Wannan waƙa ta taɓo wasu ci gaba da Harshen Hausa ya samu wanda ya sa harshen ɗaukakuwa sama da tsaransa.
Amshi: Harshen
Hausa ya yi fice,
Ya rufe ƙofa ko
ta ina.
Da sunan Allah
mai girma shi ke iko ko a ina,
Ka ƙara
basira a ƙwaƙwalwa
tawa da ke a cikin kaina,
Na tsaro zance
ra-ra-ra da babu kure ciki ko sauna,
A kanta fasahar
‘yan Hausa da ta rufe Æ™ofa ko ta ina.
Ninka salati ga
rasulu manzo mai ƙarshen girma,
Muhammadu ɗan Abdullahi mai ƙima
mai alfarma,
Har da iyalai
na gidansa da sahabu mazaje sha-fama,
Da sauran masu
biyar sunna a faÉ—in
dunya ko ta ina.
Wani ya ji ina
ta zubar zance a kanta fasahar ‘yan Hausa,
Na ce dukka a
tsaranta ta fi gaban kanwar lasa,
Sai ko ya ce
‘yar Hausar ce ta zamto gagara gun gasa?
Na ce masa
tabbas kuwa Hausa ta rufe ƙofa ko ta ina.
Na ce mar ba na
maganata sai fa da hujja mai ƙarfi,
Zauna sannan
saurara in ba ka bayani don zai fi,
Idan da abokai
ka kira su ku ji ni a tare ba laifi,
A ƙarshen
zancena tabbas ku gane ficenta ko ta ina.
Da fari a
harsunnan dunya Hausa tana a sahun farko,
A jerin dukkan
harsuna gurbin sha É—aya
taÉ— É—auko,
It ace ta É—aya a sahu na gaba idan a
Afirka ka sauko,
A Afirka ƙwarai
kuwa ta yi fice, ta rufe ƙofa ko ta ina.
Harshen fari
yawan jama’a shi ne Madarin birnin Sin,
Hausawa a ƙiyasinsu
miliyan É—ari da daÉ—in hamsin,
A baƙar
fata ba mai wannan sai ita É—ai
Hausar yasin,
Ko a fagen
adadin jama’a ta rufe Æ™ofa ko ta ina.
Suna gaba gun
wasan dambe ko kuma filin kokawa,
Sun san kan
wasa da maciji har kura su yi É—aurewa,
Ko a fagen
wasan tauri sun rufe ƙofa ko ta ina.
A fannin sana’a
sun yi fice tun tarihi can baya,
Saƙa,
fawa, dukanci, gyartai ke fafan ƙwarya,
Noma, ƙira,
wanzanci Hausawa ba sa baya,
Har a fagen su
ko a sakai sun rufe ƙofa ko ta ina.
Fage na gini
tun can baya Hausawa sun yo suna,
Ganuwa su ke
tsara ta su nemi tsari gun ‘yan É“arna,
Leƙa
ginin fadojinmu ka gane akwai manyan magina,
A Afirka karan
kaf Hausawa mun rufe ƙofa ko ta ina.
Tsari na gida a
gina a shiga Afirka a da ba tamkar mu,
Rumbu gefe ga
madafi can ga bayi sai dai mu,
Can zaurukka
can bishiya nan É—akunnan
matanmu,
Zaman gandu ma
mun yi fice mun rufe ƙofa ko ta ina.
In ko abinci ka
so magana mu ne ja-gaba gun tafiya,
Ganyaye, saiwa,
tsaba, duk na nan kaya-kaya,
Nama, kifaye
nan ma ana yin kiwo ko a saya,
Nau’i-nau’i na
abinci mun rufe ƙofa ko ta ina.
Mu leƙa adab
fannin waƙa
Hausa take farko a gaba,
Yawan kasafi na
mawaƙa
don ba ay yi ya harshen Hausar ba,
Aji da aji na
mawaƙa
duk ba ai yi kamar mu a tsari ba,
A wannan fannin
Hausawa mun rufe ƙofa ko ta ina.
Akwai na maza
ga nan sha’awa sai sana’a ku yi jerawa,
Muna da na
talla da barkwanci ko aiki aka aikawa,
Daɓe da daka da kaɗi da niƙa da
sauran aiki ko a ina.
Ana ko karantar
shi harshen a nan ƙasa da wajen Hausa,
Ingila, China
da Amurka wassu suna yi a Faransa,
Yawan adadin
farfesoshi da daktocinmu a fanninsa-
Ya sa ni nake
ta bugan ƙirji
da nuna ficenmu ta ko ta ina.
Ana digiri kan
ita Hausa FUGUS da UDUS ka ji zancena,
ABU ga BUK,
KASSU da BASUG duk su na,
Akwai UNIMAID
ga UMYUK can har da SLUK a hasashena,
Ana yi har can
FUK ta rufe ƙofa
ko ta ina.
Ka ga ana Hausa
a FULAB har da su FUDMA can su ma,
Ga FUG, GSU su
ma sun ce ba dama,
NSUK, YSU, YMSU
a Kano ma,
Fannin nazari
da karatu mun rufe ƙofa ko ta ina.
Haƙiƙa
bayan ita Hausa ba mu da harshe mai wannan-
Yawan masana da
na É—alibbai babu
kamarta a ƙasar
nan,
Yawan
littaffai, kundaye ba ta da tamka kuma sannan-
Ko a yawa na
fagen nazari ta rufe ƙofa ko ta ina.
Abin da ya
saura guda É—ai ne za
ni faÉ—o shi ku
saurara,
Hausa ta zam
harshe na ƙasa
lallai da kuwa mun mora,
Ƙasarmu
ko da ta bunƙasa
da kuwa ta kere tsara,
Sai ka ga mun
yo fintinkau mun rufe ƙofa ko ta ina.
Ka leƙa ƙasashen
duniya manya dukka ka dudduba,
In dai har ka
ga ta ci gaba ba tar riƙe harshen wani ba,
Harshen ilimi
harshen mulki ba zai zama harshen bare ba,
Sai dai harshe
na ƙasarta
da shi aka aiki ko ta ina.
Abokai nan zan
saka aya in rufe marfin ƙalamina,
Ga masu biÉ—ar wa yay yi ta
Abu-Ubaidatu sunana,
Na taso a jahar
Bauchi, Misau aka binne cibina,
Ya Jabbaru muna
roƙon
daÉ—in albarka ko ta
ina.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.