Ticker

6/recent/ticker-posts

Faskare A Garin Faskari (5)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara.

Faskare A Garin Faskari (5)

NA

ABUBAKAR HASSAN

faskare

BABI NA HUƊU

MU’AMALAR ICCE DA MAI FASKARE

4.0 Gabatarwa

            Masu faskare dai, wasu rukunin al’umma ne waɗanda suka zaɓi yin wannan sana’ar ta faskare don ta kasance hanyar cin abincinsu ta yau da kullun. Sana’ar faskare, sana’a ce wadda ake yinta da gatari, kuma matasa masu jini a jika da dattawa waɗanda suke da sauran ƙarfi a jikinsu, su ne suka fi aiwatar  da irin wannan sana’ar ta faskare. A cikin masu wannan sana’ar, akwai waɗanda suke zuwa daji su sari icce su sayar, akwai kuma waɗanda basa zuwa daji, kawai su aikinsu shi ne idan an kawo icce a cikin gari sai a kira su su faskara shi.

4.1 Dangantakar Masu Faskare Da Al’ummar Faskari

            Dangantakar masu Faskare da al’ummar garin Faskari, tun farko wanann dangantaka ta samo asali ne ta fuskar sana’a. A duk lokacin da mutanen Faskari suka buƙaci icce, to zai kasance sai sun je sun nemo mai faskare, idan suka nemo wannan mai faskaren, to zasu tattauna da mai faskaren nan kan abinda suke buƙata, wato suna da buƙatar a yi masu faskare, idan mai faskaren nan ya gama aikin shi daga nan sai a biya shi. To ta wannan hanya ce alaƙa mai ƙarfi zata ƙullu tsakanin masu faskare da mutanen gari, wadda duk lokacin da mutum ya buƙaci faskare, to waɗannan mutanen da suka yi mashi faskaren nan, to su ne zai ƙara nemowa don su ƙara yi mashi wannan faskaren.

            Bugu da ƙari, takan yiwu mutum yana buƙatar icce, to yakan nemo mai faskare wanda yake shiga daji yana yo icce, sai ya tambaye shi ya za a yi a samo mashi icce, walau faskare ne ko kuma gunduwa-gunduwa.

            To ta irin wannan alaƙa ko dangantaka mai ƙarfi take shiga tsakanin mutanen gari da masu sana’ar faskare.

4.2 Mu’amalar Itace Da Mai Faskare

Mu’amalar icce da mai faskare, mu’amala wadda ta kasance shi mai sana’ar faskare ya san itace kala-kala. Ya san icce mai ƙarfi sosai, kuma ya san icce wanda yake da taushi. Bugu da ƙari, mai faskare yasan icce wanda yake da ci sosai, kuma ya san iccen da ke yin gawayi mai kyau. Mai faskare ya san irin iccen da zaran ya saro sai ya kowa cikin gari to za a yi saurin sayewa, kuma za a siya da daraja sosai, mai faskare ya san iccen da idan ya saro shi ya kawo shi cikin gari to ba zai sha wahala wajen neman masu saye ba. To saboda wannan mu’amalar da take tsakanin mai faskare da icce ce ta sanya mai faskare ya san nau’o’in icce daban-daban, kuma ya iya sarrafa su ta yanda yake so, kamar yanda Hausawa  kan ce “A san mutum a san cikinsa, in ya bari a san ya daina”.

            Daɗin daɗawa, saboda yawan mu’amala da icce ne mai sana’ar faskare ya san duk wani abu game da icce, kuma mai faskare ya san icce mai kyau, ya san icce marar kyau.

            Haka kuma, mu’amalar icce da mai faskare ta danganci yanda mai faskare ke sarrafa icce ta kowane irin yanayi wanda ya haɗa da:

Safara

Saukewa

Tantancewa

Ƙwari

            Duk waɗannan abubuwa, mu’amala ce ta yau da kullun wadda mai faskare  ke yi da icce, sanadiyar wannan mu’amala ce ta sanya mai faskare ya san abubuwa da dama dangane da icce.

