Ticker

6/recent/ticker-posts

Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (2)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Koyar da Harsuna da Al’adu, Tsangayar Fasaha da Ilimi, Jami’ar Tarayya, Gusau don neman digiri na farko.

Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (2)

NA

HIZBULLAHI ƊANLAMI

gini

BABI NA ƊAYA: - SHIMFIƊA

1.0 Gabatarwa

            Wannan babi yana ɗauke ne da bayanin tsarin yadda aka shata binciken  da kuma yanayin gininsa. Masana harshen Hausa tun farko sun yi ƙoƙarin karkasa harshen (Hausa) ta fuskar koyo da koyarwa da kuma bincike da nazari zuwa manyan fannoni uku wato, harshe, adabi da kuma al’ada.

            Tushen wannan bincike mai suna “Magini (Birkila/messin) a garin Kwatarkwashi”, yana ƙarƙashin fannin al’ada ne, kuma yana ɓangaren sana’a ne, fannin  samar da muhalli da sauran ababen da magini (Birkila) ke ginawa domin inganta rayuwar Bahaushe.

            A ɗan hasashena, al’ada tana da muhimmanci daga cikin fannonin uku, wato harshe, adabi da kuma al’ada. Saboda al’ada, ta shafi rayuwar ɗan’ Adam ne baki ɗaya tun daga haihuwarsa har zuwa ƙabarinsa. Magini (Birkila/messin) yana cikin sahun gaba daga cikin mutanen da suke cin gajiyar al’adar garagajiya. Wato sana’ar gini da magini (Birkila/messin) ke aiwatarwa wani babban reshe ne na al’ada. Kuma birkila yana da tasiri ƙwarai da gaske wajen bunƙasa da haɓaka al’adar Bahaushe tun ba a fannin sana’o’in gargajiya ba.

            Wannan bincike za a gudanar da shi ne a kan “Birkila/Messin a garin Kwatarkwashi”, sannan za a yi ƙoƙarin bayyana yadda magini (Birkila) yake a garin Kwatarkwashi, da ci gaban da sana’ar ta samar ga shi kansa (Brikilan) da matasan garin kwatarkwashi. Haka kuma harshen Hausa ya sami bunƙasa gwargwadon hali. Domin ganin an cimma  nasarar  kammala wanann bincike, an karkasa aikin binciken zuwa babuka biyar.

            Babi na farko yana ɗauke da shimfiɗar wannan bincike da gabatarwarsa, wanda zai tattaro bayanai a kan manufar bincike da dalilinsa. Akwai kuma farfajiyar bincike, muhimmancin bincike da kuma hanyoyin gudanar da binciken. Haka kuma da hujjar ci gaba da bincike, da bitar wasu ayyukan da suka gabata.

            A babi na biyu kuwa, nan ne za a bayyana tarihi da al’adun garin Kwatarkwashi, wanda ya ƙunshi gabatarwa da taƙaitaccen tarihin Kwatarkwashi da tsarin gine-ginen Kwatarkwashi. Bayan wannan akwai bayanin al’adun garin Kwatarkwashi da kuma shigowar baƙin al’adu a garin Kwatarkwashi. Har wa yau, da tasirin shigowar baƙin al’adu a garin Kwatarkwaahsi, duk dai a wannan bincike.

            A babi na uku, za a bayyana sana’ar gini a garin Kwatarkwashi, inda ya ƙunshi gabatarwa da ma’anar gini da ire-irensa, da kuma ma’anar magini (Birkila/Messin) da kuma bayanin maginin gargajiya da maginin zamani. Sannan a ƙarshen wannan babi za a kalli gini a garin Kwatarkwashi da kuma irin gudunmuwar da magini (Birkila/messin) ke bayarwa wajen bunƙasa kalmomin Hausa.

            Babi na huɗu, ya ƙunshi tasirin sana’ar gini ga bunƙasa tattalin azikin Kwatarkwashi. A ƙarƙashinsa akwai ya haɗa da gabatarwa da samar da aikin yi ga matasa da bunƙasa kiyo da noma a garin Kwatarkwashi. Haka kuma da bunƙasa  saye da sayarwa a garin Kwatarkwashi.

