Ticker

6/recent/ticker-posts

Ganuwar Gusau Da Kofofinta (5)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Ganuwar Gusau Da Kofofinta (5)

NA

UMAR YAHAYA DOGARA

Ganuwa

BABI NA HUƊU

KOFOFIN GUSAU

4.0 Shimfiɗa

             A babi daya gabata, watau babi na uku binciken ya duba, ganuwar Gusau da tarihin ganuwar Gusau da tasirin ganuwa a gari da kuma naɗewa. Ban samu wani kundi da ya yi bayani akan ƙofofin ko nazari game da ƙofofin Gusau ba, wannan babi zai yi bayani a kan, ƙofofin Gusau da sharhi ƙofofin Gusau da kuma wasu Unguwoyin Gusau, da kuma Gusau a matsayin babban birnin jahar zamfara, da naɗewa, wannan shine makasudin wannan babi.

4.1 Ƙofofin Gusau

1.      Ƙofar kwatarkwashi

2.      Ƙofar Katsaura

3.      Ƙofar Rawayya

4.      Ƙofar Goje

5.      Ƙofar Dogo/Dokau

6.      Ƙofar Tubani

7.      Ƙofar Mani

8.      Ƙofar Jange

9.     

Ƙofar Matsattsa

 

 

 

 

 

 

Taswira mai nuna ƙofofin birnin Gusau

Ganuwa da ƙofofin Gusau an samar dasu a sanadiyyar yaƙe-yaƙe da hare-hare da ake fuskanta ne wannan zamani, an gina wannan ganuwa da ƙofofi a lokacin Sarkin Katsinan Gusau, Malam Abdulƙadir a zamin Sarkin Musulmi, Amadu dan Atiku a shekara (1859) dukkan rubuce – rubuce da aka yi akan garin Gusau ba wani akan ƙofofin Gusau wannan kundin shi ne na farko da zai yi bayanin akan ƙofofin da asalin su da kafa su, ya amfani da yin hira da mutane tsofaffin masu shekaru kuma yan asalin wanna garin na Gusau.

4.2 Sharhin ƙofofin Gusau

            Kamar yadda nayi bayani tun farko babu wani littafi ko kundi da ya yi sharhin ƙofofin Gusau da asalin su. 

ƘOFAR KWATARKWASHI

            Ƙofar kwatarkwashi na samu bayanai daga masana guda biyu zuwa uku, sun tabbatar da samuwar wannan ƙofa kuma sun fadi dai-dai inda ƙofar take, ƙofar tana nan wurin MTD kusa da tankin ruwa dake sabon gari. Ita wannan ƙofa babba ce kamar cibiya ƙofa wadda ke shigowa zuwa cikin tsakiyar garin Gusau, (Alhaji Muhammadu Kwazo Sarkin Noma. 2018) yace “ A lokacin da aka gina ganuwar an bude wannan ƙofar ne saboda mutanen kwatarkwashi, da ke shigowa Gusau domin yin hulɗoɗin kasuwanci na cinikayya da sauran mu’amaloli yau da kullum, haka shi ya sa aka saka mata sunan ƙofar kwatarkwashi. Sannan masu tsaron wannan ƙofar basu bari kowa ya shigo ta wannan ƙofa, sai mutanen kwatarkwashi, domin su aka gina ma wannan ƙofar, saboda haka akwai tsari da shamakance ta babu mutane da ke shigowa ta wannan ƙofa sai mutnane kwatarkwashi. Idan wani ya zo wanda baya a cikin su ba za’a bar shi ya shigo ba. Haka kuma mutanen Gusau idan zasu fita zuwa kwatarkwashi ta wannan ƙofa suke bi.

Alhaji Bello ɗan mai tuwo hirar da nayi dashi yace “Ƙofar tana nan a wannan bangare na wurin MTD wurin tankin ruwa”. A halin yanzu ƙofar kwatarkwashi tana cikin yankin sabon gari.

