Ticker

6/recent/ticker-posts

Faskare A Garin Faskari (3)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara.

Faskare A Garin Faskari (3)

NA

ABUBAKAR HASSAN

gatari

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0 Gabatarwa

            A cikin wannan babi na waiwayen ayyukan da suka gabata, za a yi bitar ayyukan da suka gabata, wato kundaye da kuma sauran littattafan ilimi waɗanda suke da dangantaka da irin wannan  aikin na sana’ar faskare, kuma za a binciko ma’anar fakare.

2.1 Waiwayen Ayyukan da Suka Gabata

A cikin wannan babi na waiwaye an sami wasu abubuwa waɗanda  suka danganci ayyukanmu, waɗanda manazarta da kuma ɗalibai suka rubuta.

Wasu daga cikin ayyukan  sun haɗa da:

Kabir Hassan (2014) ya yi bayani a kan “sana’o’in Hausawa na gargajiya”. A inda manazarcin ya yi bayanin yanda sana’o’in Hausawa na gargajiya suke da kuma yanda ake aiwatar dasu a aikace. Saboda haka, wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, domin sun yi tarayya wajen bayani a kan sana’o’i na gargajiya, wanda  yana daga cikin farfajiyar wannan aiki.

Abdullahi M, (2008), ya yi bayani a kan “Sana’o’in Hausawa jiya da yau”. A inda manazarcin ya yi bayanin yanda sana’o’in Hausawa su ke jiya da yau, duk da cewa ya bayyana wasu sana’o’in da kuma yanda ake aiwatar da su. Saboda haka, wanann nazari yana  da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, domin sun yi tarayya wajen bayani a kan sana’o’i na Hausawa wanda yana daga cikin farfajiyar wannan aiki.

Bala, (2012) ya yi bayani akan “amfanin itace ga rayuwar al’umma”. A inda manazarcin ya yi bayanin itatuwa da kuma yanda suke, da kuma amfaninsu a jikin mutum, saboda haka, wannan nazari yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, domin sun yi tarayya wajen bayani a kan ire-iren itatuwa, wanda yana ɗaya daga cikin farfajiyar wannan aiki.

Musa Yahaya (2014), ya yi bayani a kan yaƙe-yaƙen Faskari da nasarorin da ta samu. A inda manazarcin ya yi bayanin tarihin garin Faskari da kuma yaƙe-yaƙen da ta yi. Saboda haka, wannan nazari yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, domin sun yi tarayya wajen bayani a kan tarihin garin Faskari da yaƙe-yaƙen garin, wanda yana daga cikin Farfajiyar wannan aiki.

Abubakar Hamza (2011), ya yi bayani  a kan “Dangantakar icce da Mutum”. A inda manazarcin ya yi bayanin yanda dangantakar icce da mutum ta ke. Saboda haka wannan aiki yana da dangantaka ta kusa da wannan bincike  da ake gudanarwa, domin sun yi tarayya wajen bayani a kan dangantakar icce da mutum, wanda yana daga cikin farfajiyar wannan aiki.

Yusif (2003) ya yi bayani a kan yaƙe-yaƙen Birnin Kogo. A inda manazaricin ya yi bayanin yadda aka samar da garin Faskari, duk da cewa ya bayya wasu yaƙe-yaƙe da suka faru kafin a cimma nasarar samun garin. Saboda haka, wannan nazari yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, domin sun yi tarayya wajen bayani a kan garin Faskari wanda yana da  cikin farfajiyar wannan aiki.

Ibrahim B, (1999), ya yi bayani a kan sana’o’in Hausawa na gargajiya. A inda manazarcin ya yi bayanin sana’o’in Hausawa na gargajiya su ke. Saboda haka wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa, domin sun yi tarayya wajen bayani a kan sana’o’in Hausawa na gargajiya wanda yana cikin farfajiyar wannan aiki.

Kabir M. (2008), ya yi bayani a kan sarakunan Birnin Kogo da gudunmawar da suka bada wajen bunƙasa birnin. A inda manazarcin ya yi bayanin sarakunan Birnin Kogo da gudunmuwarsu. Saboda haka, wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da wannan bincike da ake gudanarwa domin sun yi tarayya wajen bayani a kan sarakunan Birnin Kogo wanda yana daga cikin farafjiyar wannan aiki.

