Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Nazarin Kalmomin Zamfarci
A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (4)
BABI NA HUƊU
AMFANI DA KALMOMIN ZAMFARCI A WAƘOƘIN KABIRU KILASIK
4.0 GABATARWA
Wannan babi shi ne ƙashin bayan wannan
bincike.A wannan babi za a yi bayanin ma’anar kalmomin Zamfarci da Kabiru
Kilasik ya yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa.Haka kuma za a
yi cikkaken bayani a kan waɗannan kalmomi.Wanda a kan sa ne aka aiwatar da wannan
bincike.Da ƙarshe za a rufe da kammalawa.
4.1 Ma’anar kalmmomi
Kalma dai ita ce haɗuwar baƙi da wasali su samar
da magana, lafazi ko zance mai ma’ana, ta kanta, wadda za a iya fahimta ta
hanyar rubutu ko ambatonta.Sai dai akwai ra’ayoyi mabambanta da masana harshe
suke bayyana ma’anar kalma da yadda kowane daga cikinsu yake kallon ta.
Crystal
(2008:521-523) ya ce, “kalma ginshiƙi ne na bayani a
cikin harshe da ake sadarwa ta hanyar furtawa ko rubutawa”. Ya ƙara da cewa curin
zance ne wanda take zuwa a cikin daidaitaccen tsari.
Jinju (1981-42-44), cewa ya yi,
“kalma ƙwayar sauti ce, ko haɗuwar saututtuka waɗanda ake amfani da su
ta hanyar sadarwa”,
Kalmomi
lafuzza ne masu ma’ana guda-guda.Kuma su ne zango na farko a cikin tubalai ko
kayan ginin jimla.
Bisa la’akari da
ra’ayoyin masana dangane da ma’anar kalmomi, za mu iya cewa, kalmomi jam’i ne
na kalma, wanda ake samu ta hanyar haɗuwar baƙi da wasali su samar
da kalma, idan aka haɗa kalma da kalma sai
a samar da kalmomi masu ma;ana takansu.
Ga tsarin kalmomin
daidaitacciyar Hausa nan tare da takwarorinsu a cikin karin harsdhen Zamfarci
kamar haka.
Daidaitacciyar Hausa Zamfarci
Bacci Kwana
Kookoo Kunu
Kwarkwata Ƙyaayaa
Kyanwa Mussa
Tsumma Ragga
Kalanzir Barahuni
Gyaɗa Gujjiya
Sunkuyawa Durƙusawa/ gurfanawa
Fartanya Kwasa/
kwasahe
Awara Gala
Ƙofa Gambu/ƙyaure
Ashar Ɓaci
Bazawara Zaura
Ɓeera Kusu
Faɗi Gayi
Farce Akaifa
Fusata Hushi
Gafiya Burgu
Hanta Anta
Jure Daure
Jeji Daji
Kaciya Kuidu
Kuɓewa Yauɗi
Magana Batu
Mahauci Barunje
Minshari Hansari
Musaya Canza
Rahusa Ragoowa
Waina Masa
Yashi Rairai
Alfarma Lmuni
4.2. Ma’anar Kalma
Abdulhamid (2001) ya
bayyana ginin kalma da cewa, “Ginin kalma ya shafi tsira, ƙirƙira da kuma kumburar
kalma. Ya ce, ginin kalma ya rabu biyu: na ɗaya ya ƙunshi ƙirƙira tsirar kalma daga aikatau zuwa suna ko akasin haka. Na biyu ya shafi
harɗantarwa (compouding).
Wato haɗa wata kalma da wata”
Mamman (2006) ya dubi ginin kalma in
da yake cewa, “Nazari ne wanda ya shafi ginuwa ta kalma wato yadda kalma ke
“kumbura” ta ba da ma’ana wato ta kumbura daga tilo zuwa jam’i ko kuma ta
kumbura daga na jinsin Namiji zuwa mace. Haka kuma nazarin gini kalma nazari ne
wanda ya shafi ‘tsira’ wato yadda kalma
ke tsira daga Aikatau zuwa suna ko daga suna zuwa sifa”
Alhasan (2005) ya faɗa cewa, “Idan aka ce
ginin kalma ana nufin gini ne na kalmomi, saboda ana rusa kalmomi domin a ƙwanƙwance da kuma
daidaice su”.
Idan muka yi la’akari da bayanai da suka
gabata, za mu iya cewa, kalama na nufin haɗuwar baƙi da wasali su samar
da ma’ana.Kuma ana fahimtar kalma ta hanyar barin fili tsakaninta da wata.
4.3 Ma’anar Kalmomin zamfarci
Kalmomi Ma’ana
Shingii Kalmar shingi na
nufin darni da ake ɗan killace wani abin
amfani.
Zawara Kalmar zawara tana
nufin matar da ta taɓa aure amma sun rabu
da mijinta, kuma ba tayi wani aure ba.Wato Bazawara.
Wari/ɗoi Kalmar wari a Zamfarci
tana nufin ɗoyi, wato abin da bai
da daɗin shaƙa a hanci ko mai
warin da ke cutarwa.
Gaya/hwaɗi Wannan kalma gaya/ hwaɗi a karin harshen
Zamfarci kalma ce da ke nufin faɗi, wato isar da wani saƙo ga wani mutun ko
wasu mutane.
Yatsa Kalmar Yatsa a Zamfarci
tana daukar ma’anar farce, wato tilon farce guda ɗaya, a cikin farutta biryar da mutun
yake das u a kowane hannu ko ƙafa.
Hauya Kalmar hauya a karin harshen
Zamfarci tana nufin fartanya, wata aba da ake noma da ita, wadda ta keda ruwan
fartanya na ƙarfe da kuma ɓota ta itace.
Dawo Dawa a karin harshen
Zamfarce yana nufin fura wadda ba a dama ba.
Burgu Burgu wannan kalma suna ne
na dabba, wato Kalmar tana nufin gafiya, wata dabba ce mai kama da mage kuma
mai yawan barna ko satar abinci ko kayan abincin.Ana samun ta a gari ko a jeji.
Zufa Zufa kalam ce ta Zamfarci
mai nufin gumi, wato ruwa ne da ke fitowa a jikin mutun a lokacin da ya yi wani
aiki na motsa jiki ko wahala, ko sanadiyar zafin rana,
Gujjiya Kalmar gujiya suna ne na wani nau’in
abinci, wanda Hausawa ke nomawa. Ita gujjiya tana yin ɗiya ne a ƙasa, wato tana cikin
“maɓanɓara ƙasa,” a
daidaitacciyar Hausa ana kiran ta gyaɗa.
Buda Buda wannan Kalmar tana nufin hazau, ko yanayin
hunturu wanda ke canja yanayin gari, kuma ana amfani da Kalmar a wajen sawa
wanda aka Haifa a wannan lokaci suna da ita.
