Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazari Kan
Jawabin Kama Aiki Na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019
(6)
NA
NASIRU HASSAN
BABI NA BIYAR
KAMMALAWA
5.0 GABATARWA
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai, Ubangijin dukan halittu, wanda ya kasance tun kafin
kasancewa ta kasance.
Salati da ɗaukaka su ƙara
tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu (SAW), da alayensa da sahabbansa da masu
binsu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
A wannan babi na ƙarshe, za a
gabatar da wasu ‘yan shawarwari ga ‘yan uwa ɗalibai da
jawabin taƙaitawa da na kammalawa da ta’arifin wasu
kalmomi da rataye da kuma manazarta wato ayyukan da aka duba domin ƙarin
bayani.
5.1 TAƘAITAWA
A wannan mataki, an taƙaita dukkan
abubuwan da suka faru a cikin nazarin kasancewar kowane farko na da ƙarshe,
saboda haka, wannan ɓangare na bayani kan abubuwan da aka yi ne a
taƙaice.
Wannan aiki an kasa shi gida biyar, sannan
akwai manazarta da rataye. A babi na farko ya ƙunshi
gabatarwa, dalilin gudanar da bincike, muhallin bincike, manufar bincike,
hanyoyin gudanar da bincike, muhimmancin bincike, farfajiyar bincike,
matsalolin bincike da kammalawa. A babi na biyu ya ƙunshi bitar ayyukan
da suka gabata wanda ya haɗa da gabatarwa da waiwaye kan ayyukan
da suke da alaƙa da wannan, kamar bugaggun littafai,
kundayen bincike, kundain digiri na biyu da kuma maƙalu da
kammalawa. A babi na uku ya ƙunshi
gabatarwa, taƙaitaccen tarihin jihar Zamfara, yawan jama’a,
albarkatun ƙasa, sana’o’i yanayinta, ma’anar harshe,
ma’anar siyasa, yaɗa labarum siyasa, kafuwar jam’iyyun siyasa,
lafazin siyasa da manufarta a siyasance da kuma kammalawa. A babi na huɗu, ya ƙunshi
gabatarwa, maanar salo, salo da siyasa, salo da lafuzzan siaysa, salo da
sarrafa harshe, sai nazarin jawabin kama aiki na zaɓaɓɓun gwamnonin
jihar Zafmara a shekarar 2007 da 2011 da kuma 2019. Sai kammalawa. A babi na
biyar kuma ya ƙunshi gabatarwa, taƙaitawa,
shawarwari, jawabin kammalawa, ta’arifin wasu kalmomi, rataye da manazarta.
5.2 SHAWARWARI
Ana iya ba da shawara cewa, siyasa abu ce mai
amfani, amma idan ta karkata ga ba da gudummuwa ga al’umma, ba neman matsayi da
gina kai ba. Maƙasudin yin siyasa shi ne samun ra’ayoyi
daban-daban masu nufin gina al’umma da ƙasa. Abu na
farko shi ne samun kafofin gudanar da zaɓuka da mutane na gari
su shugabanci al’umma. Yana da kyau a cigaba da ilmantar da al’umma, ilimi
ingantacce, wanda zai canja tunanensu daga son kai zuwa son ƙasa.
Shi wannan ilimi ya ƙunshi na addini da na
zamani. Ba a samun cigaba da ƙarya da zamba
da son kai da cuta da sata da ƙarɓar rashawa.
Duk waɗannan na danƙwafe
ƙasa da sana’o’inta da tattalin arzikinta, ta
koma ƙasa maras amfani.
Sannan akwai buƙatar son
harshen da mutum ya tashi da shi, domin shi ne kawai zai fahimtar da shi sosai
game da rayuwa da kuma muhimmancinta ta hanyar al’adunsa. Wannan na cikin
illolin da siyasa ta haifar mana, rashin samun harshe na ƙasa sai da
aka aro na turawa, wanda masu amfani da shi basu da yawa. Duk da cewa ana
amfani da harsunan iyaye wajen jawaban siyasa, iyakarsu nan, idan aka tafi
majalisa da kotu da harkokin gwmanati duk da turanci ake yi, wanda ‘yan boko
kawai ke fahimta. Saboda haka, akwai alamar son kai na cewa su kaɗai ke iya wa,
wato su za su yi ko yaushe.
5.3 JAWABIN KAMMALAWA
Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah
Ubangijin halittu, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu da
Alayensa da sahabbansa da masu binsu da kyautatawa har zuwa rana sakamako.
Masu iya magana kan ce “Komai ya yi farko to
zai yi ƙarshe, tafiya ta yi tafiya, tun ana tunanen
irin batun da za a bayar har zuwa yadda za a tattara bayanan su zamo abin da
suka zama ga shi Allah ya yarda an zo ga fagen yin jawabin kammalawa.
