Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarautar Fawa A Garin Gusau (2)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Sarautar Fawa A Garin Gusau (2)

NA

ABDULRASHID S. PAWA
Phone Number: 08132326047
Email: abdulrashidspawa@gmail.com

Fawa

BABI NA ƊAYA

GABATARWA

1.0 GABATARWA

Bincike na ɗaya daga cikin muhimman abubuwa da suka shafi tafiyar da rayuwa, babu wani abu da za a samo, ko a gano sabo ba tare da bincike ba. Bincike shi ne mataki na farko da ake bi domin samo, ko fito da wani abu sabo wanda ba’a san shi ba, kuma ake son a san shi a kuma samar da shi, domin a yi amfani da shi ta wasu hanyoyi daban-daban na rayuwa.

 

Wannan babi zai yi magana a kan wasu matakai daya da ce mai bincike ya bi domin gudanar da kowane irin bincike da suka haɗa da; dalilan gudanar da bincike, farfajiyar bincike, hanyoyin gudanar da bincike, muhimmancin bincike matsalolin bincike da kuma tambayoyin bincike.

 

1.1 DALILAN GUDANAR DA BINCIKE

Babu wani bincike da za a yi ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, domin kuwa ana yin bincike ne don a gano wani abu sabo a fito da shi domin a amfana da shi, daga cikin dalilan da ya sa aka gudanar da wannan bincike ya haɗa da:

 

-          Domin samun takardar shaidar kammala karatun digiri na ɗaya (B.A), domin samun damar cigaba da karatu na gaba.

-          Domin zurfafa bincike don samun bayanai a kan sarautar Fawa, domin dalibai masu nazari a kan harshen Hausa su amfana da shi.

-          Domin bayani a kan irin gudummawar da sarautar fawa ke bayarwa.

-          Domin fito da kyawawan al’adun da ke ƙunshe a cikin sarautar fawa.

-          Domin bayani akan taƙaitaccen tarihin sarautar fawa. Domin bayani a kan takaitaccen tarihin garin Gusau tare da bayyana ire-iren sana’o’insu.

-          Domin bayani akan ire-iren sarautun gargajiya da muke da su, domin a san da irin gudummawar da suke bayarwa.

-          Domin bincike a kan ire-iren sarautu, sana’ar fawa, da kuma bukukuwansu.

-          Domin bincike a kan duk wani abu da ya shafi sarautar fawa.

-          Domin bayani a kan jagoranci da sarakunan fawa suke yi ga jama’arsu wato rundawa.

-           

1.2 FARFAJIYAR BINCIKE

Wannan bincike da za a gudanar ya taƙaita ne a cikin garin Gusau, ma’ana duk wani bincike da za’a yi za a yi shi ne a cikin garin Gusau, farfajiyar bincike za ta taƙaita ne a masarautar Sarkin fawa da kuma duk wasu ɓangarori da suka shafi sarautar fawa da suka haɗa da.

 

Masu riƙe da sarautun fawa, Makaɗan Fawa, Kara da ke garin Gusau, Kwata da ke garin Gusau, masu sana’ar fawa, tsofaffin masarautun fawa, wurarenda ake gudanar da duk wasu harkokin fawa, gidan Sarkin Zango, gidan Wakilin Fawa, gidan Ajiyan Fawa da duk wasu abubuwa da suka shafi sarautar fawa. Haka kuma farfajiyar wannan bincike za ta taƙaita a cikin Kundaye, Jaridu da kuma bugaggun littattafai da suke da alaƙa da wannan bincike.

 

1.3 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE  

Ko wane bincike yana da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da shi, daga cikin hanyoyin da aka bi sun haɗa da. Bincike a cikin kundaye, Jaridu da kuma bugaggun littattafai da suka haɗa da.

 

Gusau ta Malam Sambo, Mai Dubun Nasara, Bukukuwan Hausawa, Rayuwar Hausawa, Gusau ta Malan Sambo Sabon Bugu, Gadon Feɗe Al’ada, Dabarun Bincike, Zaman Mutun da Sana’arsa, Darussan Hausa 1,2,3. Haka kuma an yi bincike a cikin Kundaye da suke haɗa da Mustapha Sa’idu (2013) da Hassana Abubakar Tunau (2003). Ɓangaren Jaridu kuma an duba Jaridar Leadership Hausa (2019), da kuma Jaridar Aminiya (2019). Bayan haka wannan bincike ya bi wasu hanyoyi, domin gudanar da shi da suka haɗa da:

 

Takardun Sarkin Fawa Bawa Gusau waɗanda suke ɗauke da bayanai a kan sarautar fawa da tattaunawa da mutane, akwai tattaunawar da aka yi da mutane da suke da alaƙa da sarautar fawa da suka haɗa da. Sarkin Fawa Alhaji Shehu Malami, masu riƙe da sarautun fawa kamar Wakilin Fawa, Ajiyan Fawa, Sarkin Zango, Makaɗan Fawa, tsofaffin mahauta da kuma rundawa masu sana’ar fawa.

