Takarda Wadda Aka Gabatar A Taron Ƙara Wa Juna Sani Na Ƙasa Da Ƙasa, A Kan Nazarin Hausa Cikin Farfajiyar Gidan Chadi Domin Girmama Farfesa Nina Pawlak, Wanda Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Fassara da Hikimomin Al’umma Tare da Haɗin Guiwar Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da na Kimiyyar Harshe da Harsunan Ƙetare, Jami’ar Bayero Kano Suka Shirya, Daga Ranar 7 Zuwa 9 Ga Watan Janairu, Shekarar 2020.
Nazarin Kura-kuren Rubutu A Cikin Wasu
Littattafan Ƙagaggun Labarai Na Hausa
Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya)
(Masters in View),
Department of Nigerian Languages, Bauchi State Uniɓersity, Gaɗau.
07066366586, 08125351694
Da
Abubakar Umar Akuyam
Goɓernment
Comprehensiɓe
Day Secondary School, Misau
08039093730
Da
Hafsat Muhammad
School of Educational Serɓices, Aminu Saleh College of Education
Azare
08062514117
Tsakure
Harshen
Hausa ɗaya ne
cikin harsunan da suka shahara a Afirka, musamman Nijeriya ta Arewa. Daga cikin
abubuwan da suka ƙara yaɗa wannan harshe na Hausa akwai rubuce-rubucen jaridu na
Hausa, mujallun Hausa da littattafan Hausa musamman na ƙagaggun
labarai na Hausa. Rubutun Hausa yana tafiya da ƙa'idoju; wanda
kaucewa waɗannan ƙa'idoji kan sauya ma'anar saƙon da
aka nufata a cikin waɗannan wallafe-wallafe. Wannan takarda ta nazarci ire-iren
waɗannan
kura-kurai da aka fi samu a cikin littattafan Hausa, da kuma yadda za a kiyaye
waɗannan
kura-kurai. A cikin takardar, an zaƙulo kura-kurai guda
biyar kacal cikin waɗannan kura-kurai, aka rubuta yadda suka rubuta, sannan
aka kawo yadda ya kamata su kasance a Daidaitacciyar Hausa da kuma ƙa'ida
karɓaɓɓiya. Wannan aiki ya
wakana ta hanyar bibiyar rubuce-rubucen masana da bibiyar waɗannan litattafai na
Hausa.
1.0 Gabatarwa
Rubutu hanya ce ta isar da saƙo a tsakanin al’umma,
wannan kuwa ya samo asali tun lokacin da al’umma ta buɗe idanuwanta ga
harkar rubutu a daɗin duniya. Al’ummar
Hausawa na daga cikin al’ummar da ta ɗauki rubutu a matsayin hanyar isar da saƙwanninta, musamman ta
hanyar wallafe-wallafen littattafai, shafukan jaridu da mujallu da muƙalu da sauran
shafukan sa-da-zumunta da zamani ya zo da su kamar: Facebook, 2go, Whatsapp,
Twitter, Instagram da sauran dangoginsu. Daga cikin hanyoyin da ake yin rubutu
domin isar da saƙwanni akwai littattafan ƙagaggun labarai na
Hausa waɗanda a yau suka
mamaye Ƙasar Hausa.
2.0 Ma’anar
Ƙagaggun
Labarai
Masana
sun tattauna wajen bayyana ma’anar ƙagaggun labarai. Misali: Yahaya da wasu (1992:65) sun
bayyana shi da cewa, Na ɗaya daga cikin rukunin adabin Hausawa na zamani da masana adabin Hausa
suka bayyana shi da zube, wanda shi ne na farko a cikin
rukunin, kafin waƙa da wasan
kwaikwayo.
Shi
kuwa Mukhtar (2016:2) a wata lakca da ya gabatar cewa ya yi, “Shi ƙagaggen labari
cike yake da zantukan hira da nishaɗi,
wanda ba da gaske
ya taɓa faruwa ba, saboda
ana samar da shi ne kawai don nishaɗantarwa”.
