Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Kishi A Cikin Finafinan Hausa

Fim shi ne bayyana rayuwar al’umma cikin fasaha a aikace, ta hanyar ɗauka da na’urori masu naɗar sautuka da hotuna masu motsi domin nuna wa al’umma don faɗakarwa.

finafinai

Nazarin Kishi A Cikin Finafinan Hausa

Ibrahim Baba

(Masters in View), Department of Nigerian Languages, Bauchi State Uniɓersity, Gaɗau.

07066366586, 08125351694

ibrahimba182@gmail.com

 

And

Hafsat Muhammad

School of Educational Serɓices, Aminu Saleh College of Education Azare

08062514117

hafsatmuhammad189@gmail.com

 

And

Audu Baba

M.A Hausa (Culture) Student, Bayero Uniɓersity Kano

1.0 Gabatarwa

      Ayyukan Adabi na Hausa cike suke da bayyana halayya na jama’a iri-iri; sawa’un waɗannan halayyar kyawawa ne ko kuwa akasinsu. A cikin ayyukan Adabin da suka fi mayar da kai a yanzu wajen bayyana hoton rayuwar al’ummar Hausawa akwai finafinai na Hausa. Masu rubutawa da tsarawa gami da shirya finafinan Hausa sun mayar da hankali matuƙa kana bin day a shafi zamantakewar al’umma, musamman abin da ya shafi rayuwar soyayya tsakanin matasa da ‘yan mata, da kuma rayuwar auratayya tsakanin ma’aurata, yadda zaman yake da kuma saɓanin da ka iya ɓullowa a sakamakon wani abu. Har wa yau, finafinan sukan ƙunshi sauran sassan rayuwar al’umma ta ɓangarori daban-daban. A wannan takarda, an duba halayyar mutane, musamman mata ta fuskar nuna kishi a cikin finafinan Hausa. Kishi wata halitta ce ta zahiri da ba ganinta ake a da idanuwa ba wadda Allah ke halittar bayinSa damɓare a zukatansu, shin wannan kishin mai kyau ne ko akasin haka. Maza da mata suna tattare da wannan ɗabi’a ta kishi; gwargwadon yadda abin yake a zukatansu da kuma yadda suke sarrafa shi. Wannan nazari ya gudana ta hanyar kallon finafinai guda goma sha biyu cikin ɗimbin finafinan da aka shirya waɗanda suka shafi kishi, dubi da yanayin lokaci. Tsakuro finafinai guda goma sha biyu kacal kuwa, ya faru ne sakamakon taƙaita lokaci da bayani. An samo waɗannan finafinai ta hanyar tattarowa da kuma ziyartar shagunan sayar da finafinan Hausa, da wuraren masu turawa a wayoyi, da tuntuɓar wasu cikin masu shirya finafinan Hausa.

1.1 Ma'anar Fim

      Fim shi ne bayyana rayuwar al’umma cikin fasaha a aikace, ta hanyar ɗauka da na’urori masu naɗar sautuka da hotuna masu motsi domin nuna wa al’umma don faɗakarwa. A wata ma’ana kuwa, za mu iya cewa, “Fim wata keɓantacciyar hanya ce da wasu masu hikima suke amfani da ita a aikace domin nuna hoton rayuwar al’umma mai kyau ko maras kyau, da nufin hannunka mai sanda ko gyara ga wanda ya ji ko ya ga wannan fim ɗin”. Shi kuwa 'Yar'aduwa (2007:30) ya yi na shi ta'arifin da cewa, "Fim wata hikima ce ta hoto mai motsi da take ɗauke da mutane, wato hotunansu maza da mata, yara ko manya, ko kuma ma wanin mutane, wanda aka ɗauka ta hanyar yin amfani da na'urar ɗaukar hoto ta musamman, tare da bai wa mutane damar tafiyar da wasu ayyuka ta fuskar kwaikwayo ko wanin sa, a wani ɗan lokaci da aka keɓe wanda shi yake ɗauke da wani saƙo na musamman kan nishaɗi da gargaɗi da wa'azi da soyayya da tarihi ko wanin haka, zuwa ga al'ummar duniya".