Jalli Jalli kalma ce ta
Zamfarci mai nufin jari.Wato kuɗi ko wasu kaya ko wani abu da mutun ya mallaka don yin
sana’a ko kasuwanci.
Daure Daure wannan kalma tana da
ma’ana biyu a Zamfaci, ta ɗaya, Kalmar na nufin aiki jure, ta biyu kuwa, Kalmar
mutuwa. A da idan mutun ya mutu ana cewa ashe wane bai Daure ba. Amma
tsowuwar kalma ce da ake amfani da ita.
Daji Daji kalamr Zamfarci ce,
mai nufin jeji, wato wajen gari.
Ɗankwali Wannan
Kalmar Zamfarci ce, mai nufin kallabi.Wato wata sutura ce ta mata da suke ɗaurawa a kai domin
rufe gashin kansu ko kwalliya.
Yauɗi Wannan Kalmar suna ne,na ɗaya daga cikin
ire-iren miyar Zamfarawa, wato Kalmar na nufin kubewa. Wata abu ce wadda ake
miya da ita, akwai ɗanya akwai
busasshiya.
Guru/kuruu/makur u Wannan
Kalmar tana nufin ƙuli-ƙuli, wani nau’in abin +amfani ne da ya
shafi dangin abinci da Zamfarwa ke amfani da shi.Ana yin shi da gyaɗa.
Mussa Mussa wannan Kalmar tana
nufin mage, kuliyanwa, wata dabbace da ake ajewa a gida, domin kiwo, kuma ba
don a ci ba, ko a sayar. Yawanci mutune na kiwon ta don samun lada ko don
maganin ɓeraye da ke masu ɓarna a gida.
Batu Batu a karin harshen
Zamfarci, wannan kalma tana nufi magana/, zance, ko lafazi.Wato kalma ce
aikatau, wadda jam’in ta shi ne batutuwa.
Barunje Kalmar Barunje a karin harshen Zamfarci, kalma ce da ke
nufinMahauci, wato mutun da ke harkar sai da nama ko fawa.
Hurhure
ko canza Kalma ce da ke nufin musaya.
Wato mutun ya ba da wani abu a ba shi wani.
Tagguwa Tagguwa kalama ce da ke nufin
riga, wata nau\in sutura da ake amfani da ita domin rufe tsaraici.
Shigihwa Wannan kalma tana nufin soro ko daki.
Wata mafaka ko mazauna ce da Hausawa ke ginawa domin zama da iyali.
Lanƙwasa Kalma ce, aikatau mai nufin tanƙwara.Wato tanƙwara wani abu kamar ƙarfe ko itace.
Haƙo Haƙo kalma ce da ke nufin
tarko, wato dabara ce, da ake yi domin kama wani abu ko wata dabba,Kamar gafiya
ko kifi, da sauransu.
Gatana Kalmar gatana, kalma ce da ke nufin
tatsuniya.Amma a karin harshen Zamfarci ana amfani da gatana.Wadda ke nufin
tsohuwar hanya ko makaranta ta farko da Bahaushe ya fara amfani da ita wajen
tarbiyantar da ‘ya’yansa. Mafi akasari iyaye mata da kakanni ko tsofi su suka
fi yin ta.
Masa Wannan kalma tana nufin waina,
wani nau’in abinci ne, da ake yi da ake yi da masara ko shinkafa, kuma ana soya
ta a tanda.
Bindi Kalmar Zamfarci ce, mai nufin
wutsiya. Kamar wutsiyar sa, ko rago/
Marece Kalmar Zamfarci ce, mai nufin yamma,
wato lokacin yamma.
Rairai Wannan kalma tana nufin yashi, wani
nau’in ƙasa mai huroza da ake ginin zamani ko siminti das hi.
Ɗiya Kalma ce, ta Zamfarci mai nufin
‘ya’ya.
4.4 Amfani da kalmomin Zamfarci a Wakokin Kabiru Kilasik
WAƘAR USMAN ƊANKALILI MAI SUNA” ‘DODO MAGAJIN DODO’
Turke: Bakura
Maradun mun aminta da Ɗankalili ya gadi dodo,
Shi kuma Gwamna mu zaɓi dodo, fi di fi
Allah sa mu dace,
Mu kauda waɗanda ka yaudararmu.
Jagora: Zamfara ga fa kabiru naku kilasik
mai kwanci na sayi,
Karɓi: Ɗan App zai ji waƙar ga tamkar tutu
ƙwarai
da ɗoyi,
Jagora: Zamfara yau mun ussuhe Jalla
an maishe mu kamar marayu,
Karɓi: Yau daɗa ba mu da mai kataɓus abinci na son
gagararmu.
A wnnan baiti Kabiru
Kilasik, ya yi amfani da kalmomin
Zamfarci. Inda ya yi amfani da kalmar “tutu” ta karin harshen Zamfarci, wadda a
daidaitacciyar Hausa tana nufin Bahaya. Ya yi amfani da ita a nan a matsayin
kamance, inda ya kamanta wannan waƙa da yake da
tutu a wajen ‘yan Jamiyyar ANPP ,domin waƙar ta ɗan takarar PDP ce.Ya
kuma yi amfani da Kalmar ‘ussuhe’ wadda ke nufin bane ko tashin hankali a
daidaitacciyar Hausa.Ita ma ya yi amfani da ita domin kwatanci, inda yake ƙoƙarin bayyana halin da
al’ummar Zamfara suke ciki. Haka kuma a ɗango na uku ya yi amfani da Kalmar ‘maishe’ Maimakon’ maida’ a
daidaitaciyar Hausa.Ya yi amfani da ita domin ya nuna yadda gwamnati ta azabtar
da al’ummar Zamfara.Har wa yu ya ƙara da cewa:-
Jagora: Mata yara suna kuka ga yinwa ga
yalwar ɓarayi,
Karɓi: Zamfara mun shiga ukku Allah mutane sun
koma kubeyi,
Jagora: Dagga a soke sai a halbe,
kisan kai Zamfara ba a shayi,
Karɓi: Ba mu barin ta garin iyayenmu komi za a yi mun
ji ga mu.
A ɗangon wannan baiti na
biyu Kilasik ya yi da kalmar Zamfarci
inda ya yi amfani da Kalmar ‘ukku’ a matsayin bala’I, ko ƙaƙa-ni-ka-yi, ya yi
amfani da wannan kalma a nan domin bayyana irin mummunan halin da al’ummar
Zamfarawa suke ta ta shiga. A ɗango na uku kuwa, ya
yi amfani da karin harshe ‘dagga’ maimakon
‘daga’. Mai nuna cigaba da bayani.
