Sarautar Fawa A Garin Gusau (3)

    Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

    fawa

    Sarautar Fawa A Garin Gusau (3)

    NA

    ABDULRASHID S. PAWA
    Phone Number: 08132326047
    Email: abdulrashidspawa@gmail.com

     

    BABI NA BIYU

    WAIWAYE A KAN AYYUKAN DA SUKA GABATA

    ”RUWA NA ƘASA SAI GA WANDA BAI TONA BA

    2.0 GABATARWA

    Wannan babi zai yi magana ne akan wasu ayyukan da suka gabata, domin an ce waiwaye adon tafiya, kuma lafiya da waiwaye na maganin mantuwa. Daga cikin ayyukan da wannan babi zai yi magana akansu, sun hada da. Kundayen bincike, Jaridu da kuma bugaggun littafai.

     

    2.1 WAIWAYE AKAN AYYUKAN DA SUKA GABATA

    Babu shakka wajibi ne ga duk wani mai bincike tilas ne ya waiwaya baya, domin, duba wasu ayyukan da suka gabata domin yasan inda aka kwana ko aka tsaya.

     

    Ta hanyar duba ayyukan da suka gabata ne mai gudanar da bincike yake samun kwarin guiwa, wajen gudanar da bincikenshi ta hakan ne zai É—auki wasu ayyukan ko kuma ya gina wasu da ba su ba.

     

    2.1.1 KUNDAYEN BINCIKE

    A cikin ayyukan da a ka duba akwai:

    Tunau H.A (2003). A cikin kundin ta kawo ma’anar fawa da asalin sana’ar fawa da yadda ake gudanar da sana’ar fawa da kayayyakin aikin sana’ar fawa da masu yin sana’ar fawa da muhimmancin sana’ar fawa da rashin muhimmancin sana’ar fawa, da kuma al’adun sana’ar fawa.

     

    Wannan aikin nata yana da matuÆ™ar alaÆ™a da binciken da za a yi, domin tayi bayani a kan sarautar fawa da kuma wasu sarautun sana’ar fawa, amma bata zurfafa bincike a kan sarautar fawa ba

     

    Haka kuma an duba kundin; Shamsu, Z. da Wasu (1988). A cikin wannan kundi an kawo ma’anar fawa, da al’adunta na da da na yanzu. An Æ™arfafa bayani a kan kayan da ake amfani da su a cikin mahauta, ko wajen sana’ar fawa da wuraren da ake gudanar da ita.

     

    Wannan aiki yana da alaÆ™a da binciken da za a yi, domin sana’ar fawa ita ta samar da sarautar Fawa, sai dai mai wannan kundin bai yi magana akan sarautar fawa ba, a nan ne binciken da za a yi suka bambanta.

     

    Sai wani kundi da aka duba na; Wada, A. (2003). A cikin wannan kundi an bayyana irin sauye-sauyen da sana’ar fawa ta samu, da kuma tasirin zamananci a cikin sana’ar fawa.

     

    Shi wannan aiki yana da alaÆ™a da binciken da za a gudanar, amma sun bambanta, domin shi mai wannan kundi ya yi bincikensa ne a kan sana’ar fawa, a wannan binciken za a duba sarautar fawa, alaÆ™ar su ita ce dukkansu suna magana ne a kan harkar fawa.

     

    Daga nan kuma an duba kundi; Bala, M.Z da wasu (1997). A wannan kundi an bayyana ire-iren sana’o’in Hausawa kamar Noma, SaÆ™a, Æ™ira, Fawa, da kuma jima da sauransu. Sannan kuma an yi magana akan sana’ar fawa, amma bayyi bayani a kan sarautar fawa ba, alaÆ™ar wannan aiki da binciken da za a gudanar ita ce fawa, amma sun bamban, domin mai wannan kundin bayyi cikakken bayani a kan sana’ar fawa da kuma sarautar fawa ba.

     

    2.1.2 JARIDU

    A É“angaren jaridu da suka yi magana a kan sana’ar fawa, da kuma sarautar fawa daga cikin su akwai.

    Rabi’u, N (2019) ya ce “Sana’ar fawa na da matuÆ™ar muhimamnci ga rayuwar kowa ce al’umma, haka kuma ya ce ita sana’ar fawa sana’a ce ta dogaro da kai wadda take da darajja.