            Babi na biyar, kuma na ƙarshe shi ne babin da ya ƙunshi kammalawar wannan bincike, wanda da ya ƙunshi gabatarwa da jawabin sakamakon bincike da shawarwari da kuma naɗewa, da kuma manazarta.

1.1 Manufar Bincike

            Manufar wannan bincike ita ce samar da wani kundin bincike wanda zai  zama a matsayin wani ɗan yunƙuri  da aka gabatar a ɓangaren al’ada, domin raya al’adun Hausawa.

            Manufofin wannan bincike suna da yawa, amma ga wasu daga cikinsu: -

(a)   Samar da ɗan abin dubawa ga mai nazari ko karatu.

(b)  Farfaɗo da al’adun Hausawa, musamman ɓangaren sana’ar gini da magini (Birkila). Ganin, yadda sauran takwarorin sana’a’oin sukayi masa fintinƙau ta fannin bincike da nazari.

(c)   Zaburar da masana al’adu da masu bincike zuwa ga sana’ar gini da magini (Birkila). Saboda gefen yana cikin jerin gwanon al’adu da suka kusa mutuwa. Saboda rashin bincike mai zurfi a wannan fanni.

(d)  ƙoƙarin tattara bayanai waɗanda suka fayyace tsakanin maginin gargajiya da na zamani.

(e)   Bayyana muhimmancin magini (Birkila) da tasirinsa da kuma irin gudunmuwarsa ga al’umma.

(f)    A ƙarshe an bayyana tsintsar rawar da  Magina (Birkila) suke takawa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da kuma inganta rayuwar matasa.

1.2    Dalilin  Bincike

            Dalilin da ke sa a gudanar da bincike suna  ɗauke da manufofi daban-daban kamar yadda ake aiwatar da shi binciken. Saboda haka, dalilan da suka sa aka gudanar da wannan bincike suna da yawa, amma ga wasu kamar haka:

(a) Babban dalili na ɗaya ga aiwatar da wannan bincike shi ne, cike wani gurbi da masana suka manta da shi cikin littafan da suka rubuta, waɗanda ba su yi magana a kan su ba.

            A fannin al’ada Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, ya rubuta littafi a fannin al’adar, amma bai ambaci sana’ar gini da magini (Birkila) ba duk da sanin kowa ne al’umma ba za ta iya rayuwa babu muhalli ba.

(b) Dalili na biyu kuwa, shi ne, rashin tsayuwar masana su yi zuzzurfan bincike a kan sana’ar gini da magini (Birkila), sai dai a shafi wurin sama-sama a  wuce, misali kamar:

            Farfesa, Ibrahim Yaro Yahaya da wasu (1992), sun kawo sana’o’in Hausawa na gargajiya, inda suka ambaci sana’ar gini a ciki, amma ba a yi bayanin sana’ar tiryan-tiryan ba, kamar yadda ya kamata. Madogarata ita ce littafin nasu mai suna “Darussan Hausa don manyan makarantun sakandare (1992). A nan ne suka kawo sana’o’in.

(c) Dalili na uku, fannin al’ada sashe ne da yake da fatara irin ta ƙarancin masana a gefen. Saboda ko a ɓangaren wasu al’adun za a ga cewa al’adun suna cikin hatsari (endangered) kamar gini da magini (Birkila).

(d) Zaburar da masana da masu bincike a kan al’ada, domin karkatar da hankalinsu zuwa fannin sana’ar gini da magini (Birkila), domin haɓɓaka bincike a gefen.

            Dukkan al’amurran duniya baki ɗayansu da ke gudana akwai dalilin kasancewarsu da kuma na faruwa, kuma dalilan na iya zama a sarari ko a ɓoye. A taƙaice, waɗannan ne da wasu dalilan da ya sa aka gudanar da wannan  bincike.

1.3 Farfajiyar Bincike

            Magini (Birkla/ Birkilanci) wani babban rukuni ne a cikin sana’o’in al’ummar Hausawa jiya da yau. Saboda kowace irin halitta ta duniya ba za ta iya rayuwa ba tare da muhalli ba. Hasali ma  yana ɗaya daga cikin abubuwa uku da ake buƙata a rayuwa. Wato muhalli (shelter). Wannan bincike zai taƙaita ne a kan “Sana’ar birkila (messin) a garin Kwatarkwashi”.