4.2.1 Safara

Idan mai faskare ya tafi daji ya saro icce, to akan ɗauki icce ne a kan abubuwa dabn-daban, wato abun da zai ɗauko iccen da aka sara ko aka faskara daga daji zuwa gida ko gari. A can zamanin da, kafin ƙarafuna su yawaita a ƙasar Hausa, idan aka sari iccen a cikin daji, to ana ɗauko shi ne a bisa kai, wato mutum yana ɗauko icce ne da kansa, ko kuma a kan jaki, wato sai a ɗauro ma jaki icce daga daji zuwa cikin gari, waɗannan mutane waɗanda suke ɗauro ma jaki icce daga daji zuwa garin, to su ne ake  ce ma “yan jakai”.

Bugu da ƙari, ana yin safarar icce da keke ko kuma mashin, har da motoci ma duk ana yin safarar icce, wato idan aka sari icce daga cikin daji sai a sanya daga cikin daji zuwa cikin gari domin a sarrafa shi a yi girki da shi.

            Haka kuma akwai mutanen da ake ce ma ‘yangudubale’, su ‘yangudubale,  wasu mutane ne da suke zuwa daji su sari icce su yi mashi gunduwa-gunduwa, idan sun sari iccen nan sun tara, to sai su kira mai mota, sai su loda ma shi wannan iccen ya kawo masu cikin gari, to  idan wannan mai motar ya kawo masu iccen nan gari, to sai su je su nemo mai sayen iccen nan, idan sun siyar da iccen sai su sallami mai motar da ya yi masu dakon iccen nan daga daji zuwa cikin gari. To ta irin waɗannan hanyoyi ne ake yin safarar icce daga daji zuwa cikin gari domin a sami abinda za a yi girki da shi. Ta irin waɗannan hanyoyi ne ake yin safarar icce daga inda aka sare shi zuwa inda ake son kawo shi don a siyar a yi buƙatun yau da kullun.

4.2.2 Saukewa/ Saukale

Idan aka yo safarra icce daga cikin daji zuwa cikin gari, to ana sauke shi ne wuri mai fili, wato wurin da bai matse hanyar wucewa ba, shi dai irin wannan wurin da ake sauke icce, to ba shida wani takamaiman sunan da ake kiran shi da shi, idan aka lodo ma jaki icce, to waɗannan mutanen masu iccen waɗanda suka loda ma wannan jaki icce, to sune suke sauke wannan icce da kansu, ba wai wasu zasu sanya su sauke masu wanann icce.

            Haka icce, idan aka lodo ma keke ko mashin ko kuma mota icce, to waɗannan mutanen da suka ɗauko wannan iccen, to su da kan su ne sauke wannan iccen ba wai kuma wasu mutane ne daban za su kira su sauke ba.

            Bugu da ƙari, koda kuwa mota ce aka lodo ma wannan iccen, to su waɗanda  suka loda mota wannan iccen, to dama za su hawo motar ne su biyo ta har inda za a sauke wannan iccen, to idan an zo daidai wurin da za a sauke wannan iccen to sai waɗannan mutanen da ake kira da ‘yangudubale’ su sauko daga bisa wannan motar su sauke iccen.

4.2.3 Tantancewa

            Idan masu faskare suka sari icce, ko kuma suka faskari icce, to suna ware su daban-daban, suna ware masu kyau da maras sa kyau, kuma suna ware masu ƙwari da maras ƙwari, suna ware masu ci sosai da kuma waɗanda ba su ci sosai. To idan sun ware waɗannan itatuwan gefe-gefe, wato  idan an gama tanatance su kenan, to sai a fara siyar da su.

Itatuwan da suka fi ƙwari, to wajen sayarwa sai sun fi daraja, wato sai sun fi tsada.

Itacen da suka fi ƙwari, kuma suka fi daraja wajen siyarwa sun haɗa da:

Iccen marke

Iccen ɗorawa

Iccen faru

Iccen ɗinya

Iccen kaɗanya

Iccen gamji

Iccen kanya d.s.s

To ire-iren waɗannan itatuwa sun fi tsada wajen siyarwa, kuma masu girki sun fi jin daɗin amfani da su, saboda sun fi ci, kuma ba su da hayaƙi sosai.

4.2.4 Ƙwari

            Masu faskare suna haɗawa da abubuwa da yawa yayin gudanar da sana’arsu ta faskare. Masu faskare, suna cin karo da ƙwari kala-kala masu cutarwa da ma waɗanda ba su cutarwa a cikin iccen da ake faskarawa.