Duba
da waɗannan ma’anoni da suka gabata, za mu iya kallon ma’anar ƙagaggun labarai na Hausa da cewa, su ne ire-iren labaran da
ake samu a rubuce ko da ka, domin samun abokin hira da ɗebe kewa ta hanyar karantawa ko sauraro. Tun bayan da Hausawa ‘yan ƙasa suka iya
rubutu, sai suka riƙi hanyar rubuta ƙagaggun labarai a matsayin wata hanya ta sana’a, musamman ta
la’akari da yadda ake ƙara samun yawaitar
masu karantawa, wanda hakan sai ya haifar da yawaitar marubuta waɗannan ƙagaggun labarai, ciki
kuwa maza da mata, matasa da manya.
2.1 Tarihin Rubutun Ƙagaggun Labarai Na
Hausa
Yahaya
(1988:77) ya bayyana tarihin rubuce-rubuce na ƙagaggun littattafai
bai daɗe sosai ba, domin an
same su ne bayan shigowar Turawa, musamman masu bincike da yaɗa addinin Kirista
irin su J.F. Schon. Schon ya yi rubuce-rubuce duk da kasancewar mafi yawan
littattafan na shi sun fi kama da na yaɗa addinin Kirista, face littafinsa na Letafin
Magana Hausa (1857) da ya yi kama da zube, sai na ƙarshe wato, African Proɓerbs, Tales and History (1886) da ya fi kama da ƙagaggun labarai. Yunƙurin haɓakarsu kuwa, ya
biyo bayan zuwan Turawa ‘yan mulkin mallaka a waɗannan
rubuce-rubucen a cikin zube na Hausa. Misali an samu Frank Edgar, Fletcher, Rattray R.S. da
Whitting. Sai kuma lokacin da aka kakkafa makarantun boko a Jihar Arewa. Misali
a Lardin Sakkwato a 1905 ƙarƙashin shugabancin Mr. Burden, wadda aka rufe ta sakamakon
rashin kai yara. Sannan a 1909 Gwamna Lugard ya sa Mr. Harns Ɓischer wato (Ɗan Hausa) ya sake buɗe wata makarantar a
Kano.
2.2 Kafa Hukumomi da Ƙungiyoyin Rubuta Ƙagaggun Labarai
Baya ga samar da ɗaiɗaikun waɗancan rubuce-rubuce, an yi ƙoƙarin haɓaka rubutattun ƙagaggun labarai na Hausa ta hanyar kafa hukumomi waɗanda za su samar da sabbin
littattafan ƙagaggun labarai, da kuma fassara wasu rubuce-rubuce. Waɗannan hukumomi da ƙungiyoyi da aka kafa, sun taka muhimmiyar rawa wajen samar
da sabbin littattafan ƙagaggun labarai.
Don haka a nan, za mu kalli haɓakar waɗannan littattafai da
fuskoki biyu, wato ta fuskar hukumomi da kuma ƙungiyoyi.
2.3 Gudumawar Hukumomi/Kamfanoni Wajen Samar
da Litattafan Ƙagaggun Labarai
Tun
bayan da rubuce-rubucen Hausa suka fara bayyana, sai aka ga dacewar samar da
wani tsari wanda zai taimaka wa harkar rubuce-rubucen, wannan ya sanya aka fara
kafa hukumomi da kuma kamfanoni domin samar da ɗab’i. Waɗannan hukumomi sun yi hoɓɓasa wajen ɗaukar nauyin da aka ɗora musu, daga cikin
su kuwa akwai:
2.3.1 Hukumar
Gudanarwa ta Makarantar Midil Katsina
An
kafa wannan Hukuma a shekarar 1927, kuma ta yi nasarar samar da wasu
littattafai waɗanda suka haɗa da:
i. Hausa
Stories na Malam H.B.G. Nuhu.
ii. Littafin
Karatu na Hausa na Malam Bello Kagara.
iii. Takobin
Gaskiya na Malam Nagwamatse.
