‘Tabban Haƙiƙan’, za a ga inda aka kawo cewa Nana Asma’u ce ta fassara waƙar. Misali:

Nana Hausance taf fa maishe ta badali,”

 

            A ɗaya ɓangaren ma, Waƙar Larura an rubuta ta ne da Fillanci, sai daga baya ne aka fassara ta zuwa Hausa. Misali:

Na gama kuma zaton da niy yo na khairu,

Shaihu Fillance yay yi to ka ji Baharu,

Taulafina garai iyaka na daharu,

Sheɗara lajju shekaran nan ta Huru,

            Cana Aljanna yo ƙida don larura.

 

1.4.1.2 Tahamisi

            ‘Waƙar Larura’ da ‘Tabban Haƙiƙan’ duka an yi musu tahamisi. Kasancewar tahamisin da aka yi wa waƙoƙin biyu na zaman wata kamanceceniya tsakanin waƙoƙin biyu (Birniwa, 2016).

1.4.2 Jigo

          Waƙoƙin guda biyu sun kasance suna da jigon wa’azi. Akwai baitoci da dama da suke nuni da hakan a cikin waƙoƙin guda biyu. Wasu daga cikin hani da aka kawo koyarwa ne daga Alƙur’ani mai tsarki, wasu kuma daga cikin hadisan Manzon Allah (S.A.W.). A cikin waƙar Tabban Haƙiƙan an faɗa ƙarara cewa:

Kun jiya wa’azu na daɗa ‘yan uwana,

An fa tasshe ku duk zumai dag ga kwana,

Don ku kau tuba kun jiya muminina,

Duk faɗin nan da anka yo gaskiya na,

            Sai fa rahama da ceto tabban haƙiƙan.

 

A ɗaya ɓangaren ma, ‘Waƙar Lalura’ tana da jigon wa’azi ne. baitocin waƙar da dama suna nuni da hakan. Misali:

Ka jiya min abinga dut na faɗa ma,

Kada ka bar ko guda karanta ka kama,

Shaihu yac ce riƙe batun mai karama,

Dukiya jangali da gado ku koma,

            Har ta yaƙi wuta halam shi larura.

 

1.4.3 Zubi da Tsari

          Zubi da tsarin waƙoƙin biyu ma na nuni da kamanceceniyar da ke tsakanin waƙoƙin biyu. Sun yi kamance da juna a fuskar amsa amo babba da ƙarami. Kowa ce waƙa tana da uwar goyon amsa amo wato kalma ɗaya ce sukutum kowa ne baiti yake ƙarewa da shi a matsayin amsa-amo, wato tabban haiƙan da lalura. Kuma kowaccensu tana da ƙaramin amsa-amo a kowane baiti. Wato kowane baiti yana da irin tasa gaɓar da yake ƙarewa da ita. Baya ga wannan, ga bisa dukkan alamu kowacensu tana hawa karin Aruli na waƙoƙin Larabci. Sannan kowace na da mabuɗi da marufi da ƙirgen lokacin wallafa na Ramzi da ambaton sunan mawallafi mai fassara da mai tahamisi. Sannan a karon farko suna da zubin tagwai. Bayan wani lokaci ne kuma aka yi musu tahamisi. Kenan a nan sun yi kamance ta ɓangaren zubi da tsarinsu.

1.4.2 Salo

          Salon waƙoƙin biyu yana ƙara danƙon kamanceceniya da ke tsakaninsu. Hasali ma dai, zamani da yanayi da ma sauran abubuwan da suka shafi rayuwar marubuci na yin tasiri a cikin waƙarsa[6] (Muhammad, 1986). Wannan ya sa dole a samu kamanceceniya ta ɓangaren salon waƙoƙin biyu, domin kuwa duka mutum ɗaya ne ya rubuta su.

1.4.2.1 Salon Wasa da Kalma

          A duka waƙoƙin guda biyu an yi wasa da kalma. Misali a waƙar Tabban Haƙiƙan ana cewa:

Masu iko su mai da himma su kyauta,

Kun jiya masu ji daɗa kada ku ɓata,

Ba ɗa tsangini garin biɗowab buƙata,

Masu matsuwat talakka ko don sarauta,

            Su ka matsuwa ga gobe tabban haƙiƙan.