ƘOFAR KATSAURA

            Wannan ƙofa itama, akwai ra’ayyi akanta, Alhaji Sulaiman (Makaho) mai shekara (95) ya tabbatar mana da cewa, ƙofar tana nana unguwar toka dai-dai wurin inda ake wankin ‘yankunne kusa da ginda burodi, wurin gidan ‘yan darika a yanzu. Ya bayyana man cewa asalin Kalmar katsaura sunan mutumen katsaura, kuma mutumin garin Nahuce ne, a lokacin da a ka ba Malam Sambo ɗan Ashafa tuta, ya biyo ta garin Nahuce ya faɗa masa cewa an gama yaƙi kuma Shaihu Usman Ɗanfodiyo,  ya bashi tuta, sai Malam Sambo ɗan Ashafa ya nemi Katsaura daya biyo shi Gusau, su zauna. Katsaura yace sai ya nemi izinin ‘yan uwansa sai ya tambayi ‘yan uwansa kuma suka bashi dama, sai ya biyo Malam ambo ɗan Ashafa ya zo Gusau ya zauna (Malam Adamu Minista hirar mu 2018) yace” ƙofa tana nana Unguwar toka wurin gidan ‘yandarki amma sai dai ya nuna cewa katsaura saunan gari ne wanda cikin garin Bunga kusa da garin Ƙaura-Namoda. Idan aka duba lokacin da aka yi ganuwa Sarkin Musulmi Amadu Dan Atiku (1859) ya ummurci da mutana Ƙaura Namoda da su taimaka wurin ginin ganuwar Gusau. Zai iya yiyuwa mutane Bunga da Katsaura sun taimaka wurin aikin kuma sun yi har aka sakawa ɗaya daga cikin ƙofofin sunan garin. Ala kulli halin waɗannan sune ra’ayoyin da suka zo a game da wannan ƙofar ta katsaura, kuma kowannen su zai iya kasancewa. Sarkin Noma Muhammadu Ƙwazo, ya tabbatar da cewa tananan Unguwar toka. A halin yanzu ƙofar katsaura tana cikin yankin Madawaki.

ƘOFAR RAWAYYA.

Akwai ra’ayoyi na mutane akan inda wannan ƙofa take, asalin ƙofar Rawayya, ƙofar Rawayya an kafa tane saboda mutane garin Rawayya da suke shigowa ta wannan ƙofa idan sun zo kasuwanci Gusau, haka mutanen Gusau idan za su tafi Rawayya ta wannan ƙofa suka bi, Bisa bayanin da na samu daga hirar da nayi da (Garba mai Gudu a shekarar 2018) yace “ya nuna man cewa ƙofar tana nan a bakin tsohuwar kasuwa wurin gidan Alhaji Goga kusa da gidan Makera, Alhaji korar hirar da nayi da shi yace” ya tabbatar man da cewa tana nan wurin shigo wurin da ake said a magani na nasiha dake tsohuwar kasuwa” Sarkin Noma Muhammad Kwazo yace” ya nuna cewa ƙofar Rawayya tananan dai-dai shagon sule mamuda da ke tsohuwar kasuwa kusa da gidan ɗan Iya”. Haka kuma bisa ga hirar da nayi da, Aliyu Rufa’I Gusau (ɗan Masanin Wonaka) mazauni ƙofar yana kusa da shagon Sule Mamuda . sai dai mun tafi akan bayanin da muka samu daga jikan mai tsaron ƙofar cewa muhallin ƙofar a yanzu yana dai-dai da gindan Alhaji Ammani a tsohuwar kasuwa wurin shagon sai da magani na Bayanaka. In ji Bello Ummaru ƙofa, hirar mu da shi ya.

