Ticker

6/recent/ticker-posts

Kalubale Wajen Koyar Da Harshen Hausa A Makarantu: Gyara Kayanka Bai Zama Sauke Mu Raba Ba

Takarda Wadda Aka Gabatar A Taron Ƙara Wa Juna Sani Na Ƙasa, Wanda Tsangayar Harsuna ta Kwalejin Shari’a da Ilimin Addinin Musulunci Da ke Ƙaramar Hukumar Nguru, Jihar Yobe ta Shirya, Daga Ranar 5 zuwa 7 ga Watan Fabrairu, 2020

aji

Ƙalubale Wajen Koyar Da Harshen Hausa A Makarantu: Gyara Kayanka Bai Zama Sauƙe Mu Raba Ba

 

Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya)

M.A Hausa (Literature) Student, Department of Nigerian Languages and Linguistics, Bauchi State Uniɓersity, Gaɗau.

07066366586, 08125351694

ibrahimba182@gmail.com

 

Da

Hafsat Muhammad

School of Educational Serɓices, Aminu Saleh College of Education Azare

08062514117

hafsatmuhammad189@gmail.com

 

Da

Tanimu Adamu

M.A Hausa (Literature) Student, Department of Nigerian Languages and Linguistics, Bauchi State Uniɓersity, Gaɗau.

07038286451, 09092489820

tanimuadamumisau@gmail.com

Tsakure

Harshen Hausa harshe ne mai cin gashin kansa a tsarin koyarwa cikin wannan Ƙasa ta Nijeriya, wannan ya sanya aka same shi cikin harsunan da aka yarda a koyar da su a dukkanin makarantun dake faɗin Ƙasar nan, sai dai makarantun da aka keɓanta da koyar da harkokin kiwon lafiya ko ayyukan fasahar ƙere-ƙere. A makarantun sakandare da firamare kuwa, harshen ya zama tilas ga kowane ɗalibi koda kuwa yana ɓangaren kimiyya da fasaha ne; idan a sakandare yake. Tare da wannan muhimmanci nasa, da yadda yake yalwatacce kuma sananne a tsarin koyarwa, harshen na samun tasgaro da ƙalubale a mafi yawan makarantun sakandare da firamare ta fuskoki da dama. Wannan takarda, ta bibiyi ire-iren waɗannan ƙalubale tare da bayyana su, sannan ta hakaito hanyoyin fita daga waɗannan ƙalubale a faɗin Jihar Yobe, musamman Ƙaramar Hukumar Nguru. Wannan aiki ya gudana ta hanyar tuntuɓa, karance-karance da ziyartar makarantu da bibiyar ɗalibai a matakan firamare da sakandare.

 

1.0 Gabatarwa

           Ko shakka babu, harshen Hausa na daga cikin harsunan da ake nazarta a matakai na ilimi daban-daban, harshe ne da ake yalwata ilimi a cikinsa dubi da bambance-bambance na ɓangarorinsa. A ƙananan makarantu na firamare da sakandare ma ba a bar Hausa a baya ba, domin tana cikin harsunan da ake koyar da su a matsayin darasi mai zaman kansa, wannan ta sanya ake samar masa da malaman da suke koyar da shi a matakin makarantun firamare da sakandare. Mafi yawan malaman da suke koyar da harshen Hausa; su ma sun karanci Hausa ne a matakin difloma, N.C.E, digiri na ɗaya, da na biyu da na uku. Amma da yawa cikin masu karantar da Hausa a makarantun firamare da sakandare; ba su wuce matakin digiri na farko ba. Amma akan samu waɗanda ba su karanci harshen Hausa ba a kowane mataki na karatu, amma sai ba su su rinƙa koyar da harshen Hausa. Karantar da harshen Hausa daga malamin da bai karance shi ba, yakan kawo babbar matsala a fagen koyon Hausa, musamman ganin yadda ake yi game da harshen cewa kowa ma yana magana cikin sa, don haka kowa zai iya karantar da shi. Sai dai abin da  ba a sani ba, ‘Ba a nan take ba, an danne bodari ta ka’. Domin a wannan aiki, za a ga illar da hakan yake haifarwa a tsarin koyar da harshen Hausa.

1.1 Ma’anar Koyarwa

           Masana sun yi ƙoƙari wajen bayyana ma’anar koyarwa, amma yawancin ma’anonin da suka bayar saƙon yana komawa kan abu guda ne. Misali, Zarruƙ (1979:1) ya bayyana ma’anar koyarwa da cewa, “Hulɗa tsakanin mutum da mutum. Kuma ana yin hulɗar ne don a kawo canje-canje cikin abin da mutum ya sani, ko wanda ya yarda da shi. Hulɗa dai ita ce zuciyar aikin, canjin halayen mutum kuwa shi ne manufarsa. Sannan kowa ya san ba a hulɗa sai da mutane; watau a ƙalla sai an sami mutum biyu sun sadu da juna tukuna”.

