Ticker

6/recent/ticker-posts

Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (3)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Koyar da Harsuna da Al’adu, Tsangayar Fasaha da Ilimi, Jami’ar Tarayya, Gusau don neman digiri na farko.

Birkila/Messin A Garin Kwatarkwashi (3)

NA

HIZBULLAHI ƊANLAMI

gini

BABI NA BIYU:

TARIHI DA AL’ADUN GARIN KWATARKWASHI

2.0 Gabatarwa

            Wannan babi zai tattauna ne a kan tarihi da al’adun garin Kwatarkwashi, wanda ya ƙunshi muhimman abubuwa da suka haɗa da: Taƙaitaccen tarihin Kwatarkwashi,da tsarin gine-ginen garin Kwatarkwashi da al’adun garin Kwatarkwashi, da kuma shigowar baƙin al’adu, har ma  da tasirinsu a garin Kwatarkwashi.

2.1 TAƘAITACCEN TARIHIN KWATARKWASHI

            Kwatarkwashi gari ne mai daɗaɗɗen tarihi, asali da jaruntaka. An samu kafuwar garin Kwatarkwashi tun a cikin ƙarni na 14, kimanin shekaru ɗari shida da sha ɗaya (611) da suka wuce wato (ƙ 1400 zuwa yau). Sunan Kwatarkwashi dutse da ganuwa inda maiki ya shahara, saboda yawan duwatsun da Allah ya albarkaci wurin da su. Garin Kwatarkwashi ya yi iyaka ne da masarautar Mada daga gabas. A kudu maso gabas kuwa garin ya yi iyaka da masarautar Tsafe. Ta ɓangaren arewa kuma ya yi iyaka da masarautar Ƙaura Namoda. Har wa yau garin ya yi iyaka da Gusau babban birnin Jihar Zamfara daga Yamma.

            Kasancewar garin na kewaye da duwatsu masu ƙayatarwa, wanda ya ba garin martaba da tsaro, haka kuma baƙi masu yawon shaƙatawa da ɗaliban ilmi kan ziyarci garin domin ganar wa idanuwansu abubuwan sha’awa da mamaki.

            Sunan Kwatarkwashi ya samo asali ne daga wanda ya kafa garin na Kwatarkwashi  tun farko mai suna (Mangul) . shi wannan bawan Allah ya yo ƙaura ne daga Katsina a bisa ga sana’arsu ta harbi lokacin sarkin Katsina Kumayo. Sunan Mangul ya ɓata sakamakon kyautatawa da alherin da yakan kai wa sarkin Katsina a cikin wani baho da ake kira “kwatashi”. Bisa haka ne, sunan Sarkin Kwatarkwashi ya canja daga kwatashi zuwa Kwatarkwashi. (Babu sunan mawallafi da shekara, sai dai sunan littafin “Tarihin kafuwar garin Kwatarkwashi”)

            A cikin sana’arsu ta harbi, sun fara zama ne ƙarƙashin dutsen da ake kira “Kundun”, cikin ƙasar Katsina, wanda suka zauna har tsawon shekaru huɗu, daga baya suka yi hijira zuwa “Dungai” (Dungai na nan gabas da Kwatarkwashi cikin yankin Gulubba ta yanzu) sun yi zama na shekaru uku (3 yrs) daga nan suka isa wani wuri da ake kira “Dukura” (Dutse mai daɗaɗɗen tarihi) wurin da garin Kwatarkwashi ya ke a yanzu. A taƙaice wannan shi ne taƙaitaccen tarihin garin Kwatarkwashi.

2.2 TSARIN  GINE-GINEN GARIN KWATARKWASHI

            Tsari wani abu ne da ke da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan Adam gaba ɗayanta, tun daga fannin zamantakewarsa, iliminsa, addininsa, har ya zuwa gine-ginensa (muhalli).

