Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara.
Faskare A Garin Faskari (6)
NA
ABUBAKAR HASSAN
BABI NA BIYAR
KAMMALAWA
5.0 Gabatarwa
A wannan babi za a
kammala dukkan abubuwan da ake binciko a kan wannan aiki tare da yin nazarin
kowane babi ɗaya bayan ɗaya a taƙaice. Haka zalika, a nan ne za a kammala wannan aiki.
Bugu da ƙari, cikin wannan babi ne za a ga shawarwari da aka yi
wajen aiwatar da wannan bincike. A ƙarshe ne ake sa ran yin bayani na kammalawa tare da
manazarta.
5.1 Taƙaitawa
A babi na ɗaya an yi bayani ne game da manufar bincike da dalilin bincike da muhallin
bincike da matsalolin bincike da kuma farfajiyar bincike, sai kuma a ƙarshen babin aka yi kammalawa.
Babi na biyu, ya yi bayani ne a kan bitar ayyukan da suka
gabata da kuma ma’anar sana’a da tarihin garin Faskari da kuma ma’anar faskare.
Sai kuma a babi na uku, an yi bayani a kan asalin sunan
faskare, sana’ar faskare a garin faskari, da kuma muhimmancin faskare a garin
Faskari da kuma ire-iren itatuwa da kuma ƙalubalen da masu faskare ke fuskanta a garin Faskari da
kuma hanyoyin da za a bi a shawo kan
matsalar faskare a garin Faskari, sai kuma daga ƙarshe aka yi kammalawa.
A babi na huɗu, an tattauna muhimman abubuwa kamar haka:
Dangantakar masu faskare
da al’ummar Faskari, da mu’amalar itace da mai faskare da kuma nau’o’in masu
faskare da kuma muhallin da ake faskare daga ƙarshe kuma aka kammala babin.
A babi na biyar ne aka kammala wannan binciken, wannan
babi an yi tsokaci a kan abubuwa kamar taƙaitawa da kuma kammalawa, sai kuma shawarwari tare da
kuma manazarta.
5.2 Kammalawa
Kamar yadda mai bincike
ya yi bincike a kan rubuta wannan kundin neman digiri na farko kan abin da ya
shafi “Faskare a garin Faskari”, wato yanda shi kan shi faskaren yake da kuma
yanda ake gudanr da shi. Haka kuma, mai bincike ya raba aikin sa zuwa
babi-babi, tun daga babi na ɗaya har zuwa na biyar.
A babi na ɗaya, mai bincike ya yi bayani a kan manufar bincike da kuma dalilin bincike
da matsalolin bincike da kuma farfajiyar bincike daga ƙarshe kuma aka kammala.
A babi na biyu kuma mai bincike ya yi bitar ayukan da
suka gabata.
A babi na uku kuma an yi
yalwataccen bayani a kan/ game da yanda ake aiwatar da sana’ar faskare.
A babi na huɗu, shima bayani ne da mai bincike ya yi a kan yanda
ake aiwatar da sana’ar faskare da kuma nau’o’in masu faskare daga ƙarshe kuma aka kammala.
Sai kuma a babi na biyar, mai bincije ya yi bayani a taƙaice game da yanda aka
gudanar da wannan aiki, sai shawarwari da kuma kammalawa sai kuma manazarta.
5.3 Sakamakon Bincike
·
A sakamakon wannan
bincike an gano itatuwan da ba a faskara su, sai dai a ɗebi wani sashe daga jikin su.
·
Haka kuma, an gano
itatuwan da ba a girki da su.
·
A sakamakon wannan
bincike, an gano matasa masu jini a jika sun fi yin wannan sana’ar ta faskare.
·
Bugu da ƙari, a sakamakon wannan
bincike, an gano sana’ar faskare ta fi cin kasuwarta a can lokacin baya, saboda
yanzu sana’ar tana ja da baya saboda tasirin zamananci.
·
A sakamakon wannan
bincike, an gano itatuwa masu sauƙin faskare da masu wahalar faskare.
·
Haka kuma, a wannan binciken an gano cewa a lokacin da mai sana’ar
faskare ya tsufa, wato ya manyanta kenan to jikin shi yana yi ma shi ciwo
sosai.
5.4 Shwarwari
To, a nan shwarwari da
za a yi basu wuce na malami da ɗalibai masu nazarin al’ada ba. Shawarata a nan ita ce,
aci gaba da nazarin al’ada da kuma sana’o’in Hausawa na gargajiya, saboda
muhimmancinsu.
Haka kuma, yana da kyau hukumar makaranta ta sanya wannan
bincike a cikin tsarin bincike da ake rubuta maƙala a kan sa, idan muka yi la’akari
da muhimmancinsa, domin ya taɓo ɓangarori da yawa na yanda ake gudanar
da faskare da ma sauran sana’o’i daban-daban.
Bayan haka kuma, gwamnati ita ma ya kamata ta inganta
wannan sana’ar ta faskare yanda za ta dace dai-dai da zamani, saboda faskare
yana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar al’umma.
Daga ƙarshe kuma ya zama dole ɗalibai masu nazarin harshen Hausa a makarantu
daban-daban, kama daga takardar Diploma,
NCE da digiri na ɗaya da na biyu da na uku, da su
tsunduma a kan sha’anin bincike akan faskare, ta hanyar rubuta kundayensu na
kammala karatu a kan Hausa. Ba ɗalibai kawai ba, har da malamai masu koyar da harshen Hausa a makarantu,
tun daga firamare har zuwa jami’a, ya kamata su zurfafa bincikensu wajen gano
abubuwan da suka danganci faskare. To wannan hanyar kaɗaice za a kauda ƙishin ruwan da ke damun mutane na rashin wani abun dubawa
wanda ya yi magan a kan faskare.
Haka kuma, ina ƙara ba ɗaliban neman ilimi ‘yan uwana shawara da su ƙara zurfafa bincike a kan
wannan fanni na faskare domin a sami
abin dubawa, kuma domin a ƙara faɗaɗa wannan fannin ya bunƙasa.
MANAZARTA
Tuntuɓi Amsoshi.
0 Comments
Rubuta tsokaci.