           Adeyeni (1985) a cikin Gambo (1998:3), ya ce, “Koyarwa wata tsararriyar hanya ce da malami ke bi wajen gwada wa ɗalibai abubuwan da ba su sani ba su koya su kuma yi amfani da shi a rayuwarsu ta yau da kullum”.

           Idan muka kalli waɗannan ma’anoni guda biyu, za mu ga aikin koyarwa shi ne aikin nuni ko gyara tsakanin mutane wanda ke farawa daga mutum biyu, wato mai koyo da mai koyarwa, har zuwa adadin mutanen da aka tsara za a koyarwa ko za a iya sanya su a gaba domin a koyar musu da dukkanin hanyoyin da suka dace da al’ada da ɗabi’a ta yanayin al’ummar da ke wurin kuma ba ta ci karo da yanayin al’adu da ɗabi’unsu ba, ko kuma amintaccen tsarin da zamani ya kawo.

2.0 Koyar Da Harshen Hausa A Makarantu

           Harshen Hausa na daga cikin harsunan da ake koyarwa a matakin makarantun firamare da sakandare, mafi yawan tsarin koyar da harshen akwai shi a rubuce cikin manhajar koyarwa kamar yadda Hukuma ta tsara. A tsarin koyarwa, kowane aji yana da nasa abin da ake koyarwa, wanda wani ke bin wani; har a kai ga abin da za a koyar a firamare, haka abin yake ga koyarwa a sakandare. A tsarin koyarwa, an duba matakin karatun kowane ɓangare, wato an yi duba ga abin da ya cancanta a koyar wa ‘yan firamare, da kuma abin da ya dace a koyarwa ‘yan sakandare; wanda ci gaba ne ga na ‘yan firamare.              

2.1 Masu Koyar Da Harshen Hausa

          Masu koyar da harshen Hausa a kowane mataki na makarantu daidai suke da masu koyar da kowane darasi, domin su ma malamai ne da suka karanci harshen Hausa a matakai daban-daban na ilimi, imma difloma ce, ko N.C.E ko digiri ko sama da waɗannan. Amma idan ka yi duba ga makarantun firamare, za ka iske mafi yawan masu koyar da Hausa ba su fice masu difloma ko N.C.E ba, sai ɗaiɗaiku cikin waɗanda suka yi digiri. Wannan ya sanya duk makarantar da ta yi wannan dace da waɗanda suka kai wannan mataki, to za ka samu ɗaliban suna da ƙoƙari wajen fahimtar darasin Hausa; saboda waɗanda suke karantar da ita, sun karance ta kuma suna karantar da ita bisa ƙa’ida da karɓaɓɓen tsari.

          Amma a wasu makarantun, za ka iske an bai wa waɗanda ba su karanci Hausa ba su karantar da ita. Wannan kuwa na da alaƙa da raina darasin ta yadda ake ganin kowa ma zai iya karantar da Hausa, ko kuma domin rashin malaman Hausa ko kuma rashin kayan aiki. Wannan ya sanya za ka ga ɗaliban ba sa fahimtar komai, a wani lokacin ma su ɗauki darasin Hausa a matsayin lokacin koyar da labarun tatsuniya ko hira.

3.0 Ƙalubalen Da Harshen Hausa Ke Fuskanta A Makarantu

          Halima (2011:384) ta bayyana cewa, za mu iya cewa an yi wa aikin koyar da Hausa riƙon sakainar kashi, kai ba ma koyarwa ba, shi kansa malamin Hausa da koyon Hausa da ma nazarinta wasu ba su ɗauke shi da muhimmanci ba. Wataƙila wannan ita ce babbar matsalar farko. Muna iya cewa alama wannan duhu ne yake dukan duhu. Dalili shi ne, waɗannan matsaloli da ake fuskanta dawurwura suke yi a tsakanin al’ummar Hausawa da kuma hukumomin ilimi da jihohin Arewacin Nijeriya. Saboda haka, a nan Gizo ke saƙarsa, a wannan kogon matsalolin suka maƙale, sai kame-kame ake yi.

          Wannan bayani na Halima, sai ya tuna mana da wasu baituka cikin wasu waƙoƙi game da Hausa da yadda ‘ya’yanta suka wofintar da ita.

                             Zarafin da mamaki, gwanin ban haushi,

                                         Mugun baƙin sha’anin Bahaushen Hausa.

                             Kowa da yare nasa bai ƙyama tai,

                                         Mu ga mu mun tozarta harshen Hausa.

                             Wai don gadarar mun jiyo Turanci,

                                         Har ba mu son magana da harshen Hausa.

                             Tsuntsu kamata yai da shi yai kuka,

                                         Ya irin na kaka nasa can mai nisa.

                             Ku sani Bature ba shi ƙin Turanci,

                                         In ya game da kininsa ko a makasa.

                                                                                (Aƙilu, 1976:34).

          Baba (Nayaya) (2018:2) ya kawo wasu baituka a inda ya ce,

                                      Harshen Hausa abin faharina,

                                      Ba wani in ba kai ba gabana,

                                      Wanga batu wallahi zumaina,

                                      Kar ku ji kunya ko kuwa ƙi na,

                                                Mu ‘yan Hausa muna da asara.

