Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazarin Kalmomin
Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (5)
BABI NA BIYAR
KAMMALAWA
5.0 Gabatarwa
A babin da ya gabata an yi cikakken bayani a kan ginin
tsarin kalmomin Zamfarci a cikin waƙoƙin Kabiru Kilasik.
Don haka a wannan babi an naɗe wannan bincike da kammalawa.
Hausawa kan ce “sannu ba ta hana
zuwa” haka zalika, masu iya magana na
cewa, “komi nisan jifa a sama ƙasa zai dawo” wato dai komi ya yi farko ƙarshensa na zuwa. Da
wannan dalili ne, ake ganin cewa bincike a kan” Nazarin Ginin Tsarin Kalmomin
Zamfarci a Waƙoƙin kilasik ya zo karshe.
5.1 Takaitawa
A taƙaice kamar yadda na
gabatar da wannan aiki tun farko a babi na ɗaya, taken wannan aiki shi ne “Nazarin Kalmomin Zamfarci A waƙoƙin Kabiru Kilasik” An
kasa shi zuwa babi biyar kuma kowane babi yana ɗauke da bayanan da suka jiɓince shi.
A babi na ɗaya an fara binciken
da gabatar da dalilin bincke da farfajiyar bincime, da muhimmancin bincike, da
hujjar cigaba da bincike da dabarun bincike da has ashen bincike, da kuma
kammalawa.
A babi na biyu kuwa, an fara ne da
gabatarwa da kuma bitar ayyukan da suka gabata. Da kuma kawao ma’anar waƙa da waƙokin siyasa. Haka
zalika, an kawo tarihin Zamfara da mawaƙan Hausa a Zamfara da
kuma waƙoƙin siyasa, sai kammalawa.
A babi na huɗu kuwa, an soma ne da
ma’anar kalmomi da kuma ginin kalmomi, da kalmomin Zamfarci, sai kuma ginin
kalmomin Zamfarci a waƙoƙin Kilasik, daga ƙarshe aka kammala.
A babi na biyar kuma an kamala
binciken tare da kawo manazarta da kuma ratayen waƙoƙin Kilasik.
5.2 Kammalawa
A wannan gaɓa ce, za a naɗe tabarmar wannan aiki mai taken” Nazarin Kalmomin
Zamfarci a Cikin Waƙoƙin Kabiru Kilasik”. Wannan bincike ne da aka gudanar a
kan Adabi wanda masana ke ambato da madubi ko hoton rayuwar al’umma.Binciken ya
keɓanta ne a kan ɓangare guda na adabi,
wato rubutattar waƙa, musamman waƙoƙin siyasa. Wato ƙarƙashin rubutaccen
adabi da ya shafi waƙa,bai shafi zube ko wasan kwaikwayo ba.
Bincike ne da aka
gudanar a kan nazarin ginin tsarin kalmomin Zamfarci a cikin waƙoƙin Kabiru Kilsaik.
Inda aka dubi baiwar da Allah ya yi wa wannan mawaƙi, An fitar da wannan
bincike ne domin zaƙulo kalmomin Zamfarci da Kilasik ke saƙawa a cikin waƙoƙinsa. An rarraba
binciken zuwa babi-babi, inda aka samu babuka biyar.
A babi na ɗaya an fara ne da
gabatarwa da ftto da dalilin bincke da farfajiyar bincime, da muhimmmancin
bincike da hujjar cigaba da bincike da dabarun bincike da has ashen bincike, da
kuma kammalawa.
A babi na biyu kuwa, an fara ne da
gabatarwa da kuma bitar ayyukan da suka gabata, da kuma kawao ma’anar waƙa da waƙokin siyasa. Haka
zalika, an kawo tarihin Zamfara da mawaƙan Hausa a Zamfara da
kuma waƙoƙin siyasa, sai kammalawa.
A babi na uku kuwa, an fara ne da
gabatar da tarihin shahararren mawaƙin Kabiru Kilasik da
kuma fara waƙarsa da ire-iren waƙaokinsa da jigon waƙoƙinsa da bayanin yadda
yake tsara waƙoƙinsa da kuma salon waƙokinsa, sai nkuma
kammalawa.
A bibi na huɗu kuwa, an suma ne da
ma’anar kalmomi da kuma ginin kalmomi, da kalmomin Zamfarci, sai kuma ginin
kalmomin Zamfarci a waƙoƙin Kilasik, daga ƙarshe aka kamala.
Babi na biyar kuma a nan aka kamala
binken da taƙaitawa da kuma shawarwari, sai naɗewa.