     

    Ita wannan tattaunawa da jaridar leadership Hausa ra’ayi da  Malam Rabi’u Nasiru tana da alaÆ™a da binciken da za a yi, domin ita sana’ar fawa ita ce Æ™ashin bayan sarautar fawa.

     

    Usman (2019) ya ce “Sarautar Fawa amana ce a masarautar katsina” ita shugabanci ce da ake bayarwa domin samun cigaban sana’ar fawa. Daga nan da a cikin bayaninshi da ya bayyanawa É—an jaridar wasu muhimman abubuwa dangane da sarautar fawa, daga cikin su akwai; Asalin sarautar fawa da muhimmancinta da kuma nasabarta da masarautar Katsina, amma bai zurfafa bayani ba a kan sarautar fawa.

    Ita wannan tattaunawar tasu tana da alaƙa da binciken da za a yi sai dai sun bambanta domin tana magana a kan sarautar fawa a garin Katsina, wannan kuwa ya taƙaita a kan sarautar fawa a garin Gusau ne. Alaƙar su ita ce duk suna magana ne akan sarautar fawa.

     

    2.1.3 BUGAGGUN LITTATTAFAI

    Alhassan H. da Wasu (1982). A cikin wannan littafi a shafi na (51) an bayyana ma’anar sana’ar fawa da muhimmancin sana’ar fawa da ire-iren kayan aikin sana’ar fawa da kuma nau’o’in mahauta manya da Æ™anana.

     

    Wannan littafi yana da alaƙa da binciken da za a yi, amma sun bambanta, domin shi binciken da za a yi yana magana ne a kan sarautar fawa, alaƙarsu ita ce duk suna magana ne akan harkar fawa ne.

     

    Haka kuma an dubi wani littafi na Yahaya I.Y da Wasu (2007). A cikin wanan littafi a darasina bakwai shafi na (48-60), an kawo ma’anar sana’a da ire-iren sana’o’in gargajiya da masu sana’ar da kuma yadda suke gudanar da ita. Haka kuma an kawo ire-iren sarautun da ake samu a cikin kowace irin sana’a ta gargajiya.

     

    Wannan littafi yana da alaÆ™a da binciken da za a yi, amma sun banbanta, domin shi littafin yana magana ne a kan sana’o’in gargajiya, amma alaÆ™arsu ita ce ya yi magana a kan sana’ar Fawa da sarautarta, amma bai zurfafa bayani ba a kan sarautar fawa ba.

    Littafi na gaba da a ka duba shi ne; Ingawa, A da wasu (1948). A cikin wannan littafi an yi bayani a kan sana’o’in gargajiya, haka kuma an bayyana cewa dukkan sana’o’in sun samo asali ne daga sana’ar Noma.

     

    Wannan littafi yana da alaÆ™a da binciken da za a yi, amma sun sha bamban, domin shi yana magana ne a kan sana’o’in gargajiya ne, shi kuma binciken da za a yi taÆ™aita ne a kan sarautar fawa, alaÆ™arsu ita ce sana’ar gargajiya ita ta samar da duk wasu sarautun gargajiya da muke da su na shugabanci a kan sana’ar.

     

    Littafi na Æ™arshe da aka duba, shi ne; Yahaya, I. Y. da Wasu (1992). A cikin wannan littafi a darasi na tara shafi na (73-75) an yi magana a kan ma’anar sarauta da asalin sarauta da tsarin sarauta da gudanar da masarauta da duk wasu abubuwa da suka shafi sarautar gargajiya.

     

    Wannan littafi yana da alaÆ™ da binciken da za a yi, domin ya yi magana akan wasu sarautun gargajiya da kuma ma’anarta sarautar da tsarinta, amma wannan littafi ya bambanta da binciken da za a yi domin shi ya yi magana a kan sarautar gargajiya, shi kuma binciken da za a yi yana magana ne a kan sarautar fawa. AlaÆ™arsu duk suna magana ne a kan sarautar gargajiya.

     

    2.3 KAMMALAWA

    Wannan babi ya yi magana akan wasu muhimman ayyukan da suka gabata. Wannan babi ya yi waiwaye adon tafiya, domin tafiya da waiwaye na maganin mantuwa, domin sanin ina aka kwana ina kuma za a tashi. Daga cikin ayyukan da aka duba sun haÉ—a da: Kundaye, Jaridu, da kuma bugaggun Littafai.

    1 comment:

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.