                                      Yo in ban da abin ban haushi,

                                      Wa zai doki kare dan haushi,

                                      Wa kuwa zai ƙi gidan da ya tashi?

                                      Sai fa Bahaushe mai ban haushi,

                                                 In ji Aƙilu Aliyu ku lura.

                                      Yau ɗan Hausa yana da Gadara,

                                      Wai shi Turai za shi tsirara,

                                      Ya sa bel ya ɗaura ɗamara,

                                      Bai cin dambu kun ji tijara,

                                                Balle koko abin da ya tsera.

                                        In ka je makarantun boko,

                                        Za ka ga malam ya sha sanƙo,

                                        Bai yin Hausa ku ji mini soko,

                                        In ka ce ya yi Turancin ko,

                                                  Za ka ji kunya kun ji asara.

                                       Ba shi ga tsuntsu; ba shi ga tarko,

                                       Mai ƙin Hausa gare ni fa soko,

                                       Kai! Malam riƙi Hausa a farko,

                                       Koyarwa da zaman kan loko,

                                                  Har a ƙasar waje ba ka asara.

                                        Kai! Ku jiye mini fallin boko,

                                        An hana Hausa a tsarin boko,

                                        In ko ka yi ta a ce maka soko,

                                        Ɓernacular za a ce ka yi a loko,

                                                     Har a fitar ka cikin ‘yan ƙara.

          Ko da jin waɗannan baituka da suka gabata, an san harshen Hausa na fuskantar ƙalubale a ɓangarori daban-daban na al’umma, ka ma daga wurin shugabanni, malamai har ma da ɗaliban da ake koyarwa a matakin karatun firamare da sakandare, amma ƙalubalen da yake fuskanta a makarantun gaba da waɗannan, akwai sauƙi sosai. A wannan gaɓa, za mu bayyana ƙalubalen ta hanyar rukunoni na jama’a daban-daban, wanda ta nan za mu gane inda matsalar ta fi ƙarfi da kuma samar da hanyoyin da za bi domin magance waɗannan matsalolin.

3.1 Ƙalubale Daga Gwamnati/Hukumomin Ilimi

          Ƙalubale na farko da wannan bincike ya gano, ƙalubale ne daga gwamnati da hukumomin ilimi, domin su ne suke da hanyoyin tsara ko gyara harkar koyar da Hausa wadda kowa zai bi ba tare da an samu wata matsala ba. Idan kuwa har an samu wata matsala, to su suke da alhakin ɗaukar dukkanin wani mataki na magance faruwar hakan a gaba. Daga cikin matsalolin da gwamnati ko hukumomin ilimi suka haifar akwai:

3.1.1 Rashin Kayan Aikin Koyarwa Na Hausa

          Kamar yadda Taiwo (1985:32) ya bayyana cewa, babu wata koyarwa a duniya da za a yi ta ba tare da kayan aiki ba, wannan koyarwar kuwa ta shafi makarantun firamare da sakandare, su kuwa kayan aikin sun shafi koda kuwa littafin da za yi amfani da shi ne wajen ɗaukar muhimman batutuwan da ake son koyarwa. Ba ya ga littattafai, akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata a ce an gabatar da su a zahirinsu ga ɗalibai, kamar ganguna; idan ana koyar da su abin da ya shafi kaɗe-kaɗe, ko launuka; idan ana koyar da su abin da ya shafi launi, ko kitso, ƙunshi, shigar al’adu ko tufafin ma’aurata; yayin da ake koyar da su al’adun aure. To duk waɗannan gwamnati ba ta aika wa makarantu, kamar yadda su ma hukumomin ilimi ba sa nemar wa makarantu su tura musu domin a koyar da Hausa. 

3.1.2 Rashin Aiki Da Manhaja Da Sabunta Littattafan Hausa

          Manhaja ita ce kundin da ake tsara dukkanin abin da za a koyar da ɗalibai a kowane mataki na karatu. (Madugu, 2000:69). Sau da dama ba a tantance manhajar Hausa kamar yadda ba a fiye sabanta ta ba; musamman ta firamare, idan kuwa an sabanta ta; to zai yi wuya ka ga ana aiki da ita a ƙananan makarantu. A yayin wannan bincike, kaso 67 cikin ɗari na alƙaluman lissafi, sun bayyana cewa mafi yawan makarantu ba sa amfani da manhaja yayin darasin Hausa, kawai dai suna amfani da littattafai ne irinsu: ‘Koyon Hausa Sabuwar Hanya’, ‘Mu Koyi Karatu’, ‘Mu Yi Ta Karatu’, ‘Makarantar Malam Mamman’ ko ‘Inna Da Baba’, waɗanda yawancinsu an wallafa su ne a kafin shekarar 1990, ko bayanta da kaɗan. Cikin wannan bincike, kaɗan ne aka samu suna amfani da Tsanin Hausa na Kamilu Ɗahiru Gwammaja wanda aka yi bugunsa na farko a shekarar 2005.