5.3 Sakamakon Bincike
A wannan bincike da
ya gudana a kan Nazarin Klmomin Zamfarci a Cikin Waƙoƙin Siyasa na Kabiru
Yahaya Kilasik, an fahimici cewa, waƙoƙin wannan mawaƙi sun samu karɓuwa ga al’ummar
Zamfara da ma Nijeriya baki ɗaya. Dalilin amfani da kalmomin Zamfarci ya sa jama’a
suka ƙara shawa’awar waƙoƙinsa.Saboda Zamafrci
karin harshe ne mai sauƙin fahimta ga kowane Bahaushe.
Bugu da ƙari wannan bincike ya
gano cewa, Kabiru Kilasik yana ba da gudummuwa wajen haɓɓaka adabin Hausa,
musaaman ɓangaren rubutattun waƙoƙi.
Binciken ya gano cewa Kilasik yana
gina mafi akasarin baitocin waƙarsa ne, da kalmomin Zamfarci.Wannan
bai rasa nasaba da kasancewar mawaƙin Bazamfare, wato
mutumin Zamfara.Wannan shahararren mawaƙin siyasa yana bada
gudumuwa wajen ƙara fito da muruwar karin harshen Zamfarci.
5.4 Shawarwari
Hausawa kan ce, “shawara ɗaukar ɗaki”, a bisa wannan
bincike da na gabatar ina mai bada shawari ga ‘yan’uwana ɗalibai da ke da
sha’awar gudanar da bincike a wannan bagire na adabin Hausa cewa, akwai ɓangarori da dama da
za su iya ɗauka a waɗannan waƙaƙi na Kabiru Kilasik
ba sai a kan kalmomin Zamfarci kawai ba.
Haka kuma ina ƙara ba da shawara ga ɗalibai masu sha’awar
bincike a kan waƙoƙin Kilasik cewa suna iya tuntuɓarsa domin ƙara samun haske a kan
binciken da suke yi. Domin mutun ne mai saukin kai kuma mai maraba da jama’a.
Ana iya samun sa a lambobin wayarsa ko kuma a same shi a gidansa dake cikin Damɓa a nan cikin garin Gusau.K o a gidansa na
mahaifarsa Tudun Wada Talatar Mafara.
BABI NA
BIYAR: KAMMALAWA
5.0
Gabatarwa
A
babin da ya gabata an yi cikakken bayani
a kan ginin tsarin kalmomin Zamfarci a cikin waƙoƙin Kabiru Kilasik.
Don haka a wannan babi an naɗe wannan bincike da kammalawa.
Hausawa
kan ce “sannu ba ta hana zuwa” haka
zalika, masu iya magana na cewa, “komi nisan jifa a sama ƙasa zai dawo” wato dai komi ya yi farko ƙarshensa na zuwa. Da
wannan dalili ne, ake ganin cewa bincike a kan” Nazarin Ginin Tsarin Kalmomin
Zamfarci a Waƙoƙin kilasik ya zo karshe.
5.1
Takaitawa
A
taƙaice
kamar yadda na gabatar da wannan aiki tun farko a babi na ɗaya, taken wannan
aiki shi ne “Nazarin Kalmomin Zamfarci A
waƙoƙin Kabiru Kilasik” An
kasa shi zuwa babi biyar kuma kowane babi yana ɗauke da bayanan da suka jiɓince shi.
A babi na ɗaya an fara binciken
da gabatar da dalilin bincke da farfajiyar bincime, da muhimmancin bincike, da
hujjar cigaba da bincike da dabarun bincike da has ashen bincike, da kuma
kammalawa.
A
babi na biyu kuwa, an fara ne da gabatarwa da kuma bitar ayyukan da suka gabata.
Da kuma kawao ma’anar waƙa da waƙokin siyasa. Haka zalika, an kawo
tarihin Zamfara da mawaƙan Hausa a Zamfara da kuma waƙoƙin siyasa, sai
kammalawa.
A
babi na huɗu kuwa, an soma ne da
ma’anar kalmomi da kuma ginin kalmomi, da kalmomin Zamfarci, sai kuma ginin
kalmomin Zamfarci a waƙoƙin Kilasik, daga ƙarshe aka kammala.
A
babi na biyar kuma an kamala binciken tare da kawo manazarta da kuma ratayen waƙoƙin Kilasik.