Jagora: Fi di fi babban gari ce, da ta yi
yalwa da ɗarin iyaye,
Karɓi: Wanga ya ƙoshi da kifi wanga
da nama wanga da maye-maye,
Jagora: Sannu uwa mai ba da nono fi di fi
sharan hawaye,
Kraɓi: Fi di fi ɗaki na alatu za mu shiga mu ci duniyarmu.
A wannan baiti mawaƙin ya yi amafni da
kalmomin Zamfarci har sau uku, inda ya yi amfani da Kalmar ‘wanga’ wadda ke nufin
‘wannan’ a daidaitaccyar Hausa.Wadda ke
nuni da abu ɗaya tilo, wanda ke
kusa da mai magana.Amma ya yi amfani da ita domin nuna rin daɗin da al’umma ke sha
a lokacin mulkin fi di fi.
Jagora: Waƙar Usman ɗankalili da shauƙi Kabiru za ni yin
ta,
Karɓi: Sannan in ɓarje gumina in yo wada ma su biɗa ka son ta,
Jagora: Kilasik na iya takusheren ɗumi don waƙa zan karanta,
Karɓi: In yi kashashshaɓa in yi zari ga ƙwaro mai cin
shukunanmu.
A wannan baiti
Kilasik ya yi da kalmomin Zamfarci a wurare da dama.Aɗango na biyu ya yi
amfani da Kalmar ‘wada’ maimakon’ yadda’ a daidaitaciyar Hausa. A gaba kuma ya yi
amfani da kalmar ‘biɗa’ ta karin harshen Zamfarci a matsayin ‘nema’ a
nan ya yi amfani da kalmar domin nuna yadda zai yi waƙarsa, a
daidaitacciyar Hausa.Haka zalika a ɗango na uku ya yi amfani da ‘takushere’ ya yi amfani da Kalmar domin ya ba kansa, ko
kurara kansa, cewa ya iya ƙiƙirar magana ko waƙa.da kuma ‘ɗumi’ mai nufin ‘magana’ ko ‘surutu’ a
daidaitacciyar Hausa.
Jagora: Kowab bak kaza da gashi kwaɗai sai ya taɓi lahiyatai,
Karɓi: Sai ka riƙa ta mu hige
Kabiru kowaƙ ƙwantan sai na ƙwantai,
Jagora: Ku Mafara kun sare iccenku amma sai
ku ka bar hawattai,
Jagora: Ya yi tsiri ya girmu sayen da Allah
yay yi da shi ya girmu.
Mawaƙin ya yi amfani da
kalmomin Zamfarci a wannan baiti, kamar
inda yace, ‘kowab bak kaza’ maimakon ‘kowa ya bar kaza’ a nan ya yi amfani da waɗanna kalmomi domin
yin hannuka mai sanda ga wanda yake yi wa waƙar, cewa duk wanda ya
yi masa ya rama.Haka kuma, ya yi amfani da Kalmar ya yi amfani da wannan kalma ne, domin yin
zambo ga ‘yan siyasar garin Mafara. Bugu
da ƙari
ya yi amfani da Kalmar Zamfarci a ɗango na uku inda ya
yi amfani da ‘lahiyata’ mai nufin
‘lafiyarsa. Ya yi amfani da Kalmar domin ƙara tunatar da wanda
yake yi wa waƙar cewa idan ya ƙyale abokin adawa to
zai cutar da shi.
Jagora: Kusu ko baƙo yag gane shi
za ya kira shi ƙane ga burgu,
Karɓi: Lallai ganga ko ƙabila ya ganta tana
da kamar kalangu,
Jagora: Misallai dai na nan zuwa
‘yan’uwa ku biyo ni fa kar ku damu,
Karɓi: Da ka ga Kilasik kag ga mai Maradun ka san
da akwai alamu,
A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da
kalmomin Zamfarci inda ya ya amfani da‘kusu’ a matsayin ‘ɓera’
wanda ya kawo shi ne a matsayin kamancen kasawa..Da kuma Kalmar ‘burgu’ mai ma’anar ‘gafiya’ ya yi amani da Kalmar domin nuna fifiko.Haka
zalika ya yi amfani da Kalmar ‘misallai’
a matsayin ‘misalai’ a daidaitacciyar Hausa.Inda yak e lurar da mai sauraren waƙar cewa kar ya ƙagara zai zo da
kyawawan misalai da za su sa ya fahimci waƙa.
Jagora: Karen bana ya kashe wanga
zomo, ashe bana gawa ta yi yalwa,
Karɓi: Dashen Allah, Allah ka ishe shi babu
ruwan shi da mai kulawa,
Jagora: Muna nan fi di fin amana Kilasik
babu batun tsayawa,
Karɓi: Mu ƙara nitso a wajen
ibada Ta’ala Jalla ka agazarmu.
A nan Kabiru Kilasik
ya yi amfanin da kalmomin Zamfarci, inda
ya yi amfani da Kalmar ‘wanga’ mai
nufin ‘wannan’ mai nuna mutun ɗaya tilo na kusa da mai magana. Kuma a nan ya yi amfani
da kalmar ne domin yin zambo ga wani abokin hammaya, cewa ya sha ƙasa. Da kuma kalmar ‘ishe”
mai ma’anar ‘idar’ ko ‘ida’
wato kammala aiki, a daidaitacciyar Hausa. A nan kuma yana gugar-zana
ne, ta nuna cewa wanda yake yi wa waƙa Allah ne ke tare da
shi ko ba kowa idan Allah ya nufa sai ya yi.
WAƘAR CIKI DA G ASKIYA
Turke: Anpp ba ni da kuwa, kuma kun san ba ku da ‘niya,’
Kar muka kallon juna
Kabiru nai maku kallon mai
bisa ruwa,
A wannan baiti
Kilasik ya yi amfani da kalmomin
Zamfarci, inda ya yi amfani da Kalmar ‘niya’
a matsayin ‘ni’ mai nufin
mutum mai magana tilo. Ya yi amfani da
Kalmar a nan domin yin gugar-zana ga abokan adawarsa, cewa yadda bai da kowa
cikin su shi ma sun yi asarar waƙi.Da kuma kalamr ‘nai’ a maimakon ‘na yi’ a daidaitacciyar Hausa.Ya
yi ta ne domin nuna yadda ya ɗauke su.
Karɓi: Mai ƙaunarka uban Faɗimatu Annabi ba shi
ba gunaguni,
Annabi Manzo sahibul
karama bayan kai ba ni da wani,
Ko tayi ki ƙaunarka ‘baɗininai ‘ ya zarta wa bajini,
Ɗaha maceci na ƙaunarka Annabi ‘niɗ ɗoka’ ina ƙawa.
A nan Kabiru Kilasik
ya yi amfani da ginin kalmomin Zamfarci,
karma inda ya yi amfani da ‘baɗininai’ a maimakon ‘baɗininsa’ ya yi amfani da Kalmar ne domin bayyana abin
da ke cikin zuciya. Da kuma ɗango na huɗu inda yayi amfani da ‘niɗ ɗoka’ mai
nufin ‘na ɗauka’ a
daidaitacciyar Hausa. Ya yi amfani da Kalmar domin nuna aikin da yake, wato ƙaunar Annabi(S.A.W.).
