Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara.

Faskare A Garin Faskari (2)

NA

ABUBAKAR HASSAN

faskare

BABI NA ƊAYA

GABATARWA

1.0 Gabatarwa

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, Allah ya daɗa tsira ga Annabi Muhammad (S.A.W). godiya ta tabbata da Allah maɗaukakin sarki da ya halicci al’umma daban-daban, kuma ya basu fasahar aiwatar da sana’o’i daban-daban, domin su sami abin da za su saka ma bakin salati. To kamar yadda muka sani, Hausawa sun da sana’o’insu na gargajiya tun kafin zuwan addinin muslunci da kuma Turawan mulkin mallaka ƙasar Hausa. Daga cikin sana’o’in nan na Hausawa har da “faskare” a cikin su. Faskare sana’a ce da al’ummar Hausawa suka daɗe suna aiwatarwa a tsakaninsu, suna yin wannan sana’a ne domin su sami abinci.

Kamar yadda sunan wannan bincike ya nuna, wato “Faskare a garin Faskari”, wannan aiki, zai yi ƙoƙarin binciko tarihin garin Faskari, haka zalika, wannan aiki zai yi ƙoƙarin gano ya ya ake gudanar da sana’ar fakare a garin Faskari, kuma suwa ne ne ke gudanar da wannan sana’ar, da dai sauran abubuwa makakamntan haka.

1.1 Manufar Bincike

Kamar kowane irin bincike, a kan buƙaci a nemo wasu muhimman abubuwa da ba a san su ba tun farko, ko kuma an san su amman ba a tsara su ko rubuta su ba domin nazari ba,  don haka wannan aiki zai yi ƙoƙarin gano waɗannan keɓaɓɓun abubuwan da ke cikin sana’ar Faskare. Har ila yau, wannan kundi zai bayyana ma ɗalibai da masu sha’awar wannan fanni yanda za a ƙara fahimtar sana’ar faskare, kuma a inganta ta yanda za ta dace daidai da zamani. Manufar wannan bincike, shi ne ya fito da abubuwan da mutane suka daɗe suna fama da ƙishiruwarsa ta fannin wannan sana’a ta faskare.

1.2 Dalinin Bincike

Kamar yadda aka riga aka sani, komai na rayuwa akwai dalilin aiwatar da shi. Babban dalilin aiwatar da wannan bincike shi ne, domin cike wani babban gurbi na ilimi wanda ba a cike ba. Fakare dai sana’a ce mai cin gashin kanta kamar sauran sana’o’in Hausawa, amman har yanzu ba a taɓa wani bincike a kan sana’ar ba, duk da ceawa mutane sun san muhimmancin  sana’ar kuma sun san matsayinta. An yi bincike a kan sauran sana’o’i daban-daban, kamar: fawa da rini da noma da ƙira da dai  sauran sana’o’i daban-daban, amman ba a taɓa wani bincike a kan sana’ar faskare ba, to wannan dalilin ne ya ban damar in yi bincike a kan sana’ar faskare domin in cike wannan babban gurbin da yake fama da ƙarancin abubuwan dubawa na ilimi. Yin wannan bincike ne zai ba da damar a ƙara fito da wannan sana’ar fili a idon duniya, kuma yin wannan binciken ne zai ba da damar tabbatar  ma duniya cewa shima fa faskare sana’a ce mai cin gashin kansa kamar sauran sana’o’i.

1.3 Muhimmancin Bincike

Har ila yau, duk al’amari na rayuwar yau da kullun, yana da matuƙar amfani ko da kaɗan ne. Muhimmancin wannan bincike shi ne, zai taimaka wajen samar da wani abin karantawa ko kuma  dubawa a kan abin da ya danganci sana’ar faskare, zai taimaka ma ‘yan uwanmu ɗalibai don su sami sauƙin yin binciken su, kuma  wannan bincike zai ƙara haskaka sana’ar ta faskare ga masu aiwatar da ita da kuma sauran al’umma.

Haka zalika, wannan bincike zai ƙara bani damar fahimtar fagen da na zaɓa don gudanar da bincike, haka kuma zai ƙara sa in fahimci abubuwa da dama dangane da bin da nake yin bincike a kansa. Kuma wannan bincike ana sa ran zai cike wani babban gurbi wanda ya daɗe yana ci ma mutane tuwo a ƙwarya.

Bayan haka kuma, gudanar da wannan bincike abu ne muhimmi domin zai kasance abu mai fa’ida ga sauran ɗalibai waɗanda ake sa ran za su duba shi domin amfani da shi ta fannin nazarin wasu sana’o’in al’ummar Hausawa na yau da kullun.