 

A shaɗara ta biyu an kawo jiya, sannan aka ce masu ji. Wannan wasa da kalma ne kamar yadda aka jero cikin ɗango ɗaya. Sannan a ɗango na huɗu aka ce: “Masu matsuwat talakka ko don sarauta.” A nan matsuwa na nufin takurawa ko musgunawa. A ɗangon ƙarshe na baitin kuma sai aka ce: “Su ka matsuwa ga gobe tabban haƙiƙan.´A nan kuma kalmar matsuwa tana nufin uƙuba ta ranar gobe kiyama.

 

A ‘Waƙar Lalura’ ma akwai wurin da aka yi wasa da kalma. Misali:

Dubi aikinka aikata yo ma Allah,

Kowane kaj jiya da aikin jahala,

An faɗi ka jiya bi addin ka lela.

Maslaha an aje guda kankamala,

                                                Dai buƙata guda tana kan larura.

A ɗangon farko an yi amfani da kalmar aiki sau biyu, inda aka ce; “Dubi aikinka aikata yo ma Allah.” A ɗango na uku ma an maimaita kalmar: “Kowane kaj jiya da aikin jahala. A waɗannan ɗangogi aiki na nufin bautar Ubangiji Maɗaukaki.

 

 

1.4.2.2 Salon Aron Kalma

            Akwai wuraren da aka yi aron kalma a cikin duka waƙoƙin biyu. Misali a Tabban Haƙiƙan ana cewa:

Wanda duk ya zamo yana shina son salama

Nan da can gobe sai shi bar yin zalama,

Kwaƙ ƙi foron ga dut shina yin nadama,

Wanda yaz zam fa hakimi yay yi rahama,

            Shi ka tsira ga gobe tabban haƙiƙan.

 

            Kalmar salama wadda ta fito a ɗangon farko kalamr Larabci ce. Asalinta a Larabci shi ne salamatun, wanda ke nufin aminci ko tsira. Kalmar zalama kuwa asalinta a Larabci shi ne az-zulmu, wanda ke nufin zalunci. Asalin kalmar nadama kuwa a Larabci shi ne an-nadamu, wana ke nufin da-na-sani. Sannan kalmar rahama, asalinta a Larabci shi ne ar-rahma.

 

A cikin ‘Waƙar Lalura’ ma akwai baitoci da suke ɗauke da aron kalmomi. Misali:

Bari ƙasak kufru kar ka zamna yi ƙaura,

Wanda bai tashi duk shina cim ma sharra,

Don zaman nan cikinsa shi ag garura,

Ba halat na ba fun musulmi shi barra,

            Sai zama dole na shikai kan larura.

 

            A nan, kalmar kufru ta samo asali ne daga Larabci wato al-kufrun. Kalmar na nufin duk wani wanda bai karɓi addinin Musulunci ba. kalamr sharra kamar yadda ta zo a ɗango na biyu ta samo asali ne daga kalmar Larabci ta sharrun. Kalmar tana nufin abin ƙi ko a she sharri/sheri. Kalmar halat ma daga Larabci aka aro ta. Asalin kalmar ita ce al-halal, wanda ke nufin abin da aka amincewa. Kalamar musulmi ma an aro ta ne daga Larabci. Asalinta shi ne al-muslim, wanda ke nufin duk wani mabiyin addinin musulunci.

 

            Waɗannan misalai da ma wasu da dama da za a samu a cikin baitocin waƙoƙin suna nuni ne zuwa ga dangantaka ko kamanceceniya da ke tsakanin waƙoƙin guda biyu.

