Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarautar Fawa A Garin Gusau (5)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Sarautar Fawa A Garin Gusau (5)

NAABDULRASHID S. PAWA
Phone Number: 08132326047
Email: abdulrashidspawa@gmail.com

mahauta

BABI NA HUƊU

SARAUTAR FAWA A GARIN GUSAU

4.0 GABATARWA

“Matsi shi kesa kalangu Zaƙi”

Wannan babi zai yi magana ne a kan wasu muhimman abubuwa da suka ƙunshi sarautar fawa, da suka haɗa da taƙaitaccen tarihin sarautar fawa a garin Gusau da ma’ana sarautar Fawa. Haka kuma wannan babi zai yi magana da kuma wasu sarautun da ke ƙarƙashin sarautar fawa da masu tsarin sarautar fawa da kuma hanyoyin da ake bi wajen zaɓen Sarkin Fawa da masu zaɓen Sarkin Fawa tare da gudummawar da sarautar fawa ke bayarwa da kuma magungunan da sarautar fawa ke samarwa.

 

Haka kuma wannan babi zai yi magana a kan shugabancin Sarkin Fawa. Wannan babi zai yi magana a kan al’adun sarautar fawa da kuma ire-iren al’adun sarautar fawa. Daga ƙarshe wannan babi zai yi magana a kan Makaɗan Fawa da jerin sunayen sarakunan fawa a garin Gusau.

 

4.1 TAƘAITACCEN TARIHIN SARAUTAR FAWA A GARIN GUSAU 

An fara gudanar da sana’ar fawa tun bayan kafuwar garin Gusau a shekara ta (1811). Babu wanda zai bugi gaba ya ce ga adadin sarakunan fawa da aka yi tun bayan kafuwar garin, sai dai za a iya kawo kaɗan daga cikinsu waɗanda aka sani, kuma a ka samu tarihinsu.

 

Garin Gusau, gari ne da yake da tarin sana’o’in gargajiya daban-daban, mutanen garin sun shahara a kan sana’o’in da suke yi da suka haɗa da Noma, Ƙira, Fawa Wanzanci da kuma Su (kamun kifi), da sauransu.

 

Kasancewar duk sarakunan da aka yi a garin Gusau Fulani ne, amma duk da haka suna da kyakkyawar fahimta tsakanin su da mahauta hakan ma yasa ga sarki Bahillace, amma sai ya jawo mahauci ya naɗa shi Sarkin Fawa shugaban mahauta.

 

Kamar yadda tarihi ya nuna Sarkin Fawa Ummaru wanda aka fi sani da Sarkin Fawa Tsoho, shi ne Sarkin Fawa na farko a garin Gusau wanda aka samu tarihin shi ya kasance babban mahauci ne, kuma ya yi ma sarakuna hidima daidai gwargado, a shekara ta (1935). Daga baya ya sauka bisa dalilai mabambanta. Dalili na farko an ce ya sauka ne saboda wahalhalun hidimar da ake ma sarakuna baƙi waɗanda suke zuwa daga Sakkwato, ya ce shi ba zai iya ba ya sauka. Dalili na biyu ance ya ce yana son ya koma gida (daji) domin ya ci gaba da noma da kuma kiyo.

 

Bayan Sarkin Fawa Ummaru ya sauka sai aka naɗa Sarkin Fawa Muhammadu Mande Ɗan Arba a shekara ta (1940). Sarkin Fawa Muhammadu Mande Ɗan Arba babban mahauci ne mai tarin garken shanu da bisashe an ce a zamanin shi ya yi ma sarakuna hidima kuma mutum ne mai yawan alheri mai yawan kyauta da son dangi da kuma yakana. Bayan ya tsufa kwarai sai ya bayar da sarautar ga babban ɗan shi Muhammadu Ala a shekara ta (1945).

 

Sarkin Fawa Muhammadu Ala ya hau sarautar fawa a shekara ta (1945), mutun ne wanda baya da kwaramniya, amma bai daɗe kan sarautar fawa ba ya rasu a shekara ta (1955) sai aka naɗa ƙaninshi Alhaji Ibrhim Shago.

 

Sarkin Fawa Alhaji Ibrahim wanda aka fi sani da Shago ya hau sarautar fawa a shekara ta (1955). Kuma an ce “a zamaninshi ya yi ma sarakuna hidima fiye da tunani, kuma mutun ne mai kyauta da, kuma son taimakawa al’umma. Mutane da yawa a garin Gusau sun amfana da dukiyar shi wasu ma har suna cewa shi wai ko dai Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello ya ba shi mazubin kuɗin shi ne, domin ganin irin kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin su, domin idan Sardauna ya zo garin Gusau ba ya sauka ko ina sai gidan Sarkin Fawa Alhaji Ibrahim Shago. Sarkin Fawa Alhaji Ibrahim Shago, ya rasu a shekara ta (1973).