          Idan ka koma ta fuskar makarantun sakandare kuwa, nan ma za ka iske mafi yawa suna amfani ne da littattafai irin su: Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa (1987), Darusan Hausa (1992) da makantansu. Haka wajen nazarin littattafan zube, da na wasan kwaikwayo, su ma ba a canjawa, domin har yanzu ana amfai ne da ire-irensu: Ruwan Bagaja (1933), Shehu Umar, Tauraruwa Mai Wutsiya (1969), Tabarmar Kunya (1968), Zamanin Nan Namu (1970), Wasan Marafa (1949) da Waƙoƙin Hausa (1957) da sauransu wanda yanayin zamanin da aka rubuta su ya bambanta da wannan zamani.

3.1.3 Rashin Shirya Wa Malaman Hausa Tarukan Bita

          Kusan kowane sashe na malaman firamare da sakandare ana shirya musu tarukan bi-ta ko ƙara wa juna sani, amma ban da malaman Hausa, zai yi wuya ma ka ji an ce an shirya bi-ta ga malaman Hausa a kan tsarin koyar da Hausa ko a kan bin da ake karantarwa; kamar yadda ake shiryawa sauran malaman da suke wasu sassa. Wannan ya sanya su kansu malaman Hausa suke guduwa zuwa wani sashe domin su samu a tura sunayensu cikin waɗanda za su je wannan taron bi-ta la’akari da ɗan abin da ake samu daga waɗanda suka shirya wannan taro.

3.1.4 Rashin Ɗaukar Ƙwararrun Malaman Hausa

          Hausa tana fama da rashin ƙwararrun malamai ta la’akari da yadda ɗalibai ba sa samun gogewa. Domin idan har akwai gogaggun malamai kuma ƙwararru, to za su yi amfani da hikim da gogewarsu wajen karantar da ɗalibai; koda kuwa suna da ƙarancin kayan aikin koyarwa.   

3.1.5 Mayar Da Darasin Hausa Koma Baya Da Rashin Ba Shi Muhimmanci

          Ko shakka babu, darasin Hausa ba shi da wani muhimmanci a wurin shugabanni da Hukumar Ilimi, wannan ta sanya ba a sayan kayan koyar da Hausa da shiryawa malaman Hausa tarukan bi-ta kamar yadda muka bayyana a sama.

          Ta fuskar jarabawa ma, akan samu wannan ƙalubalen, domin ba a ba ta muhimmanci koda ta fuskar tsaro ne a yayin rubuta ta; imma  jarabawar kammala karatu ce ko kuma ta sauyin aji ce. Shi ya sa za ka ji ana cewa, ‘Cin ki banza; barinki banza’, ko kuma ka ji an ce ‘Gida da masallaci’, wato Hausa da Islamic Studies.      

3.1.6 Raina Malaman Hausa Da Nuna Musu Wariya

          Malamin Hausa mutum ne maras gata koda ta fuskar gwamnati ce ko kuma Hukumar Ilimi, domin za ka iske ba a martaba shi ko nuna kulawa irin yadda ake nunawa ga malaman da suke koyar da English, Maths, Primary Science da sauransu.

3.2 Ƙalubale Daga Shugabannin Makaranta

          Akwai ƙalubale mai yawa da Hausa take samu daga wurin shugabannin makarantu. Daga cikin ƙalubalen akwai:

3.2.1 Rashin Girmama Malaman Hausa

          A ɗabi’ar ɗan’adam; yana son girmamawa, amma malamin Hausa ba ya samu wannan girmamawar a wurin da yawa daga cikin shugabannin makarantu. Wannan ta sanya koda malamin ya nemi a kawo wasu kaya domin yin darasi, za ka ga ba a kawowa, sannan idan ya nemi ɗalibai su sayi wasu takardu; shugabannin ba sa bayar da goyon baya, domin suna ganin Hausa ce ba ta da wani muhimmanci.

3.2.2 Rashin Bayar Da Darasin Hausa Ga Wanda Ya Karance Ta

          Hausawa na cewa, ‘A rashin uwa; akan yi uwar ɗaki’. To fagen koyarwa ba a la’akari da hakan, bal ma a wani lokacin akwai uwar, amma sai ka ga ana ƙoƙarin yin uwar ɗakin, ko ma ka ga an yi uwar ɗakin. Za ka iske ga malamin da ya karanci Hausa, kuma yana da ƙwazo, amma ba za a ba shi ya koyar ba, sai a ba shi Ciɓic Education, Social Studies ko Islamic Studies, idan ya so sai a ɗauki malamin da bai kai shi ƙwazo ba, ba shi da ƙwarewa ta fuskar Hausa, sai a ba shi darasin a ce shi zai koyar da Hausa.

3.2.3 Rashin Sanya Darasin Hausa A Muhimmin Gurbi A Jadawalin Shiga Aji

          Sau da dama za ka ga an mayar da darasin Hausa ƙarshen lokaci, wato dab da za a tashi, a wannan lokaci kuwa ɗalibai sun gama galabaita, kowanensu na marmarin tafiya gida sakamakon gajiya ko yunwa; ta yadda cikkunansu ke kiran ciroma. To a irin wannan yanayi babu yadda za a yi darasi ya samu gurbin zama a zukata ko ƙwaƙwalen ɗalibai walau manya ne ko ƙanana; sai ɗaiɗaiku.

