Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara.
Faskare A Garin Faskari (4)
NA
ABUBAKAR HASSAN
BABI NA UKU
SANA’AR FASKARE
3.0 Gabatarwa
Sana’ar faskare, daɗaɗɗiyar sana’a ce wacce
al’umma suka daɗe suna yi domin samun abinci.
Al’ummar Faskari , suma ba a bar su a baya ba wajen aiwatar da sana’o’i irin na
gargajiya daban-daban, wadda mutum zai iya yin amfani da ƙarfinsa da kuma fasaharsa wajen
neman abin da zai ci. To ita ma, kamar haka sana’ar faskare ta ke sana’a ce
wacce ake yin amfani da ƙarfin jiki da kuma dabara wajen yin wannan sana’ar. Mafi
yawanci maza ne ma su ƙarfi a jika ke aiwatar da irin wannan sana’ar ta faskare, kuma ana amfani
da gatari mai ƙarfi wajen yin wannan sana’ar ta faskare.
Mutanen Faskari, sun daɗe suna yin wannan sana’ar a tsakaninsu, yayin da su ke
daddatsa icce gunduwa-gunduwa, kuma daga nan su faskara shi ɓari-ɓari. A cikin waɗannan itacen da suke faskarawa, akwai masu sauƙin faskare, kuma akwai ma su wahalar
faskarawa.
3.1 Asalin Faskare
To kamar dai yanda aka yi
fira da mutane daban daban masana wannan harkar ta sana’ar faskare, haka kuma
an yi fira da manyan malamai masana al’adu da kuma sana’o’in Hausawa, sun
tabbatar mana da cewa, “Faskare dai asalin sunan shi kenan faskare”. Sun ƙara da cewa, “tun fil
azal asalin sunan faskare kenan faskare”. Sun ce, “Faskare shi ne, daddatsa
icce gunduwa-gunduwa, kuma daga nan a faskara shi ɓari-ɓari da gatari, wannan shi ne faskare. To kamar yanda aka gani a bayanin da
ya gabata, faskare dai asalin sunan shi kenan “faskare”. Masana sun ƙara da cewa “faskare, bai da wani
suna kafin wannan, kuma baida wani sunan bayan wannan.
Asalin sunan faskare kenan “Faskare” tun fil azal.
Tun lokacin da al’ummar Hausawa ta ginu da kanta tun
wajen ƙarni na 15 – 16 ne al’ummar Hausawa ta kafu da kanta, tun kafin zuwan
Larabawa da Turawan mulkin mallaka, to tun daga wannan lokacin ne Hausawa suke
da dabarar yin sana’o’i irin na gargajiya domin rufa ma kan su asiri. To tun a
wannan lokacin, Hausawa suke da fasahar aiwatar da sana’ar faskare wacce ake
amfani da gatari wajen sarrafa icce yadda ake buƙata. To tun a wannan lokacin ake
kiran irin wannan sana’ar faskare, wannan na nuna mana cewa tun asali dai,
ainihin sunan sana’ar faskare kenan, wato “Fasakare”, kuma har yau da irin
wannan suna ake kiran wannan sana’ar wato ‘Faskare”.
3.2 Sana’ar Faskare a Garin Faskari
Faskare dai sana’a ce ta
garagjiya ta Hausawa, mai cin gashin kanta kamar kowace sana’a. A yayin
gudanar da sana’ar Faskare, ana amfani
da gatari mai kaifi wajen yin faskare. Idan mai faskare ya je yin faskare, yana
tarar da itace ne a tare guri guda, idan
ya tarar da waɗannan itace, daga nan sai ya yi
jinga da mai wannan iccen, wato su shirya kenann, idan sun gama yin jinga, sun
shirya, daga nan sai mai faskaren nan ya fara aikin shi.
Da farko dai, mai yin
wannan faskaren zai fara da daddatsa iccen ya yi mashi gunduwa-gunduwa, misali
daidai iya tsawon guiwa, ko kuma yanda ya ga zai iya. To idan an daidaita iccen
an yi ma sa gunduwa-gunduwa, daga nan sai kuma a faskara su ɓari-ɓari, daidai yanda za a iya sanya su cikin murhu a yi girki da su.