1.4 Matsalolin Bincike

Kowane irin al’amari  na rayuwar yau da kullum yana da irin matsalolin da yake fuskanta, to haka shima bincike yana da irin matsalolin shi wanda ake fuskanta yayin gudanar da shi. Babbar matsalar da na fuskanta/ manyan matsalolin da nake fuskanta yayin gudanar da wannan bincike su ne, akwai ƙarancin littattafan dubawa,  da kuma ƙarancin mujallu da ƙasidu da kuma rashin wasu kundayen ilimi waɗanda aka wallafa na wannan sana’a ta faskare, tabbas rashin waɗannan abubuwan dubawa ba ƙaramin matsala ba ne ga mai bincike, domin bai san ina zai tunkara ba, kuma bai san daga ina zai fara ba. Tabbas waɗannan,  da ma wasu makamantan su, su ne manyan matsalolin da suka fi damun ma su binciken ilimi, wato matsalar rashin kayan aiki da kuma matsalar ƙarancin lokaci, da kuma matasalar kuɗi.

1.5 Hasashen Bincike

Kowane irin abu na rayuwa akwai irin hasashen da ake ma shi, ana  fata in Allah ya so wannan bincike na sana’ar faskare ya  zamo silar da zai sa a riƙa kallon “Faskare” a matsayin sana’a mai cin gashin kan ta,  kuma sana’ar da ake neman kuɗi da ita. Kuma ana hasashen wannan bincike ya zamo wani abu wanda ɗalibai za su yi alfahari da shi wajen kore ma su ƙishirwar da suke fama da ita na rashin wani abin dubawa wanda ya danganci sana’ar faskare.          

Ina sa ran wannan kundi na sana’ar faskare ya zamo wani jigo ko abin dubawa wanda zai sanya ɗalibai da kuma masu bincike su sami sauƙi wajen nazarin abin da ya shafi sana’ar faskare, wato ina hasashen wannan binciken ya zamo  haske abin alfahari ga ɗaliban ilimi.

1.6 Farfajiyar Bincike

Domin samun nasarar wannan bincike, an keɓe wannan bincike ne zuwa ga wani muhalli na yankin Faskari, wato yankin Faskari a cikin Jihar Katsina. Wannan bincike mai  suna “Faskare a garin Faskari”, ya keɓanta ne kawai a yankin garin Faskari.

Domin abu ne mai wuya a ce za a nazarci sana’o’in faskaren ƙasar Hausa gaba ɗaya, saboda a sakamakon bambancin wurin zama, ana iya samun bambance-bambance dangane da yanda ake gudanar da sana’ar fakare a ƙasar Hausa baki ɗaya.

A bisa wannan dalili ne aka ga ya dace a keɓe wannan bincike a ƙasar Faskari kamar yanda aka gani a taken binciken. Duk wani nazari da za a yi a wannan binciken ya keɓanta ne kawai ga yanda ake gudanar da faskare a garin Faskari, domin gano yadda suka ɗauki wannan sana’a ta su ta faskare da matuƙar muhimmanci har su ke aiwatar da ita a tsakanin su.

1.7 Hanyoyin Gudanar da Bincike

Wajen ƙoƙarin gudanar da wannan bincike, an bi wasu hanyoyi na musamman domin ganin cewa an binciko abubuwa masu muhimmanci da suka shafi wannan bincike. Daga cikin waɗannan hanyoyi da aka bi akwai; fira da mutane domin samun bayanan da suka kamata, ziyarar ɗakin karatu domin duba littatafai da  kundaye da mujallu da sauran su.

1.8 Kammalawa

To Alhamdulillahi, kamar yadda aka ɗauki ƙudirin yin bincike a wannan fannin, kuma a kan sana’ar faskare wanda binciken ya keɓanta ne kawai a garin Faskari, za a gudanr da wannan binciken ne ta hanyoyi daban-daban, musamman wajen yin fira da jama’ar da suke gudanar da irin wannan sana’ar ta faskare a garin Faskari. Za a yi ƙoƙarin gano shi kan shi tarihin garin Faskari da kuma waɗanda suka kafa garin, haka zalika kuma, za mu yi ƙoƙarin binciko mine ne faskare, kuma ya ake gudanar da faskare a cikin garin Faskari, kuma  suwa ne ne ke gudanar da wannan sana’ar ta faskare a garin Faskari, kuma sannan za a gano wane irin ƙalubale ne sana’ar Faskare ke haifar wa a garin Faskari.

Kuma za a gudanar da wannan bincike ne ta abubuwan ilimi da suka gabata wato abubuwa na ilimi da aka wallafa waɗanda za su taimaka wajen samun nasarar wannan bincike, da kuma fira da masana waɗanda su ke yin  wannan harkar.