 

Bayan ya rasu sai aka naɗa ƙaninshi Alhaji Abdullahi Bawa a shekara ta (1973). Sarkin Fawa Alhaji Abdullahi Bawa an ce “a zamanin shi ya yi ma addinin musulunci hidima kuma ya taimaki al’umma da dukiyar shi, mutun ne mai son gaskiya da riƙon amana, amma bai jima ba akan sarautar sai ya ba ƙaninshi Alhaji Shehu Malami a shekara ta (1973).

Sarkin Fawa Alhaji Shehu Malami ya hau sarautar fawa a shekara ta (1973), ya yi ma sarakuna hidima, kuma an ce a zamanin shi ne a ka samu sauyi da kuma canje-canje da naɗa wasu sarautu na fawa da suka haɗa da Wakilin Fawa, Ajiyan Fawa Sarkin Zango da sauransu.

 

Sarkin Fawa Alhaji Shehu Malami, mutun ne mai tausayi da taimakon al’umma, kuma shi ne Sarkin Fawa da ya fi kowane Sarkin Fawa daɗe a kan sarautar fawa a garin Gusau a tarihin da aka samu kuma aka sani, kuma har yanzu shi ke kan sarautar fawa ta garin Gusau, Allah ya ƙara mashi lafiya da tsawon rai, amin.

____________________

 

An samu waɗannan bayanan ne a wajen mutane da a ka tattauna da su a kan tarihin sarautar fawa a garin Gusau, mutanen sun haɗa da:

1.      Sarkin Fawa Alhaji Shehu Malamai                      22/9/2019

2.      Wakilin Fawa Mustafa Ɗandada               30/9/2019

3.      Ajiyan Fawa Alhaji Sani Yaba                                01/10/2019

4.      Bello Ɗan Sarkin Fawa Ummaru Tsoho   05/04/2019

5.      Alhaji Hassan Sarkin Fawa Ibrahim                     30/06/2019

 

4.2 MA’ANAR SARAUTAR FAWA

“Ko da damina Fawa tafi noma Raggo”

Sarautar Fawa dai tana nufin mulki ko iko, wato ko kuma ɗaukar nauyin jagorancin al’umma wato mahauta ko rundawa da ta haɗa da yi masu shugabanci ta hanyar tsara hanyoyin kiyaye lafiyarsu da ta dukiyarsu, da shirya musu ƙa’idojin zaman tare ta fuskar shari’a da gudanar da hulɗa a tsakanin mahauta ko rundawa da sauran al’umma masu wasu sana’o’i na gargajiya.

 

Wanda yake yin sarauta shi ne sarki, kuma shugaba ne ga al’ummar da yake yiwa shugabanci, don haka za suyi mashi biyayya kuma suna bin umurnin shi tare da kiyaye dokoki da ƙa’idoji tare da tsarin da ya ɗaura su a kai, domin samun ci gaba a rayuwa.

 

Sarautar Fawa kamar sauran sarautun gargajiya take, kuma sarauta ce mai matuƙar muhimmanci ga rayuwar al’umma, sarautar Fawa jagoranci ce ko shugabanci ne na duk wani mahauci ko mahauta da yake gudanar da harkar sana’ar fawa. Duk wani Barundaye yana yin biyayya ga Sarkin Fawa wato shugaban mahauta, wanda ke masu jagoranci ko ya shugabancesu wajen gudanar da harkokin fawa.

 

Haka kuma sarautar da ta fi kowace muhimmanci a cikin sana’ar fawa ita ce Sarkin Fawa, wannan sarauta ana samunta ta hanyar gado, abun nufi a nan shi ne ba ko wane mahauci ke zama Sarkin Fawa ba, sai wanda yake mahaifinshi ko kakanshi ya taɓa yi, bayan an naɗa shi ya zama sarki wato sarkin mahauta, to duk sauran mahautan za su mara mashi baya, kuma su zama masu bin umurninshi ga duk wani abu da ya buƙaci su yi, za su yi shi cikin ladabi da biyayya da girmamawa da kuma darajjawa a matsayin shi na Sarkin Fawa shugaban mahauta.

 

Akwai hujjojin adabi a kan sarautar fawa daga cikin su akwai.