Yayin gudanar da wannan
faskaren, ana yin amfani da gatari mai kyau kuma mai kaifi, yanda za a ji daɗin aiwatar da wannan aiki na faskare.
Haka kuma, yayin da masu
faskare suka zo domin aiwatar da aikin su, idan suka zo inda za su yi faskaren,
da farko dai za su fara yin jinga da mutumin da ke da waɗannan itacen , wato su shirya da shi, idan sun gama
shiryawa, daga nan sai kowa ya fiddo da kayan aikin shi, daga nan sai su fara,
kowa ya koma gefe ɗaya ya ci gaba da aikin, bayan sun gama, daga nan sai a biya su kuɗin su, sai kowa ya ɗauki kayansa ya tafi.
3.3 Muhimmancin Faskare a Garin Faskari
To kamar yanda aka sani,
kowace irin sana’a ta duniya tana da matuƙar amfani, musamman ma san’o’i irin na gargajiya waɗanda al’umma su ke yi domin samun abinda za su saka ma
bakin su. Sana’ar faskare tana da matuƙar amfani ga al’ummar Faskari sosai, domin kuwa ta samar
ma al’umma da dama abinci.
Muhimmancin sana’ar faskare a garin Faskari sun haɗa da: -
Samar ma al’umma da aikin
yi: Sana’ar faskare ta samar ma da al’ummar garin Faskari da aikin yi, matasa da kuma dattawa masu ƙarfi. Domin kuwa, da
sana’ar faskare mutane da yawa waɗanda su ke yinta, suna samun abinda za su ci, su kuma ci da iyalansu, har
ma su yi masu sutura, kuma su rufa ma kansu asiri da ‘ya’yansu.
Sana’ar faskare tana
taimakawa wajen samar da itacen da ake yin girki da su a cikin gidajen al’umma
da kuma sauran wurare daban-daba. Da ace babu masu sana’ar faskare a garin
Faskari, to da mutane da yawa sun ta shan wahala wajen samun itacen da za su yi
amfani da su wajen yin girki na yau da kullum . dalili kuwa shine, masu
faskare, su ne su ke zuwa daji su sari itace sannan su kawo su cikin gari su
faskara su, sannan sai mutane su zo su saya su yi amfani da shi.
Sana’ar Faskare, ta ƙara bunƙasa sana’ar ƙira a garin Fasakari: Maƙera, suna amfanuwa da
masu sana’ar faskare a garin Faskari, domin kuwa, masu faskaren nan a wajen maƙera su ke zuwa su sawo
“Ruwan gatari”, wanda ake sanyawa a cikin ƙotar gatarin, kuma “kuɗar gatari’ wato washin gatarin kenan. Da wannan maƙera suna ƙaruwa da ma su san’ar
faskare domin kuwa suna samun kuɗi ta dalilinsu.
Masu faskare, suna
taimakawa wajen samar da itace daga cikin daji zuwa cikin gari: Waɗannan itatuwan ne
da masu faskare ke sarowa daga daji zuwa cikin gari, su ne ake faskarewa
ana amfani da su a cikin gidaje da
sauran wurare daban daban.
Masu sana’ar faskare, suna
taimakawa wajen samar da waɗansu magunguna na gargajiya a garin Faskari; idan masu faskare za su tafi daji wajen saro
itace, suna sassaƙo magunguna daban-daban, irin na maganin “basir” da “shawara” da sauransu.
3.4 Ire-Iren Itace
Itace dai, wasu tsirrai ne
da suke fitowa ta ƙarƙashin ƙasa, watau dasa su ake yi, ko kuma hakanan kawai suka fito, amma dai duka
suna fitowa ta ƙarƙashin ƙasa da izinin Allah ne. Haka kuwa abin yake ko a cikin ƙasar Faskari, Faskari tana da babban daji, wannan dalili ne ya sa
Faskari take da itatuwa daban-daban. Wasu daga cikin itacen nan sun haɗa da:
i.
Iccen marke
ii.
Iccen Ɓaure
iii.
Iccen Taɓo
iv.
v.
Iccen tawatsa
vi.
vii.
Iccen kanya
viii.
Iccen mangoro
ix.
x.
Iccen maɗaci
xi.
Iccen tsada
xii.
xiii.
Iccen dirimi
xiv.
Iccen ɗinya
xv.
Iccen hano
xvi.