3.2.3 Nuna Wariya Ga Malaman Hausa

          A tsakanin shugabannin makarantu, wasu daga ciki kan nuna wariya tsakanin malaman da suka karanci Hausa kuma suke koyar da ita, da waɗanda suke koyar da wani darasin da ba Hausa ba. Wannan ta sanya koda wani ɗan kuskure aka samu, an fi ƙarfafa na malaman Hausa a kan na wanda ba Hausa suke koyarwa ba, har ma su akan yi musu afuwa a nan take.

          A gefe guda kuwa, idan malaman Hausa suka nemi kafa wata ƙungiya irin wadda tsarin ilimi ya aminta a kafa a makaranta domin kaifafa tunani da samar da wani yanayi na sanya gasa tsakanin malamai, za ka iske ba sa bayar da goyon baya.

 

3.3 Ƙalubale Daga Malamai

          Malamai a junansu suna haifar da babbar matsala a tsakaninsu wanda wannan shi ma babban ƙalubale ne. Daga cikin irin ƙalubalen da ake samu ta ɓangaren malamai akwai:

3.3.1 Rashin Mutunta Malaman Hausa

          Malaman da suke koyar da darusan kimiyya, fasaha, yanayi, harkar gona da ilimin sanin halittu ko Turanci, za ka iske ba su fiye  ɗaukar malamin da yake koyar da Hausa da muhimmanci ba, bal ma a wani lokacin sukan ɗauke shi a matsayin abokin tsokana, wannan kuwa koda a cikin ɗalibai ne. Hakan ta sanya za su iya gaya wa malamin Hausa dukkanin kalmar da suka ga dama idan wani saɓani ya ɗan gitta tsakaninsu.

3.3.2 Nuna Wa Ɗalibai Karantar Hausa Ɓata Lokaci Ne

          Sau da dama za ka iske malaman da suke koyar da wani darasi da ba Hausa ba, suna ɓata malaman Hausa a gaban ɗalibai ko kuma su nuna wa ɗaliban yin karatun Hausar ma asarar lokaci ne.

3.4 Ƙalubale Daga Malaman Hausa

         Bahaushe kan cewa, ‘Da ɗan gari kan ci gari’, kuma ‘Sai bango ya tsage; ƙadangare ke samun wurin shiga’. Wannan magana haka take, domin mafi yawan wasu ƙalubalen da ake samu a cikin makaranta game da Hausa suna samo asali ne daga malaman da suke karantar da Hausa. Daga cikin ƙalubalen da ake samu daga wurinsu akwai:

 

 

3.4.1 Rashin Ɗaukar Darasinsu Da Muhimmanci

          Mafi yawan malaman Hausa ba sa ɗaukar darasinsu na Hausa da suke koyarwa da muhimmanci, a wasu lokutan ma za aka iske suna jin kunyar su ce Hausa suke koyarwa. Wannan kuwa ba ƙaramin ƙalubale ba ne, domin ba yadda za a yi su karantar da ɗalibai yadda ya kamata dubi da yadda su ma ba son abin da suke koyarwar suke yi ba. Da wuya ka ji su sun zauna suna tattauna wasu muhimman batutuwan da ake koyarwa a Hausa, ko ƙara wa junansu sani.

3.4.2 Rashin Zurfafa Bincike

          Aikin koyarwa dole sai da bincike ta hanyar karance-karance da sayen litattafan da za su taimaka masa wajen ƙara wa kansa sani da zurfafa iliminsa. Har wa yau, zai yi wuya ka ga malamin Hausa yana da niyyar ci gaba da karatunsa a mataki na gaba domin karantar Hausa, in dai a matakin firamare ne ko sakandare sai ɗaiɗaiku. Domin waɗanda suka karance ta ɗin ma, suna ganin sun karance ta ne ala dole, amma ba wai domin sun so ba.

3.4.3 Rashin Kafa Ƙungiyoyin Hausa (Hausa Kulob) A Makarantu

          Kafa kulob-kulob a makarantu abu ne da yake jan ra’ayin ɗalibai kuma yake sanya musu son harshen da ake amfani da shi. To a yankunanmu, babu ire-iren waɗannan kulob ɗin da aka buɗe domin raya harsunan Hausa a makarantu. Ire-iren waɗannan kulob ɗin ne ke shirya tarukan Makon Hausa domin raya al’adu da harshen Hausa a makarantun sakandare da na sama da su, musamman a wasu jihohin da suke wannan Ƙasa.