Idan aka tattara dukkan waɗannan bayanai za’a ga cewa ƙofar Rawayya tana nan dai a wannan yanki na tsohuwar kasuwa tsakanin shagon Sule Mamuda da Nasiha. Zai iya yiyuwa ƙofar babba ce tana da tsayi sosai ta yadda tsawonta zai iya game dukkan wannan yanki bayanin jikokin waɗanda suka yi tsaron ƙofar, sunan mai tsaron ƙofar Rawayya, Muhammadu ƙofa, manomine kuma makeri ne, zuri’ar sa har yanzu tana wanzuwa kuma gidan sa yana na gab da gidan Alhaji Idi Mai kwai, bakin kasuwa tsohuwa. Daga cikin jokokin sa akwai, Bello Ummar Muhammad ƙofa. A halin yanzu ƙofar rawayya tana cikin yankin rikon Galadima idan aka shiga mazaunin ƙofar Rawayya; daga  gabas zata sadar  da mutum zuwa tsohuwar tasha, daga yamma zata sadar da mutum zuwa makabarta da gangaren gulbi, kudu kanwuri da zawiyya daga arewa, asibitin Farida.

ƘOFAR GOJE

            Wannan ƙofa kamar yadda marubuta tarihi suka rubuta akwai sunan wannan ƙofa, to amma a cikin binciken nawa, ban samu tabbacin inda wannan ƙofar take. Sannan a cikin mutanen da na yi fira da su, suna gayaman Gusau tana da kofofi guda tara (9) amman ba su san wannan ƙofa ba, amman duk rubuta da akayi a wannan gari na Gusau ana sanya sunan wannan kofar ta goje, amman dukkan mutanen da na yi fira dasu sukan gayaman cewa ba su san da wannan ƙofar ba, sai dai sukance man abin da ake nufi da goje shi ne manomi, kila takan iya yiyuwa ƙofa ce ta hanyar manoma wato hanya ce ƙila ta manoma.

ƘOFAR  DOGO/DOKAU

            Kamar yadda na samu bayanai daga ma zauna wannan garin na Gusau, domin su bani bayani in da ƙofar ta ke ta dogo, duk wanda naje wurinsa na tambaye shi sai dai ya yi maganar ƙofar dokau suka sani, ba kofar dogo ba. Haka kuma dukkan wanɗanda na sami bayani wurins su suna lissafawa da ƙofar dokau, amman basu lissafawa da ƙofar dogo bayan haka akwai wasu mutane dake cewa akwai ƙofar dogo, idan na tambayi ƙarin haske sai su kawo min littattfan da aka rubuta takan iya kasancewa ƙila ƙofar dokau ce, sai suce ƙofar dogo. Kuma babu wani littafi da ya yi bayani ko sharhin waɗannan ƙofofin na Gusau.

            Ƙofar dokau, ƙofa ce ta mu’amala tsakani mutanen garin Gusau, da na mutanen garin dokau, mutane Gusau sukan bi hanyar zuwa dokau, haka mutanen dakau, kamar yadda muka samu bayani wurin sarkin noma Alh. Hassan Muh’d Ƙwazo. Ya sheda muna cewa wannan ƙofar ta dokau na nan wurin filin gunza, wurin gidan ‘yan goro, shi ma Malam Shehu Ladan Kurmi, ya gayaman ƙofar dokau tana nan wurin gidn mai shanu wurin gidan ‘yan goro. Ƙofar dokau tana cikin yankin Gundumar Mayana, a gabas za ta kai ka maƙera ta tsohuwar silima, kudu za ta kai ka kwanar birnin ruwa, yamma za ta kai ka gidan sarkin kudu.

ƘOFAR TUBANI

            Ƙofar tubani ɗaya ce daga cikin ƙofofin Gusau. Mazaunin wanna ƙofar tana nan wurin bayan maƙera ta gidan Isah Mayana, yanzu haka, (Hirarmu da Malam Sani Madugu da Sani Ɗan Kwamma da Sarkin Noma Muhammadu Ƙwazo kamar yadda na samu bayanin, shi tubani manomi ne, kuma shine ya yi tsaron kofar, babu wanda ya sami asalin sa kamar yadda mazuana wurin suka fada. ƙofar na nan kusa da ginda Muhammadu Noma, kusa da inji nin nika, kamin zawuyya da gabas tana fita da mutum ƙofar mani daga kudu, yamma kuma gan garen na damau zuwa kauyoka, ƙofar na cikn rikon Mayana.