            Saboda haka, tsarin gine-gine a garin Kwatarkwashi za a kalle shi ta fuska biyu. (Tattaunawa da Engr. Kabiru U. K/Kwashi) kamar haka: -

(a) Tsarin gine-ginen

(b) Yanayin rufin gine-ginen

a- Tsarin gine –ginen: Garin Kwatarkwashi gari ne wanda yake da tsari ta ɓangaren gine-ginensa tun asali, dalili kuwa maginansu na gargajiya da na zamani ƙwararri ne wajen fitar da ɗaki ko shago ko ma gida baki ɗayansa. Tun asali an gina garin da tsari irin na zamani wato (town planning) a turance. Dalilin wannan, lokacin da Gwamna Abdulaziz Yari Abubakar ya bayar da kwangilar hanyoyin (Tituna) cikin garin a shekarar 2016 ba a sami wata matsala ba sosai ta fannin roshe-roshen gine-ginen, saboda suna a kan tsari irin na zamani.

Bugu da ƙari, kusan  kowace unguwa za ka shiga haka abin yake, har zuwa sauran sabbin shiyoyi da aka samu daga bayan nan; irin su Barakallahu da kuma Nasarawa. Saboda haka, garin Kwatarkwashi  gari ne wanda ke da tsarin gine-gine na musamman. (Tattaunawa da Engr. Kabiru U.D Kotorkoshi).

b- Yanayain rufin gine-ginen: A ɓangaren rufin gine-ginen garin Kwatarkwashi na farko shi ne rufin jinka (thatch roof), wanda muka taso cikinsa kaka-da- kakanni. Rufin jinka shi ne yin  amfani da ciyawa wajen rufe ginin da aka yi a matsayin muhalli. (Soba, 2015).

            To, mutanen Kwatarkwashi kan yi amfani da wannan nau’in rufi  a can baya, amma da aka sami ci gaba sai suka koma rufin soro daga rufin Jinka. Wannan rufin na Soro al’ummar Kwatarkwashi sun daɗe suna amfani da shi har zuwa lokacin da baƙin al’ummomi suka shigo ƙasar Hausa, musamman Turawa. Daga wannan lokacin tsarin gini da yanayin rufinsa ya canja zuwa na zamani (ginin bulo da bulo na siminti).

Wannan ke nan dangane da abinda ya shafi tsarin gine-ginen garin Kwatarkwashi.

2.3 AL’ADUN GARIN KWATARKWASHI

            Kafin shiga cikin bayanin abin da wannan matashiya ke buƙata ya kamata mu san ainihin asalin ita wannan kalma ta al’ada da ma’anarta.

Kalmar Al’ada

Ainihin wannan kalma ba Bahaushiya ba ce, aro ta Hausawa suka yi daga Larabci. A luggar Larabci al’ada na nufin wani abin da aka saba yi, ko ya saba wakana, ko aka riga aka san da shi. A harshen Hausa kalmomin da suka fi kusa da kalmar al’ada su ne, kalmar “sabo” da “gado” da “hali” da “sada” da “gargajiya” (Bunza 2006). Dukkan waɗannan kalmomi suna da ma’anoni makusanta idan aka nazarce su kamar haka:

i.                    Sabo: Tana daga cikin kalmomin da Bahaushe ke amfani da  ita idan yana son ya nuna wani abu da aka saba yi irin al’adun gargajiya. Kalmar sabo takan ɗauake ma’anoni da dama idan aka kalle ta kamar haka”

(a)   Sabo Turken wawa 

(b)  Kowa ya saba  da kai gida, sai ya kai

(c)   Hannu ya iya jiki ya saba.

Waɗannan duk suna nuna cewa, sabo shi ne abin da aka saba da shi yau da gobe.

ii.                  Gado: - Kalmar gado ta fi kusanta ga abubuwan da suka shafi gado na dukiya ko hali.  A idon manazarta al’ada, a wasu lokuta takan ɗauki ma’ana irin ma’anar kalmar “al’ada”. A cikin wasu zantukan hikima na Hausawa mukan ji suna cewa: -

(a)   Kunya aka soro mutuwa ta zama gado

(b)  Gadon  gida alala ga raggo

(c)   Gado ba ya wofinta 

Waɗannan duka na nuna gado kalmar al’ada yake,  abu ne da aka tarar kaka da kakanni ka kuma ci gaba da shi yadda aka tarar da shi.