A taƙaice dai an
kutsa ga masana daban-daban kuma an yi ƙoƙarin
fito da bayanai dangane da wannan bincike waɗanda ake
ganin masu alfanu ne ga al’umma da ɗaliban ilimi kamar yadda masana suka
yi bayani kan a bin da ya shafi tarihin Zamfara da ma’anar siyasa da shugabanci
da ma wasu abubuwa da dama da aka yi bayani a baya. Wannan aikin an ba shi
taken “NAZARI KAN JAWABIN KAMA AIKI NA ZAƁAƁƁUN
GWAMNAN JIHAR ZAMFARA DAGA SHEKARAR 2007 – 2019”.
A nan wannan bincike ya kawo ƙarshe
da aka gudanar, muna roƙon Allah (SWT) ya sa
shi mai amfani a garemu da kuma ɗaukacin al’umma gaba ɗaya, ya kuma
sa ya zama sanadin ɗaukakar harshen Hausa a faɗin duniya.
Sakamakon da wannan aiki ko bincike ya gano
shi ne:
·
Ta hanyar wannan nazari an gano irin yadda zaɓaɓɓun Gwamnoni
ke gudanar da jawabansu da irin alƙawuran da
suke yi zuwa ga al’ummarus, da kuma yadda suke ƙoƙarin
cika alƙawuran
·
Haka ma an gano ta hanyar wannan bincike irin
muhimmancin da ke tattare wajen nazartar irin waɗannan
jawabai, domin ta hanyar nazari ne ake fito da ɗimbin abubuwa
da suka shafi harshe da salo da kuma sarrafa harshe.
·
Haka kuma ta hanyar wannan nazari an gano
irin kalaman da ‘yan siyasa kan yi amfani da su musamman gwamnoni, wajen jawo
hankalin jama’arsu don su yarda da abin da suke faɗa.
5.4 TA’ARIFIN WASU KALMOMI
1. Alaye = Iyalan gidan Annabi (SAW)
2. Bagire = Wuri
3. Bincike = Nazari
4. Farfajiya = Muhalli, Haraba
5. Gudana = Cigaba
6. Tuntuɓa = Bibiya
7. Sigogi = Ire-ire
8. Mu’amala = Hulɗa
9. Maƙasudi
= Manufa
10. Rangwame = Jinƙai,
tausayi, nasiha, sauƙi
11. Ɓullowa
= Fitowa
12. Ƙirƙira
= Samarwa
13. Ɗumi
= Zafi
14. Bishiyoyi = Itatuwa
15. Kuza = Zinari
16. Ƙiraga
= Fatu
17. Manufa = Dalili
18. Ɓirɓishi = Alama
19. Maƙalu
= Takardu
20. Ɗorawa
= Azawa, Farawa
21. Internet = Yanar gizo
22. Sharhi = Bayani
23. Kwatantawa = Sifantawa
24. Martani = Mai da jawabi
25. Martaba = Ƙima, daraja
26. Rataye = Waiwaye
27. Fanni = Sashe
28. Shige = Kama
29. Tattaunawa = Harhaɗawa
30. Natsuwa = Amincewa, yarda, gamsuwa
31. Ɗorawa
= Azawa, farawa
32. Sharhi = Bayani
33. Kwatantawa = Sifantawa
34. Martani = Maida jawabi
35. Tattarawa = Harhaɗawa
36. Natsuwa = Amincewa, yarda, gamsuwa
4.5 RATAYE
Samfari na ɗaya (2007)
“Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai,
tsira da aminci su tabbata ga Manzonsa Annabi Muhammadu (SAW).
Ina fara wannan jawabi da godiya ga Allah maɗaukakin sarki
da ya nuna man wannan rana mai cike da tarihi, wato lokacin karɓar ragamar
mulkin Jihar nan, inda aka samu tarihin da ba a taɓa samu ba a
siyasar ƙasar nan, inda aka samu gwamna mai barin gado
ya miƙa wa mataimakinsa ragamar mulki.
Ina ƙara miƙa
godiya ga al’ummar jihar Zamfara da kuka bamu goyon baya ganin mun samu nasara
ta hanyar jefa mana ƙuri’unku a
jam’iyyarmu ta ANPP, inda aka zaɓi dukan ‘yan takararmu a kowane
mataki.
Ya ku masu
girma mahalarta wannan taro goyon bayan da kuka ba gwamnatin da ta gabata. Ina
fatar ku cigaba da bani shi domin kawo ayyukan raya ƙasa da na haɓaka tattalin
arzikin wannan jiha. Zamu cigaba da shirye-shiryen tsohuwar gwamnati ta “Alhaji
Ahmad Sani Yariman Bakura” tare da fito da wasu sababbi kamar inganta noma duba
da irin gudummuwar da yake bayarwa wajen haɓaka tattalin
arziki.