ƘOFAR MANI

            Ƙofar Mani na daya daga cikin ƙofofin Gusau, ta amu sunan ta ne daga wani mutum manomi mai suna Mani. Ma zaunin ta a yau unguwar kofar mani (an sakawa unguwar sun ƙofar Mani) ƙofar na nan inda wata ‘yar kasuwa take, kuma gidan shi mani yana nan gefe ana satar da hatsi a wurin. A dukkan binciken da na yi ban samu wani birbishin zuri’ar Mani ba, haka na iya nuna cewa bai taba haihuwa a rayuwarsa ba. (Hirar da nayi da Malam Audu Mai wanki 2018) mazauni unguwar ƙofar mani mai shekara (80) a duniya, haka kuma akwai Malam Yahaya wanda yake makwabcin gidan Mani. A halin yanzu kofar Mani tana cikin yankin Mayana, idan aka shigo ta mazaunin ƙofar Mani daga gabas zata iya kai mutum makarantar boko ta “kanwuri” zuwa gidan sarki, da kuma unguwar zawuyya, da tullukawa har zuwa gulbi.

ƘOFAR JANGE 

            Ƙofar Jange asalin muhallin da, ƙofar mashaya ce; wuri ne da yake magudanar ruwa mutane na dibar ruwa a wurin kuma suna shayar da dabbobin su, Jange sunan wani mutum ne Mayaƙi, Jarumi, Maharbi, da ke zaune a wurin yana farautar namun daji lokacin da aka gina ganuwa sai aka sakawa ƙofar da ke wurin sunansa. ƙofar ta na nan kusa da gidansa gaba kadan da gidan Alhaji Namadi Bola. Gidansa har yanzu yana na kuma na samu shiga gidan har muka yi fira da wata mace mai suna Indo mai shekera (80) daga cikin zuri’arsa, kuma na samu wasu kayan tarihi das hi Jange ya bari. Ba’a shigowa Gusau ta wannan ƙofar. Asalin jange badakkare ne ya fito daga garin Zuru, babban sadauki ne wanda an nuna cewa ba’a taba cinsa yaƙi ba. Jikan yarsa Indo ta sheda man cewa har yanzu duk Jarumnta wadda suka yi gado daga kakan su. ƙofar Jange tana daga cikin ƙofofin Gusau da suka samu shahara da daukaka har yanzu sunan yana wanzuwa ko karamin, yaro aka tambaya za’a ga cewa ya san wannan ƙofa dalilin da haka har aka sakawa Unguwar dake kusa da wurin sunan ƙofar Jange. A halin yanzu ƙofar Jange tana cikin yankin Galadima.

KOFAR MATSATTSA

            Ƙofar matsattsa a yau mazauni ta yana nan a marnar talilkkai gab da makaranta Allo ta Malam Sanda Asalin wannan ƙofa sanadiyyar wani da ake kira “kako” kakansu (Senator Hassan Nasiha da Muhammadu Bawai) wanda mutumin Katsina ne ya fito daga ‘yan Tumaki. Lokacin da ya zo Gusau, sai ya tafi bayan gari ya zauna, saboda sansanin ne na mayaƙa, nan suke bi. Ammamn shi kuma kako ya nuna dai nan yake so a bashi, karshe dai ya bashi mazauni a bayan gari ya zauna, wannan a sandiyyar sa ne aka gina wannnan ƙofa. Idan mayaƙa sun shigo sai masu tsaron ƙofar su bede masa ya shigo cikin gari, sannan a rufe, idan sun wuce ya dawo wurin sa. (Hirar da nayi da Muhammadu na Kumgu mai shekara 103) yana zaune a marnanr talikkai, Malam Muhammadu ya bani labarin cewa kakansa ya yi tsaron wannan ƙofar ta matsattsa. Sunan kakan na sa Muhammadu ɗan Mairi, it ace ƙofa  ta ƙarshe cikin ƙofofin Gusau. A yau ƙofar matsatstsa tana cikin yankin Galadima, daga gabas zata sadar da mutum, rijiyr sarki da ƙofar Rawayya da kasuwa, yamma makabarta kudu ƙofar Jange, Arewa danfili da Sabon fegi.