      Idan muka yi la'akari da waɗannan ma'anoni guda uku, za mu iya kallon ma'anar fim a taƙaice da cewa, wata keɓantacciyar hanya ce tsararriya ta sarrafa hikima da fasaha a aikace; wanda ake amfani da na'urar ɗaukar hoto mai motsi da sautuka, domin isar da wani saƙo na musamman ga al'umma, ta hanyar zayyano matsaloli da hanyoyin magance su ko uƙubar wanda ya munana.

1.2 Ra’in Bincike

      Hausawa kan cewa, “Kowane allazi da nasa amanu”, kamar haka abin yake ga kowane bincike na ilimi da nasa ra’in, wanda zai zama shi ne maɗosar wannan bincike, sannan ya zama abin karɓuwa ga masana manya da ƙanana. Bisa haka, wannan bincike an ɗora shi a kan Ra’in Nason Adabi a Al’adu (Folk-Cultural Theory) wanda William Bascom ya zama ɗaya cikin manyan mabiyanta, sannan ya yi rubuce-rubuce a ƙarƙashin wannan mazhaba. Daga bayan sa, an samu masana irinsu Robert Gorges, M. O. Jones, Daniel Crowley da sauransu.

      Wannan mazhaba ta mayar ta hankali wajen daidaita hikima ta isar da ma’ana ko ƙaramin saƙo ko harshen magana da ayyuka na gyara rayuwar al’umma ta yau da kullum. Haka kuma mazhabar tana biyar sawun yadda al’umma take ƙoƙarin bayyana abin da ya shafe ta. Asalin wannan mazhaba ya faro ne ta kallon yadda hikima da sauran dabaru na fasahar baka suka danganci abubuwan da al’umma take gudanarwa. A yau, ayyukan mazhabar ba su tsaya a haka ba, an shigar da fasahar zamani ta amfani da na’urorin kwamfuta ajen alaƙanta maganganun adabi da al’adu, musamman a Amurka. A Amurka an fi amfani da wannan ra’I wajen nazarin al’adu na Hip-Hop da rawar disco da rawa ta masu tsiraici da al’adun da ake shirya finafinai a kansu (finafinan Hollywood, Bollywood, Nollywood da Kannywood) da sauransu. (Gusau, 2015:49-50).

1.3 Dabarun Gudanar Da Bincike

      Wannan bincike, ya gudana ta hanyar ginshiƙin hanya ta tattara bayanai, wato bayanan da suka wakana a faya-fayen bidiyo, bayan an kalla aka kuma naƙalto ɓangarorin da ake buƙata domin gudanar da aiki a kai.

2.0 Asalin Samuwar Finafinan Hausa

      'Yar'aduwa (2007:30) ya bayyana samuwar fina-finan Hausa, abu ne da ya faru a ƙarshen ƙarni na ashirin (20). Amma farkon abin da ya ɗora tubalin samuwar sa shi ne wasan kwaikwayo. Kuma shi kan sa wasan kwaikwayo ya samu ne bayan Turawa mulkin mallaka sun kafu, kuma har sun yi nisa wajen shimfiɗa tsare-tsare da suka shafi ilimi da tsarin mulki da sarauta.

      Binta (2008:11-16) ta bayyana tarihin samuwar fina-finan Hausa dubi da nazarce-nazarce daga mawallafe-wallafen masana, misali Bargery (1934), Chamo (2005:36), Inuwa (2009) da Garba (2009), inda yawancinsu bakunansu sun daidaita da na juna ta fuskar asalin fina-finan Hausa. Misali, majigi hoton farko da Hausawa suka fara cin karo da shi kafin sauran hotuna da ake nunawa. An fara nuna majigi ta hanyar sanya allon kallo a saman mota.

      Binta (2008:15-16), bayan tattara bayanan masanan da ta yi game da samuwar fina-finan Hausa, sai ta nuna cewa, a cikin shekarar 1998 ne masu shirya finafinai suka yunƙuro suka kafa ƙungiya ta masu wannan harkar domin su yi magana da murya ɗaya. Tun daga wannan lokaci sana 'ar shirya fim ta bunƙasa, kuma ga shi ƙofar shiga wannan sana'ar a buɗe take, sai aka dinga tururuwa cikin ta maza da mata, saboda amfanin da ake ganin masu wannan sana'a sun fara samu. Gaskiya ne, wannan sana'a ta samar wa matasa da dama aiki, maza da mata sun zama 'yan wasa da masu shiryawa da masu ba da umarni da masu ɗaukan nauyi, masu waƙoƙi da masu kwalliya da masu ɗaukan hoto da 'yan kasuwa da sauransu. Wannan sana'a ta haɗa mutane iri-iri, kuma kowa yana da tasa wadda ta shigo da shi wannan sana'a. Da wannan sana'a suka yi mata rajista suka sa mata suna Kannywood Industry (wato masana’antar shirya finafinai ta Hausa). A ƙarƙashin wannan masana’anta akwai kamfanoni da suke shirya fina-finai kuma cibiyar wannan ƙungiya Kano. Kamfanoni sun haɗa da Kaduna, Abuja, Sakkwato, Maiduguri da sauran wurare.