            A ƙarshe, binciken zai bayyana ma’anar birkila da kuma ire-iren abubuwan da magini (Birkila) yake ginawa da kuma irin gudunmuwar da magini (Birkila) yake bayarwa wajen bunƙasa harshen Hausa, sannan da muhimmancinsa ga rayuwar al’umma.

1.4 Muhimmancin Bincike

            Kamar yadda masana al’ada suka bayyana ta da cewa “hanya ce da ta shafi rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwarsa, har zuwa ƙabarinsa”. Wato ke nan sana’ar gini wata abu ce mai muhimmancin gaske musamman ta hanyar samar da muhalli ga al’umma.

            Saboda haka, magini (Birkila) yana a sahun gaba cikin mutanen da suke ba da gudunmuwa wajen bunƙasa al’adu da sana’o’in gargajiya da kuma tattalin arziƙin al’ummar Hausawa.

            A taƙaice, babban muhimmancin wannan bincike shi ne samar da bayanai nagartattu game da sana’ar magini (Birkila) da rawar  da suke takawa, wajen samar da aikin yi  ga matasa da rage raɗaɗin talauci cikin al’umma.

1.5 Hanyoyin Gudanar da Bincike

            Kamar yadda yake a bayyane sanin kowa ne cewa, kowa ne irin bincike  ne za a gudanar  ko gabatar, musamman ma na ilmi ba zai kammalu ba, ba tare da an bi hanyoyi da dabarun gudanar da shi ba. Saboda haka, kafin a kammala wannan bincike, za a yi amfani da hanyoyin da suka dace tare da dabaru daban-daban domin ganin haƙa ta cimma ruwa. Za a ziyarci ɗakunan karatu da cibiyoyin ilmi daban-daban domin samun bayanai daga ayyukan masana daban-daban a kan abin da ake  nazari na sana’ar gini. Hanyoyin wannan bincike sun haɗa da: -

-          Nazarin littafan da aka wallafa a kan al’ada

-          Nazarin littafan da aka walllafa a kan fannin Hausa guda uku (Harshe, Adabi da Al’ada) don koyo da koyarwa.

-          Nazarin maƙalu waɗanda malamai da masana suka gabatar a Jami’o’i da cibiyoyin ilmi daban-daban, masu dangantaka  da wannan bincike.

-          Tattaunawa ta musamman da malamai da suaran masana dangane da abin da ake bincike a kansa, domin neman ƙarin haske da shawarwari.

            A taƙaice, waɗannan su ne hanyoyi da dabarun da aka gudanar a lokacin  da ake wannan bincike.

1.6 Hujjar Ci Gaba da Bincike

            Bincike a kan “Magini (Birkila) a garin Kwatarkwashi”.  Yana da hujjar da za a ci gaba da gudanar da shi. Hakan ya tabbata ne la’akari da bitar ayyukan magabata da aka yi, da sauran ayyukan da suka gabaci wannan bincike. Ba shakka masana da dama sun yi rubuce rubuce a kan gini da sauran abubuwan da suka danagance shi. Ɗalibai ma sun rubuta kundaye daban-daban. Amma duk da haka wannan bincike yana da mashiga da hujjar da za a ci gaba da shi domin ba a ba shi muhimmanci ba a baya sosai. Idan an yi kuma, to wannan binciken zai fito da wasu muhimman abubuwa waɗanda ba a ambata  a na farko ba.

1.7 Bitar Ayyukan da Suka Gabata

            Al’adun Hausawa sun daɗe ana rubuta su da nazari a kan su, saboda an ɗan sami lokaci ana taskace sassan al’ada daban-daban ta rubutawa da wallafawa.

            Masana da manazarta da marubuta da yawa sun yi ayyuka da dama da suka shafi sana’o’in Hausawa na gargajiya, da ma yadda ake kallonsu a al’adance. Dalilin haka ne ya sa gabanin aza tubalin wannan aiki aka yi ɗan ƙoƙarin bitar ayyukan da suka gabaci wannan bincike, masu dangantaka da wannan aiki gwargwadon hali. Saboda tantance wuraren da aikin ya yi kama, da inda aka bambanta.