1.5 Bambance-bambance Tsakanin ‘Tabban Haƙiƙan’ da ‘Waƙar Lalura’

Haƙiƙa duk da cewa akwai alaƙa ko kamanceceniya tsakanin ‘Waƙar Lalura’ da ‘Tabban Haƙiƙan’, akwai kuma wurare da suka bambanta da juna. Waɗannan bambance-bambance za a iya karkasa su kamar haka:

1.5.1 Tarihi

          Tarihin rubuta waƙoƙin ya samar da kamanceceniya tsakaninsu ta wasu ɓangarori. A ɓangare guda kuma, tarihin ya samar da bambanci a tsakaninsu. Kamar yadda aka faɗa a sama, duka waƙoƙin an fassara su ne daga harshen Fillanci. Bambancin a nan shi ne na waɗanda suka yi fassarar. Nana Asma’u ce ta fassara ‘Tabban Haƙiƙan’, yayin da Isan Kware kuma ya fassara ‘Waƙar lalura’. Akwai baitocin waƙar da suke tabbatar da hakan. Ga nan abin da aka faɗa a ‘Tabban Haƙiƙan’:

Shehu na yaf fa waƙi waƙa ta asali,

Nana Hausance taf fa maishe ta badali,

Isa tahmisi yay yi kau ya halili,

Ya yi Hausance kun ji shi ko dalili,

            Wa’azu na don ku ji shi tabban haƙiƙan.

 

            A ‘Waƙar Lalura’ kuma cewa aka yi:

Shehu asalinta Isa na bi ma baya,

Don fa lada ta samu har dud da shirya,

Niy yi Hausance don darajjassu manya,

Nan da can in gane shi in samu tariya,

            Don darajassu sun bi sunna larura.

 

1.5.2 Salo

          Duk da cewa waƙoƙin guda biyu suna da jigo guda, akwai bambanci tsakanin yadda aka isar da saƙonnin da ke cikin waƙoƙin. ‘Tabban Haƙiƙan’ dai ta kasance mai tsauri sosai. An lissafo laifuka sannan aka tabbatar da cewa mai irin waɗannan ayyuka wuta zai shiga. A ɗaya ɓangaren kuma, ‘Waƙar Lalura’ tana da rangwame. Laifuka da dama da aka yi maganarsu, tare da nuna hukuncinsu a matsayin wuta, an nuna a cikin ‘Waƙar Lalura’ cewa, wani dalili zai iya kawo rangwame a hukunci. Misali a ‘Tabban Haƙiƙan’ ana cewa:

Wansu ko sun bi sun tsaya inda haddi,

Wadda Allahu yay yi sun yo jahadi,

Wansu ba su bi su sun ƙiya sun bi liddi,

Masu yawon gari suna yin fasadi,

            Su ka yawon wuta fa tabban haƙiƙan.

 

A cikin ‘Waƙar Lalura’ akwai takwaran wannan baiti. Sannan ya zo ne da nuni da cewa, akwai rangwame saboda lalura. Ga nan yadda baitin yake:

Anniya kan ta nan akan aikatawa,

Kowane za ka yi ka bar daƙilewa,

Bari fululu da munkari jimre kewa,

Maslaha aikata ƙi banna da kowa,

            Tsari ibada ka san ta shi al larura.

 

A wani baitin kuma na daban a cikin ‘Tabban Haƙiƙan’, an tabbatar da wuta ga mai mulki ko babba da yake danne na ƙasa da shi:

In daɗa ka zamo imamun mutane,

To tsare alhakinsu balle ubanne,

Ka ji kyauta daɗa fa don kar ka ƙone,

Wanda yaz zam imamu don cin mutane,

            Shi wuta kan ci gobe tabban haƙiƙan.

 

A ‘Waƙar Lalura’ akwai takwaran wannan baiti. A ciki ya zo da sassaucin zance. Ga baitin kamar haka:

Wanda yab bi ka duk bar sa shi kuka,

Masu iko kuna jiyawa ku falka,

Kun ji Allah abin da yac ce ku ɗauka,

Bari  walakanta wajibi kway yi suka,

Ha wuta Walla ha wuta sai larura.

 

Haƙiƙa a waɗannan misalai da ma wasu da dama da za a gani a cikin waƙoƙin, ‘Waƙar Lalura’ tana da sassaucin hukunci.