Karin Magana: Wata babbar taskar adabi ce ta adana muhimman abubuwa da suka ƙunshi fasahar ɗan’adam daga cikin karuruwan magana a kan sarautar fawa da kuma sana’ar fawa sun haɗa da:

1.      Daga ganin Sarkin Fawa sai miya tayi zaƙi

2.      Fawa ta gagari ‘yan fawa bare ‘yan fince

3.      Saniya ko ta lalace ta ɗau ƙahonta

4.      Sarkin Fawa rikici gado, ka sawo bashi ka sayar bashi

5.      An ce da akuya Sarkin Fawa ya mutu, ta ce “Oho ya mutu da wuƙar yanka ne?”

6.      Abun kunya nama na jan Kare

7.      Abun mamaki Kare da tallar tsire

8.      Abin duniya mene ne? Sarkin Fawa da kyautar ƙaho

9.      Ko da damina fawa tafi noman raggo

10.  Mun ƙoshi da nama, warinsa muke ji

Haka kuma akwai wata hujjar adabi a kan sarautar Fawa da ta haɗa da waƙar Dokta Mamman Shata Katsina – Ta Idi Natajo mai Saniya, Inda yake cewa:

Gindi:             Idi Natajo mai Saniya.

Jagora: Idi Natajo mai Saniya.

Y/Amshi:         Idi Natajo mai Saniya.

Jagora:            Mahautan nan masu yanka Awaki.

            :           Wuce waɗannan, Natajo ba naka ba,

            :           Irin mahautan nan masu yanka Tumaki,

            :           Wuce waɗannan Natajo ba naka ba,

            :           Kamar mahautan nan masu fawa hanji,

            :           Wuce waɗannan Natajo ba naka ba,

            :           Su na yanka ƙanana Shanun Kurmi,

            :           Idi Natajo ba naka ba,

            :           Bari sai dai ƙasar Gabas ta danno,

            :           Daɗa Idi Natajo ga naka nan.

 

4.2.1 SARAUTUN DAKE ƘARƘASHIN SARAUTAR FAWA 

“Hannu ɗaya bai ɗaukar jimka”

Akwai sarautun da Sarkin Fawa ke bayarwa ga wasu mutane, domin su taimaka mashi a kan harkokin gudanar da sha’anin sarautar Fawa da kuma ita kanta sana’ar fawa ɗin, daga cikin sarautun da ke ƙarƙashin sarautar fawa sun haɗa da:

 

Wakilin Fawa: Sarauta ce ta wakilcin wasu harkoki sarautar fawa da kuma sana’ar fawa, Wakilin Fawa shi ne mai wakiltar Sarkin Fawa ga duk wani sha’ani da ya shafi sarautar fawa da kuma sana’ar fawa a lokacin da Sarkin Fawa baya nan, ko ayyuka sun mashi yawa, ko kuma baya da lokaci, to sai ya tura Wakilin Fawa domin ya wakilce shi. Sarautar Wakilin Fawa a garin Gusau babbar sarauta ce a masarautar Sarkin Fawa, matsayin shi kamar Sarkin fawa ne, domin shi ke zama a kan kujerar Sarautar fawa idan Sarkin Fawa baya nan, kuma yana da dammar gudanar da harkokin masarautar fawa da kuma sana’ar fawa, ita wannan sarauta Sarkin Fawa ne ke bayar da ita. Akwai Wakilan Fawa da aka yi a garin Gusau da suka haɗa da:

1.      Wakilin Fawa Ɗangiwa                                          (1965 – 1980)

2.      Wakilin Fawa Ambaya                                           (1980 – 2001)

3.      Wakilin Fawa Mustafa Ɗandada               (2001 – Date)

 

Ajiyan Fawa: Sarauta ce da take cikin jerin Sarautun Fawa, masarautar Sarkin Fawa ita take da Ajiyan Fawa, Sarautar Ajiyan Fawa tana da tarihi aikin Ajiyan Fawa kamar ma’aji ne a masarautar Sarkin Fawa, Ajiyan Fawa shine mai aje duk wasu bisashe kamar tumaki, raguna, awaki, shanu da kuma raƙuma a ƙarƙashin masarautar Ajiyan Fawa a je su tun daga waɗanda suka ɓata ba a san ma su su ba, har ma da na masarautar fawa, Ajiyan Fawa shi ne mai kula da wannan lamari. Haka kuma duk wasu kuɗi da za a tara a masarautar fawa da kuma waɗanda za a taimakawa al’umma da su, to waɗannan kuɗi suma suna hannun Ajiyan Fawa, duk wani lamari na kuɗi da za a yi a masarautar fawa dama mahautu to suna cikin kulawar Ajiyan Fawa, haka kuma duk wasu harkoki na bashi kamar rancen kuɗi da kuma biyan bashi duk suna hannun Ajiyan Fawa.