Aliyu G, (2013) ya yi bayani a kan tasirin zamananci ga sana’o’in Hausawa na gargajiya. A inda manazarcin ya yi bayanin tasirin zamananci a kan sana’o’in Hausawa na gargajiya, duk da cewa ya bayyana wasu muhimman abubuwan da suka kawo ci gaba ga sana’o’in. Saboda haka, wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da wanann bincike da ake gudanarwa, domin sun yi tarayya wajen bayani a kan tasirin zamananci  ga sana’ar faskare, wanda yana cikin farfajiyar wannan aiki.

To waɗannan kundaye da litttattfai su kaɗai ne hannuna ya kai gare su, sakamakon ba a yi wani aiki a kan sana’ar faskare ba, ko da an yi, to hannuna bai kai gare shi ba.

2.2 Ma’anar Sana’a

Masana da dama sun bayar da gudunmuwa wajen fito da ma’anar sana’a kamar haka:

Bageri (1986) ya bayyana ma’anar sana’a da cewa, “Sana’a na nufin duk wata hanyar saye da sayarwa, wacce ɗan Adam ke yi, domin samun kwabon kashewa  da buƙatunsu na yau da kullum.

Yahaya (1992) ya ce “Sana’a hanya ce ta amfani da azanci da hikima da sarrafa albarkatu da ni’imomin da ɗan Adam ya mallaka don buƙatunsa na yau da kullum. Don haka kenan, sana’a, wata abu  ce wadda mutum ya jiɓanci yi da  nufin smaun abin masarufi don gudanar da harkokin rayuwa.

Haruna da wasu (2011) sun bayyana ma’anar sana’a  da cewa “aba ce wadda ake yin kimiyya da fasaha da ni’imomin da ke tattare da ɗan Adam  da  sha’anin kasuwanci da saye da sayarwa da ciniki.

2.3 Ire-Iren Sana’a

Kamar yanda muka sani, sana’o’in Hausawa suna da yawa, amman ga wasu daga cikin su, sun haɗa da:

-          Noma

-          Ƙira

-          Saƙa

-          Fawa

-          Faskare

-          Jima

-          Wanzanci

-          Rini

-          Ɗori

-          Dukanci

-          Su.

        i.             Noma: - Sana’a ce da ake yi domin samun abincin da za a ci da kuma wanda za a siyar domin samun kundin da za a yi amfani da su wajen al’amuran rayuwar yau da kullum.

      ii.             Ƙira: - sana’a  ce da ake domin samar da kayan aikin noma da kuma ayyukan gida.

   iii.             Saƙa: - sana’a ce da ake yi domin samun tufafin sakawa, da kuma na wasu ‘yan aikace-aikace, a kan yi amfani da zare, ko gashi ko kaba a mayar da su abun amfani.

   iv.             Fawa: - Sana’a ce wadda ake siyan dabbobi a yanka, domin samun nama ga al’umma.

      v.             Faskare: - Sana’a ce wacce ake yin amfani da gatari wajen  faskara icce domin a sami itacen da za’a ƙona a yi girki.

   vi.             Jima: - Sana’a ce wacce ake sulluɓe fata domin a fitar da gashin da ke jikinta, majema na amfani da bagaruwa wajen gudanar da aikinsu.

 vii.             Wanzanci: - Sana’a ce da ake amfani da askar aski domin yin aski da gyaran fuska da yin kaciya da kuma amfani da kalaba da ƙoshiya wajen cire hakin wuya.

viii.             Rini: - sana’a ce da ake sauya wa tufafi ko zare kalar da suke da ita.

    ix.             Dukanci: - Sana’a ce da ake sarrafa fatar dabbobi domin a mayar da su wani abun amfani na yau da kullun, misali: takalmi, jakunkuna, bante, da sauransu.

      x.             Su:- Sana’a ce ta kamun kifi da sauran namun cikin ruwa.

2.4 Tarihin Garin Faskari

To kamar yanda tarihi ya nuna, Wari da Raɗɗa da Gido da Ɗan’yabani su ne suka kafa birnin Kogo, tun cikin shekarra (1778). Amma kuma daga baya, Wake Ɗanjataun ɗaya daga cikin zuriyar Ƙaura kuren Gumari, shi ne ya gina Birnin Kogo a shekarra 1848, a lokacin sarkin Katsina Muhammadu Bello.