2.1 Ma'anar Kishi

      Masana da dama da masu nazari sun bayyana ma'anar kishi a cikin kundayensu. Misali, Rabi (1998) a cikin Binta (2009:92) ta bayyana cewa "Kishi wani hali ne da mutum yake tsananin son abu ba tare da tarayya da wani ba".

      Garba (1998:334) ya kawo ma'anar kishi da cewa, "Kishi cikin jikin mutum yake, sai dai kuma mata sun fi nuna shi da aiwatar da shi. Mata na da hanyoyin nuna kishi kanar ta magana, da habaici da karin magana da lugude da waƙa, ko ta shanti ko ta niƙa ko zungurar wani abu inda kishiya take, yadda za ta farga da ita ake, ko wata shewa, ko dai wani abu makamancin waɗannan".

2.2 Rabe-raben Kishi

      Masana sun bayyana kishi kan iya zama kyakkyawa ko mummuna, kuma dukkansu ana iya gane su ta irin yanayin da aka bayyanar da su.

      Binta (2009:94 – 118) ta yi bayani game da rabe-raben kishi, inda ta kasafta su zuwa gida uku, kuma kowane ta yi bayani da buga misalai gwargwadon iko. A dunƙule, ga yadda ta kasafta su:

2.2.1 Kishi tsakanin kishiyoyi, wato irin kishin dake tsakanin matan mutum guda. Irin wannan kishin ya faru a fina-finai da dama kamar Rikicin Cikin Gida (2018) na kamfanin Ɗan Hajiya Film Production Kano.

2.2.2 Kishin uwar miji, irin kishin da uwar miji ke yi ga matar ɗanta. Irin wannan kishi ya faru a fim ɗin Uwar Miji da sauransu.

2.2.3 Kishin faccala, wato irin kishin dake tsakanin matan wa da ƙani a junan su.Irin wannan kishin ya faru a fim ɗin Ƙawayen Amarya (2018) na kamfanin 2 Effect Empires Kano.

3.0 Kishi A Fina-finan Hausa

      A rayuwar zahiri, kishi kan sanya mata aikata abubuwa daban-daban na halaka wanda a ƙarshe yake zama sababin jefa rayuwar kishiyoyi ko mazajensu ko kuma su ɗin a karan kansu cikin mawuyacin hali. Idan aka leƙa ga fina-finan Hausa ma za a iske cike suke da fina-finai masu ɗauke da irin waɗannan halaye na kishi tsakanin mata. A nan, za a kawo wasu fina-finai da kishi ya bayyana ƙarara da kuma irin abin da mace take aikatawa a sakamakon wannan kishi, sawa'un a kan kishiyarta ce, ko 'ya'yan kishiya, ko maigida ko kuma wani cikin dangin miji, musamman mahaifiyar miji.

3.1 Kishi kan sa mace ta kashe kishiyarta

      A cikin fim ɗin Akushi (2018) na kamfanin Oscar International an ga yadda Lami ta hallaka kishiyarta ta hanyar amfani da magani. Lami wadda suke auren Malam tare da kishiyarta, ta rasa haihuwa wanda kishi ya hana ta nutsuwa, a ƙarshe kuma ta halaka ta.

3.2 Kishi kan sa mace ta yi wa kishiyarya asiri, ta shiga duniya

      A cikin fim ɗin Matar Uba (2018) na kamfanin Halifa Abubakar Inɓestment Nigeria Limited, ya zo da irin wannan kishin, a inda aka bayyana:

Malam: Ai ni ma ba cewa na yi zai rabu da ita ba, ita za ta rabu da shi, za mu kore ta ta bar gidan ta shiga duniya har abada ba wanda zai ƙara jin labarin inda take, kuma har abada ba za ta dawo ba.