Kamar yadda na faɗa a cikin bayanai a baya ana radawa kofa suna sanadiyar wata salsala ko kuma nasaba kofa dai tana samun asalin suna sanadiyar wata nasaba, idan muka duba tsofoffin garuruwa waɗanda suke da ƙofofi, duk suna da wata nasaba daya da aka rada masu suna. A nan garin Gusau ƙofofin namu sun, samu suna ne sanadiar wasu nasabobi: Misali: kamar ƙofar rawayya da ƙofar kwatarkwashi da kuma ƙofar Mani, da Jange, wadannan ƙofofin akwai dalilin raɗa masu waɗannan sunaye. Jange mutun ne kuma shi ke tsaron ƙofar, haka  ƙofar Mani mutun ne zarumi kuma manomi, sannan ƙofar kwatarkwashi an rada mata suna ne saboda mu’amala dake tsakenin Gusau da Kwatarkwashi ita ma ƙofar Rawayya mu’amala dake akwai tsakanin mutanen Gusau da na Rawayya, haka kuma ita ma ƙofar dogo/dokau.

4.3 WASU UNGUWOYIN GUSAU

            Garin Gusau ya samu cigaba da habaka da bunkasa da kere-keren ganuwa, saboda wasu mutane baki, a bisa ga wannan karuwa Gusau ta Samu wasu shiyoyi da kuma Unguwoyi da yawa, a cikin littafin (Gusau ta Malam Sambo 2012) an yi bayanin Unguwoyin Gusau.

SABON FEGI. A zamanin Sarkin Katsina Gusau Muhammadu Bello mai a kwai (1929-1943) aka yayyanka gonaki aka ba mutnae fegi fegi son su samu wurin zama kamarsu , Hassan Maigwada, Basakwacce da Mamman Audu Bazzazagi mai dinkin Tela, Sune suka fara zama wurin da kuma, Halilu Emos Bakatsine da sauran su. Ana kiran Unguwar da wannan suna saboda fegogi ne sababbi aka rarraba wa ja’ama, wannan unguwa yanzu ta samu bunkasa da haЪaka da yalwa ta ƙara samun yawan mutane saЪanin wancan lokacin kamar Alhaji Ɗan Manga, Alhaji Umar Tanko, da Alhaji Aliyu Haido duk suna cikin wannan yanki na sabon fegi ayanzu, Tana karkashin ri kon Galadima.

SHIYYAR TUDUN WADA

Lokacin da aka yi ƙarin kasuwa da asibiti aka tayar da mutane da ke wurin wato unguwar ka-fama-ni aka mayar da Tudun Wada a 1958. Da mutane suka koma wurin sai suka yalwata, suka wadata, sai suka rika kiran sa da sunan tudun wada, wurin da mima wato tudun wada mai wada ta (Hirarmu da kungiya mutane 1978). Unguwar tudun wada ta kafu ne a zamanin Sarkin Kudun Gusau (1948). Yanzun shiyar tasamu bunƙasa da ha Ъaka da yalwa da yawan mutane, Kamar Alhaji Shehu Idirs Zuru, Alhaji Ibrahim Ruwan Dorawa, Alhaji Aminun Makaranta, Alhaji Abdullahi Zabarma, da Farfesa Bawa Hassan, tana cikin yankin Gundumar Tudun Wada.