iii.               Hali: - wani abu ne da Bahaushe ke dangantawa da sababen abu.  Hali yana da makusanciyar ma’ana da “al’ada” domin a ganin wasu al’adar abu shi ne halinsa. Ga wasu karin maganganu dake shaida hakan: -

(a)    Hali zanen dutse

(b)  Mai hali ba ya barin halinsa

(c)   Halin uwa ɗiya kan ɗauka

            Babu wai, waɗannan duka suna bayyana mana cewa “hali” wata al’ada ce ta rayuwa da aka riga aka saba da ita.

iv.               Sada: A cewar Bunza (2006: ɗɗi) kalmar Sada gurbinta ɗaya da kalmomin hali, da gado, da  sabo. A lugga tana nufin abin da aka saba  yi yau da gobe kuma ba a daina  yin sa ba. Misalin wannan ya zo a wani ɗan waƙa na Alhaji Gambu Fadaga yayin da yake yin hikayar tatarniyar Tudu Tsoho da Muhammadu Inuwa Danmaɗacci. Ga shi kamar haka: -

                              “In na ga alamun ya kula min

                              In yi wurin ‘yan koli sada

                              Ina cinikin banza da yohi

                              Ko an bar min ban biya tai”

Ita ma wannan kalma ta “sada”, duk da kasancewarta mai makusanciyar ma’ana ce da al’ada.

v.                  Gargajiya:- A cewar Bunza daga kalmar “gado” ne aka sami “gadajje” da “gargajiya”. Kalmar gargajiya ta yi ƙaurin suna musamman idan aka ce gargajiyar Bahaushe da ke takin-saƙa da kyawawan aƙidojin musulunci. Nason addinin musulunci a zukatan Hausawa ya jawo wa kalmar gargajiya cikas da a yi amfani da ita ta wakilci nazarin al’ada na gaba ɗaya.

            Bisa la’akari da  ma’anoni na takwarorin wannan kalmar ta al’ada Bunza (2006: ɗɗɗii) ya bayyana ma’anar al’ada da cewa “Tana nufin dukkanin rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwarsa har zuwa ƙabarinsa. A ko’ina mutum ya sami kansa, duk wata ɗabi’a da ya tashi da ita tun farkon rayuwa ya tarar a wurin da ya rayu, ko yake rayuwa, ita ce al’adarsa da za a yi masa hukunci a kai. (Bunza, 2006).

            Yahaya, I.Y. da wasu (1992), sun bayyana ma’anar al’ada da cewa “wata hanya ce da ake yin nuni game da abubuwan da mutum ya saba yi a rayuwarsa ta yau da kullum. Sannan kuma tana bayyana yanayin rayuwar al’umma da harkokin da suke yi don zaman duniya”.

            La’akari da waɗannan ma’anonin da suka gabata a iya cewa “al’ada ita ce sabo ga abin da mutane suke aikatawa a rayuwarsu ta yau da kullum: Yanzu za a tafi zuwa ga babban bayanin al’adun garin Kwatarkwashi.

AL’ADUN GARIN KWATARKWASHI

            Al’ummar Kwatarkwashi kamar kowace al’ummace ta duniya, suna da nasu al’adu da suke bi domin gudanar da rayuwarsu. Al’adun sun taɓo lungu da saƙo na rayuwarsu, misali: akwai al’adun da suka shafi rayuwar Bahaushe, wato haihuwa d a mutuwa. Haka kuma akwai al’adu da suka shafi zamantakewa da sana’o’i da addini da bukukuwa da kuma wasanni. Akwai kuma fitattun al’adun da aka san mutanen Kwatarkwashi da su, ga su kamar haka: (Yahuza da wasu, 2019).