Wari da Rada suna da waɗansu duwatsuna guda biyu, inda sukan yi al’adu irin na tsafe-tsafe, ɗayan dutsen yana da ƙaton Kogo, wanda komai girman mutum zai iya shiga cikinsa. Saboda haka a duk lokacin da yaƙi ya tashi a zamanin su, to za ka ji ana guɗa a duwatsun nan, wanda ke nuna alamar cin nasara ko rashin ta. Banda wannan kuma, Wari da Raɗɗa, sukan je wajen kogon dutsen nan da rana tsaka, ana yi masu kaɗe-kaɗe na gargajiya. A ƙarshen wannan shagali, za a fito da kayan lambu kamar albasa da gero da kifaye, waɗanada ake bai wa jama’a su rarraba. Kabir M, (2008).

2.4.1 Asalin Sunan Garin Faskari

Dangane da kafa garin Fasakari kuwa, lokacin da Giɗo da Ɗan’yanbani suka zo daga alƙalawa, sai suka iske Maguzawan nan suka yaƙe su, suka kama bayi, kuma suka karɓe wurin. Daga nan sai suka tambayi waɗannan bayin sunan wannan wuri da suke zaune, sai arnan nan suka ce sunan sa “Faskari”. Don haka, da suka ji sunan wannan wuri sai suka ce, “tun da haka sunan wannan wuri yake,  to lallai ba za mu je ko ina ba”, wannan yasa sai suka sami wuri suma suka zauna.

2.4.2. Waɗanda Suka yi Sarautar Faskari

Tarihi ya nuna cewa Giɗo da Ɗan’yanbani asalin su Gobirawa ne,  kuma su ne mutanen da aka fi sani da cewa su ne suka kafa garin Faskari.  Ɗan’yabani shi ne ya fara sarautar garin, daga baya kuma ya baiwa ɗansa Isah. Bayan wannan kuma sai faskari Yunusa, wanda ya kafa Guga a cikin ƙasar Bakori, sai Faskari  Ɗan Zangina, koda yake  sarautar Barantaka ya yi. Daga shi kuma sai Faskari Abdu ɗan Isah, sai Faskari Abdu ɗan Tandu, koda yake tsohonsa bai yi sarauta ba. Bayan wannan kuma sai aka naɗa Faskari ɗan Ali ɗan Isah, sai Faskari  ɗan Barda, koda yake shima tsohonsa bai yi sarauta ba. Bayan wannan kuma sai aka naɗa Faskari Abu, sai faskari ɗan Kurciya wanda yake da zuri’ar Mainasara, ɗaya daga cikin abokan tafiyar su Giɗo. Daga nan sai Faskari Isiyaku ɗan Ali, banda wannan kuma sai aka naɗa Faskari Sani ɗan Nakalle ɗan Faskari Abu, koda yake shima tsohonsa bai yi sarauta ba. Sannan sai Faskari Ummaru I, sai Faskari Abu, dukkan waɗannan sarakai suna zaman magadai ne, kuma da wuya a sami shekarun kowane a bisa gadon sarauta. Kabir M, (2008).

A zamanin Faskari  Abu ne garin Faskari ya fara bunƙasa, har mutane suke yi masa kirari da cewa:

“Faskari, Faskararren gari,

Ta Ɗan’yanbani

Taba mai shiga zuci”

Ka zo da niyyar yini, ka kwana

2.5 Asalin Sunan Kogo

To yanzu sai mu koma maganar Birnin Kogo, tun da can ne asalin. Waƙe ɗan Jatau ɗan Kaura Gumari, shi ne ya tada birnin Kogo, a zamanin Sarkin Katsina Muhammad Bello, Ƙaura kauren Gumari, wanda ya gina birnin Ƙogo, yana daga cikin sarakunna  Katsina na Haɓe. Dalilin kiran wannan gari Ƙogo shi ne, wai lokacin da ya  zo tare da mutanen sa sai ya ce “ga wani wuri nan za mu yi kogo mu fake yaƙi,faɗar haka yau da gobe, ya sanya wurin ya sami sunan Ƙogo. Amman Ƙogo da Faskari a yau duk ɗaya ne, amman sarautar garin ana kiranta da suna Ƙogo,  hasali ma da wannan suna ne ake kiran hakimin garin ,. Wato sarkin Ƙogo, kafin yanzu da sunan sarautar ya canza zuwa sarkin yamma. Yusif (2003).

2.6 Sarakunna Ƙogo da Yaƙe-yaƙen su.

Dalilin zuwan wake da Jatau wannan wuri shi ne, wai waɗansu malamai suka yi masu bayani cewa, idan ya tafi yamma zuri’arsa za ta yi arziƙi, don haka da jin haka ya kama hanya ya tafi, bai zame ko’ina ba sai wannan wuri inda ya kafa Birnin Ƙogo. An ce sai da suka yi shekara huɗu shi da jama’arsu suna aiki, sannan suka ƙare, kuma ba a daɗe da ƙarewa ba ya rasu.