Iccen turare
xvii.
xviii.
Iccen tsamiya
xix.
Iccen gamji
xx.
Iccen kuka. Da sauran su da dama.
To daga cikin waɗannan itatuwan da aka lissafa, akwai masu wahalar faskarawa, kuma akwai
masu sauƙin faskarawa.
3.4.1 Masu Wahalar
Faskarawa
To su dai itace kala-kala ne, sun bambanta da junansu,
daga cikin su, akwai masu wahalar faskarawa, kuma akwai masu sauƙin faskarawa.
Kaɗan daga cikin
itatuwa masu wahalar faskarawa sun haɗa da: -
i.
Iccen tawasa
ii.
Iccebn marke
iii.
Iccen taɓo
iv.
Iccen gamji, ƙirya
v.
Iccen tsamiya.
Kamar yanda aka gani, waɗannan itace suna ɗaya daga cikin iatauwa masu wahalar faskarawa, dalilin da ya sa suke
wahalar askarawa shi ne: -
(a)
Na farko dai, itacen ba
su da ruwa a jikin su sosai; wato ba su da ruwan da zai sa jikin su ya yi
taushi, wanda zai sa iccen ya yi daɗin faskare. Saboda ƙarancin ruwan da suke da shi ne ya sanya idan ana faskara
su gatarin bai shigewa cikin iccen sosai.
(b) Na biyu, kuma dalilin da ya sa itacen ke da wahalar faskara shi ne, idan an
sari iccen da gatari, to gatarin bai tasowa, sai dai ya maƙale a cikin iccen.
(c)
Na uku kuwa shi ne,
abinda ya sa waɗannan itatuwan su ke da wahalar
faskarawa shi ne, itacen sun cika yin ƙarfi ne, ba su da
taushin da gatari zai iya shigewa ciki ya tsaga su sosai, sai an sha wahala sosai kafin a faskara su.
To kamar yanda aka yi bayani. Waɗannna su ne jerin iatauwa ma su wahalar faskarawa.
4.4.2 Masu Sauƙin Faskarawa
To kamar yadda aka sani, komai na rayuwa baya taɓa zama ɗaya, dole ne sai an sami ‘yan bambance –bambance ko da kaɗan ne a tsakani duk da kasancewar su jinsi ko kuma suna ɗaya. To haka
abin yake a cikin itatuwa, itace dai
duka duk halittar Allah ne, amman wasu sun bambanta da junansu.
Daga cikin waɗannan itacen akwai masu sauƙin faskarawa, kamar yanda aka sami masu wahalar faskarawa.
Kaɗan daga cikin itacen da ke da sauƙin faskarawa sun haɗa da:-
i.
Iccen ɓaure
ii.
Iccen maɗaci
iii.
Iccen hano
iv.
Iccen kuka
v.
Iccen kanya
vi.
Iccen mangoro
vii.
Iccen bedi
viii.
Iccen dirimi
ix.
Iccen faru
x.
Iccen turare d.s.s
To kamar yadda muka gani, waɗannan itatuwan, suna ɗaya daga cikin
itace masu sauƙin faskarawa, kuma masu sana’ar faskare suna jin daɗin faskara irin waɗannan itatuwa. Abinda ya sa waɗannan itatuwa su ke da daɗin faskarawa shi ne:
(a)
Waɗannan itace, suna da wadatattun ruwa a jikinsu, wanda zai
sanya iccen ya yi taushi yanda da zaran mai faskare ya buga gatarinsa to
gatarin zai shige cikin iccen ya fasa shi ne.
(b) Itatuwan ba su da ƙarfi sosai, wato ba su da ƙarfin da zai sa mai faskare ya ji wahalar faskara su
yayin da yake gudanar da aikin shi na faskare.
3.5 Kayan Aikin Gudanar
da Sana’ar Faskare
Kowace irin sana’a ta duniya, tana da kayan aikin da ake
aiwatar da ita da su, wanda idan babu waɗannan kayan aikin to wannan sana’ar ba zata yuwu ba. To haka shi ma
faskare, kamar kowace irin sana’a yake, yana da kayan aikin da ake aiwatar da
shi da su, wanda idan babu waɗannan kayan aikin , to wannan sana’a ta faskare ba zata taɓa yuwuwa ba. Su waɗannan kayan aikin su ne ginshiƙi, ko kuma jagaba wajen aiwatar da wannan sana’ar ta
faskare.