 

SABON GARI

Wannan unguwa wani mutumin siraliyo ne Wanda ake cewa Morgan ya fara zama a cikin, kuma ya riki mai unguwarta, kafin ta sami hakimi, a lokacin Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai’akwai (1929) Morgan shi ne ya fara karЪar haraji a wurin, daga baya, ta sami magaji Muhamamdu Taula wanda aka ɗauka daga mada ya zama hakiminta na tan a farko. Da tafiya ta mika aka sami kabilu daban-daban suka zauna a wannan unguwa ta sabon gari, daga cikin akwai Igbo da Yarbawa da wasu Hausawa, yanzun wannan unguwa ta samu bunƙasa da ƙaruwar jama’a, kamar su Alhaji Ladan Mada, Alhaji Adamu Samanja, tana cikin gundumar sabon gari.

BIRNIN RUWA  

Ana kiran wannan wuri da suna Birnin Ruwa, saboda wuri ne mai dausayi da ni’imar sanyi, wuri ne har ko da yaushe baya rabo da ruwa a lokacin damina, a zamanin Sarkin Gusau Muhammadu TuЪuri (1976) a nan ne kuma aka yi wa mutane da ake turawa Jos zuwa aikin masauki kuma ake fara aikin B.C.G.A har wayau, nan leburorin zinare suka yi wa kan su dakunan bacci. Daga nan, unguwar ta bunkasa har a zamanin Sarkin Katsina Gusau Muhamamdu Giɗe ya haɗa tada birnin haza Matsayin hakimi ɗaya ubandawaki Buharin Haza, wannan unguwa yanzu ta kara samu habaka da bunkasar mutane, tana cikin gundumar Mayana.

‘YARLOKO

Wannan unguwa ta tsiru azamnin Sarkin Katsinan Gusau ummaru Malam  (1917-1929) mutane sun fara zama a wurin a shekara 1929, lokacin da masu aikin tashar jirgin kasa suka kafa dakunan baccin su a wurin. Daga cikin ma’aikatan jirgin kasan akwai kabilar Fulani da suaran wasu mutane (Hirarmu da M.M.W.N Gusau 1978).

4. 4 GUSAU A MASTAYIN BABBAN BIRNIN JAHAR ZAMFARA

            an kirkiro Jihar Zamfara daga tsohuwar jihar sakkwato ta wancan lokaci, jihar tayi iyaka da jihar sakkwato daga arewa, jihar katsina daga gabas, Jihar niger daga yamma, da kuma jiihar Kaduna daga kudu, kanana hukumomin zamfara bayan Gusau, sun kunshi:- Gummi, Kaura-Namoda, Shinkafi, Birnin Magaji, Tsafe, Bakura da Zurmi, an nada kanar Jibril Bala Yakubu, FSS, Mss, Pcs Matsayin gwannan farko na jihar zamfara.

            Gwagwarmaya day akin neman jihar zamfara abu  ne mai tarihi a kasar zamfara ta kasance daula ce mai cin gashin kanta tun a da c an kamar yadda masana tarihi suka rubuta. Kasa ce mai tsarin muliki da tarihin sarauta da tayi gwagwarmaya da yake-yake da gobirawa da kabawa da katsinawa. Bayan zuwan turawan mulkin mallaka sai daulolin Hausa suka fadi kuma tsarin mulkin gargajiya da iyakokin kasa ya samu sauye-sauye masu yawa. Turawa a farko sun raba yankin arewa zuwa larduna sannan daga baya sai suka kirkiro jihohi, bayan samu ‘yanci kai a shekarar 1960 sai kasar zamfara ta zamanto karkashin rikon tsohuwar jihar sakkwato. Kasancewar zamfara kasa ce mai yalwar mutane, karfin nomad a kiwo ingantaccen tattalin arziki, da tarihin albarkatun kasa ne ya kara kaimi ga ‘yan jihar wurin dagewa da kokarin akan fara yakin neman kafuwar jihar zamfara mai zaman kanta.

            Duk wasu alkalumma da sharudda da ake bukatar cikawa domin jiha ta samu ikon zama da kafa funwanta kasar zamfara ta cika su. Hakan ya nuna cewa kasar zamfara za ta iya rike kanta a matsayin jiha mai cin gashin kanta. Wannan hakikancewa shi ne mafarin guguwar yakin neman jihar zamfara inda wasu zakarkaru, jajirtattu, hazikan ‘ya’yan jihar suka zage damtse, wurin fafutuka, rook, lallashi, kai kawo, da yekuwar ganin cewa wannan mafarki na su ya zama gaskiya.