1-      Ɗaukar Maiki: - Maiki wata halitta ce ta tsuntsu da Allah ya yi daga cikin tsuntsaye wanda Allah ya hore mai hangen nesa. Wannan shi yasa Hausawa kan yi masa kirari da cewa “Maiki mai hangen nesa”. Dutsen Kwatarkwashi wato (Dukura)  shi ne wurin zaman wannan halitta (maiki). Kuma Allah ya albarkace su da zuri’a a wurin. Sannu a hankali har maguzwan Kwatarkwashi suka fara gasar ɗaukar waɗannan halittu domin nuna ƙwarinsu da buwayarsu ta fuskar tsafi. Don haka kusan kowace shekara a wancan zamanin akan saka rana da maguzawan ƙasar za su haɗu domin su ɗauko maiki daga saman Dukura. Sai dai an ce akan yi sadakar bakinsa, a bayar da Jinin ga dutsen domin a yi gasar a wanye lafiya. Wasu ma suna ganin cewa har da Jinin mutum ake ba su domin a hau lafiya a sauko lafiya.

2-      Wasan Baura: - Baura wata wasa ce da ake kira damben ƙarfe. Tarihi ya bayyana cewa wasar tana daga cikin muhimman al’adun gargajiya na garin Kwatarkwashi.

Ita wasan Baura gado ce, ba ta kowa da kowa ba ce. Waɗanda suka gaje ta, sai sun shirya mata ta hanyar tanadar kayan  gargajiya kamar haka: -

(a)   Wani ƙarfe da ake ɗaurawa a hannaye, agala (wanda ake rufe shi da fatar shanu)

(b)  Gato ko kuma wata ƙawa mai gashi da ake ɗaurawa a baya kuma ita ke ɗauke da duk sihirin da ke tattare da wasan Baura.

(c)   Haka kuma akwai ƙawa da ake ɗaurawa tare da gato.

(d)  Boge ko keɓe (wasu zane-zane ne domin kwalliya kurum)

3-      Kalankuwa: - Wasa ne da ake yi duk a shekara idan lokacin kaka ya yi. Ana yin wannan biki/wasa ne domin nuna murnar kaiwa ga amfanin gona. Kuma lokaci ne na kece raini don kowa ya sami amfanin gona kopwa yana jin kansa. Sarkin gari ko hakimi ko dagaci ko mai unguwa ne zai zaɓi sarkin samari, wanda shi kuma zai zaɓi mataimakansa. Wannan al’ada ta biki/ wasan kalankuwa na ɗaya daga cikin manyan-manyan al’adun garin Kwatarkwashi.

4-      Bautar kyauka: - Wata nau’in ibada (bauta) ce da mutanen ƙasar Kwatarkwashi suka yi ga wannan dodo (Kyauka) wanda tarihi ya nuna cewa Kyauka yana biyo wa ne daga cikin garin Kurah zuwa Kwatarkwashi. A wannan lokacin ne mutane kan gudanar da nau’o’in bautar (Kyauka) da kuma irin kirarin da suke yiwa dodon. Ga kirarin Dodo na Kyauka a Kwatarkwashi.

 

“Dodo maye

Dodo na ba kashi,

Kashe mutum mu tai gida,

Dodo na ba kashi,

Dodo ɗan doguwa,

Dodo na ba kashi,

Birkiɗa ba kyakya”. (Gusau, 2003)

5-      Hawan  Alagwai:- Alagwai wani dutse ne da ke cikin garin Sankalawa. A al’adance idan za a ɗaurawa budurwa aure, ‘yan mata ne kan hau dutse har  inda alagwai yake. Sukan fara hawan dutsen ta wata unguwa da ake kira “kaurar gata” daga nan sai su isa wani wuri da ake  kira “murhu” inda anan  za a gane amarya takai bante ko kuwa,  idan takai bante za a taras da murhu lafiya lau, idan kuma ba ta kai ba za a taras ya gware. Daga nan sai su ba da abinci kamar ɗan dawo da nono da aya da turare da sauransu. Kafin zuwan musulunci idan suka tinkari alagwai sukan ce “Ahuwanku dai masu nan” , amma bayan zuwan muslunci sai suce “Assalam-salam”.

Daga nan idan suka ƙare abin da suke sai su jefa masu abinci daban-daban kamar ɗan wake, tuwo, fura,, ɗan dawo, ruwa, da sauransu suna cewa:

                                                “Ga tuwanku nan ba mu ci

                                                Ga fuararku nan ba mu sha.”