Kayan aikin sana’ar
faskare, sun haɗa da:
i.
Gatari
ii.
Abin washin gatari
(Magagari)
iii.
Ƙotar gatarin
iv.
Ruwan gatarin.
Da ƙotar gatari da kuma ruwan gatari su
ne idan aka haɗa su duka su ke bada gatari, kuma ɗaya bai yi dole sai da ɗaya.
i.
Gatari: Gatari dai, da
shi ne ake faskara icce, a yi mashi gunduwa-gunduwa, kuma daga nan a faskara shi ɓari-ɓari. Idan babu gatari to babu yanda za a yi a iya aiwatar da sana’ar
faskare. Gatari shi ne ƙashin bayan sana’ar faskare, kuma da shi ake yin faskaren.
ii.
Abin washi: Shi dai abin
washi da shi ne ake wasa gatari idan ya dakushe. Ana wasa gatari idan ya
dakushe saboda ma su sana’ar faskare su ji sauƙi wajen aiwatar da aikin su na
faskare, yanda da zaran sun buga icce zai buɗe ne.
Idan ya kasance gatari baya da washi, to mai faskare zai wahala sosai kafin
ya gama aikin shi na faskare, kuma duk
sai hannunshi ya yi kanta ko kuma ya faffashe kafin ya gama wannan faskaren da
yake yi.
iii.
Ƙotar gatari: Ƙotar gatari, ita ce wacce ake saka ruwan gatari ko kuma ƙarfen gatari a cikinta.
Ita ƙotar gatari Maduka ne ke sassaƙa ta.
iv.
Ruwan gatari: Ruwan
gatari, shi ne ƙarfen gatari, kuma shi ne ake sawa cikin ƙotar gatari sai a buga icce da shi.
Shi dai ruwan gatari, Maƙera ne ke ƙera shi.
To waɗannan abubuwa, su ne mai yin sana’ar faskare yake amfani da su wajen
aiwatar da sana’ar shi ta faskare. Idan babu waɗannan abubuwa to ba yanda za a yi sana’ar faskare ta
yiwu, ba zata taɓa yuwuwa ba. A taƙaice dai gatari shi ne
babban jigon aiwatar da sana’ar faskare, idan babu gatari, to babu faskare.
3.6 Masu aiwatar da
sana’ar faskare
Kamar yanda aka riga aka
sani, kowane irin al’amari na duniya akwai masu aiwatar da shi, kuma haka
zalika, akwai masu jagorantar shi. To haka ita ma sana’ar faskare akwai
mutanen da suke aiwatar da ita. Faskare
dai sana’a ce da al’umma ke yi domin neman abinci.
Masu aiwatar da sana’ar faskare dai, mutane ne, waɗanda suka zaɓi wannan sana’ar ta faskare ta zama ita ce hanyar cin abincin su.
Matasa masu ƙarfi a jika, ko kuma dattawa waɗanda suke da
sauran ƙarfi a jikinsu, su ne suka fi yin sana’ar faskare, domin kuwa ita sana’ar
faskare, sana’a ce irin ta masu ƙarfi, raggon mutum bai iya yin sana’ar faskare.
Waɗannan mutane masu sana’ar faskare, suna da ƙungiya wadda su ne suka kafa abin su
domin taimakon kansu- da- kansu. Kuma a cikin wannan ƙungiya, akwai shuwagabanni
daban-daban waɗanda su ne ke jagotantar wannan ƙungiya.
3.7 Tasirin Zamananci A
Sana’ar Faskare
Yanzu kowace irin sana’a ta duniya, to zamananci ya yi
tasiri a kanta, wato zuwan zamani ya sanya sana’ar ta ƙara tasiri a idanun duniya. Wanda za mu ga cewa, zuwan zamani ya sanya
sana’ar ta ƙara inganta, kuma mutane da ke aiwatar
da irin wannan sana’ar, za su sami sauƙi wajen aiwatar da ita a rayuwa ta yau da kullun.
To ita ma sana’r
faskare, kamar kowace irin sana’a mai cin gashin kanta a duniya, bugu da ƙari, ita ma wannan
sana’ar ta faskare zamananci ya yi tasiri
a kanta sosai.