Jagora: In ke ƙare Gusau je ki gaida
Shinkahwawa kun hi kakkarai
Karɓi: Kowa ba ni da Shinkafi sai amarya matar Saminu
Zulai,
Jagora: Zan nuna maki matan ƙwarai na kirki na san
su duka sarai,
Karɓi: In Allah ya kai ni Shinkafi zan zaunawa ba ni
damuwa.
A ɗangon farko na wannan
baiti mawaƙin ya yi amfani da
kalamr Zamfarci inda yayi amfani
da ‘hi’
a maimakon ‘fi’, ya yi amfani
da ita domin nuna fifikon mutane garin Shinkafi da wasu dab a su ba. A ɗango na huɗu kuwa ya yi amfani
da Kalmar ‘sarai’ ta karin harshen Zamfarci mai nufin ‘gaba
ɗaya’ ko ‘duka’. Wato,
amsa-kama, ya yi amfani da ita a nan a matsayin jam’i, duka ko gaba ɗaya.
Jagora: Ga ni da sabon launi Kabiru yankan ƙauna za ni yi ciki,
Karɓi: Mai algaita shi yaɗ ɗaram ma kowa cin ribar muƙamuƙi,
Jagora: Bayan tsoron Allah Kabiru da na
daure na ci alhaki,
Karɓi: Koda ba kowa cikin garinmu ko ni ɗai sai na ci kassuwa.
Mawaƙin ya yi amfanin da
kalmomin Zamafrci a wannan baiti, a ɗango na biyu ya yi amfani da kalmomin ‘yaɗ ɗaram ma’ a matsayin ‘ya ɗara ma’ a
daidaitacciyar Hausa. Ya yi amfani da waɗannan kalmomi domin nuna fifiko ta
hanyar awo. da kuma Kalmar ‘kassuwa’
mai nufin ‘kasuwa’ a daidaitacciyar Hausa.Ya yi amfani da ita a nan
domin nuna ƙarfin hali da juriya, domin ya nuna ko ba kowa a
Jam’iyyarsu shi sai ya tsaya ciki.
Jagora: Daddaɗar
magana ta mayar da zaki ɗan taure na bunsuru,
Karbi: Ni sai na ɗinko babalange ran
sallah na samu kurkunu,
Jagora: Zamfara kun ji ina nan ashe da
saurana kuma ba ni yin shiru,
Karɓi: Zamfara kowa ban daƙile ba al’umma barka
da shan ruwa.
A wannan baiti a ɗango na huɗu Kabiru Kilasik ya
yi amfani ginin tsarin Kalmar Zamfarci ‘daƙile’ mai nufin ‘bari’ ko ‘mantawa’ a
daidaitacciyar Hausa.Ya yi amfani da ita a nan domin nuna cewa kowa na shi ne a
Zamfara.
Jagora: Ni mamuda Aliyu ba ni mance gwarzo
na karhen hwashin tama,
Karɓi: Mai komi dozin mai gida ga Saratu taken dauri
zan yi ma,
Jagora: Don
ko yau kai ne mijin Mariya shirya zo kai shirin zama,
Karɓi: Angon Aisha mai dogaro ga Allah ka hurce su natsuwa.
A nan ma mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Zamfarci inda ya yi amfani
da ‘ƙarhe’ a matsayin ‘ƙarfe’, ya yi amfani
da Kalmar domin yaba ko wasa ko kururuta ko
wasa mai gidansa, Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi, inda ya yi amfani da
salon abuntarwa.Da kuma ‘hwashi’ a matsayin ‘fashi’ Ya kawo Kalmar domin nuna jarunta ko irin ƙoƙarin da maigidansa ke
yi.Da kuma Kalmar ‘hurce’ mai nufin ‘zarta’ ko fi’ a daidaitacciyar Hausa.
Jagora: Kabiru kilasik na gode Rabbana don
baiwa yai mani ita,
Karɓi: In da gwamnati ke rabon fasaha da na san ba ka
da ita,
Jagora: Sai yaz zan ba magi ba ce da zinari
dolin mijin wata,
Karɓi: Ai ko mina ne kag gani gidan
sarki da irin shi kasuwa.
A wannan baiti a ɗango na ƙarshe mawaƙin ya yi amfani da
ginin tsarin kalmomin Zamfarci, inda ya yi amfani da ‘minane’ ‘kag gani’ Ya yi amfani da waɗannan kalmomi domin
nuna cewa duk abin da ke ga wannan gwamnati to su ma suna da shi, domin sun riƙa kafin su na yanzu
su zo.Kuma wannan habaici ne ya yi ga gwamnati mai ci.. Sai mawaƙin ya yi amfani da
karin harshen Zamfarci.
Jagora: Komai sai da sila kar a bar dalili
tushe na kudandani,
Karɓi: Kwargon masu bara ya cike da tsaba albarkar
rashin gani,
Jagora: Mai nema ka ɗan gajeren bayani na
hana kai hana wani,
Jagora: Kowac ce a yi hurhure na shi yar raina
shi zai yi ƙwaruwa.
A wannan baitin waƙa mawaƙin ya yi amfani da
fasahar saƙa kalmomin Zamfarci maimakon yayi amfani da
daidaitacciyar Hausa, a ɗango na huɗu ya yi amfani da
Kalmar ‘hurhure’ mai nufin
‘musaya’ kuma ya kawo ta ne domin
yin habaici ga waɗan da suka kira shi
cewa ya bisu, inda yake nuna cewa sun raina nasu mawaƙan.Da kuma ‘kowac
ce’ a maimakon ‘kowa ya ce’. Ya yi
amfani da wannan kalma domin ya kammabama maganar da ya yi.
Jagora: Alamonin tashin ƙiyama a ɗauke ilimi ba a ƙaruwa,
Karɓi: Ba neman ilimi kodayaushe jahilci ɗai za shi yaɗuwa,
Jagora: Malamman kuma sun ka zabi duniya
don ƙuna ba su damuwa,
Karɓi: Hayinka
da kuɗɗi na raina ƙasarin kalwa dan ba y
a shawuwa.
A nan mawaƙin ya yi amfani da
Kalmar ‘mallamai’ a maimakon ‘malamai’, Kuma ya yi amfani da ita a nan domin nuna
halin da malamai suka tsintsin kansu a cikin, na rashin bin dokokin Allah da zaɓen duniya, Da kuma
kalamr ‘hayinka’ mai nufin
‘kashedi’ Ya yi amfani da ita domin nuna
yadda kuɗi ke sauya wa mutun
ra’ayi ko kais hi ga halaka.Da kuma Kalmar ‘kuɗɗi’ wadda ke nufin ‘kuɗi’ a daidaitacciyar
Hausa, amma sai ya saƙa ta da tsarin kalmomin
Zamfarci.