Daga nan sai su tafo zuwa “tanda”da “ceɗiya” (wurare ne) inda  suke zuwa a bisa  al’ada, amma ba komai suke yi ba, hanyar saukowa ce daga alagwai. 

6-      Ɗaukar abokai: - Al’ada ce wadda samari da ‘yan mata na gari ke yi da kamar sauran bukukuwan Hausawa, kuma yana da alaɗa da kalankuwa amma  sun bambanta, domin ɗaukar abokai samari da ‘yan mata gari ne za su yi ƙungiya su yi tunanen wane gari za su gayyato domin yin abota da su domin ƙara danƙon zumunta tsakaninsu.

Daga zarar an gayyato su za su tsaya bakin gari sannan mutane su fito duk wanda ya burgeka sai ka ɗauke shi wani yakan ɗauki biyu, namiji ya ɗauki namiji macce kuma ta ɗauki mace. Kowa sai ya tafi da abokaninsa gidansu ya ba shi abinci iri-iri kamar shinkafa, tuwo,  nama da kuma lemu (coca-cola), bayan an ci abinci an gaida iyaye, sai a fita ka nuna masa wasu muhimman wurare na garin, sannan za a kwana kamar biyu ko uku ana kaɗe-kaɗe.

Daga nan su kuma, idan sun koma  gida sai su sanya ranar da kuma za ku je garinsu, da zarar mutum ya ga wanda ya ɗauke shi, shima sai ya tarbeshi ya ɗauke shi kamar yadda ya yi maka a garinsu. Waɗannann al’adu sukan kasance tsakanin garuruwan: -

-          Kurah da Sankalawa

-          Sankalawa da Riɓe d.ss

7-      Bautar Magiro: - Wata al’ada ce, wadda ta shafi bautar iskoki da al’ummar ƙasar Kwatarkwashi ke yi, musamman yankin Sankalawa da Zabaro da kuma Ƙawari. Kowane magajin waɗannan garuruwa yana da nashi magiron, kuma ana yin wannan bauta ne lokacin da za a kai amarya. Kafin a kaita gidan miji za a tafi da ita “duhu” ayi yanke-yanke, a sha giya, sannan Magiro ya shige gaba yana ruri (ƙara) har cikin ɗakin amarya suna tafiya suna waƙa suna cewa: - 

                                    “Kai Magiro ina za ka?

                                    Kai na Bakuro ina za ka?

                                    rura mu tafi

                                    rura mu gani”.

Sannan kuma, tsarin bautar Magiron kowa ya bambanta, kamar dai tsafin kan gida ko na uwar gona.

8-      Bautar Ƙunƙurutu: - Bauta ce da mutanen ƙasar Kwatarkoshi ke aiwatarwa, musamman a garin Dashi da Zabaro da kuma Sankalawa, ana yin wannan bautar ne da kaka (lokacin cire amfanin gona). A wurin bautar akan yanka baƙaƙen bunsura (namijin akuya), a kuma sha tuluwan giya, idan an tsima sannan a ɗauka iskan da ake so, daga nan sai ya hau hanya ko kuyye  ya yi ta gudu duk kuma abin da ya haɗu  da shi a wannan hanya zai mutu. Bincike ya tabbatar da cewa, idan ‘yan ƙunƙurutu suka zauna ranar suna shan giya sandunansu kan tashi tsaye su yi ta karo duk wadda aka ture ta faɗi, to mai ita ne ya faɗi zai mutu.

9-      Bautar Kurjenu: - Kurjenu sunan wani gunki ne na ƙasa na mace. Wannan wai nau’in bauta ne da al’ummar ƙasar Kwatarkwashi suka yi, musamman a garin Sankalawa. Masu wannan bauta suna yi mata yanke-yanke a duk shekara domin iskokin wannan wuri su sha  jini, kuma,  duk wanda ba ɗan gado ba, ba wanda ya isa ya matsa inda ɗakin kurjen yake, saboda iskoki daban-daban da suke tu’ammali da su. Galibi suna yanka mata baƙaƙen shanu guda bakwai (7).