A masarautar fawa, sarautar Ajiyan Fawa ita ma Sarkin Fawa ke bayar da ita, haka kuma an yi Ajiyar Fawa a garin Gusau da suka haɗa da:

1.      Ajiyan Fawa Ɗanmakwarwa                                 (1960 – 1970) 

2.      Ajiyan Fawa Ummaru                                             (1970 – 1992)

3.      Ajiyan Fawa Alhaji Sani Yaba                               (1992 – Date)

 

Sarkin Zango: Sarautar Sarkin Zango, sarauta ce da take a ƙarƙashin sarautar Fawa, aikin Sarkin Zango shi ne, idan baƙi mahauta sun shigo gari a wajen shi suke sauka su yada zango su kwana wajenshi kafin gari ya waye. Sarkin Zango shi ne ke shugabantar Kara ta Gusau, kuma basarake ne wanda duk wanda ya shigo da shanun na sayarwa yana ƙarƙashin nai, Sarkin Zango yana shari’a ga mahauta da kuma mutane masu saye da sayarwa a wannan waje, Sarkin Zango shi ne mai kula da shanu da kuma bisashe, sannan Sarkin Zango yana hukunci ga mahauta da kuma dillalai. Haka kuma duk wasu shanu da bisashe da ake tuhuma daga hukuma, ko wasu shanu da bisashe da suka ɓace wannan aiki yana ƙarƙashin sarautar Sarkin Zango, kuma ita wannan sarauta Sarkin Fawa ne ke bayar da ita  tare da amincewar Gwamnatin Jiha, domin magance cikice-cikicen harkokin saye da sayarwa na shanu da bisashe. An yi Sarakunan Zango a garin Gusau da suka haɗa da:

1.      Sarkin Zango Ƙira                                                    (1975 – 1982)

2.      Sarkin Zango Ibrahim Ƙane                                   (1982 – 2000)

3.      Sarkin Zango Bello                                      (2000 – 2019)

4.      Sarkin Zango Nasiru Mai Kwahi              (2019 – Date)

4.2.2 MASU TSARIN SARAUTAR FAWA

“Kama da wane bata wane”

Sarauta sai ɗan gado, ba kowa ne mahauci ke iya zama Sarkin Fawa ba sai wanda yake ya gaji sarautar. A taƙaice masu tsarin sarautar fawa a garin Gusau su ne waɗanda suka yi gadon sarautar daga wajen uwayensu maza ko kakannin su maza su suke da tsarin sarautar fawa a garin Gusau, domin ɗan mace baya sarauta, ma’ana ko da mutun mahaifiyarshi ya yi gadon Sarautar fawa wajen mahaifinta, ko wajen kakanta to abun da ta haifa ko da namiji ne ba zai zama Sarkin Fawa ba, don haka ɗiyan maza ke da tsarin sarautar Fawa a garin Gusau.

 

4.2.3 HANYOYIN DA AKE BI WAJEN ZAƁEN SARKIN FAWA

“Domin naman sarki na bisa karaga, ba a hana ungulu gewaye”

Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen zaɓen Sarkin Fawa, domin samun nagartaccen shugabanci ga mahauta ko rundawa. A taƙaice ba don mutun ya gaji sarauta fawa ba ake zaɓen shi ya zama Sarkin Fawa, sai idan ya cika sharuɗɗa kamar haka.

·         Hanya ta farko ana duba wanda yake shi ne babba a gida, ma’ana babban ɗan sarki na farko.

·         Hanya ta biyu ana duba cancanta, domin kowane ɗan Sarki ya cancanci zama sarki ba.

·         Hanya ta uku ana duba gwanancewa ga harkokin da suka shafi sarautar fawa da kuma harkokin gudanar da sana’ar fawa.

·         Hanya ta huɗu ana duba kamala, da jaruntaka da amana da gaskiya da tausayi da kuma adalci da sauran halaye na gari.

·         Hanya ta biyar ana duba wanda yake mai kwarjini ga jama’a wanda jama’a suke so, kuma suka yi amanna da shi.

·         Hanya ta shida ana duba mai arziki, mai kyauta wanda yake taimakawa jama’a.

 

4.2.4 MASU ZAƁEN SARKIN FAWA

“Koshin wake na ruwa ne”

Koda mutun ya gaji sarauta ba zai iya naɗa kanshi ba har sai an zaɓe shi sannan za a naɗa shi ya zama sarki. Akwai rukunin mutanen da suke da alhakin zaɓen Sarkin Fawa daga cikin su akwai, jama’a waɗanda za ai ma shugabanci, wato rundawa, ko mahauta. Idan suna son wanda zai shugabance su sai a naɗa shi, idan ba su son shi ko da an naɗa shi to za a cire shi, domin za su iya yin bore a gareshi.

