Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarautar Fawa A Garin Gusau (1)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Sarautar Fawa A Garin Gusau (1)

NA

ABDULRASHID S. PAWA
Phone Number: 08132326047
Email: abdulrashidspawa@gmail.com

Mahauta

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aikin bincike ga mahaifina Sarkin Fawan Gusau Alhaji Abdullahi Bawa (Allah ya jiƙanshi da rahama amin) da kuma mahaifiyata Hajiya Halima Abubakar Bube Sarkin Bazai Jangeru (Allah ya ƙara mata lafiya da tsawon rai amin), bisa ga ɗaukar ɗawainiyar tarbiyata da ta karatuna, domin ganin na zama mutum nagari wanda za su yi alfahari dashi, kuma al’umma ta amfana, Allah ya saka masu da mafificin alheri da samun dacewa da gida aljanna Firdausi amin.

GODIYA

Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah Muhammad ɗan Abdullahi (SAW) da sahabbansa da iyalan gidansa da waɗanda ke koyi da su ya zuwa ranar sakamako.

 

Da farko ina matuƙar godiya ga mahaifina Sarkin Fawan Gusau Alhaji Abdullahi Bawa (Allah ya jiƙanshi da rahama amin), da kuma mahaifiyata Hajiya Halima Abubakar Bube Sarkin Bazai Jangeru (Allah ya ƙara mata lafiya da tsawon rai amin) bisa ɗaukar ɗawainiyar tarbiyata da ta karatuna Allah ya saka masu da mafificin alheri amin.

 

Haka kuma ina godiya ga uwayena maza da mata, Sarkin Fawan Gusau Alhaji Shehu Malami, da Alhaji Garba Ibrahim (Garba Manager), da Hajiya Hadiza Muhammad Shagamu, bisa taimakona da suka yi a kan karatuna, Allah ya saka masu da alheri amin.

 

Ina miƙa godiya ga ‘yan uwana maza da mata, Alhaji Hassan Ibrahim S/Pawa da Alhaji Kabiru S/Pawa (KSP) da Abdulrahman S/Pawa da Abdulgaffar S/Pawa da Hajiya Shafa’atu S/Pawa nagode da gudummawar da kuka bani a lokacin karatuna Allah ya saka maku da alheri amin.

 

Ina miƙa matuƙar godiya da jinjina ga babban Malamina, kuma yayana malami uban malamai Farfesa Aliyu Muhammad Bunza shi ne wanda ya karantar da ni ya bani ilimi mai tarin yawa, kuma ya duba ni a lokacin da nake gudanar da wannan aikin bincike. Allah ya ƙara mashi sani da ɗaukaka da lafiya da tsawon rai ya kuma saka ma shi da mafificin alheri, amin.

 

Haka kuma ina godiya ga malamai na waɗanda suka karantar da ni kuma suka nuna min hanya ta gari, malan Rabi’u Aliyu Ɗangulbi, malan Musa Abdullahi Zaria, malan Isah Sarkin Fada, Allah ya biyasu da alheri amin.

 

Ina miƙa matuƙar godiya ga manyan malamai na waɗanda suka koyar da ni karatu mai tsada, Farfesa Ahmad Halliru Amfani da Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa da Farfesa Abdulhamid Ɗantunbishi da Farfesa Adamu Ibrahim Malumfashi da Farfesa Magaji Tsoho Yakawada da Farfesa Muhammad Lawal Amin da Farfesa Abdullahi Balarabe Zaria, Allah ya saka masu da mafificin alheri amin.

 

Haka kuma ina godiya ga malamai na, Dokta Yakuba Aliyu Gobir da Dokta Abdullahi Sarkin Gulbi da Dokta Adamu Rabi’u Bakura da Dokta Nazir Ibrahim Abbas da Dokta Musa Fadama da malan Haruna mai kwari da malan Abu-Ubaida dukkansu Allah ya saka masu da alheri amin.

 

Ban manta da ku ba malamaina, na sashen Ingilishi, ina godiya a gareku Dokta Shehu Ibrahim Sidi da Malam Mudassir Isma’il Moyi Kaura da malan Kabiru Musa Mafara da malan Sani Galadima da Farfesa Ɗahiru Muhammad Argungu da Dokta Ango Aleru Allah ya biyasu amin.

Ina godiya ga malamaina na sashen Haɗakar Darussa Dokta Rabi’atu da Dokta Giɗaɗo da sauran su, Allah ya saka masu da alheri amin.

 

Ba zan taɓa mantawa da kuba, kuma ina miƙa matuƙar godiya maras adadi ga abokan karatu na, Nasiru Hassan Kabara (Class-Rep), ina jinjina ma a kan namijin ƙoƙarin wakilcinmu da kayi tun tsawon shekaru huɗu (2015 – 2019), Allah ya biya ka da alheri amin. Haka kuma ina godiya ga Sani Adamu (Malan Bala) da Ahmad Muhammad Kabir (MK) da Bashar Isyaƙu (BI) da Abdulrahman Bala Garba Tsafe (ABG) da Hassan Galadima (Sarkin Hausawa) da Ɗayyaba Mustapha Ibrahim (Allah ya jiƙan Mahaifiyarta amin).

 

Ina miƙa matuƙar godiya ga Mustapha Sa’idu Faskari (Faskari II) da Abubakar Hassan Faskari (Faskari I) da Amina Abubakar Moriki (Ɗanmoriki) da Aliyu S. Ibrahim (Alikuwa) da Hizbullahi Ɗanlami Kura da Nura Sani Kwatarkwashi dukkan su Allah ya saka masu da mafificin alheri ya kuma ƙara danƙon zumunta ta zama sanadiyar shigarmu aljannah Firdausi, amin.

 

Ɗan da ba na kwaraiba shi ke manta mafari ban manta da ku ba malamai na da abokan karatuna na Muslim Foundation Nursery and Primary School Gusau (1999 – 2005). Da kuma malamaina da abokan karatuna na College of Islamic Science Gusau (2005 – 2011) dukkansu ina godiya a garesu Allah ya saka masu da alheri ya kuma ƙara danƙon zumunta amin.

 

Daga ƙarshe ina miƙa matuƙar godiya ga duk wanda ko wadda ta / ya taimakamin a rayuwata daban samu dammar kiran sunansu ba, Allah ya saka masu da alheri amin.

TSAKURE

Wannan kundin bincike, ya yi maganganu a kan muhimman ɓangarori daban-daban da suka haɗa da dalillan gudanar da bincike, da farfajiyar bincike da hanyoyin gudanar da bincike da muhimmancin bincike da matsalolin bincike da kuma tambayoyin bincike, sannan an yi waiwaye a kan ayyukan da suka gabata, kamar kundaye da jaridu, da kuma bugaggun littattafai. Haka kuma wannan kundin bincike ya yi magana a kan taƙaitaccen tarihin garin Gusau da mutanen da ke ciki da kuma sana’o’insu da sarautunsu na gargajiya tare da ma’anar sarautar da amfaninta da matsalolinta. Haka wannan kundin bincike ya yi magana a kan taƙaitaccen tarihin sarautar fawa a garin Gusau da duk wasu lamurra da suke da alaƙa da ita, kamar sarautun da ke ƙarƙashinta da tsarinta da kuma al’adun da ake samu a cikinta da sauransu. Daga ƙarshe wannan kudin bincike ya yi magana a kan jawabin kammalawa da taƙaitawa da shawarwari da kuma sakamakon bincike da aka samo tare da manazarta.

Post a Comment

0 Comments