            Ayyukan da aka duba lokacin gudanar da bitar sun haɗa da wallafaffun littafai, mujallu da maƙalu da kuma kundayen  bincike. Ga jerin ayyukan  da hannu ya sami kai wa gare su kamar haka: -

1.7.1 WALLAFAFFUN / BUGAGGUN LITTAFAI

            Akwai wallafaffun ko bugaggun littafai da dama masu alaƙa da wannan aiki nawa. Daga ciki akwai littafin:

            Rimmer, da wasu (1966) a cikin littafinsu mai suna “Zaman mutum da sana’arsa”, marubutan sun rubuta littafin ne a kan babuka, wato daga babi na ɗaya har zuwa babi na biyar, yayin da babi na biyu suka yi bayanin noma da asalin sana’o’in lambu da noma tsohon ciniki da gonar gwamnati da noma a Ingila, da noma a ƙasar Masar da kogin Nile da ganuwa da ƙasar Asiya da manoma a ƙasar Sin da kogunan ƙasar Sin da kuma mutanne Sin.

            A babi na biyar suka yi bayanin ginin tukwane a Nijeriya ta Arewa da kuma faɗi-ka-mutum (Tangaram).

            Wannan littafi yana  da alaƙa da wannan aiki nawa, saboda sun yi bayani ne a kan sana’o’in Hausawa, musamman ginin tukwane, sai dai sun bambanta da wannan aikin, domin littafin sun gina shi ne game da zaman mutum da sana’arsa, yayin da aikina yana bayani a kan magini (Birkila/ messin) a garin Kwatarkwashi.

            Alhassan da wasu (1982) a cikin littafinsu mai suna “Zaman Hausawa”. Marubutan sun yi ƙoƙarin kawo wasu sana’o’in Hausawa, waɗanda suka haɗa da noma da ƙira da fawa da Farauta da kiwo da saƙa da kaɗi da rini da fatauci da  sarauta da maƙamai da sauransu.

            Aikin yana da alaƙa da nawa aikin,  domin ya shafi sana’o’in Hausawa da al’adunsu. Bambancin da ke tsakanin aikin  nasu da nawa shi ne, aikina yana magana ne a kan birkila/ messin a garin Kwatarkwashi, su kuwa nasu a kan sana’o’in Hausawa gaba ɗaya.  

            East, R.M (1968) a littafinsa mai suna “Labaru na da da na yanzu”. Marubucin ya rubuta littafin a kan babuka goma.

            A babi na farko ya kawo tarihin fitattun sana’o’in Hausawa na gargajiya, tare da bayaninsu gwargwadon fahimta. Yayin da babi na biyu kuma ya bayyana wasu fitatun sana’o’in mata na gargajiya. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin  ainun ta fuskar sana’o’i da al’ada. Bambancin da ke tsakaninsu shi ne, aikina yana magana a kan “Magini (Birkila/ messin)  a garin Kwatarkwashi, da  yadda sana’ar ta taimaka wajen samar da aikin yi ga matasa da sauransu.

            Yahaya da wasu (2001) a cikin littafinsu mai suna “Darussan Hausa don manyan Makarantun Sakandare na biyu”. Marubutan sun yi magana ne a kan sana’o’in gargajiya, ma’anar ita kanta sana’ar tare da kawo sana’o’in maza da na mata da kuma na tarayya, sai dai ba su ambaci magini (Birkila/ Messin) a cikin wannan littafi ba. Amma yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar sana’o’in gargajiya, duk da haka sun bambanta  da nawa aikin domin su nasu yana magana ne a kan Hausawa baki ɗaya, yayin da nawa aikin yake bayani a kan birkila/messin a garin Kwatarkwashi.

            Shi kuwa Yakasai, (2002) a littafinsa mai suna “Mordern Comprehensiɓe Hausa Language for Schools and Colleges”. Marubucin ya yi ƙoƙari wajen tsettsefe sana’o’in gargajiya na maza da na mata, da kuma tasirin  sana’o’in ga al’umma. Babu shakka  wannan aikin yana da alaƙa makusanciya da nawa aiki. Bambancin da ke tsakanin wannan aikin da nawa shi ne, nawa aikin na magana ne a kan birkila/messin a garin Kwatarkwashi, yayin da nasa aikin ke magana kacokan a kan al’adun Hausawa.