Jagora: Ɓarawo in ya gahurta
za ya sata ai ba ya kashae wuta,
Karɓi: Don tsananin iko ya ma kunna Tɓ da ma ga shi ga ita,
Jagora: Na bayar da buhun goro dan karama na bi rabin tiyar
ata,
Karɓi: Gwamma gidan kowa da dauɗa gidana in dai ga ni
da ruwa.
A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da
kalmomin Zamafarci, inda ya yi amfani da Kalmar ‘gahurta’ ya yi amfani da
Kalmar domin nuna yadda wani ke yin sata ba
tare da jin kunyar idanun jama’a ba. Da kuma Kalmar ‘gwamma’ ‘ƙara’ Ya yi amfani da
Kalmar domin nuna son kai.
WAƘAR BILYA SHINKAFI
Turke: Zauna lafiya ɗan Sadauki tashi da layiya,Bilya,
Bilya Shiunkafi duniyar
nan bata rago bace,
Yanzu Abuja mun yi
wakili mai raba gardama Bilya.
Jagora; Bara na gaya ma Bilya irin halayen
duniya,
Kodan ya sani in tuna ma
kunne ya jiya,
Ita kullun tazbaha ta
nai mata kallon tsakiya.
Na runtse idanuna ban
dubin kudun kariya.
A wannan baiti a ɗango na biyu ya yi
amfani da karin harshen Zamfarci, inda ya yi amfani da ‘jiya’ mai nufi ‘ji’, ya yi amfani da Kalmar a
matsayin jin magana a kunne. Wato ya tuna wa wanda yake yi wa waƙar halin duniya
kodayake ya sani. Ya kuma yi amfani da ‘nai’ ya yi amfani da ita a matsayin Kalmar ‘na
yi’.wato aikin da ke nuna aikin da ake
yi.
Jagora: Bilya Shinkafi ɗan siyasa mai raba
gardama,
Komi girman mutum ya bi
ka ya tsira da lalama,
Mai ƙyamar ka Bilya
gidansa tuwansa ɗatun rama,
Mai daraja mijin daga na dace sanin Bilya.
A wannan baiti a ɗango uku ya yi amfani
da kalmar Zamfarci, ‘ɗatu’ mai ma’anar ‘kwado’ a daidaitacciyar Hausa.
Wadda ke nufin haɗa abinci iri biyu,
domin a ci kamar haɗa kuli da ƙanzo ko
makamantansu.Amma a nan mawaƙin ya yi amfani da ita domin
gugar-zana ga maƙiyan Bilya, inda ya
nuna cewa tuwan gidansu bai wuce ɗatun rama ba.
Jagora: Duk mai Bilya gidansa ya fi gaban ya
ci karkare,
Ga wani ya ja da kai
tuwon kwanonai ya ɓare,
Ya faɗa cikin shara to, daɗa bashi da ko ƙire,
Wagga hasara
ta yi yawa daɗa baka da ko miya
Bilya
A nan mawaƙin ya yi amfani da
kalmomin Zamfarci inda ya yi amfani da Kalmar, ‘wagga’ a matsayin
‘wannan’ Wadda ke nuna kusancin mai
magana da abu. Ya yi amfani da ita domin
bayyana irin asara da abokin
hamayyar Bilya ya yi.Da Kalmar ‘hasara’ a matsayin ‘asara’ a daidaitacciyar Hausa. Ya
yiamfani da ita a nan domin nuna faɗuwa.
Jagora: Aminu waziri membanka ya zama gulbin
tsakkiya,
Kowa ya sha sai ya ɗiba kyauta ba biya,
Bilya ya kai muzakkari mai
ɓad da bataliya,
Bilya kad da ka
kasa daure na san ka iya Bilya.
A nan ma Kilasik ya
yi amfanin da kalmomin Zamfarci, kamar inda ya yi amfani da kalmar ‘ɓad’ a maimakon ‘ɓatar’ ya yi amfani da ita a wannan ɗango domin nuna
jarunta ta wannan mutun. Ya kuma yi
amfani da kalmar ‘tsakkiya’ a maiamkon ‘tsakiya’ amma a nan ya yi amfani
da Kalmar a matsayin mahaɗa. Har way au ya yi amfani da kalmar ‘kad’ a matsayin ‘kada’ Ya yi amfani da ita a matsayin shawara, duk da Kalmar tana nuni da korewa ko
hani. Waɗannan duk kalmomin
Zamfarci ne.
Jagora: Bilya Shinkafi martabobi Allah ya yi
maka,
Ga adalci da taimako ga ɗinbin ɗaukaka
Ƙurjin zucciyar
wane yau daɗa sai ya harzuƙa,
Na san yanda kak
kwana yau haka nan kak kwan jiya.
Kilasik ya ya yi
amfani da hikimar saƙa kalmomin Zamfarci a wannan baiti, kamar inda ya yi
amfani da ‘zucciya’ maimakon ‘zuciya’ mai nufin wata tsoka a cikin jikin mutun.
Haka zalika ya yi amfani da ‘’kak kwana’ a
matsayin ‘ka kwana’ , a nan ya yi amfani da Kalmar a matsayin kalma mai nuna
halin da mutun yake ciki.Duk da cewa tana nufin bacci.
Jagora: Shinkafi Jalla kar ya haɗa ka da tuntuɓe,
Bilya duk inda zaka
Jalla yayi maka godaɓe,
Mai Allah ina ruwanai
da gudun wani ya laɓe,
Komai za a ce ma Bilya
Allah ya jiya Bilya.
Mawaƙin ya yi amfani da
kalmomin Zamfarci a wannan baiti, a ɗango na biyu ya yi amfani da Kalmar ‘godabe’ mai nufin ‘titi’ ko ‘hanyar mota’, amma a wannan baiti ya yi
amfani da ita a jagora. Ya kuma yi
da kalmar ‘ruwanai’
a matsayin ruwansa. Ya yi amfani da
ita domin nuna rashin damuwa, ko tsoron
abokin gaba.Da kuma kalmar ;jiya’ mai nufin ‘ji’
Ya kawo Kalmar domin nuna cewa Allah na tare da Bilya.
Jagora: Ga wani ya yi biɗa ka kasai na ga shi
Zariya,
Ya san na ga nai
zai sayan kwandon kayan miya,
Yacce mallan
ka raga man ni ne mutumin jiya,
Sari zan yi in nemi sisi
ya san na jiya.