Wannan shi ne bayanin al’adun garin Kwatarkwashi.

2.4 SHIGOWAR BAƘIN AL’ADU A GARIN KWATARKWASHI

            Kamar yadda aka bayyana a baya cewa, garin Kwatarkwashi gari ne daɗaɗɗe ta fuskar kafuwarsa. Saboda haka baƙin al’adu sun shigo wannan gari (Kwatarkwashi) a sanadiyar zuwan baƙin al’ummu (turawa) a ƙasar Hausa, wato a farko farkon ƙarni na ashirin a dai-dai shekara ta 1903.

            Mutanen Kwatarkwashi sun samu baƙin al’adu, waɗanda suka ɗora rayuwarsu a kai, sakamakkon shigowar baƙin al’ummu. Al’adun sun ƙunshi wasu nau’o’in halaye da ɗabi’u da nau’o’in gine-gine da nau’o’in abinci da sutura. Haka  kuma da waɗanda suka shafi huɗɗoɗin zamantakewa da na tattalin arziƙi da suka haɗa da sana’o’i da sauran hanyoyin saye da sayarwa; da kuma wasu al’adun waɗanda suka shafi addini da dangogin rayuwar Hausawa.

            A ɓangaren muhalli al’ummar kwatarkwashi a da, suna yin gine-gine ta fasahar bunu da haki da yumɓu, wanda mutane suka haɗe suna aiwatarwa shekaru aru-aru da suka shuɗe. Kamar dabi da kudandan da rufewa da rudu da sauransu. Amma shigowar waɗannan baƙin al’ummu, suka sauya zuwa na zamani.

2.5 TASIRIN BAƘIN AL’ADU A GARIN KWATARKWASHI

            Kamar yadda aka bayyana a sama  da cewa “al’ada tana nufin dukkanin rayuwar  ɗan ‘Adam tun daga haihuwarsa har zuwa ƙabarinsa. A ko’ina mutum ya samu kansa duk wata ɗabi’a da ya tashi da ita tun farkon rayuwa ya tarar a wurin da ya rayu, ko yake rayuwa , ita ce al’adarsa da za a yi masa hukunci a kai”. (Bunza, 2006).

            To idan kau haka ne, babu shakka baƙin al’adu sun yi tasiri matuƙa ga rayuwar al’ummar garin kwatarkwashi. Al’adun sun shiga lungu da saƙo na al’ummar garin (kwatarkwashi).

            Dalili kuwa, idan aka fara dubawa tun daga matakan rayuwar Bahaushe wato aure, haihuwa da mutuwa za a ga sauye-sauye da yawa, waɗanda sakamakon cuɗanyarsu da baƙin al’ummomi suka samu. Haka kuma, tasirinsu ya canja tsarin sufurin mutanen garin, wanda a da mutanen kwatarkwashi na yin zirga-zirga a kan raƙuma da jakuna da alfadarai. Wasu kuma a ƙafa. Amma cuɗanya da baƙi ya haifar da samuwar wasu hanyoyi domin sauƙaƙa sufuri. Kamar irinsu mota, mashin, keke, jirgin  ruwa, da na sama. Waɗannan ababe duk sun  yi tasiri ga rayuwar mutanen garin kwatarkwashi da ma al’ummar Hausawa.

            Haka ma, a sashen gine-gine baƙin al’adu sun yi tasiri ainun ga mutanen kwatarkwashi, wajen sauya tsarin fasalin muhalli tun daga kan gini har zuwa kayan aikin ginin da shi kansa maginin (Birkila), da sauran abubuwa da dama da baƙin al’adu suka yi tasiri da su ga rayuwar mutanen garin kwatarkwashi.

2.6 Naɗewa

            A cikin wannan babi an tattauna game da taƙaitaccen tarihin garin kwatarkwashi da kuma tsarin gine-ginen garin kwatarkwashi da kuma irin al’adun da ake gudanarwa a garin kwatarkwashi, haka kuma an bayyana shigowar baƙin al’adun da kuma irin tasirin baƙin  al’adun ga rayuwar mutanen kwatarkwashi.

Post a Comment

0 Comments