            Bunza, (2006) kuwa a littafinsa mai suna “Gadon feɗe Al’ada”. Marubucin ya yi magana a kan sna’o’in Hausawa, musamman maƙera da ma’aska da masunta da manoma da mahauta da kuma maɗora ta fuskar tsafi ko gado, sai dai bai yi magana a kan sana’ar gini ko magini (Birkila) ba, amma aikin nasa yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar al’adu. Bambancin da ke tsakaninsa da nawa shi ne, nasa yana magana ne a kan al’adun Hausawa baki ɗaya, yayin da nawa aikin ke magana a kan magini (Birkila/ messin) a garin Kwatarkwashi.

            Gusau, G.U. (2012) a littafinsa mai suna “Bukukuwan Hausawa”. Marubucin ya yi ƙoƙari matuƙa, don kuwa ya yi magana a kan sana’o’i daban-daban tun daga kan Fatauci da noma da Farauta da gini da wanzanci/, da sauransu. Ya bayyana ma’anar gini ne kawai da ire-irensa da kuma irin sauyin da ginin ya samu tasirin zamani. Bambancin da ke tsakanin aikina da nasa shi ne, nasa aikin na magana ne kaco-kan a kan Hausawa baki ɗaya, yayin da nawa kuwa ya keɓanta a kan birkila/messin a garin Kwatarkwashi.

1.7.2 MUJALLU DA MAƘALU

            Muhammad (2016) a maƙalarsa mai taken “Gudunmuwar sana’ar  ƙira wajen samar  da kayayyakin Hausawa na gargajiya”. Wadda ya gabatar a cikin mujallar Argungu Journal of Language Studies. Marubucin ya yi bayani a kan su wane ne Hausawa da ƙasar Hausa da muhimmancinta da sauransu. Wannan maƙala tana da alaƙa da wannan aikin ta fuskar sana’a, sai dai bambancin da ke tsakanin maƙalar da  aikina shi ne, aikinsa ya taƙaita ne a kan sana’ar ƙira kawai, yayin da nawa aikin yake magana a kan birkila/messin a garin Kwatarkwashi.

            Zabi, M.A. da Aliyu (2016) a cikin maƙalarsu mai taken “Tasiri da barazanar zamani a kan sana’ar noma”, wadda suka gabatar a cikin Mujallar Argungu Journal of Language Studies. Marubutan sun yi magana ne a kan Hausawa da sana’ar noma a ƙasar Hausa, da ma’anar tattalin arziƙi da bunƙasar tattalin arziƙin Bahaushe da suaransu. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar sana’o’i da al’adu. Abin da ya bambanta tsakaninsu shi ne, aikinsu na magana ne a kan tasiri da barazanar zamani a kan sana’ar noma ne, nawa kuwa ya fi mayar da hankali ne a kan birkila/ messin.

            Maryam (2015) a maƙalarta mai taken “Sana’o’in Hausawa na gargajiya da tasirinsu a zamanance”, wadda ta gabatar a cikin mujallar garkuwar Adabin Hausa. Marubuciyar ta yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wajen fito da sana’io’in Hausawa na gargajiya kamar noma da kiwo da fatauci da ƙira da saƙa da jima da dukanci,  da sauransu. Wannan maƙalar tana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar sana’o’in Hausawa na gargajiya da al’adu, amma bambancin da ke tsakaninsu da nawa aikin shi ne: Nata aikin na magana ne a kan sana’o’in  Hausawa na gargajiya baki ɗaya, yayin da nawa aikin ya shafi Birkila/ messin.

            Gusau, (2013) a maƙalarsa mai taken “Tsokaci a kan al’adun Hausawa”,  wadda ya gabatar a cikin mujallar Harsunna Nijeriya. Marubucin ya yi ƙoƙari ainun wajen fito da al’adun a sarari kamar yadda ya yi bayani a kan al’adun al’umma, da al’adun Hausawa da kuma wuraren tanadin al’adun Hausawa. Wannan maƙalar tana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar al’adu. Abin da ya bambanta aikinsa da nawa shi ne; Nasa aikin yana magana ne a kan “Tsokaci a kan al’adun Hausawa” yayin da nawa ya keɓanta a kan birkila/messi.