A nan kilasik ya yi amfani da kalmomin
Zamfarci, kamr inda yace, ‘biɗa’ a matsayin ‘nema’ ya yi amfani da kalmar ne a matsayin takara a
nan. Da kalmar ‘kasai’ mai nufin ‘kada shi’, ya yi amfani da ita
domin nuna faɗuwa.Sai kuma kalmar ‘nai’
maimakon ‘sa’ ko mai nufin mutum na uku, wato shamagana tilo. Haka
kuma ya yi amfani da kalmar ‘Yacce’ maimakon ‘yace’ da Kalmar ‘mallan’ mai nufin ‘malam’, ya yi amfani da ita a matsayin ɗan kasuwa. Haka
zallika ya yi amfani da Kalmar ‘jiya; mai
nufin ‘ji’ a daidaitacciyar Hausa.
Jagora: Mine ne na ɓoyo saboda sana’a ce kakai
In ka samu riba ka sai
dawo in ta yi kai,
Don jarinka bai sayen
shinkafa ƙarya ka kai,
In kuma ka yi zwari
ka taɓe dan shi ka iya.
A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da
kalmar Zamfarci a ɗango na farko, inda
ya yi amafni Kalmar, ‘kakai’ a
matsayin ‘kake’ mai nufin aikin da ake cikin yi, ya yi amfani da ita a nan
domin bayyana aikin da wannan mutn ke yi.A ɗango na huɗu ya yi amfani da kalmar, ‘zwari’ a maimakon ‘zari’ mai nufin wuce-gona-da-iri a
daidaitacciyar Hausa. Amma a nan ya kawo ta domin tsoratarwa.
Jagora: Ni dai in da Allahu yat tsaisan
nan nit tsaya,
PDP nikai ko akwai wani
mai man tambaya,
Shi gulbi komi girmanai
bai kai maliya.
Don haka nir riƙe PDP ta don ita na
iya.
A ɗango na farkon wannan
baiti mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Zamfarci, inda ya yi amfani
da ‘yat tsai san’ a maimakon ‘ya tsaida ni’, ya yi amfani das u domin nuna ɗa’a ko biyayya.Da
kuma ɗango na biyu in day a
yi amfani da ‘nikai’ a maimakon ‘nake’ ya
yi amfani da kalmar domin nuna Jam’iyya da yake. Haka kuma a ɗango
na uku ya yi amfani da ‘girmanai’ a
matsayin ‘girmansa’ ya yi amfani da ita domin kwatance.
WAƘAR IBRAHIM AMMA
Turke: Asalamu alaikum ‘yan’uwa,
Tanbihi ne na zo da shi na gaskiya, Allah ya
gani,
PDP
Ciyaman sai Nasiru Ibrahim Ammani,
Gaba
dai-gaba-dai ba baya ba.
Jagota: Kai birnin Sambo muna nan dai har
yanzu damu bamu ƙaura ba,
Kuma PDP muka yi har yau kuma masu biɗa baku girma ba,
Im ma kun girma da
sauranku hansari ne ku baku ƙusa ba,
Da ma in Allah ya tsaya
ma wani bai iya muzanta ka ba.
A nan Alhaji Kabiru
ya yi amfani da karin harshen Zamafrci, indaya yi amfani da Kalmar ‘hansari’ mai nufin ‘rubabe ko hirtsi” ya yi amfani da kalmar domin nuna ƙaranatr ko kasawar
abokan adawa. Ya kuma yi amfani da kalmar ‘biɗa’ a maimakon ‘nema’ a daidaitacciyar Hausa.Ya yi
amfani da kalmar a matsayin masu neman mulki
Karɓi: Kabiru Kilasik na taso da gudu na ci illar begara,
Ta kwana da yunwa na ɓoye cikin buhu ta ga
tubagara,
Abin ya zarce tinanina
bari in gwama kida kokara,
In dan kyilla ko shingi
kyalla wallahi dai baki tsira ba.
A nan ma mawaƙin yi yi amfani da
kalmar karin harshen Zamfarci inda ya yi amfani da kalamr ‘killa’ mai nufin ‘darni’ a daidaitacciyar Hausa.Ya yi amfani da ita
domin nuna haɗari dake fuskantar
abokan adawa.
Jagora: Karsa yaron masu abinci an ƙware ga satar
malmala,
Kullun fuskatai ga sanhwara
ko dan ya ga tsoka santala
Mu yanzu mun gane ke ka
shigo kaga aikin ƙwanƙwala,
AI dama yaron karuwwai
bai damu ya koma baya ba.
A ɗango na biyu ya yi
amfani da karin harshen Zamfarci inda ya yi amfani da kalmar‘sanhwara’
mai nufin ‘tale’ da kuma Kalmar ‘karuwwai’
maimakon ‘karuwai’ da ake amfani da ita a daidaitacciyar Hausa.
Jagora: Ni ɓarawo na ban shawa in dai ba a kamik ke shi ba,
Shi
wanga ɓarawon an cinmai gudunka ƙato ba ka tsira ba,
Kuma an
ka gwado shi ga NTA aka ce ba hairi ya yi ba,
Am bar
wa iyali abun hwaɗi har yanzu kare bai tuba ba.
A wannan baiti Kilasik ya yi
amfani da kalmomin Zamfarci, kamar kalmar, ‘shawa” a maimakon “sha’awa” , amma a nan mawaƙin ya yi amfani da kalmar a
matsayin ba’a, wato maganar da ba haka ake nufi ba.da. Kuma “kamik
ke” a matsayin ‘kamo’ A ɗango na biyu ya yi amfani da
kalmar “wanga” a maimakon ‘wannan’.
Ya yi amfani da ita domin nuna kusancin shi da wannada yake yi wa zambo. Waɗanan duk kalmomi ne, da ake
amfani da su a karin harshen Zamfarci.
Karɓi: Ya gadi mutunci tun farko sabba ya ɗauke ‘yan’uwa,
Da wane yazan Ciyaman
Gusau, ai gara a yo ɓannanr ruwa,
Ɗandaudu kana da halin
mata wani mai bakin shan romuwa,
Gun fasta yayi wani
gadan-gadan ya aza ban ganikke shi ba.
A wannan baitin ma
Kilasik ya yi amfanin da kalmomin Zamfarci, kamar kalmar ‘sabba’ mai nufin ‘bare’ wato wanda ba ɗan’uwa ba. Da kuma
kalmar ‘ganikke’ maimakon ‘gano’ ya yi amfani da ita a matsayin fahimta.
WAƘAR ABDULLAHI MUHAMMAD TALBAN ZURMI
Turke: Mazan ƙwarai na Mamuda ban
raina ma ba,
Talban Zurmi mijin
Khadija alkairi yay yi,
Mijin Inno Sa’a da taf
fi manyan kaya.
Jagora Mazan ƙwarai suna Zurmi masu ma alfarma,
Irin nau Talban Zurmin
ka ji zakin fama,
A kyauta haza wassalamu
kai ne kurma,
Taho maza ba ji ba gani
kiɗe turɓaya.