Asabe: To ai ni Malam a daidai na, ai in wannan ita kenan sharaɗin, na amince. Mata ta shige min rayuwa, haka kawai ta same ni da mijina ta raba ni da shi.

      A nan, mun ji yadda aka yi, kuma ƙarshe hakan ta faru, inda ta yi asirin da ya sanya Mariya ta shiga duniya, ba a ƙara ganin ta ba sai labarin mutuwarta aka ji.

3.3 Kishi kan sa mace ta kashe uwar mijinta

      Kamar yadda aka sani, kishi kan sanya mace kisan uwar miji. Ya zo a cikin fim ɗin Dalal (2018) na kamfanin A. Y. I Uniɓersal Motion Pictures Kano inda hakan ta faru. Hafsat matar Jamil ta haɗa kai da mahaifiyarta da ƙanin mahaifiyar Jamil, wato Alhaji Bala domin ganin bayan mahaifiyar Jamil ɗin. Mahaifiyar Jamil ta sanya ya ƙara aure sakamakon rashin mutunci da tsatsube-tsatsuben da Hafsat da mahaifiyarta Hajiya Mama suke yi don ganin sun mallake shi. Haka kuwa aka yi, amma bayan ya yi auren sai da suka rinƙa asirai, ƙarshe sai da kishi ya sanya ta kashe uwar Jamil ɗin da goyon bayan Hajiya Mama da Alhaji Bala.

3.4 Kishi kan sa mace ta kira danginta/ƙawayenta domin dukan kishiyarta

      Hafsat ta aikata irin wannan a cikin fim ɗin Dalal (2018), bayan Mijinta Jamil ya ƙara aure. Ga yadda suka yi:

Ƙawa 1: Ai ni haushinki nake ji, ya za a yi a ce kina zaune duk kishin kin nan wai har mijinki ya yi aure ya shigar da amaryar gida kina zaune a falo ba ki ɗauki wani mataki ba, kin ban kunya wallahi.

Hafsat: To ya zan yi? Ai ba kwa nan ne, ko ba gaskiya ba?

Ƙawa 1: To ai yanzu ga mu mun zo.

Ƙawa 2: Ai wannan cin mutunci ne da cin amana.

Hafsat: Ai dama na sani, daman jira nake ku zo mu afka musu.........

Ƙawa 3: Ai ga mu mun zo, sai ki tashi yanzu mu afka musu.

Hafsat: Abin da nake ao, kirawo min su Falmata, kafin su zo mu je mu afka musu, duk abin da ta tafasa ta ƙone.

      Haka kuwa aka yi, domin daga nan sai suka nufi ɗakin Amaryar inda suka rufe ta da duka bayan ta fito daga ɗakin.

3.5 Kishi kan sanya mace ta daina yi wa mijinta biyayya da kyautatawa

      Fim ɗin Lubna (2018) na kamfanin Ƙalarawi Enterprises ya nuna hakan, yayin da Ibrahim ke zaune lafiya da matarsa, amma sakamakon ya nuna mata zai ƙara aure sai da kishin ta ya bayyana, har ta canja masa a yanayin mu'amala da kyautatawa.

Ibrahim: Tun lokacin da na ce zan ƙara aure shi kenan kika bi kika canja.

Mata: Me ka gani? Ni ba komai.

Ibrahim: A'a da komai, walwala ta canja, clearing ya canja, akwai abubuwa da yawa da kike min a gidan nan kin daina su. Kai amma kina da zafin kishi!

Mata: Ai kishi dole ne, duk macen da ka ga ba ta da kishi to wallahi ba ta son mijinta. Amma kishi ya zama dole, abin da kake so dole ka yi kishi..

      A nan, mun ga yadda kishi ya janyo ta daina kyautata wa mijinta, walwala ta sauya, ladabi ya sauyu.

      A fim ɗin Matar Mijina (2018) na kamfanin Al-Rahuz Film Production Kano, an ga yadda Jalila ta sauya mu'amalarta da mijinta a sanadiyyar ya ce zai ƙara aure, inda suna zaune cikin zaman lafiya da walwala, amma da ya zo da maganar aure sai matsala ta nemi kunnowa.