 

Haka kuma daga cikin masu zaɓen Sarkin Fawa akwai Sarkin gari, ko hakimin Ƙauye, suna zaɓar wani daga cikin gidan sarautar Fawa su naɗa shi a matsayin Sarkin Fawa, shugaban mahauta wanda zai jagorancesu ya yi masu adalci tare da tsara masu dokoki domin gudanar da sana’ar fawa da kuma sarautar fawa.

 

4.4 GUDUMMAWAR DA SARAUTAR FAWA KE BAYARWA

“Kowane al’lazi da na shi amanu”

Sarautar fawa na da gudummawar da take bayarwa da ta haɗa da:

·         Samar da kuɗin shiga ga Gwamnati, domin haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa.

·         Samar da isasshen nama ga jama’a, domin sarautar fawa na tallafawa ƙananan mahauta ta basu bisashe bashi, domin su tallafawa kan su da samar da nama ga jama’a

·         Samar da nama lafiyayye: Sarautar fawa na kula da kuma kiyaye irin bisashen da mahauta za su yanka, domin kare al’umma daga kamuwa da cututtuka.

·         Samar da nishaɗi: Sarautar fawa na samar da abubuwa domin al’umma su nishaɗantu da su kamar ire-iren bukukuwan da suke yi a cikin al’amurran su na yau da kullum.

·         Samar da aikin yi: Sarautar fawa na taimakawa al’umma wajen samar masu da ayyukan yi da suka haɗa da sayar da fata, Jima da kuma Dukancin takalma da sauransu.

·         Samar da Magani: Sarautar Fawa na taimakawa al’umma wajen samar masu da wasu magunguna na wasu cututtuka da al’umma suke fama da su.

·         Samar da al’adu: Sarautar Fawa na bada gudummawarta wajen haɓaka al’adu da suka haɗa da hawan ƙaho, wasan dambe, shan gumba da sauransu.

·         Samar da ɗaukaka da martaba: Sarautar Fawa tana ƙara martabar al’ummar Hausawa, domin ita ta kasance shuganci ne na mahauta, wannan shugabanci na ƙara ɗaukaka sana’ar fawa.

·         Samar da lafiyar jiki: Sarautar Fawa na samar da lafiyar jiki ta hanyar motsa jiki da mahauta ko rundawa ke yi a lokacin da suke gudanar da al’amurransu na fawa.

·         Samar da lafiyar dabbobi: Sarautar Fawa na samar da magani ga dabbobi da kuma kula da su domin hana yaɗuwar cututtuka ga sauran dabbobi masu lafiya da kuma kare lafiyar al’umma.

 

4.3.1 MAGUNGUNAN DA SARAUTAR FAWA KE SAMARWA

Sarakunan Fawa tsofaffin mahauta ne, kuma rundawa ne da suka shahara wajen taimakama al’umma da wasu magunguna da suka shafi fannin sana’arsu da suka haɗa da:

1.      Maganin Ƙashi: Magani ne da rundawa ke bayarwa idan ƙashi ya maƙale a maƙushi, suna ba da magani a zuba a ruwa a sha, ko su yi addu’a ga dawo su ba wanda ƙashin ya maƙalema ya ci da yaddar Allah kuma a dace.

2.      Maganin Dabbobi: Magani ne mahauta ke bayarwa idan dabbar mutun ta kamu da rashin lafiya, wani lokacin idan mahauci ya shahara ko kallon dabbar ya yi yasan abun da ke damunta, kuma zai bata maganin daidai ciwonta.

3.      Maganin Suga: Magani ne da mahauta ke bayarwa ga masu ciwon suga, kuma shi wannan magani ana samunshi ne ga ɗatannar raƙumi, da kuma antar raƙumi.

4.      Maganin Shawara: Magani ne da mahauta ke taimakawa da shi ga al’ummar da suke fama da shawara, kuma shi wannan magani ana samunshi ne ga ɗatarnan Sa, ko ta Saniya sai aba mai shawara yasha.

5.      Maganin Lala: Magani ne da mahauta ke bayarwa ga yara masu ɗauke da Lala, ana basu hitsarin raƙumi suna sha.

6.      Maganin Sanyi: Magani ne da mahauta ke ba masu fama da sanyin ƙashi, ana samun wannan magani ga ɓargon Sa, ko Saniya.