A wannan baiti a ɗango na biyu Kilasik
ya yi amfani da karin harshen Zamafrci inda ya yi amfani da kalmar ‘nau’ maimakon ‘nawa’ ya yi amfani da
ita domin nuna dangantaka ko mallaka. Da kuma kalmar ‘kiɗe’ mai nufin ‘ture’ a
daidaitacciyar Hausa, amma shi ya yi amfani da ita a matsayin zuga.Haka zalika
ya yi amfani da kalmar ‘taho’ mai nufin ‘zo’ amma sai ya yi namfani da
Kalmar ta amfani da karin harshe.
Jagora: Ashe gadagi ya zame hasarar gero,
Mawaƙan dauri suna faɗi musamman Ƙwairo,
A bar ni da damma na a
jakkuna in ɗauro,
Idan na gaji kahin zurmi
na huta kurya.
A nan ma mawaƙin ya yi amfani da
kalmomin Zamafrci, inda yace, ‘jakkuna’ maimakon
‘jakuna’ mai nufin jam’i na jakai.kuma ya yi amfani da kalmar ‘kahin’ maimakon ‘kafin’ wanda karin harshen shi ne na Zamfarci.
Karɓi: Kabiru kilasik bana ina da sha’war noma,
Awo dai ya dame ni ga
iyali su ma,
Da gona ta kuyya bakwai na dama ni ma,
Cikin wari na kar
a barni nine baya.
A wannan baiti a ɗango na karshe
Kilasik ya yi amfani da Kalmar ‘wari’ mai
nufin ‘tsara a daidaitacciyar Hausa. Kuma ya yi amfani da ita ne a matsayin
kamancen daidaito.A karin harshen Zamfarci ana amfani da kalmar ‘wari’ domin a
bayyana mutane masu shekaru ɗaya ko tsarar juna.
WAƘAR CIGARIN
ƘAURA “RAMAU TA
FI FARAU ZAFITA”
Turke: Baba dawo baba dawo,
Cigari
I.O maza da mata,
Yara
da manya suna jiranka,
Kacancanta
da mulki Ƙaura,
Dan
ba ka saba da yaudara ba.
JJagora: Kusu ya tare turbar kyanwa ya
ce shege ka bi wuringa,
Karɓi: Ashe kare ya yi mai Katanga da shi da kusu
sun ka yi jinga,
Jagora: In ban cin hwaɗa da mai rabo ya ya
turu za ya ja da ganga,
Karɓi: Kowa dai ya tsaya matsayi nai in ba neman yawan hwaɗa ba.
Kabiru Kilasik ya yi
amfani da kalmomin Zamfarci a cikin wannan baiti. Ya yi amfani da Kalmar ‘kusu’
amma a nan kalmar bay a yi
amfani da ita bane domin nuna ɓarna ko sata, ya yi
amfani da kalmar domin nuna abin da bay a yiwowa ne. Amma a sanadin wani dalili sai ya kasance ya
yiwo. Da kuma Kalmar ‘wuringa’ a
matsayin ‘wajennan’ ya yi amfani da ita
a nan domin nuna bagire.da kuma kalmar ‘hwaɗa’ mai nufin ‘faɗa’ a daidaitacciyar
Hausa.
Jagora: Mai riga da maho an taɓe girtsatstse
bai ƙi cin tayi ba,
Karɓi: Wane siyasa riƙe ta wasa ba gaba ko
yawan hwaɗa ba,
Jagora: Ai in bai yi hwaɗa ba gaba ɗai ya gwaji bai gadi
kangara ba,
Karɓi: Mai neman kuka tun farko ba zai rena ma tunkuɗa ba.
,Anan mawaƙin ya yi amfani da
Kalmar ‘girtsattse’ domin nuna fanɗara ta wannan mutun
da rashin nutsuwa. Da kalmar ‘hwaɗa’ maimakon ‘faɗa’ da kalmar ‘tunkuɗa’ mai nufin ‘turi ko mangaza’, ya yi amfani da ita a nan a matsayin dalili.
Jagora: Halshe ya ji gamin garwashi
rannan ko ƙala bai hwaɗi ba.
Karɓi: Ashe
wurin wargi aka wargi mu ba mu saba da gallaza ba,
Jagora: Zamfara kun ga irin ta ashe MAS ba
mai watse jahar ku ne ba,
Karɓi: Yau bakin magana ya ƙare su wane zaben ku
bai yi kyau ba.
A wannan baiti a ɗango na farko ya yi
amfani kalmar ‘halshe’ maimakon ‘harshe’ ya yi kawo kalmar ne domin nuna raki ko
rashin juriya. Da kuma kalmar ‘wargi’ a matsayin ‘wasa’, amma a nan yana nuna
bambanci ne. Haka kuma, ya yi amfani da kalmar ‘watse’ mai nufin ‘watse’,
amma a nan ya kawo ta ne a domin kariya ga wanda yake yabo. Da kuma kalamr
‘gumi’ mai nufin ‘zafi’ ko ‘kaifi’ misali, kamar mutum yace, yajin nan ya cika
gumi.
Jagora: Mallamai ko dai ku bi Allah
kad da ku manta da Annabinku,
Karɓi: Dan Allah ku ji tsoron Allah kun san kabri yana
jiran ku,
Jagora: Bayan wannan cikin kushewa mala’iku za su tambayar ku,
Karɓi: Akwai azaba wurin mutum in dai bai amsa
ma tambaya ba.
A nan Kilasik ya yi
amfani da karin Harshin Zamfarci, kamar ‘mallamai’ a matsayin ‘malamai’ kalmar suna ne, amma a nan jam’in sunanan
ne.Ya yi amafani da ita domin jawo
hankali da bada shawara.da kuma ‘wurin’
a matsayin ‘wajen’ amma a nan ya yi amfani da ita ne, a matsayin kalma mai nuna
dangataka.Wanɗannanhduk kalmomin
karin Harshen Zamfarci ne.
Jagora: In su ɗai suke babu bagarde kare da kura ba
su ƙawance,
Karɓi: Wagga siyasa ni na gane cikin biyat ukku
yaudara ce,
Jagora: In bayan gyaran addini yanzu siyasa
abun gudu ce,
Karɓi: Guda-gudatta baƙar manufa ce ba wai
duk zani ambata ba.
A wannan baiti
Kilasik ya yi amfani da ginin kalmoni Zamfarci, karma inda yace, ‘wagga’ maimakon ‘wannan’ da kuma Kalmar
‘abun’
maimakon ‘abin’ sai kumaa Kalmar’ukku’
mai nufin ‘uku’ da Kalmar ‘biyat’ maimakon ‘biyar’ . Haka kuma inda yace, ‘guda-gudatta’ maimakon ‘guda-gudarta’ ya yi amfani da kalmomin domin nuna adadi.