        A shekarar 1962 ne mutane zamfara suka fara yunkurin neman tabbatuwar jihar zamfar mai zaman kanta, amma sai aka binne yunkurin har tsawon shekara ashirin (1962-1982). A zamanin mulkin shehu shagari sai yunkurin ya dawo inda mutanen zamfara suka gabatar da kudurin neman kafa jihar zamfara daga jihar sakkwato a gaban majalisar  dokokin ta kasa. Daga acikin kudorora sittin da biyar (65) da aka gabatar a Majalisa, kudurin kafa jihar zamfara shi ne a sama, gwannatin fara hula ta Sheh Shagari ta hango da cewa da cancantar kafa jihar zamfara kuma tayi a zamar aiwatar da haka amma sai akahambara da ita a juyin mulki shekara 1983 (Zamfara state hand book, 1997:4).

              Haka aka yi a shekara 1991, zamanin mulkin Gen. Ibrahim Badamasi Babangida lokacin da aka kirkiro jijohi tara (9) jihar zamfara tana daya daga cikin jerin sunayen jihohin da za’a bayar amman daga karshe sai aka canza aka baiwa jihar Kebbi wadda a lokacin bat a ma nemi samun jahaba (Alapiki, 2005;60). Daga haka ne za’a gane cewa mutann zamfara sun yi gagarumar hubbasa wurin neman ‘yanci ba tare da gajiya wa ko kasawa ba. Daga cikin mutane da suka bada jijinsu da karfin su ga wannan tafiya akwai Injiniya Abdu Gusau (Garkuwan Sakkwato). Alh. Ummaru (Dan galadima Birnin Magaji). Malam Yahaya Gusau, da Dr. Garba Nadama da Alhaji Muhammad Lawal Mande, Sarkin Fawa Malami, Alhaji Abubakar Tinau, Alhaji Sa’idu Muhammad Dansadau, Alhaji Aliyu Abara Gummi, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, Injiniya Dama Abdullahi Gusau da sauran su (Zamfara State hand Book, 1997;5)

         Juriya jajircewa da addu’oin mutanen zamfara sun kai ga gaci inda a ranar daya ga watan oktoba 1996, shugaban mulkin soja na wancan lokacin Janar Sani Abacha ya bayyan tabbatuwar Jihar Zamfara tare da ayyana garin Gusau a matsayin cibiya kuma babban birnin jiha. Wannan Muhimmiyar nasara ta zama mabudi ga samun gagurumin cigaba a bangarorin ilimi da bunkasar tattalin arziki da kuma ababen mure rayuwa da hada-hadar mutane inda garin ya zamo babar cibiyar gudanar da mulki da huldodin kasuwanci a jihar zamfara.

4.5 NAƊEWA

Wannann babi wato babi na hudu, babi ne day a ƙumshi shimfida da kofofin Gusau. In da aka yi muhimman abubuwa wadan da suka hada, da gabatarwa, kofofin Gusau, da sharhin kofofin Gusau, da kuma wasu unguwoyin garin Gusau da nadewa, manufar wannan binciken it ace bayyan kofofin Gusau.

Kamr yadda masu Magana kace “Komi yayi farko yana da karshe” domin haka wannan babi na hudu ya kawo karshe, don an yi bayanin cewa babu wani littafi ko kundi da ya yi sharhi koffofin Gudau, kuma a cikin babi na yi sharhin kofofin da in da suke, ta yin mafanin da hira da mutane tsofaffi ‘yan asalin garin Gusau. A cikin babi  anyi maganar wasu shiyoyin na garin Gusau, wanna babi na hudu ya yi bincike kofofin Gusau da sharhin su da unguwoyin na garin Gusau, shi ne makasaduin wannan babi.

Post a Comment

0 Comments