            Waɗannan ƙananan halittu da suke rayuwa a cikin icce, waɗanda ababuwan cutarwa ne, waɗansu kuma ba masu cutarwa ba ne. To idan ya kasance masu faskare sun fara saran iccen da waɗannan ƙwari suke, idan waɗannan ƙwari mugaye ne to suna iya kawo ma mai faskaren nan hari su cutar  da shi. Idan kuma waɗannan ƙwari ba manya ba ne, to ba bu ruwansu da wannan  mai faskaren, sai dai su kama wani wuri su canza muhalli na daban.

Ire-iren Ƙwarin da masu faskare ke cin karo da su yayin gudanar da aikinsu sun haɗa da:

Kiyashi

Tsutsa

Muzanya

Maciji

Kunama

Ɓera

Gafiya

Cinnaka

Tarmani.

            To waɗannan su na ɗaya daga cikin ire-iren ƙwari da masu sana’ar faskare ke cin karo da su yayin gudanar da aikinsu na saran icce. A cikin waɗannan ƙwarin, akwai waɗanda suke masu cutarwa, akwai kuma waɗanda basu cutarwa.

Ƙwari masu cutarwa sun haɗa  da:

Maciji

Kunama

Cinnaka

Tarmani.

Ƙwari waɗanda basu cutarwa sun haɗa da:

Kiyashi

Ɓera

Gafiya

Muzanya.

To waɗannan sune ire-iren ƙwarin  da ake iya samu a cikin icce.

4.3 Nau’o’in Masu Faskare

Kowace irin sana’a ta duniya, tana da rukuni-rukunin al’ummar da ke aiwatar da ita. To haka shi ma faskare, kamar kowace irin sana’a yake, yana da nau’o’in mutanen da ke aiwatar da shi, daga cikin su akwai:

-          ‘yan jakai

-          ‘yan ina-da-faskare

-          ‘yan gudubale

-          Masu yo icce da mashin/ keke

-          Masu yo icce da baro

-          Masu zama waje ɗaya sai an kira su. 

(i)                 ‘Yan jakai: - ‘Yan jakai su ne masu zuwa yo icce daji da jaki ko jakai, idan sun saro iccen nan sai su zo gari su siyar. Daga cikin su akwai ma su zuwa da jaki ɗaya, wasu kuma fiye da ɗaya.

(ii)              ‘Yan –ina-da-faskare: - su ne waɗanda ke yawo layi-layi, kwararo-kwararo, suna yawo da gatarin su rataye a kafaɗa suna neman inda za su yi faskare, ko kuma wanda zai kira su su yi ma shi faskare.

(iii)            ‘Yan gudubale: - Su ne waɗanda su ke zuwa daji su sari icce mai yawa, idan sun sari wannan  iccen, sai su kira wani  mai mota ya yi masu lodin wannan iccen sai ya kai masu cikin gari a siyar, idan an saida sai su biya mai motar dakon da ya yi masu.

(iv)            Masu yo icce da mashin ko keke: - Su ne waɗanda su ke zuwa daji da mashin ko keke ko baro sai su sari icce sai su yo lodin shi sai su kawo shi cikin gari su siyar, don su rufa ma kan su asiri.

(v)              Masu zama waje ɗaya sai an kira su: Suma waɗannan gungun masu faskare ne, waɗanda ba yawo suke yi ba, kuma ba su zuwa daji don yo icce, su suna zaune a gida ne, idan mutum yana da buƙatar  a yi mashi faskare, to sai dai ya je ya kira su.

4.4   Muhallin da ake Faskare

            A lokacin da ake gudanar da faskare, ana buɗatar a sami fili mai faɗi, wanda zai isa a ajiye itatuwa komi yawansu, to idan aka sami irin wannan filin ana iya yin faskare a cikin shi, a ƙofar gida  ko kuma a cikin gida. Ba’a ware wani fili na musamman ba wanda ake yin faskare a cikin shi ba.

            Bugu da ƙari, duk filin da aka samu, za a  iya yin faskare a cikin shi, walau a cikin gida yake, ko kuma a waje.

4.5   Kammalawa

            To kamar dai yanda muka gani a bayanin da ya gabata, faskare dai kamar kowace irin sana’a yake mai cin gashin kanta, yana da irin nashi hanyoyi ko tsare-tsaren da ake bi domin gudanar da shi.

Post a Comment

0 Comments