Adam: Ya za ki ji idan aka ce miki zan ƙara aure? (Bayan abin da ya bayyana a fuskarta na damuwa da kiɗimewa). Ya ya na ga duk jikinki ya yi sanyi?

Jalila: Ka ga duk zaman lafiyar da muke, ka ga duk ƙaunar junan dake tsakan na da kai, da zarar ka ƙara aure za ka neme su ka rasa.

Adam: Ban gane me kike nufi ba!

Jalila: Ina nufin zan buɗe wani sashi na daga Jahannama! Wallahi da faɗuwar gaba za ka rinƙa shigowa gidanka.

      Wannan ya nuna a baya suna zaman lafiya, amma sakamakon maganar ƙarin aure da ya yi mata, sai ta furta waɗannan kalamai.

3.6 Kishi kan sa kishiyoyi rikici a cikin gidansu, su rinƙa faɗa a junansu

      Fim ɗin Rikicin Cikin Gida (2018) na kamfanin Ɗan Hajiya Film Production ya nuna irin wannan kishi, inda A'isha da Maryam waɗanda matan Sadiƙ ne suke faɗa a junansu a koyaushe.

      Bayan Maryam ta ɗebo ruwa ta watsa wa A'isha wadda ke kwance a kan doguwar kujera a falo, sai A'ishan ta miƙe tsaye.

A'isha: Ni kika watsa wa ruwa?

Maryam: An watsa miki.

A'isha: Lalle kin yi kuskure, wallahi sai kin yi nadamar abin da kika aikata a jikinki.

Maryam: Ke da Allah dakata! Wacce take faɗa a baki ba za ta iya aikatawa ba, ke kin san tsohuwar kuka ta wuci runguma wallahi sai dai sara.

A'isha: Haka kika ce?

Maryam: Ƙwarai kuwa.

      Sai A'isha ta ɗauki kwalba ta kwaɗa wa Maryam a ka, nan take faɗa ya kaure a tsakaninsu. A taƙaice dai, kishi kan sanya irin wannan faɗa a kowanne lokaci, ta yadda ba wani sauran zaman lafiya a gidan.

3.7 Kishi kan sa mace ta rinƙa yi wa mijinta rashin kunya, ƙarshe ma ta iya lalata auren ta

      Irin wannan al'amari ya faru a fim ɗin Mubeenah (2017) na kamfanin Mai Shadda Inɓestment, inda Mubeenah ta ɗauki aniyar cin zarafin mijinta a yayin da ya zo mata da maganar ƙarin aure.

Adnan: Bai kamata 'ya'yanmu su gane cewa akwai wata matsala tsakaninmu ba, ko kaɗan ba ni da niyyar na cutar da ke ko na wulaƙanta ki, ba wai na yi shi da niyya ba ne.

Mubeenah: Dan Allah ka dakata min! Kana so ka ce min yarinyar ce ta janyo ka ta ce lalle sai ka aure ta? Kana so ka ce min ba ka taɓa furta mata kana son ta ba kenan?

Adnan: Ni fa ban ce haka ba, amma ina so ki fahimce ni, kuma ina so ki yi min kyakkyawan zato.

Mubeenah: Ka ga dan Allah ka yi haƙuri kar ka min wata lakca ba abin da za ka faɗa min na fahimta. Don haka ka je ka yi duk abin da ka ga dama, amma ina so ka sani, ni ban isa na hana ka abin da ka ga dama ba, amma idan ka yi kuskuren yin aure, wallahi tallahi za ka yi nadama, za ka ga kuma abin da zai biyo baya.

      Haka al'amarin ya faru, domin bayan auren ta yi ta fitina har sai da ta kai ta lalata rayuwar auren ta hanyar saki suka rabu.

3.8 Kishi kan sanya kishiya ta kira kishiyarta da karuwa

      Fim ɗin Rikicin Cikin Gida (2018) na kamfanin Ɗan Hajiya Film Production ya zo da hakan, wato yayin da Maryam ta gyara falo a ranar girkinta, sai A'isha ta zo ta kwanta.

Maryam: To tsohuwar kilaki! Sai ki tashi ki fita daga falon nan saboda yau ba ke kika gyara falon ba, ballantana ki zo ki wani kwanta ki baje, sai ki bari lokacin da kika yi sai ki zo ki kwanta.