3.4.4 Rashin Sabunta Tunani Da Sanya Al’amura na Zamani A Yayin Koyarwa

          Hausawa suka ce, ‘Zamani riga; kowane da irin tasa’. To a nan ba a samun sauyi ta fuskar koyar da Hausa, ba a sanya al’amuran zamani, ba a yin amfani da kayan zamani koda kuwa a cikin manhaja ne. Wannan ta sanya ɗaliban ba su san abubuwa da dama ba, domin rashin kyakkyawar fassara ko rashin kwatanta wasu abubuwan al’ada ta hanyar amfani da abubuwan zamani.

3.4.5 Rashin Gogewa Ta Musamman

          Himma ba ta ga rago’ in ji ‘yan magana. Akan samu rashin gogewa ga kaso mai yawa daga cikin malaman da suke koyar da Hausa a matakin firamare ko sakandare. Wannan kuwa ya biyo bayan wasu cikin abubuwan da suka gabata, ko dai ba su karanci Hausa ba, ko kuma suna karantar da ita ce tilas, domin ba darasin da za su iya koyarwa.

3.4.7 Rashin Kai Ɗalibai Yawon Gane Wa Idanu Wasu Muhimman Abubuwan Da Aka Karanta A Aji

          A tsarin koyarwa, akwai kai  ɗalibai yawon gani da idanu kan abin da aka koyar musu a cikin aji. A darasin Hausa, ba a ɗaukar ɗalibai domin kai su ire-iren wuraren tarihi ko wasu sana’o’i na gargajiya, malami mai ƙoƙari ne kaɗai yake nuna wa ɗalibai hotunan wasu abubuwa, kamar su ganguna, tukwane da wanin waɗannan.

3.5 Ƙalubale Daga Ɗalibai

          Ɗalibai a nasu matakin, su ma suna da nasu gudumawa wajen haifar da wasu matsalolin da ake samu. Daga cikin ƙalubalen da ake samu ta fuskar ɗalibai musamman waɗanda ke sakandare akwai:

3.5.1 Zuga A Junansu

          Sau da dama ɗalibai kan zama a junansu suna tattauna irin abin da suke son zama idan sun kammala karatunsu, wannan ya sanya za ka ji mafi yawansu suna mayar da hankali ne kan son zama likita, ko ma’aikacin jirgin sama, ko dai wani babba a wata ma’aikatar tarayya. Kaɗan ne cikin ɗalibai ke marmari ko burin zama malamai; su ɗin ma ba za ka ji sun nuna sha’awarsu ga zama malaman Hausa ba. Idan an samu wani ɗalibi/ɗaliba ya/ta nuna sha’awar son karantar Hausa ko burin zama malamin Hausa, to za ka ji sauran ɗaliban suna zuga shi/ta cewar me zai/za ta yi da Hausa? Ai karantar Hausa shiririta ce da ɓata lokaci. Irin wannan zugar kuwa, takan yi tasiri a zukatan da yawa cikin ɗalibai har ta kai ga sun haƙura da wannan buri da yake ransu.

3.5.2 Fahimtar Lokacin Darasin Hausa A Matsayin Lokacin Hira Da Wasa Da Sharholiya

          Duk lokacin da malamin wani darasi ya shiga aji, za ka iske ɗaliban sun nutsu tare da mayar da hankali a kan abin da ake koyar musu. Amma ga darasin Hausa; abin ba haka yake ba, domin sau da dama za ka iske wasu ɗaliban sukan guje wa darasin Hausa; musamman idan ya kasance malamin na da doka da bibiyar komai, idan kuwa malamin maras tsawatarwa ne, za ka ga ajin ya zama tamkar kasuwa a ranar jajiberen sallah.

3.6 Ƙalubale Daga Iyaye

          Iyaye suna da rawar da suke takawa imma wajen kawo wa darasin Hausa cikas ne ko kuma wajen ciyar da shi gaba. Cikin irin ƙalubalen da ake samu ta fuskar iyaye akwai:

3.6.1 Rashin Bayar Da Goyon Baya Ga ‘Ya’yansu Masu Son Karantar Hausa

          A matakin sakandare imma ƙarama ce ko babba, iyaye ba sa bayar da goyon baya ga ‘ya’yansu da suke nuna sha’awarsu ga darasin Hausa. Sau da dama iyaye ba sa ɗaukar ɗansu ko ‘yarsu da suka yi ƙoƙari a darasin Hausa a matsayin abin birgewa da so. Za su iya bayar da kyauta ga ‘ya’yansu da suka yi bajinta a wasu darusa, amma ban da Hausa.

3.6.2 Rashin Bincikarsu Darasin Hausa

          Daga cikin abin da yake ƙara ƙoƙarin ɗalibai akwai binciken da iyaye suke musu game da darusan da aka koya musu a makaranta. A irin wannan binciken, za ka iske iyaye ba su fiye bincikar ‘ya’yansu abin da aka koyar musu a Hausa ba, domin su a wurin su; yin ta da barinta duk ɗaya.

3.6.3 Rashin Ganin Muhimmancin Malaman Hausa

          A duk lokacin da iyaye suka ziyarci makarantun da ‘ya’yansu suke karatu, za ka ga suna nuna farin ciki ga malaman da suke koyar da darusan kimiyya ko Turanci, a daidai lokacin da ba sa nuna irin wannan fara’a ga malaman da suke koyar da darusan Hausa, har ma idan malamin mai bin aikinsa da bibiyar ayyukan ɗalibai da yi musu horo kan sakacinsu ne, to iyaye akn ji haushinsa.