1.7.3. KUNDAYEN BINCIKE

            Bunguɗu da wasu (1999) a kundinsu na takardar shaidar N.C.E mai taken “Bincike a kan sana’o’in Kaɗi da daddawa da mazanƙwaila da tukanen laka na da da na zamani a ƙasar Hausa”. Wanda aka gabatar a sashen Hausa na kwalejin ilmi ta Shehu Shagari, Sokoto. Manazartan sun yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wajen bayyana ma’anar kaɗi, kayan aikinta, yadda ake gudanar da ita. Ma’anar daddawa da yadda ake aiwatar da ita da kuma kayan aikinta. Ma’anar mazanƙwaila, yadda ake yin mazanƙwaila, kayan aikinta, yadda ake  tukanen laka na da da na zamani da kuma tasirin zamani a kan dukkan sana’o’in Hausawa da al’adunsu. Bambancin da ke tsakanin aikina da nasu shi ne, nasu yana magana ne a kan keɓaɓɓun sana’o’in ƙasar Hausa baki ɗaya, yayin  da nawa aikin yake magana a kan magini (Birkila/ messin).

            Maru, S.I. da wasu (2012) a kundin bincikensu na takardar shaidar N.C.E mai taken “Sana’o’in Daddawa a jihar Zamfara”. Manazartan  sun yi bayani a kan sana’ar Daddawa da yadda ake yinta, kayan aikinta tare da muhimmancinta. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta fagen san’a, amma bambancin da ke tsakain aikinsu da nawa shi ne, nawa yana bayani ne a kan birkila/messin (magini) a garin Kwatarkwashi.

            Mallaha da Atiku, (2014) a nasu kundin na takardar shaidar N.C.E mai taken “nazarin hanyoyin Bunƙasar mutanen yakin kwatarkwashi”. Manzartan sun yi ƙoƙari sosai wajen bayyana hanyoyin bunƙasar rayuwar mutanen ƙasar Kwatarkwashi da ma’anar tattalin arziƙi da albarkatun ƙasar Kwatarkwashi da suaransu. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta ɓangaren al’adu a Kwatarkwashi. Bambanci da ke tsakanin aikinsu da nawa shi ne, aikina yana magana ne a kan magini (Birkila/ mesin) a garin Kwatarkwashi.

            Yahuza da wasu (2019) a kundin digiri na farko mai taken “Nazarin Fitattun Al’adun Maguzawa a ƙasar Kwatarkwashi”. Wanda aka gabatar a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Mai reshe a kwalejin kimiya da ƙere-ƙere ta ‘yan mata, Gusau (F.C.E.T). Manazartan sun yi ƙoƙari matuƙa wajen fito da al’adun garin  Kwatarkwashi ƙwansu da kwarkwatarsu, da muhimmancin al’adun na maguzawan kwatarkwashi da sauran muhimman abubuwa da kundin ya ƙunsa. Tabbas, wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin ta fuskar al’adun garin Kwatarkwashi.

            Bambancin da ke tsakanin aikinsu da nawa shi ne; Nasu aikin yana magana ne a kan “Nazarin fitatun Al’adun maguzawa a ƙasar Kwatarkwashi, yayin da nawa aikin ya keɓanta a kan magini (Birkila/messin) a garin Kwatarkwashi.

1.8 NAƊEWA/ KAMMALAWA

            Wannan babi na ɗaya shi ne shimfiɗar wannan bincike, an bayyana abubuwa kamar haka: gabatarwa, wadda a cikinta ne aka bayyana babi-babin da wannan bincike ya ƙunsa da kuma abubuwan da babi-babin suka yi magana, daga babi na ɗaya har zuwa babi na biyar. Haka kuma bayan  gabatarwa, babin ya bayyana abubuwa kamar haka: Manufar bincike da dalilin bincike da farfajiyar bincike da muhimmancinsa da hanyoyin bincike da hujjar ci gaba da bincike da kuma bitar ayyukan da suka gabata.

Post a Comment

0 Comments