7.      Maganin Ido: Magani ne da mahauta ke ba masu fama da ciwon ido, ana samun wannan magani ga wasu ruwa da ke jikin antar raƙumi, ana amfani da su cikin kwalli fari, kuma mai ciwon idon zai dinga shafa shi dare da rana.

8.      Maganin Jini: Magani ne da mahauta ke bayarwa ga wanda ya kamu da bugun jinni, suna ba da wani garin magani ga wanda bugun jini ya kama sa a bashi ya sha.

9.      Maganin Kunburin Jiki: Magani ne da mahauta ke bayarwa ga wanda yake fama da kunburin jiki, kuma da an bashi ya sha zai samu sauƙi.

10.  Maganin Nakwangwalo: Magani ne da mahauta ke taimakama yara masu fama da Nakwangwalo, shi wannan magani ana samun shi ne ga kashin raƙumi.

 

4.4 SHUGABANCIN SARKIN FAWA

“Daga ganin Sarkin Fawa sai miya tayi zaƙi”

Sarkin Fawa shi ne shugaban mahauta mai jagorantar duk wasu harkokin da suka ƙunshi sarautar fawa da kuma sana’ar fawa, Sarkin Fawa shi ne mai darajja ta ɗaya, wanda yake da ikon gudanar da mulki da tsara dokoki tare da bayar da umurni na ayi ko a bari ga mahauta masu sana’ar fawa.

 

A garin Gusau Sarkin Fawa shi ne shugaban mahauta, wanda yake shugabantar su ga duk wasu harkoki tare da wuraren da ake gudanar da harkokin fawa, daga cikin waɗannan wurare sun haɗa da:

Kwata: Wata mayanka ce babba da dubban mahauta ke taruwa, domin yanka dabbobi manya da ƙanana, a wannan mayanka Sarkin Fawa shi ne shugaba, mai ba da umurni ga mahauta masu sana’ar fawa. Haka kuma akwai harajin da duk wani mahauci yake bayarwa idan ya yi yanka a cikin kwata domin samun kuɗin shiga.

 

Kara: Wani katafaren waje ne da ake saye da sayarwa na manyan dabbobi da ƙanana kamar shanu, raguna, tumaki, awaki da kuma raƙuma. A wannan waje duk da yake akwai Sarkin Kara wato Sarkin Zango, wanda yake basarake ne a wannan waje, amma shi ma yana bin umurnin Sarkin Fawa ne, domin shi ne shugaban duk wani barundaye, ko mahauci mai saye da sayarwa a wannan waje.

 

Sauran Mahautu: Sune kamar kwata da take cikin kasuwa, ko kuma wadda take kan hanya to duk waɗannan wuraren suna a ƙarƙashin shugabancin Sarkin Fawa ne, kuma duk mahautan dake wannan waje suna masu yin biyayya ga duk wasu umurni na Sarkin Fawa shugaban mahauta.

 

Haka kuma Sarkin Fawa shi ne mai ba da damar yanka a jajibirin ƙaramar sallah da kuma babbar sallah, domin gudanar da shagulan bukin sallah, a lokacin ne Makaɗan Fawa ke taruwa kofar gidan Sarkin Fawa suna kiɗe-kiɗe irin na mahauta su na habaici da zambo ga wasu da kuma kirari da yabo.

 

Daga ƙarshe shugabancin Sarkin Fawa a garin Gusau bai tsaya nan ba, domin kuwa Sarkin fawa yana ɗaya daga cikin sarakuna masu darajja a majalisar masarautar Gusau, waɗanda ake amfani da shawarwarinsu, domin cigaban masarautar Gusau.

 

Haka kuma, a ɓangaren Gwamnatin jiha, Sarkin Fawa na taimakawa Gwamnati domin ganin an shawo kan matsalar tsaro ta sace-sacen shanu da ake fama da ita a garin Gusau da kewaye. Gwamnatin Jiha tana tuntuɓar Sarkin Fawa akan shugabancin da yake yi na mahauta da kuma masu sayen shanu, domin ba da shawarwari na yadda za a kai ƙarshen matsalar tsaro a garin Gusau.

4.5 AL’ADUN SARAUTAR FAWA

Akwai al’adu da ke ƙunshe a cikin sarautar fawa da kuma sana’ar fawa waɗanda rundawa da mahauta ke yi domin inganta sarautar su da sana’ar su da kuma al’adunsu na rayuwa, daga cikin al’adun sarautar fawa sun haɗa da: Dambe da hawan ƙaho da shan gumbu da sauransu.

 

4.5.1 IRE-IREN AL’ADUN SARAUTAR FAWA

Dambe: Dambe na ɗaya daga cikin manyan al’adun sarautar fawa, ana gudanar da was an dambe a lokacin hunturu, wato lokacin sanyi, kuma akasarin maza ne rundawa ke yin shi.