3.6.4 Ƙin Saya Wa ‘Ya’yansu Takardun Hausa

          Kusan kowane darasi ƙunshe yake da littattafan da ake karantawa, musamman a matakin sakandare, ko kuma ƙananan littattafan da ake koyarwa na koyon rubutu na Hausa ko harufa. Za ka iske iyaye ba su damu da su saya wa ‘ya’yansu ire-iren waɗannan littattafai ba; duk kuwa da ƙarancin kuɗaɗen da ake sayar da su. Amma ga wasu darusan, za ka iske iyaye na gaggawa wajen sayen littattafai da sauran kayan da za su taimaka wa ‘ya’yansu su koyi waɗancan darusa.

4.0 Hanyayin Magance Waɗannan Ƙalubale

                                      In dai ana so ta yo ƙarfi,

                                      Hausar ga yare daɗo zurfi,

                                      Ta zarce komai cikin zarafi,

                                      Ku karɓi zancen cikin zafi,

                                                A dubi zancen ga ba gyara.

                                        A ture son rai a sa himma,

                                        A sa ƙwararru su tsattsarma,

                                        Hikima ta yau dubi al’umma,

                                        A sa takardun da ba ƙyama,

                                                A Manhajarmu a gyaggyara.

                                                                  (Baba (Nayaya), 2018:5).      

          A duk lokacin da aka fahimci matsala, to ko shakka babu an samu tushen magance ta, domin fahimtar matsala yana tattare da hanyoyin magancewa. A wannan bincike, an nazarci muhimman batutuwa game da ƙalubalen da Hausa ke fuskanta a makarantu. Idan har waɗannan su ne matsalolin, to ke nan magance matsalolin ba zai zama abu mai wahala ba; ganin yadda an riga an san matsalolin. 

4.1 Ɗaukar Ƙwararrun Malaman Hausa

          A duk lokacin da aka samu ƙwararre a fanni; to lalle za a samu abin da ake buƙata game da abin da ya sanya aka same shi. Don haka, matuƙar ana son magance wannan matsala, to wajibi gwamnati ta samar da ƙwararrun malaman Hausa waɗanda suka karance ta, kuma suke da kishin abin da suka karanta. Sannan a gefe guda, a wadata su da kyakkyawan albashin da zai ba su damar sauƙe nauyinsu da kuma sayen abubuwan da ake buƙata domin ingiza koyarwa; koda gwamnati ba ta saya ba.

4.2 Samar Da Kayan Aikin Koyarwa Da Zamanantar Da Tsarin Koyar Da Hausa

          Kayan aikin koyarwa abubuwa ne da suke taimakawa wajen koyo ga ɗalibai da kuma isar da saƙo cikin sauƙi daga malamai. Ke nan, dole ne a samu kayan a kowane mataki na makarantu imma firamare ce ko sakandare. Waɗannan kayan aikin sun haɗa da littattafai da sauran dangin kayan kowane darasi kamar ganguna, kayan noma, kayan ƙira, kayan saƙa da sauran dangogin dukkanin abin da zai taimaka ga ɗalibai su fahimci wani abu.

4.3 Shirya Tarukan Bita Ga Malaman Hausa

          Taro bita ga malami abu ne da yake ƙara fito masa da wasu abubuwa fili, kamar yadda mahanga ce ta ƙara wa malamai ilimi. To a nan, wajibi ne matuƙar ana son gyara harkar koyar da Hausa; a rinƙa shirya wa malaman Hausa tarukan bita irin yadda ake shirya wa wasu da ba su ba. Har wa yau, a rinƙa ɗaukar malaman bisa cancanta ana tura su domin ƙara sani ko zurfafa ilimi.

4.4 Tura Malaman Hausa Ƙaro Karatu

          Sanin kowa ne, karatu mataki-mataki ne. Idan malamin Hausa yana mataki na ƙasa, wajibi ne a ba shi dama domin zuwa ƙaro ilimi a mataki na gaba da shi. Misali, idan difloma ce da shi, a ba shi dama ya tafi N.C.E, idan N.C.E ne da shi, ya tafi digiri. Kuma a sanya idanu lalle yana wannan karatu da gaske, domin yanzu ba domin kansa yake yi ba, yana yi ne domin ɗaliban da gwamnati ta ɗauke shi ya koya musu.

4.5 Samar Da Sabuwar Manhaja Da Bibiyarta Da Samar Da Takardun Zamani

          Dukkanin wani abu da ake koyarwa da ɗalibai a kowane mataki na karatu; yana ƙunshe cikin manhaja. Ita kuwa manhajar akan samu sauyi a wasu lokutan daga wasu jihohi. Misali, manhajar Jihar Jigawa ta makarantun sakandare ta bambanta da ta Jihar Yobe, yayin da ta Jihar Jigawa ta fi ƙunsar muhimman batutuwa da warware komai filla-filla, saɓanin ta Jihar Yobe. To a nan, yin amfani da manhajar Jigawa shi ya fi, domin cikin ta akwai yalwar ilimi da sanya zamananci cikin abin da za a koyar.