Babban tasirin zamananci
a kan sana’ar faskare shi ne:
Zamananci ya samar da
inji (engine) na yankan itace. Wannan inji, yana taimakawa masu sana’ar faskare
sosai wajen aiwatar da sana’ar su, kuma yana
rage masu wahala. Wanann inji da suke amfani da shi, yana taimaka masu
sosai wajen daddatsa itace, saɓanin can da, da suke daddatsa icce da gatari, wato su yi ma shi
gunduwa-gunduwa kenan.
Samuwar inji na yankan
icce a ƙasar Hausa, ba ƙaramin taimakawa ne ya yi ba ga masu
sana’ar faskare ba, domin kuwa da wannan
injin ɗin ne suke zuwa daji, su kada icce komi girman shi, sannan su
yayyanka shi su yi ma shi gunduwa-gunduwa, idan sun yi mashi gunduwa-gunduwa,
daga nan sai su sanya gatari su faskara shi daidai yanda suke buƙata.
Tabbas sana’ar faskare,
ta samu bunƙasa sosai a garin Faskari, dalilin samuwar wanann inji na yankar icce wanda
zamananci ya kawo samuwar wannan inji na
yankan icce, yana rage ma masu sana’ar faskare wahalar da suka daɗe suna fama da ita shekara da shekaru, kuma yana
sawa su yi sauri su gama aikin su na
saran icce ko kuma faskare.
Tabbasa zamananci ya yi
rawar gani ga masu sana’ar faskare, domin kuwa ya samar masu da injin ɗin da za su riƙa amfani da shi wajen aiwatar da sana’ar su ta
faskare.
3.8 Barazanar Zamananci
ga Sana’ar Faskare
Kowane irin abu a
duniya, yana da matuƙar amfani, kuma ta wani ɓangaren yana da rashin amfani, dole ne zai yi ma wasu daɗi kuma dole ne zai ɓata ma wasu rai. Zuwan zamananci ya sanya sana’ar faskare ta fara taɓarɓarewa a cikin garin Faskari, domin kuwa zamani ya zo da waɗansu abubuwa waɗanda ake amfani da su a maimakon itace. Samuwar waɗannan abubuwa da zamani ya yi, ya sanya sana’ar faskare
ta fara ja baya, kuma cinikin sana’ar ya yi ƙasa sosai.
Waɗannan abubuwa da
zamani ya kawo waɗanda ake amfani da su a maimakon
itace wajen yin girke-girke sun haɗa da:
i.
Gas cooker (gas kuka)
ii.
Electric stoɓe (Risho mai amfani da wutar lantarki)
iii.
Risho mai amfani da
kalanzir
iv.
Charcoal (gawayi) d.s.s
Duka waɗannan abubuwa, zamananci ne ya kawo su, kuma babbar barazana ce ga masu
sana’ar faskare. Dalili kuwa shine, duk waɗannan abubuwa ana amfani da su ne wajen aiwatar da
girke-girke na yau da kullun, kuma indai har akwai waɗannan abubuwa a cikin gida, to bai zama dole a riƙa yin amfani da itace ba
wajen yin girki ba. Samuwar waɗannan abubuwa da zamani ya kawo, ya sanya masu sana’ar faskare na cikin
garin Faskari kasuwancinsu ya fara ja baya sosai, kuma sana’ar ta su ta taɓarɓare sosai.
3.9 Kalubalen da Masu
Faskare ke Fuskanta a Garin Faskari
Kowace irin harka ta duniya da ake aiwatarwa, to dole ne
ya kasance tana da irin ƙalubale waɗanda take fuskanta na yau da kullun. To haka abin yake kasancewa ko a
sana’ar faskare, domin kuwa shima faskare yana da irin ƙalubale waɗanda yake fuskanta, ƙalubalen nan suna iya zama cikas ga
wannan sana’ar ta faskare, wato su kawo mata tangarɗa kenan.
Ire-iren ƙalubalen da faskare ke
fuskanta sun haɗa da:
i.
Rashin tsayayyar ƙungiya mai cin gashin
kanta ta faskare
ii.
Rashin kayan aiki
wadatattu
iii.
Mai faskare yana fama da
ciwon jiki sosai
iv.