 

Ana gudanar da was an dambe ne idan aka samu ɓangarorin rundawa biyu masu hamayya da juna sai a samu makaɗa biyu masu yin kiɗa, suna kirari, idan wannan ya yi kirari, sai abokin hamayyarshi ya tashi ya ja mai kirarin da nufin su shirya su gwabza sai su kama hannuwan junansu wanda ke nuna alamun yarda kenan.

 

Daga nan ne sai a tsaida kiɗi jama’a su maida hankalinsu wurin yan wasa, yan damben za su fito tsakiyar filin su gaisa sau uku, wato su haɗa  hannuwansu sau uku daga nan sai su fara wasa suna riƙa junansu har dai ɗaya ya faɗi, faduwar shi shi, ke nuna ɗaya ya yi nasarar canye wasan.

 

Wasan dambe na da matuƙar muhimmanci ga sarautar fawa da kuma sana’ar fawa, domin yana ƙarfafa guiwa domin ganin mutun ya yi suna a cikin harkar rundanci, haka kuma wasan dambe yana hana zaman banza, yana sanya nishaɗi.

 

Rundawa na amfani da layu da tsumma da camfi da kiɗa da waƙa a lokacin da a ke gudanar da wasan dambe.

 

Hawan Ƙaho:  Hawan ƙaho wata al’ada ce da mahauta ke yi a lokuttan bukukuwan ƙaramar sallah da kuma babbar sallah. Ana shirya wasan ne domin sarki da sauran jamaa su nishaɗantu.

 

A lokacin wannan wasa na hawan ƙaho, Sarkin Fawa ya kan tanadi bajimin Sa, mai faɗan gaske wanda za a yi wasan da shi, a ɗaura mashi igiya a ƙafar baya da ta gaba, ko kuma a ƙafar baya kawai, sai wanda zai yi wasan ya shiga gaban bajinin San nan shi kuma San zai nufoshi da fushi, shi kuma wanda zai yi wasan sai ya jira isowar bajinin San a lokacin da ya iso wajensa sai shi wanda zai yi wasan ya yi tsalle ya haye saman bajinin San, shi kuma bajinin San zai yita yawo da wanda ya haushi yana ƙoƙarin kaɗa shi ga ƙasa. Ana ɗaura igiya a ƙafar bajinin Sa ne domin gudun kar ya nufi mutane da gudu ya ji masu ciwo.

 

A lokacin hawan ƙaho, Sarkin Fawa da yaransa mahauta su kan hau san da ya gagari hawa. Makaɗa da maroƙa suna kirari tare da kaɗe-kaɗe. Haka kuma rundawa na shirya wasan hawan ƙaho a lokuttan bukukuwan da suka danganci sana’ar su ba wai sai a lokutan bukukuwan sallah ba.

Shan Gumba: Wata al’ada ce da rundawa ke yi a lokuttan da suke gudanar da bukukuwansu. Farkon abin da ake tanada domin yin wannan al’adar za a tanadi gumba, a kawo ta cikin kwarya, ko cikin baho, rundawa su gewata suna sha suna rawa su kuma makaɗa suna kiɗa suna waƙa tare da kirari.

 

A lokacin da makaɗa suke kirari jikin rundawa na tsima, saboda yabo da ake masu, su kuma suna rawa suna shan gumba. Ita wannan gumba ana yin ta ne da hatsi wato gero, amma ana sa kayan koli da kuma dauri.

Al’adar shan gumba na da muhimmanci a cikin al’adun sarautar fawa da kuma sana’ar fawa domin kasancewar ita gumbar da suke sha hatsi ce kuma ana sarrafata wajen sa mata kayan koli masu sa nishaɗi da kuma lafiyar jiki.

 

4.5.2 MAKAƊAN FAWA

Makaɗan Fawa, makaɗa ne da kiɗinsu ya bambanta da na sauran makaɗa, wanda ba ayiwa kowa shi sai mahauci wanda ya gaji fawa za a tada shi ayi mai kirarin gidansu tun daga kakanninshi da uwayenshi har zuwa ga zuri’ar gidansu. Haka kuma kiɗin fawa ya bambanta da kowane kiɗi, akwai makaɗan da suke kiɗi da tasa da kuma kalangu, mata suna masu amshi a can duniyar da. Sauran makaɗan fawa suna kiɗi suna ƙirari ga abin nan na fawa da mutun ya gada.