3.9 Kishi kan sanya mace ta rinƙa zargin mijinta

      Ya zo a cikin fim ɗin Halin Kishi (2008) na kamfanin Global Time Moɓies yayin da Abdallah ya yi yunƙurin ƙarin aure, sai kishi ya sanya matarsa Zainab ta rinƙa zarginsa da fasiƙanci. A gefe guda kuma ta rinƙa yin barazanar kisa ga Zara'u (Budurwar mijinta) matuƙar ba ta rabu da mijin nata ba.

3.10 Kishi kan sanya mace ta rinƙa yi wa kishiyarta ƙage da sharri a gaban mijinsu

       Irin wannan, ya faru fim ɗin Matar Uba (2018) na kamfanin Halifa Abubakar Inɓestment Nigeria Limited, inda Malam Nasidi ya zauna yana jimamain rashin sanin inda Mariya ta shiga, sai Asabe take mata ƙage.

Malam Nasidi: Yau fa kwana uku ba mu ga Mariya ba, ba mu san halin da take ciki ba har yanzu.

Asabe: Kai kake ta da hankalinka, ni fa ina ganin Mariya gajiya ta yi da zaman gidan nan, tana so ta ga duniya, duniya ta ganta ta gogu, ta buɗe ido, idonta ya yi tar a duniya.

Malam Nasidi: Dakata, Mariya ba za ta yi haka ba, na san ta sarai.

Asabe: Ba a shaidar mutum, mutum ai shege ne, Malam mutum shege ne........

      A nan, duk da Mariya ba ta nan, ta ma ɓata, amma sai ga shi kishi ya sanya Asabe aibantata; ta hanyar yi mata ƙage.

3.11 Kishi kan sanya kishiya ta rinƙa azabtar da 'yar kishiyarta

      Sanin kowa ne, kishi kan haddasa ƙiyayya da gaba da kuma tsana. Haka zalika, kishi kan sanya mace ta rinƙa azabtar da ‘ya’yan kishiyarta. A cikin fim ɗin Matar Uba (2018) na kamfanin Halifa Abubakar Inɓestment, an ga yadda Asabe ta rinƙa azabtar da Amira 'yar gidan Mariya; bayan ta yi wa Mariya ɗin asiri. Ta rinƙa ɗaura mata talla, kuma idan ba ta sayar ba ta rinƙa jibgar ta, ba isasshen abinci, ba barci wadatacce, wanda a ƙarshe sai da K.B saurayinta ya yi sanadiyyar tafiyar ta bariki.

3.12 Kishi kan sanya kishiya ta kashe mijinta

      Fim ɗin Mariya (2018) na kamfanin Mai Shadda Inɓestment Limited an ga yadda hakan ta faru. Mariya, wadda aka yi mata auren dole da Sarkin Fawa Malam Sada ba tare da tana son sa ba. Shi kuma ya kasance mai auri saki ne, sannan yana da 'ya'ya. A haka aka yi auren, wanda bayan yin sa Mariya ba ta ba da kai ga Malam Sada ba.

      Wata rana ta aika a sayo mata maganin ɓera domin ta zuba masa a abinci ya ci ya mutu, a dalilin ba ta son shi sai bayan ta zuba, tausayi, da imani ya zo mata, sai ta ɗauka ta je za ta zubar. Ashe duk abin da yake faruwa a idanun Talatu (uwargidan Malam Sada) ake yi, inda ita kuma tuni ta faɗa kogon kishi da Mariya. Ganin Mariya za ta zubar da wannan abinci mai guba, sai ta zo ta karɓe abincin ta aika masa; alhali ta san da guba a ciki. Malam Sada bayan ya ci abincin, cikinsa ya murɗe har ya mutu, sai Talatu ta koma tana cewa ai Mariya ce ta kashe shi. Bayan Shari’a ta yi zurfi, gaskiya ta bayyana cewa Talatu ce ta kashe shi saboda kishi.

3.13 Kishi kan sanya mace ta rinƙa haukar ƙarya

      Mace takan yi haukar ƙarya da da'awar aljanu sun kama ta yayin da mijinta ya nemi ƙarin aure. Ya zo a fim ɗin Hawainiya (2014) inda Jamila ta rinƙa haukar ƙarya yayin da mijinta Shu'aibu ya zo mata da batun ƙarin aure.