Mai faskare hannunshi
yana fashewa ko kuma duk yayi kanta, ya yi ƙarfi
v.
Zuwan zamananci, shi ma
babban ƙalubale ne ga masu sana’ar faskare, domin kuwa ya samar da abubuwa kamar
haka:
(a)
Gas kuka (Gas cooker)
(b) Risho na wutar lantarki
(c)
Risho na kalanzir
Waɗannan abubuwa duk ƙalubale ne ga sana’ar faskare, kuma duka zamani ne ya
samar da su. Masu sana’ar faskare, gwamnati bata kulawa da su, kuma bata yi
masu wani ingataccen wuri inda za su riƙa aiwatar da aikin su na faskare ba.
vi.
Akwai ƙarancin kayan aiki na
zamani ga sana’ar faskare. Masu faskare suna fuskantar rashin kayan aiki na
zamani, wanda za su sanya sana’ar su ta inganta sosai, kuma ta bunƙasa a idon duniya.
a.
Yana da kyau a ce an
samar ma masu faskare da kayan aiki irin na wannan zamani, yanda sana’ar ta su
za ta dace da irin wannan zamanin da ake ciki yanzu.
b.
Sana’ar faskare kamar
kowace irin sana’a ce ta duniya wadda mutane ke aiwatarwa domin neman abinci.
To yana da kyau ita ma sana’ar a inganta ta yanda zata dace da irin wannan
zamanin da ake ciki a yanzu. Wato a samar ma su da kayan aiki irin na zamani,
yadda ma su aiwatar da irin wannan
sana’ar za su sami sauƙi.
vii.
Mai faskare yana sare ƙafarsa da gatari,
yayin gudanar da aikin shi na faskare.
Wannan shi ma babban ƙalubale ne ga masu sana’ar faskare.
viii.
Mai faskare icce yana faɗa mashi a cikin ido yayin da yake yin wannan faskaren, ko
kuma iccen ya faɗa a cikin idon mai kallon shi ko
wanda ya zauna a kusa da shi. Saboda haka ma ake yi ma faskare kirari da cewa
“Da kallon mai faskare, gara kallon mai kashi”.
Waɗannan suna ɗaya daga cikin ƙalubalen da masu faskare ke fuskanta a cikin garin Faskari.
3.10 Hanyoyin da za bi
Domin Shawo Kan Matsalar Faskare
Kowace irin matsala ta duniya, akwai hanyoyin da ake bi
domin shawo kanta ko kuma magance ta gaba ɗaya . to ita ma sana’ar faskare, tana da irin nata
matsalolin da take fuskanta na yau da
kullun, kuma akwai hanyoyin da za a bi domin shawo kan waɗannan matsalolin.
Ire-iren waɗannan hanyoyi sun haɗa da:
·
Yana da kyau a samar ma
masu faskare da kayan aiki irin na zamani, waɗanda za su temaka masu
wajen aiwatar da ayyukansu.
·
Yana da kyau gwamnati ta
kula da masu faskare, wato ta basu
kulawa, kuma ta inganta su kamar sauran al’umma masu sana’a.
·
Yana da kyau masu
faskare su riƙa kula da ƙafafunsu yayin da suke gudanar da aikinsu na faskare.
·
Kuma yana da kyau mutane
su daina tsayawa kusa da masu faskare, yayin da suke gudanar da aikinsu na
faskare, domin gujewa faɗawar icce a cikin ido, ko kuma makamantan haka.
·
Yana da kyau masu
faskare su daina tsayawa a kan hanya a lokacin da suke aiwatar da aikin su na
faskare. Domin kuwa idan suna yin faskare a kan hanya, to icce yana yin tsalle
ya faɗa a kan wani abun.
3.11 Kammalawa
To kamar yanda muka gani a bayanan da suka gabata a baya,
faskare dai wata sana’a ce ta gargajiya mai cin gashin kanta, wadda al’umma ke
aiwatarwa domin neman abinci, kuma mutanen da ke aiwatar da wannan sana’ar
mafiyanwanci matasa ne masu jini a jika da kuma dattawa waɗanda suke da sauran ƙarfi a jikinsu, su ne ke yin wannan
sana’ar. Kuma ana amfani da gatarii ne yayin gudanar da wannan sana’ar ta
faskare.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.