Muhammadu Ɗanmama ya yi yaƙe-yaƙe da yawa daga cikin yaƙe-yaƙen da ya yi har da yaƙin Kazaga, inda ya ci garin, kuma sarkin garin ya mutu.  Haka kuma ya sake zuwa yaƙin Kakihun cikin ƙasar Gwari,  nan ma ya samu bayi ma su  yawan gaske, bayan wannan kuma, ya sake fita yaƙin Sakan da yaƙin Kamuka, waɗanda ya ciwo nasara. Haka kuma ya ci Mushin da Iragogo,  daga nan ya dawo gida. Da Muhammadu Ɗanmama ya huta, sai ya sake fita yaƙin Nufe, sai dai ba a yi yaƙin ba, domin sulhu aka yi  aka ba shi kyautar doki ɗari da kyankyandi ɗari, wato wata irin jakar saƙa ta Hausawa wadda ake cikawa da manyan riguna da wanduna ma su yawa. Daga nan Muhammadu Ɗanmama bai zame ko ina ba sai yaƙin Lemu da  Tagina cikin ƙasar Kwantagora da Katako da kuma Kwantagora ta Zuru, daga nan ya wuce ya kai yaƙi Bama ta Anka da magajin Azarfa da Bakura ta cikin ƙasar Zamfara. Haka kuma Muhammadu Ɗanmama ya sake fita zuwa yankin Garewa ta Ummaru, ya wuce Zaria da kuma Kusheri ta Birnin Gwari. Bayan dawowarsa daga wurin yaƙe-yaƙe ne ya rasu, ya yi shekaru da yawa a bisa gadon sarauta.

            Bayan rasuwarsa kuma, sai a cikin shekarar 1903 sarkin Katsina Abubakar ya naɗa Kogo ɗan Magarya, ɗan Muhammadu Ɗanmama, Kogo Ɗanmagarya, ya je yaƙi da yawa, a ciki kuwa har da yaƙin magamin mai Tarko ta cikin ƙasar Gusau, kuma ya kai yaƙi Ɗangulbi da Rindin ta Ɗansadau ta cikin ƙasar Sarkin kudu. Bayan Ƙogo Ɗanmagarya ya rasu,  sai aka naɗa Kogo Ɗankeji Ɗan Muhammadu Ɗanmama a cikin shekarar 1906. Daga nan kuma sai Kogo Dodo Ɗanmama wanda tun yana ɗan sarki ya kai ma Damari da Bakun yaƙi.

            Cikin shekarar 1915  ne sai aka naɗa Kogo Musa ɗan Magajiya, yana ɗan sarki ya je yankin Burwaye ta Ɗansadau, kuma ya ci nasara. Bayan rasuwarsa a shekarar 1922 sai aka naɗa Kogo Ummaru ɗan Muhammadu wanda shi ne yana ɗan sarkinsa ne ya je yaƙin sabon gari ta Zaria da Magaji da Kagara ta cikin ƙasar Maska.

            Kogo Ummaru shi ne wanda ya taso daga birnin kogo ya dawo  Faskari da zama, kuma shi ne wanda a ka fitar daga sarauta har sau uku ana mayar da shi. Da farko, bayan ya yi shekara bakwai bisa gadon sarauta, aka fitar da shi, garin ya zauna wata biyar ba a naɗa kowa ba, sannan aka sake mayar da shi. Na biyu kuma, garin ya zauna ‘yan watanni ba a naɗa kowa ba, kuma daga baya aka mayar da shi, kuma bayan ya sake hawan gadon sarauta sai aka fitar da shi,  sannan kuma bayan ya sake hawan gadon sarauta, sai aka fitar da shi a cikin shekarar 1932. Dalilin da ya sanya haka kuwa, shi ne, wai faɗar wani malami ne da ake kira “Malam Hassan”, gaba, ba zai hawura shekara bakwai ba a bisa gadon sarauta ba. Kuma an ce wannan malamin ya sake roƙon Allah, ya kautar da hanyar motar da ya ji labarin za ta bi ta birnin Kogo. Wannan hanya kuwa, ita ce wadda aka zagaya da ita ‘yantumaki zuwa Ƙanƙara.