3.14 Kishi kan sanya mace ta rinƙa tozarta mijinta da yi masa gori

      Ya zo a fim ɗin Mu Zuba Mu Gani (2018) inda Sakina ta fara goranta wa mijinta Ahmad jarin da ta ba shi a dalilin ya zo ƙara aure. Bayan ta same shi a falo yana shirye-shiryen fita ɗaurin aurensa kamar yadda aka gaya mata, sai ya yi ta ƙoƙarin nuna mata ba wurin kowa zai je ba, ƙarshe ta nemi mintuna biyu a wurinsa. Bayan ta juya za ta shiga ɗakin girki, sai ya ce:

Ahmad: Wayyo uwargidana.....

Sakina: (Ta juyo da mamaki a fuskarta) Uwargida kuma?

Ahmad: Kuma Amaryata, ki bari na ƙarasa zance, ke an fara magana ba a ƙarasa ba sai ki shigo.

      Bayan ta tafi zuwa kicin, ta dawo hannunta a baya, ta nufo shi, sanna ta nemi ya rufe idanuwansa, sannan ta watsa matsa manja a babbar rigarsa. Daga cikin maganganun da suka yi akwai:

Ahmad: Ban gane ba, ya aka yi na yaudare ki? Me kike nufi da haka?

Sakina: Kar ka yi tsammanin Allah bai toni asirinka ba, duk abin da kake Allah ya tona asirinka na sani. Wato an ɗaura auren ka yau kana sauri za ka tafi wajen dinner. To bari na faɗa maka, wallahi tallahi ba za ka cuce ni ka ce na ba ka kuɗi mu yi kasuwanci ka je ka yi aure da shi ba.

      Haka dai rikici ya ɓalle tsakaninsu, har bayan an yi auren ta ci gaba da goranta masa wannan kuɗi, ta hana amaryar zuwa wurinsa. Dukkanin tashe-tashen hankulan da suka faru, sun faru ne a dalilin ƙarin auren da ya yi, wanda kishi ya jagoranci aikata komai.

4.0 Abin Da Bincike Ya Gano

      A cikin takardar, an gano yadda masu shirya finafinan Hausa suka mayar da hankali wajen shirya finafinai masu alaƙa da kishi, sannan kuma aka gano yadda kishin ke gudana. Har wa yau, binciken ya gano zurfin kishi na ‘ya’ya mata da yadda suke ƙoƙarin bayyana shi a aikace. Har wa yau, an nuna yadda mata ke ƙyamatar kishiya ta hanyar nuna baƙin kishi. Takardar, ta hakaito yadda mace kan sauyawa ga mijinita a dalilin ya yi niyyar ƙarin aure, da kuma yadda suke nufatar mummunan ƙudiri a yayin da aka yi musu kishiya. Takardar ta nuna yadda zahirin kishi yake a tsakanin al’ummar Hausawa wanda finafinai mabambanta suka yi hasashe.

      A cikin takardar, an gano halin da mummunan kishi ke jefa kishiyoyi da mazajensu da kuma ‘ya’yan kishiyoyin, sannan kuma ta bayyana sakamakon da ake samu a dalilin aiwatar da mummunan kishi ga wadda ta kasance ta aikata.

5.0       Kammalawa

      Bayan tattaro bayanai da aka yi yayin buɗe wannan takarda, waɗanda suka haɗa da ma'anar fim da samuwarsa, sannan aka yi bayani dangane da kishi da yadda yake aukuwa. A cikin takardar, an bayyana sababin faruwar kishi a tsakanin al'umma, inda aka karkatar da bayanin kishin dake tsakanin kishiyoyi, wato matan da suke auren mutum ɗaya. Har wa yau, a cikin takardar, an ga yadda kishi yake a cikin fina-finan Hausa, ta yadda aka ciro misalan a cikin fina-finai daban-daban wanda yawan su ya kai goma sha biyu, sannan aka ga irin illar da ke bayuwa ga mazajen da matansu ke aiwatar da mummunan kishi, da waɗanda ake aikawatar, da kuma sakamakon da ke komawa kan masu aikatawar. Takardar ta ƙarƙare da bayanin abin da bincike ya gano a tattare da kishi da kuma tabbacin samuwar finafinan Hausa masu alaƙa da kishi. 

 

Manazarta

Tuntuɓi masu takarda.

Post a Comment

0 Comments