Kammalawa

          Aikin ya kawo ma’anar waƙa da ma’anar rubutacciyar waƙa, sannan taƙaitaccen tarihin samuwar rubutacciyar waƙa. Baya ga haka aikin ya kawo tarihin mutane uku – a taƙaice – da ke da hannu cikin rubutun waƙoƙin biyu. Daga nan sai aikin ya yi taƙaitaccen tsokaci kan waƙoƙin guda biyu. Haƙiƙa ‘Tabban Haƙiƙan’ da ‘Waƙar Lalura’ tamkar tagwaye suke. Baituka da dama daga cikin Tabban Haƙiƙan na da takwara a cikin Waƙar Lalura. Baya ga haka, jigon waƙoƙin wa’azantarwa ne. A ɗaya ɓangaren kuma, akwai bambanci a tsakanin waƙoƙin kamar ta wurin sassaucin da ke cikin ‘Waƙar Lalura’ koma bayan ‘Tabban Haƙiƙan’ da ke da tsauri sosai.

Shawarwari

1.      Ya kamata ɗalibai da sauran al’umma su tuna cewa, rubutattun waƙoƙi suna ɗauke da ɗimbin darrussa, ba nishaɗi kawai ba. A riƙa nazartar waƙoƙi tare da gane saƙonnin cikinsu.

2.      Malaman waƙa su ƙara ƙaimi wajen fayyace falsafar da ke cikin waƙa ga ɗalibai tare da danganta saƙonnin waƙar da rayuwar yau-da-kullum.

3.      Masana waƙa su ƙara ƙaimi wajen nuna wa marubuta waƙa irin tasirin da waƙoƙi suke da shi a cikin zukatan al’umma. Marubutan su riƙa karkata jigogin waƙoƙinsu zuwa ga abubuwan da za su kawo cigaban al’umma ba koma-baya ba.

Manazarta

Tuntuɓi masu takarda.



[1] Sai dai akwai waɗanda suke kallon cewa, Abdullahi Mai Boɗinga shi ne ya yi wa Waƙar Lalura tahamisi, ba Isan Kware ba (Birniwa, 2016). Sai dai ko ma yaya abin yake, ya tabbata cewa an fassara waƙar ne daga Fillanci zuwa Hausa sannan daga baya aka mata tahamisi.

[2] Masana da marubuta waɗanda suka yi tsokaci kan ma’anar waƙa sun haɗa da: Gusau, 1993; Ƙaura, 1994; Yahya, 1996; Bunza, 1988; Habibu, 2001; Zurmi, 2006.

[3]Daga cikinsu waɗanda suka kawo tarihin samuwar rubutacciyar waƙa akwai Habibu, 2001, da kuma musamman Birnin-Tudu, 2002 inda ya yi ƙoƙarin tattaro bayanai sosai game da tarihin samuwa da bunƙasar rubutacciyar waƙa.

[4] Wasu na ganin cewa addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa tun ƙarni na goma sha biyu. Wasu ma sun ce tun ƙarni na bakwai (Habibu, 2001). Amma akwai tabbacin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa tun zamanin sarkin Kano Ali Yaji. Wato shekarar 1349 zuwa 1385 (Birnin-Tudu, 2002).

[5] Bayan an yi nasarar jihadi, Musulunci ya yi ƙarfi, rubutattun waƙoƙi sun ci gaba da bunƙasa har aka shiga ƙarni na ashirin. Bayan nan ne kuma jigogin waƙoƙin suka bunƙasa, suka wuce iya na addini kawai, suka shafi na duniyaci (Birnin-Tudu, 2002).

[6] Saboda haka ne ma ake iya hasashen yanayin mawaƙi da yadda rayuwarsa take ta hanyar nazartar waƙoƙinsa kawai. Sannan wannan na ɗaya daga cikin abubuwan da suka bambanta waƙoƙi daga ƙarni zuwa ƙarni. Dalili kuwa shi ne, kowane ƙarni na zuwa da abin da ke jan hankalin marubuta waƙoƙin, sannan yana tasiri kan tunaninsu.

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.