          Sannan littattafan da ake koyarwa musamman a matakin sakandare, zamanin su ya ja baya, an samu sauye-sauye, ya kamata a koma amfani da waɗanda zamani ya kawo irin su: Tsanin Hausa (2005) na Kamilu Ɗahiru Gwammaja, Mu Koyi Hausa A Sauƙaƙe (2010) na Abdullahi Baba Nguru. Game da litattafan karantar da wasu darusa kuwa, irinsu Magana Jari Ce, Ruwan Bagaja, Shehu Umar, Ganɗoki da sauransu, yana da kyau a sake bitar su da gyaran Hausar su irin yadda Malumfashi da wasu (2015) suka sabunta aikin littafin Dare Dubu Da Ɗaya. Littattafai irinsu: Hikayoyin Shehu Jaha (1999) na Tijjani M. Imam, Hikayoyin Kaifafa Tunani (1979) na Malam Aminu Kano, Tatsuniyoyi Da Wasanni 1-6 (1971) na Ibrahim Yaro Yahaya za su taimaka matuƙa, sannan a gyara Hausar littafin Labarun Gargajiya 1-2 (1974) na IbrahimYaro Yahaya. Akwai litattafai da a yanzu ake rubutawa waɗanda suka dace da wannan zamani kuma ba su saɓa wa koyarwa ba, su ma ya kamata su biyo layin.

4.6 Kafa Ƙungiyoyin Raya Harshen Hausa A Makarantu

          Kulob a makarantu na daga cikin abin da yake jan hankalin ɗalibai wajen son wasanni. Hausa tana da ire-iren waɗannan kulob ɗin a wasu makarantu musamman a wasu jihohin. To a nan ma, ya kamata malaman Hausa su rinƙa kafa ire-iren waɗannan kulob ɗin domin raya al’adu da harshen Hausa, kuma da wannan za su rinƙa shirya tarukan Makon Hausa a makarantunsu.

4.7 Sanya Darasin Hausa A Jerin Darusa Masu Muhimmanci

          Lokaci a yayin darasi abu ne mai matuƙar muhimmanci, domin yana bayar da damar fahimtar karatu ko akasin haka. A nan, dole ne kwamitin tsara jadawalin karatu a makarantu su rinƙa sanya darasin Hausa a lokuta na musamman irin yadda suke sanya sauran darusan kimiyya.

4.8 Gina Ɗakunan Amon Sautuka Da Gwaje-gwaje Na Hausa

          Gina ɗakunan gwaje-gwajen amon sautuka abu ne da zai taimaka wa harshen Hausa da gyara darusan a makarantu. Gwamnati ita ce ke da haƙƙin gina ire-iren waɗannan ɗakuna a kowace makaranta, musamman makarantun sakandare, da kuma samar musu da kayan ayyukan da ake buƙata a ciki.

4.9 Sanin Muhimmancin Abin Da Ake Karantawa Daga Malaman Hausa

          Wannan kuwa ya shafi ɗalibai, dole ne a nuna musu muhimmancin abin da ake koyar da su na Hausa. Hakan kuwa ba zai yiwu ba, har sai su ma malaman sun riƙe darusan Hausar da muhimmanci, suna jin haka a jikinsu, sun gamsu da abin da suke karantarwa.

4.10 Samun Mutuntaka Tsakanin Malamai

          Ganin mutuncin juna abu ne da yake kawo ƙauna da soyayya tsakanin mutane, kamar yadda girmama juna kan dasa so a zukatan al’umma da kuma yarda. Wajibi ne malamai su rinƙa girmama junansu, shin waɗannan malaman suna koyar da darasi guda ne ko kuma mabambantan darusa suke koyarwa.

5.0 Kammalawa

          Daga cikin abin da ya gabata a wannan bincike, an bayyana ma’anar koyarwa sannan aka ɗora bayani a kan koyar da harshen Hausa a makarantun firamare da sakandare. A cikin nazarin, an bibiyi ƙalubalen da yake kan darusan Hausa a makarantun firamare da sakandare ta fuskoki da dama, ta fuskar gwamnati da hukumar ilimi, ta fuskar shugabannin makarantu, ta fuskar malaman da suke koyar da wasu darusa waɗanda ba Hausa ba, ta fuskar malamn da suke karantar da Hausa, ta fuskar ɗalibai da kuma iyayen yara. Takardar, ba ta tsaya hakaito matsaloli kaɗai ba, sai da ta bibiyi hanyoyin da ake kyautata zaton matuƙar an bi su; to ko shakka babu za a fita daga cikin waɗancan ƙalubale na matsalolin da suka yi wa darasin Hausa katutu a makarantun firamare da sakandare.

 

Manazarta

Tuntuɓi masu takarda.

Post a Comment

0 Comments