Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau
Karin Harshen
Zamfarci (Musamman A Garin Gusau) (1)
NA
BASHIRU HARUNA
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan bincike ne ga kakannina da iyayena da wanda ya bani gudunmuwa wajen karatu da kuma dukkan
malamai na da abokanan karatu na. Allah (S.W.T) ya saka musu da mafificin
alhairi.
GODIYA
Godiya ta tabbata ga Ubangiji Subhanahu Wata’ala mai kowa mai komai mai iko
a kan komi wanda ya halicci ‘yan Adam da kuma Duniya baki ɗaya da ya ba ni damar kammala wannan aiki.
Ina kuma miƙa godiya ta musamman ga kakannina malan Haruna da Malama Hauwa’u, waɗanda su ne suka yi mini tarbiya, da kuma mahaifaina,
Alhaji Sani Ibrahim da hajiya Hauwa’u Abubakar da kuma Alhaji Abdullahi Musa
wanda ya taimakaman sosai da Hajiya Saratu Ibrahim Birnin tsaba Allah ya saka
musu da alhairi.
Bayan haka, ina miƙa godiya ta musamman ga malamaina Malam Isah Sarkin Fada da ya ba ni
gagarumar gudunmuwa ta hanyar shawarwari da taimako da kulawa domin ganin na samu
nasarar wannan aiki, Allah ya saka masa da alhairi Amin.
Haka kuma ina miƙa godiya ta musamman ga malaman wannana sashe, sashen Harsuna da Al’adu
Jami’ar a fagena neman ilimi, ta hanyar shawarwari, da fatan alhairi da kuma
gudunmuwarsu ta yau da kullum: Farfasa Aliyu Muhammad Bunza, da Farfesa Ahmad
Haliru Amfani da Farafesa Atiku Ahmad Dunfawa da Farfesa Abdulhamid Ɗantumbishi da Farfesa,
Magaji Tsoho Yakawada da Farfesa Balarabe Abdullahi, da Farfesa Aliyu Musa da
Dr. Y. A Gobir da Dr. A. S Gulbi da Dr. M. G Fadama da Dr. R. Bakura da Dr.
Salisu Sadi Tsafe da Malam Aliyu Ɗangulbi da malam Musa Abdullahi. Allah ya saka musu da
mafificin alhairinsa. Amin.
Haka zalika, ina miƙa godiyata ga ‘yan uwana maza da mata da abokaina bisa goyon bayan da
taimako da shawarwari da suka bani tun farkon fara karatu na har zuwa kammalawa
kamar: Shehu Aminu da Yahaya Usman Bakura da Lawali Harun da Khadija barau
Sulaiman da fatima Abba Zanna da Ruƙayya Ɗanjuma da Musa Abdullahi da Talatu Haruna da Hafasat
Dauda da Haruna Abubakar Harun. Allah ya saka masu da alhairi.
Haka kuma, ina godiyata ga abokan karatuna a kan shawarwari da taimako da
suka bani kamar Mukhtar Abubakar da Sama’ila Aliyu da Shafa’atu Salihu Labbo da
Jafar Usman da sadiya kabir da Umar Yahaya Dogara da Aminu Muratala da
Abdulrahman Lawali da Bilya Umar.
ƊUNGURMIN NAU’I (ABBREƁIATION)
/ / = Alamar ƙwayar sauti
D. H = Daidaitacciyar Hausa
K.H.G
= Karin Harshen Gusau
0 Comments
Post your comment or ask a question.