Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari Kan Jawabin Kama Aiki Na Zababbun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019 (1)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Nazari Kan Jawabin Kama Aiki Na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019 (1)

NA

NASIRU HASSAN

jawabi

SADAUKARWA

Wannan bincike an sadaukar da shi ga iyaye maza da mata, waɗanda suke abin alfahari bisa ga irin gudummuwar da suka bayar wajen tarbiyya da ilmantarwa da duk abin da uba da uwa kan yi zuwa ga ‘ya’yansu. Allah ya jiƙansu, ya kuma saka masu da mafificin alkhairinsa amin. Bayan haka, ba za a manta da Malamai ba waɗanda suka yi tsaye wajen inganta tarbiya tare da cusa ilimi a zukatanmu, wanda da himmarsu ne tare da taimakonsu wannan aiki ya kammala. Allah ya saka masu da alkhairinsa amin.

GODIYA

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai girma da ɗaukaka. Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka bi su da gaskiya har zuwa ranar sakamako.

 

Ina ƙara miƙa godiya ga iyayena bisa ga tarbiyar da suka bani tun daga ƙuruciya har zuwa yau. Allah ya saka masu da mafificin alhairi. Godiya ta musamman ga Madugu uban tafiya wato Malam Musa Abdullahi wanda ya kula da duba wannan aiki tare da ba da shawarwari da gyare-gyare don tabbatar wannan kundin bincike ta yadda zai zama mai amfani ga jama’a. Duk da ɗimbin aikin da ke gabansa bai yi ƙasa a guiwa ba wajen ba da lokacinsa ganin samun nasarar wannan bincike. Allah ya saka masa da alhairi ya cika masa burinsa amin.

 

Haka ma ina ƙara miƙa godiya ga Malamanmu na wannan sashe bisa koyarwa da shawarwarinsu. Musamman Malam Aliyu Rabi’u Ɗangulbi mai kula da sashen jarabawa (Eɗam officer) da Malam Isah S/Fada da kuma uwa uba shugaban sashe wato Farfesa Aliyu Muhammad Bunza.

 

Haka ba zan manta da waɗanda suka taimaka man wajen wannan bincike ba, irin su Alh. Adamu Sani Katuru (Zamfara Radio), Abdullahi Musa (FM Radio) Sani Adamu Gusau (Friend) da Ahmad Muhammad Kabir (Friend) da kuma ma’aikatun gwamnati kamar Ma’aikatar Yaɗa labaru ta jiha da Ɗakin aje bayanai na jiha (State Library) da kuma gidan tarihi na jiha (History Bereau), Allah ya saka masu da alkhairi amin.

TSAKURE

Wannan bincike mai taken “Nazari kan Jawabin Kama aiki na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara daga shekara ta 2007 zuwa 2019” An gudanar da shi domin ganin kalaman da zaɓaɓɓun gwamnoni ke yi don amfani da su a matsayin hanyar jawo ra’ayin jama’a domin natsuwa da abin da suka faɗa zuwa ga al’ummarsu na abin da ya shafi tattalin arziki da walwala da sauransu. Wannan binciken zai mai da hankali ne wajen nazarin jawaban tare da fito da abin da jawaban suka ƙunsa ta fuskar manufa, salo da kuma sarrafa harshe.

Post a Comment

0 Comments