            Haka kuma bayan cire Ummaru, sai sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya naɗa Kogo Abdullahi Ɗangaladima Salu. Haƙiƙa a nan za a iya mamaki yadda wanda ke zuri’ar Galadanci zai zo ya yi sarautar Kogo. To alal haƙiƙa, katin zuwan Turawa a ƙasar Kogo, bata yi zama a ƙarƙashin hakimin kanta ba sai bayan da aka rarraba ƙasashen cikin shekarar 1915.

            A cikin shekarar 1936 ne, aka buɗe makarantar Firamare ne ta cikin garin Faskari, sannan a shekarar 1937 ne aka buɗe ƙaramar asibiti ta garin Faskari. Bayan Kogo Abdullahi ya rasu, sai aka naɗa Kogo Musa da magajiya ɗan ‘yartauje Idris. An sauke Kogo Musa saboda wani laifi da ya yi wa N.A ta Katsina. Don haka a cikin shekarar 1947 sai sarkin Katsina Alhaji Usman Nagoggo, ya naɗa Kogo Ibrahim ɗan Ummaru. Daga kansa ne, maganar Malam Hassan ta cewa ba za a sake naɗa wani Kogo wanda zai wuce shekara bakwai a bisa gadon sarauta ba ta sha ruwa. Dalili shi ne, Kogo Ibrahim ya haura shekara bakwai, har ma ya nunka bisa ga shekaru bakwai a kan gadon sarauta.

            Lokacin da aka naɗa Kogo Ibrahim, sai ya taso daga tsohuwar Faskari, wato tsohon gari kenan inda Faskarin ta fara kafuwa ko zama, sai ya  dawo inda take yanzu, ya zauna. Shi da kansa ya shata garin. Dalilin tasowarsa daga can Tsohon garin shi ne, tsohon garin cike yake da duwatsu ko ina.

To wannan gari da Kogo Ibrahim ya shata da kansa, yanzu ya zama abin sha’awa, kafin Kogo Ibrahim ya zo ga wannan matsayi, sai da ya yi aiki a PWD ta Katsina da kuma ta Kano.

A shekarar 1952 ne girman ƙasar Faskari ya kai murabba’in 1712.

A yanzu haka ƙasar tana da garuruwa guda goma (10), inda magadan  suke zaune. Waɗannan garuruwan sune kamar haka:

Faskari

‘Yankara

‘yarmalamai

Maigora

Sabon layi

Daudawa

Mairuwa

Ruwan Godiya

Tafoki

Nasarwa

Wannan shi ne ɗan taƙaitaccen tarihin garin Faskari ta jihar Katsina. Musa Y, (2014)

2.7 Ma’anar Faskare

Ma’anar faskare: - Faskare wata sana’a ce ta gargajiya wadda matasa da masu ƙarfi a jika kan yi domin samun abun sakawa a baka. Ita wannan sana’a ta faskare, ta ƙunshi saran gungumen itace, inda ake farfasa su zuwa ƙanana, wato filla-filla kenan ta yanda za a iya amfani da su wajen girki na yau da kullun a gidaje da sauran wurare daban-daban. Usman K, (1998).

Faskare: wata sana’a ce wadda ake yi da gatari domin saran itace a yi ma shi  gunduwa gunduwa, sannan a rarraba shi ɗaya bayan ɗaya a yi amfani da shi. Ibrahim B, (1999).

Faskare: Wata sana’a ce ta majiya ƙarfi wadda suke yi domin samun biyan buƙatunsu na yau da kullun. Haka kuma wannan sana’a ana gudanar  da ita ne ta hanyar amfani da gatari a farfasa gumaguman itace, domin yin amfani da su wajen girke-girke, ko wasu abubuwa makamantan waɗannan. Bala Usman (2007).

Faskare: Sana’a ce da waɗansu al’umma ke yi, wacce ake yin amfani da gatari wajen faskara icce domin neman abinci.

2.8 Kammalawa

            To kamar yanda muka gani, a wannan babi na waiwayen ayyukan da suka gabata, abubuwan duka sun ƙunshi bayani ne a kan waiwaye da kuma ma’anar sana’a da ire-iren sana’o’in gargajiya na Hausawa, da kuma tarihin ƙasar Faskari da kuma ma’anar Faskare. Kasancewar ba a taɓa yin wani aiki a kan sana’ar faskare ba, shi yasa abubuwan suka yi wahala sosai. Sai dai fira da na yi ta yi da mutanen  da suke gudanar da irin wannan sana’ar ta faskare.

Post a Comment

0 Comments