Makaɗan fawa suna amfani da kalangu da tasa da kuma ganga domin gudanar da kiɗin fawa, kuma su kan zo da mata domin suyi masu amshi, a can da, amma yanzu maza ne kawai ke yin kiɗan fawa a garin Gusau, kuma suna amfani da ganga da kuma kalangu domin aiwatar da kiɗan. Akwai maza da kuma mata Makaɗan Fawa a garin Gusau da suke haɗa da:

Makaɗan Fawa Maza:

1.      Dakashe

2.      Jikan Karo

3.      Mamman Ɗantunƙyaso

4.      Bawa Ƙaura

5.      Sale Bunguɗu

Makaɗan Fawa Mata

1.      “Yar Modi

2.      Yar Mage

3.      Jumma ‘yar Hajiya

Kaɗan daga cikin waƙoƙin Makaɗan Fawa

Waƙar Bawa Ƙaura – Ta Shehu Malami

            Gindi:              Sarkin Yanka Shehu Malami

            ‘Y/Amshi:        Sarkin Yanka Shehu Malami

            Jagora: Shehu Mijin Binta, mai halin isa,

            ‘Y/Amshi:        Sarkin Yanka Shehu Malami

            Jagora: Sarkin Yanka Shehu Zuwaira, Alhaji Sarkin Fawa

Namairi          

            Y/Amshi          Sarkin Yanka Shehu Malami

            Jagora: Shehu Kaban mota

            ‘Y/Amshi:        Mai halin isa

Waƙar Sale Bunguɗu: - Ta Sarkin Yanka

Gindi:              Sarki Nabawa

‘Y/Amshi:        Sarki Nabawa

Jagora: Hannuka sani Nabawa Namairi

‘Y/Amshi         Sarki Nabawa

Jagora: Kayan tsire ba a yassai daji

‘Y/Amshi         Sarki Nabawa

Jagora: Duk kowa ka riƙa

‘Y/Amshi         Sarki Nabawa

Jagora  Kai adda Mahautan Gusau

Y/Amshi          Sarki Nabawa

Jagora: Ɗan Kabo takarda

Y/Amshi:         Sarki Nabawa

 

Waƙar Sale Bunguɗu – Ta Mai Kuɗɗin Gusau

            Gindi:              Mai kuɗɗin Gusau

            Jagora: Ya a sarki ni kai Nakabo Nama’a

                        :           Na’ala Komai nibbiɗa ga rai na samu

                        :           Mai kuɗɗin Gusau uban Dagaji

                        :           Datse Na’abu Sarkin Yanka Ɗankabo ƙanen Sarki Ala

                        :           Sarki Namata’a

                        :           Sarki Naburzun

                        :           Sarki Nashago

:           Na’abu Ɗanmani kar kasake Ɗanmani tafi danashar manyan shanu Ɗankabo.

                        :           In dawo ga Shehu shi as Sarki

                        :           Mai kuɗɗin Gusau uban Dagaji

 

 

4.6 SARAKUNAN FAWA A GARIN GUSAU

(Gidan Sarkin Fawa Ummaru Tsoho)

1. Sarkin Fawa Ummaru Tsoho                                                     (1935 – 1940)

(Gidan Sarkin Fawa Muhammadu Mande Ɗan Arba)

1.      Sarkin Fawa Muhammadu Mande Ɗan Arba                       (1940– 1945)

2.      Sarkin Fawa Muhammadu Ala                                               (1945 – 1955)

3.      Sarkin Fawa Alhaji Ibrahim Shago                             (1955 – 1973)

4.      Sarkin Fawa Alhaji Abdullahi Bawa                           (1973 – 1973)

5.      Sarkin Fawa Alhaji Shehu Malami                                          (1973 – Date)

 

4.7 KAMMALAWA

Wannan babi kusan shi ne jigon wannan bincike da yake da matuƙar muhimmanci. Wannan babi ya yi magana a kan taƙaitaccen tarihin sarautar fawa a garin Gusau, tare da ma’anar sarautar fawa, da kuma sarautun da ke ƙarƙashin sarautar fawa.

 

Haka kuma wannan babi ya yi magana a kan waɗanda suke da tsarin sarautar fawa, tare da hanyoyin da ake bi wajen zaɓen Sarkin Fawa da kuma masu zaɓen Sarkin Fawa da gudummawar da sarautar fawa ke bayarwa tare da magungunan da sarautar ke samarwa.

 

Wannan babi ya yi magana a kan shugabancin Sarkin Fawa da al’adun sarautar fawa tare da ire-iren al’adun sarautar fawa, daga ƙarshe wannan babi ya kawo sunayen sarakunan fawa na garin Gusau da kuma kammalawa.

Post a Comment

0 Comments