 

Ta ɓangaren ziyarori sun haɗa da: Ziyara gidan Sarkin Fawa tsoho da ziyara zuwa Kar da kwata da ZACAS da FCET da kuma masarautar Gusau. Waɗannan sune hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan bincike.

 

1.4 MUHIMMANCIN BINCIKE

Ba wani abu da za a ɗauki lokaci ana zurfafa bincike a kanshi ya zama ba mai muhimmanci ba, domin ana bincike ga wani abu mai muhimmanci da za a amfana da shi.

 

Muhimmancin bincike a fili yake, domin duk wani abu da aka binciko sabo aka ganshi aka sanshi aka jishi ko, kuma aka fahimce shi aka yi amfani da shi to wannan bincike ya zama mai muhimmanci.

 

Muhimmancin bincike ya zama tamkar hantsi leƙa gidan kowa domin duk abun da ya shige ma mutum duhu daga baya ya yi bincike a kanshi ya fahim ce shi wanda da can bai fahimce shi ba to wannan bincike ya zama mai muhimmanci a gare shi, musamman ɗalibai masu nazari a kan fannoni na fasaha da ilimi, da kuma nazarin harshen Hausa.

 

Muhimmancin bincike shi ne bayar da wata gudummawa a fagen ilimi ta hanyar gano ko samo wani abu sabo domin a amfana da shi.

 

1.5 MATSALOLIN BINCIKE

Duk wani abu da za a yi bincike akan shi ba zai rasa wasu matsaloli da aka fuskanta ba a lokacin da ake gudanar da shi. Matsalolin da ake fuskanta sun haɗa da. Rashin samun wadatattun littattafai da ke da alaƙa da bincike. Saɓa lokacin da za a tattauna da mutane, wasu mutanen suna saɓa lokacin da suka bayar domin tattaunawa da su.

 

Bincike a kan abun da bai shafi aikin mutun ba, wani lokacin mutun kan zurfafa bincike a kan wani abu daga baya ya fahimci baya da alaƙa da wannan bincike. Rashin isassun kuɗi, domin cigaba da gudanar da bincike, ita ma babbar matsala ce, domin kusan duk wani abu da za a yi sai anyi amfani da kuɗi.

 

Ganawa da mai duba bincike, rashin samun ganin wanda yake duba aikin bincike ita ma babbar matsala ce, domin a kan ɗauki tsawon lokaci ba a kammala bincike ba.

 

1.6 TAMBAYOYIN BINCIKE

Tambayoyin bincike sun ƙunshi duk wasu abubuwa da suke da alaƙa da bincike, tambayoyi sun haɗa da;

Taƙaitaccen tarihin sarautar fawa da sarautunta da al’adun sarautar fawa da sauransu. Akwai tambayoyin bincike da aka tattauna da mutane, daga cikin su akwai tambayar suna da shekaru da sana’a da kuma mazaunin wanda aka tattauna da shi. Haka kuma akwai wasu tambayoyin bincike da suka haɗa da.

 

Taƙaitaccen tarihin sarautar fawa a garin Gusau da ma’anar sarautar fawa da sarautun da ke ƙarƙashin sarautar fawa da masu tsarin sarautar fawa da hanyoyin da ake bi wajen zaɓen Sarkin Fawa da masu zaɓen Sarkin Fawa da gudummawar da sarautar fawa ke bayarwa da magungunan da sarautar fawa ke samarwa da shugabancin Sarkin Fawa da al’adun sarautar fawa da ir-iren al’adun sarautar fawa da Makaɗan Fawa da kuma sarakunan fawa a garin Gusau. Waɗannan sune tambayoyin da suka shafi wannan binciken da za a yi.

 

1.7 KAMMALAWA

Wannan babi ya yi magana a kan wasu hanyoyi da ake bi domin shirya bincike sun haɗa da; dalilan gudanar da bincike, farfajiyar bincike, hanyoyin gudanar da bincike da kuma tambayoyi yin bincike, waɗannan su ne abubuwa masu muhimmanci domin gudanar da kowane irin bincike.

Post a Comment

0 Comments