Faskare A Garin Faskari (1)

    Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara.

    Faskare A Garin Faskari (1)

    NA

    ABUBAKAR HASSAN

    faskare

    SADAUKARWA

    Na sadaukar da wannan kundin digiri ga mahaifiyata Hama, Allah ya jiÆ™anta ya gafarta mata dukkan kurakuranta, da kuma babana malam Hassan faskari da yayata Maryama da Kabir da Maharazu da Rabi’atu da Hadiza da kuma Jafar.

    TSAKURE

    A wannan bincike da ake gudanarwa, za a yi Æ™oÆ™arin binciko asalin sunan faskare da ma’anar faskare da kuma yanda ake gudanar da faskare a cikin garin Faskari. Bugu da Æ™ari, a wannan É—an Æ™warya-Æ™waryar bincike, za a yi Æ™oÆ™arin gano illolin da ke tattare da sana’ar faskare da kuma muhimmancin sana’ar. Haka kuma, a wannan bincike, za a yi Æ™oÆ™arin binciko ire-iren itatuwa masu sauÆ™in faskare da masu wahalar  faskarawa. Daga Æ™arshe kuma za a kammala wannan aiki tare da shawarwarin da malamai suka bada da kuma sauran mutane.  

    GODIYA

                Ina mai godiya ga Allah maÉ—aukakin sarki mai kowa mai komi mai rahama mai jin Æ™ai zuwa ga bayinsa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da sahabbasa da zuri’arsa da dukkan wanda ya bishi har zuwa ranar sakamako.

                Bayan haka,  ina miÆ™a godiya ta da jinjina zuwa ga mahaifina Malam Hassan bisa jajircewa da ya yi na ganin cewa na kammala karatuna, kuma na gode da irin addu’o’in da ya yi ta yi man dare da rana. Allah ya saka masa da mafificin alkairi, kuma Allah ya saka masa da gidan aljanna Amin.

                Bayan haka, ina miÆ™a godiyata ta musamman zuwa ga yannena da kuma Æ™annena, bisa ga gudunmuwar da suka bani da kuma tayani da  addu’o’i da sukyi, kamar Maharazu da maryam da Kabir,  da Rabi’atu da Hadiza da Jummai Allah ya gafartamata da Jafar da Musa da  Ibrahim da Nasir. Allah ya saka masu da mafificin alkairi amin summa amin.

                Ba zai yiwu in yi tuya in manta  da albasa ba, ina miÆ™a godiya da ban jinjina zuwa ga Mama (Asabe) bisa gudunmawar da ta ba ni tun daga lokacin da na fara karatu har zuwa lokacin da Allah ya sa na kammala, tabbas ta yi namijin Æ™oÆ™ari, Allah ya saka mata da mafificin alkhairi, Allah ya saka mata da gidan aljanna, kuma Allah ya albarkaci zuri’arta amin.

                Bayan haka, ina farin cikin miÆ™a godiyata ga malamaina na sashenmu da irin gudunmawar da suka bani da kuma shawarwari.

                Ina miÆ™a godiyata ta musamman ga malamai na kamar haka: Prof. Aliyu M. Bunza, da Dr. Tahir, da malam Rabi’u Aliyu ÆŠangulbi, da Malam Musa Abdullahi da Prof. Magaji Tsoho Yakawada da Prof. Ahmad Halliru Amfani da Dr. Nazir Abbas da Prof. Balarabe da Dr. Fadama da malam Isah S. Fada  da dai suaransu. Allah ya saka masu da mafificin alkhairi amin.

                Bayan haka, ina miÆ™a godiya da jinjina ga malamina, kuma mai duba wannan aiki nawa Dr. Tahir, bisa jajircewa da ya yi da kuma shawarwarin da ya bani na ganin cewa wannan aiki ya kammala, Allah ya saka masa da mafificin alkhairi amin.

                Ina miÆ™a godiyata  zuwa ga abokaina kamar: Yahaya Umar Barau, Musa Magaji, Abubakar Abdulrahman (Attah), Kabir Tajudddeen, Abubakar Muhammad (Dodo),. Ibrahim Nasir (Ibson) da sauransu. Nagode sosai Allah ya saka da mafificin alkhairi.

                Bayan haka ina miÆ™a godiyata zuwa ga aboka nan karatu na kamar Mustapha Sa’idu Faskari,  da Abdulrahman Bala da Abdulrashid Sifawa da ÆŠayyaba Mustapha Ibrahim da Amina Abubakar da  Nasiru Hassan da Ahmad Muhammad Kabir da Sani Adamu da Bashir Isiyaku da Hizbullahi ÆŠanlami da Nura Sani Kwatarkwahi da Aliyu S Ibrahim da Hassan Galadima, da dai sauransu. Allah ya saka da alkhairi amin.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.