WAƘAR BACIRI SARKIN
FULANI
Turke: PDP zan yabawa, Fati mai karramawa,
Baciri sarkin Fulani,
Maru Bunguɗu shi za mu zaɓa.
Jagora: Wanga in lokacin kamfen ya zo ban
san me za yace ba!
Shi
da maigidanai wani ƙauyen in sun tafi ba zasu sha ba,
Maigidan
burgu shi kuma kusu, Allah waddan ku ban ruhe ba,
Ita
ijjiya in in tana ruwa kwali tuzali in ayo ba za ya yi ba.
A nan ma Kabiru
Kliasik ya yi amfani da kalmomin Zamfarci, ya yi amfani da Kalmar ‘matanai’
maimakon ‘matansa’ ya yi
amfani da ita domin nuna alaƙa.Da kuma “gidanai” a maimakon ‘danginai’ , ya kawo kalmar
domin nuna mallaka.Har way au ya yi amfani da kalmar ‘wanga’ mai nufin ‘wannan’.
Da kalmar “burgu” amma a nan yana nufin babban ɓarawo. kalmar “kusu” kuwa, yana nufin ɓarawo ƙarami, Idan muka lura
za mu ga cewa kusan duk da kalmomin karin Harshen Zamfarci mawaƙin ya gina wannan
baiti.
Jagora: Zomon bana kad da ka hau turba don na ga kare na jiran ka,
Baƙin maƙwabci mai cin gona
duk ya ɗebe min iyaka,
Wanga
cin iyaka ya yi yawa ranar tsayuwa kaico kanka!
Da dai
ka mayar tun a duniya ba yahe ma zani yi ba.
Mawƙin ya yi amfani da
kalmomin Zamfarci a cikin wannan baiti, ya yi amfani da ‘’kad da’ maimkaon ‘ka da’ ya yi amfani da kalmar domin yin kashedi, ko hani.Da kuma ‘ɗebe’ mai nufin ‘cire’ ya yi amfani da kalmar ne, domin nuna irin
zaluncin da aka yi masa. Haka kuma, ya yi amfani da ‘yahe’ a matsayin ‘yafe’ da
kuma ‘wanga’ a maimakon ‘wannan’. Idan muka lura mawaƙin ya yi aiki da
karin harshen shi na Zamfarci.Inda ya yi amfani da Kalmar ‘hanƙuri’ maimakon ‘haƙuri’ da kuma ‘hannunai’ maimakon ‘hannunsa’ haka kuma ya yi
amfani da ‘kaɗa’ a matsayin
‘auduga’ a daidaitacciyar Hausa.
Jagora: Burgu tafi da gidan ka yakai,
akwatin sawa a ce kumatu,
Shi nan
yaka ɓoye gujjiyatai domin
ta biya mai buƙatu,
Mai gyaɗa cikin baki jama’a
ya zaya fahimatr karatu?
Idan
mallami ya ce ya faɗi da alama ba zai faɗi ba.
A nan ma Kilasik ya
shigar da wasu kalmomi na karin Harshen Zamfarci, kamar Kalmar ‘burgu’ mai nufin ‘gafiya’ da ma kalmar
‘gujjiya’ mai nufin ‘giɗa’ a ɗango na huɗu ya yi amfani da kalmar ‘mallami’ maimakon ‘malami. Da muke da shi a
daidaitacciyar Hausa.
Jagora: Kowane tsuntsu ya dai riƙe kukan gidansu,
Komai
lalacewar mussa ku san cewa ta hi kusu,
Waɗansu maza sun mace,
Allah Ka jiƙan su,
Sun
shiga ramin da ba matsera ba hitowa ba.
A wannan bati Kilasik
ya yi amfani da ginin kalmomin Zamfarci
inda ya yi amfani da kalmar ‘kusu’
wadda ke nufin ‘ɓera’ da kuma kalmar ‘mace’ wadda ke nufin ‘mutu’ a
daidaitacciyar Hausa. Haka kuma ya yi amfani da kalmar ‘mussa’ mai nufin ‘mage ko
kyanwa. Sai kuma kalmar ‘hitowa’ maimakon
‘fitowa’ da kuma ‘hi’ maimakon ‘fi’, Waɗannan duk kalmomin Zamfarci ne.
Turke: Mu Shinkafi mun gode Allah bai bar mu ƙarshe ba,
Koguna za ya sake
maimaici Allah ya riga ya yi,
Ya Allah mun yi godiya
jama’a bas u ba mu baya ba.
Jagora: ‘Yan Shinkafi salamu alaikum na zo
nuna tau baiwa,
Yaro
har da manya da tsawhi i ba na tsambarin kowa,
Mata
har da ku a waƙata ba na sanya gaugawa,
Tun da
fashin baƙi ya tashi taɓarya ba zata ƙahwa ba.
A nan mawaƙin ya yi amfani da
kalmomin Zamfarci karma kalmar ‘tsawhi’
mai nufin ‘tsofaffi’ da kalmar ‘gaugawa’ maimakon ‘gaggawa’, ya yi amfani da kalmar
domin nuna nutsuwa. Haka zalika ya yi amfani da kalmar ‘ƙanhwa’ a matsayin ‘ƙanfa’. Ya yi amfani da ita domin nuna gushewar abu y
azan babu shi.Idan muka lura a nan mawaƙin ya yi amfani ne,
da tsarin kalmomin karin Harshen shi na Zamfarci kansancewar shi Bazamfare.
Jagora: Mai alka ga kumci ta goge biɗi wanzami ya tusa
maka,
Karɓi: Ko ka taɓa jin ban kaunarka yau na shirya na faɗa maka,
Jagora: Cire takalmiki ƙawar waƙa na yarda da ke ki
wuce ɗaka,
Karɓi: Omo shi ne babban gaccin dauɗar matar ɗan garuwa ba..
A wannan baiti a ɗango farko Kilasik ya
yi amfani da Kalmar “alka” mzi nufin
‘tsaga’ ya yi amfani da ita a nan domin
yin zambo. Da kuma Kalmar “biɗa” mai nufin ‘nema’.
Haka kuma, ya yi amfani da Kalmar “ɗaka” mai nufin ‘cikin ɗaki’ Wadannan duk
kalmomin karin harshen Zamfarci ne.
4.5 Kammalawa
Kamar yadda bayani ya
gabata, wannan babi shi ne ƙashin bayan wannan aiki. Kuma a cikin
shi ne aka yi cikkaken bayanin wurare da
baituttukan na waƙoƙi da Kilasik ya yi amfani da karin harshen Zamfaci na waƙoƙinsa da aka nazarta.
Haka zalika, an yi bayanin ma’anr kalmomi, da tsarin kalmomin Zamfarci,
kamaryadda Kabiru Kilasik ya yiamfani da su a cikin waƙoƙinsa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.