Za mu ba da kulawa ta musamman a ɓangaren ilimi
da gine-gine da ɓangaren kiwon
lafiya da samar da ruwan sha masu tsafta da taimaka wa samari maza da mata.
Daga ƙarshe ina
tabbatar wa da iyayenmu sarakuna cewa wannan gwamnati za ta tafi da ku tare da
karɓar
shawarwarinku. Ina ƙara godewa Allah maɗaukakin sarki
da kuma dattijan wannan jam’iyya tamu mai albarka da al’ummar jihar Zamfara
baki ɗaya.
SAMFURI NA BIYU (2011)
Ina matuƙar godiya ga
Allah maɗaukakin Sarki
da kuma godiya ga Shuwagabannin Jam’iyya, musamman jagora Alh. Ahmad Sani
Yariman Bakura, ina ƙara godewa al’ummar
Jihar Zamfara da kuka fito ƙwanku da ƙwarƙwatarku
kuka zaɓe ni a wannan
matsayi da nake kai a yau. Wannan babu ko shakka nasara ce tamu baki ɗaya. Bayan
haka, ina kira ga waɗanda suka sha ƙasa a wannan
tafiya (‘Yan adawa) da su zo mu haɗa hannu waje ɗaya domin
cigaban wannan jiha tamu baki ɗaya ta kowane fanni. Dukaninmu
Zamfarawa ne, babu abin da ya fi mana Jiharmu. Don haka, dole mu haɗa kanmu domin
ba za mu bari ‘ya’yanmu da jikokinmu su lalace kan siyasa ba”
“Za mu mai da hankali ganin an dawo da ɗaliban da
suka bar makarantunsu a sanadiyar rashin biya masu kuɗaɗen makaranta
tare da basu ilimi kyautata faɗin jihar nan. Haka ma za mu jawo masana’antu
da masu hannu da shuni da su saka jari a wannan jiha domin cigaban tattalin
arziki a wannan jiha, Wannan gwamnati ba za ta ɗauki sakaci
da almubazziranci da dukiyar jama’a ba.
Gwamnatin da ta gabata ta bar ɗimbin bashin
biliyoyin kuɗi kama daga
na bankuna zuwa na ‘yan kwangila wanda ya kawo sanadin taɓarɓarewar
tattalin arzikin jiha.
Daga ƙarshe, ina
kira ga al’umma da ku bamu goyon baya domin fito da wannan jiha halin da take
ciki”.
SAMFURI NA UKU (2019)
Ina godiya ga Allah Subhanahu wata ala da ya
nuna mana wannan rana da na zama gwamnan Zamfara.
Yau rana ce mai cike da tarihi gare ni da
jam’iyyata ta PDP wanda ba a taɓa samu ba a tsawon shekara ashirin
(20) ana gudanar da mulkin wannan jiha.
Jama’ar Zamfara zaɓe ya ƙare
don haka, mu aje duk wani bambancin siyasa mu haɗu mu ciyar da
jiharmu gaba. Alhamdulillahi! Yau ni ne Gwamnan Zamfara don haka zan yi aiki da
kowa domin gudanar da mulki a wannan jiha insha Allah!
Ina sane da ƙalubalen da
jihar nan take fuskanta, jama’ar Zamfara na buƙatar gwamnati
da za ta kula da matsalar tsaro da ke addabarsu. Zamu yi duk mai yiwuwa domin
kawo ƙarshen matsalar tsaro a faɗin jihar nan.
An san jihar Zamfara da noma, abin damuwa ne
idan aka yi la’akari da sunan da ta yi a ƙasa da duniya
baki ɗaya. Don haka,
zamu farfaɗo da noma ta
hanyar tallafawa manoma da inganta noman zamani na (ZACAREP) ta hanyar
tallafawa manoma don inganta noma. Haka ma zamu bunƙasa ilimi
wajen ganin duk yaranmu sun shiga makaranta. Haka ma zamu tallafawa harkokin
lafiya. Zamu fito da hanyoyi don samar da gine-gine musamman a babban birnin
jiha Gusau. Mun lura da cewa an barmu baya, gwamnati za ta gina hanyoyi don
ganin an yi amfani da albarkatun ƙasa da Allah
ya hore mana don kakkaɓe talauci da samar da walwala a faɗin jihar nan,
tare da kula da yan gudun hijira da suka bar muhallansu sanadiyar rashin tsaro
a yankunansu.
Daga ƙarshe, ina
addu’a ga Allah subhananu Wata’ala da ya bamu damina mai albarka da yabanya mai
yawa amin”.
MANAZARTA
Tuntuɓi masu gudanarwa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.