5.2
Kammalawa
A wannan gaɓa ce, za a naɗe tabarmar wannan aiki mai taken” Nazarin Kalmomin
Zamfarci a Cikin Waƙoƙin Kabiru Kilasik”. Wannan bincike ne da aka gudanar a
kan Adabi wanda masana ke ambato da madubi ko hoton rayuwar al’umma.Binciken ya
keɓanta ne a kan ɓangare guda na adabi,
wato rubutattar waƙa, musamman waƙoƙin siyasa. Wato ƙarƙashin rubutaccen
adabi da ya shafi waƙa,bai shafi zube ko wasan kwaikwayo ba.
Bincike ne da aka
gudanar a kan nazarin ginin tsarin kalmomin Zamfarci a cikin waƙoƙin Kabiru Kilsaik.
Inda aka dubi baiwar da Allah ya yi wa wannan mawaƙi, An fitar da wannan
bincike ne domin zaƙulo kalmomin Zamfarci da Kilasik ke saƙawa a cikin waƙoƙinsa. An rarraba
binciken zuwa babi-babi, inda aka samu babuka biyar.
A
babi na ɗaya an fara ne da
gabatarwa da ftto da dalilin bincke da farfajiyar bincime, da muhimmmancin
bincike da hujjar cigaba da bincike da dabarun bincike da has ashen bincike, da
kuma kammalawa.
A
babi na biyu kuwa, an fara ne da gabatarwa da kuma bitar ayyukan da suka
gabata, da kuma kawao ma’anar waƙa da waƙokin siyasa. Haka
zalika, an kawo tarihin Zamfara da mawaƙan Hausa a Zamfara da
kuma waƙoƙin siyasa, sai kammalawa.
A
babi na uku kuwa, an fara ne da gabatar da tarihin shahararren mawaƙin Kabiru Kilasik da
kuma fara waƙarsa da ire-iren waƙaokinsa da jigon waƙoƙinsa da bayanin yadda
yake tsara waƙoƙinsa da kuma salon waƙokinsa, sai nkuma
kammalawa.
A
bibi na huɗu kuwa, an suma ne da
ma’anar kalmomi da kuma ginin kalmomi, da kalmomin Zamfarci, sai kuma ginin
kalmomin Zamfarci a waƙoƙin Kilasik, daga ƙarshe aka kamala.
Babi
na biyar kuma a nan aka kamala binken da taƙaitawa da kuma
shawarwari, sai naɗewa.
5.3
Sakamakon Bincike
A wannan bincike da ya gudana a kan
Nazarin Klmomin Zamfarci a Cikin Waƙoƙin Siyasa na Kabiru
Yahaya Kilasik, an fahimici cewa, waƙoƙin wannan mawaƙi sun samu karɓuwa ga al’ummar
Zamfara da ma Nijeriya baki ɗaya. Dalilin amfani da kalmomin Zamfarci ya sa jama’a
suka ƙara shawa’awar waƙoƙinsa.Saboda Zamafrci
karin harshe ne mai sauƙin fahimta ga kowane Bahaushe.
Bugu
da ƙari
wannan bincike ya gano cewa, Kabiru Kilasik yana ba da gudummuwa wajen haɓɓaka adabin Hausa,
musaaman ɓangaren rubutattun waƙoƙi.
Binciken
ya gano cewa Kilasik yana gina mafi akasarin baitocin waƙarsa ne, da kalmomin
Zamfarci.Wannan bai rasa nasaba da kasancewar mawaƙin Bazamfare, wato
mutumin Zamfara.Wannan shahararren mawaƙin siyasa yana bada
gudumuwa wajen ƙara fito da muruwar karin harshen Zamfarci.
5.4
Shawarwari
Hausawa
kan ce, “shawara ɗaukar ɗaki”, a bisa wannan
bincike da na gabatar ina mai bada shawari ga ‘yan’uwana ɗalibai da ke da
sha’awar gudanar da bincike a wannan bagire na adabin Hausa cewa, akwai ɓangarori da dama da
za su iya ɗauka a waɗannan waƙaƙi na Kabiru Kilasik
ba sai a kan kalmomin Zamfarci kawai ba.
Haka
kuma ina ƙara ba da shawara ga ɗalibai masu sha’awar bincike a kan waƙoƙin Kilasik cewa suna
iya tuntuɓarsa domin ƙara samun haske a kan
binciken da suke yi. Domin mutun ne mai saukin kai kuma mai maraba da jama’a.
Ana iya samun sa a lambobin wayarsa ko kuma a same shi a gidansa dake cikin Damɓa a nan cikin garin Gusau.K o a gidansa na
mahaifarsa Tudun Wada Talatar Mafara.
Manazarta
Tuntuɓi masu gudanarwa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.