2.3.2 Hukumar
Fassara (Translation Bureau)
An
kafa ta a shekarar 1927, kuma ta samar da littattafai da dama, kamar yadda Maƙera (2009) da Lawan
(2011) suka bayyana a cikin Abu Sabe (2013:1-5).
Daga cikin littattafan da aka samar a ƙarƙashin wannan hukuma
sun haɗa da:
i. Dare
Dubu da ɗaya (1933) na Mamman
Kano da Frank Edger
ii. Littafin
Hausawa da Maƙwabtansu
iii. Labaru
Na Da da Na Yanzu (1931)
iɓ. Fassara
littafin kiwon lafiya (1931) (Muktar, 2004:18).
A
cikin shekarar 1933 ne aka canja sunan daga Hukumar Fassara zuwa Hukumar
Talifi, wato Literature Bureau a Turance. An yi hakan saboda la’akari da ayyukanta ba su tsaya a fassara ba, har da sanya
gasa domin samar da littattafan ƙagaggun labarai. An naɗa Dr.
R.M.
East a matsayin Shugaba, sannan an samar da wasu littattafai a yayin gasar
farko da Hukumar ta sanya, musamman guda biyar da suka yi nasara waɗanda suka haɗa da:
i. Ruwan
Bagaja (1933) na Malam Abubakar Imam.
ii. Ganɗoki (1933) na Malam
Bello Kagara.
iii. Shehu
Umar (1933) na Malam Abubakar Tafawa Balewa.
iɓ. Idon
Matambayi (1933) na Malam Muhammadu Gwarzo.
ɓ. Jiki
Magayi (1933) na John Tafida da R.M. East.
2.3.3 Kamfanin
Gaskiya Ta Fi Kwabo
An kafa wannan
kamfani a shekarar 1945, musamman la’akari
da aka yi da yadda Gwamnatin Mulkin Mallaka ta Arewacin Nijeriya ta zaɓi ‘yan Arewa a shekarar 1939 domin su taimaka a cikin yaƙin duniya na ɗaya,
saboda buƙatuwar a yawaita
labaran yaƙi ta taso. Wannan
Hukuma, an naɗa Alhaji Abubakar Imam ya zama Edita; yayin da Mr. Rupert M.
East ya zama mataimakinsa. Daga shekarar da aka kafa ta, wato 1945 zuwa ƙarshen 1949 ta samar
da littattafai kamar:
i.
Ikon Allah na Dr. R.M. East da Alhaji Abubakar Imam.
ii.
Kyaftin Makama na Abdulkadir Makama.
iii.
Zamanin Nan Namu na E.M. Rimmer da Ahmadu Ingawa.
iɓ. Bala
Da Babiya na Nuhu Bamalli.
ɓ.
Mango Park Mabuɗin Kwara na Alhaji
Nuhu Bamalli.
ɓi.
Yawon Duniya Hajji Baba na Alhaji Abubakar Tunau Mafara ya fassara
(Abu-Sabe, 2013:7, Mukhtar, 2010:19).
2.3.4 Hukumar
NORLA (Northern Region Literature Agency)
An kafa wannan
hukumar a shekarar 1953, kuma aka damƙa ta ga Alhaji
Abubakar Imam; domin ya gudanar da azuzuwan yaƙi da jahilci da kuma
samar da littattafai don waɗannan azuzuwan. Wannan Hukuma, ta ci gaba da gudanar da
ayyukanta har zuwa shekarar 1959, lokacin da aka rushe ta aka mayar da aikinta
zuwa Kamfanin Gaskiya. A tsakanin waɗannan shekaru, wato daga shekarar 1953 zuwa
1959, wannan Hukuma ta samar da littattafai guda shida (6), waɗanda suka haɗa da:
i. Hali
Zanen Dutse na Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar na III.
ii. Littafin
Addini na Alhaji Halliru Binji.
iii. Tarihin
Fulani na Wazirin Sakkwato Alhaji Junaidu.
iɓ. Littafin
Mamaki na Abdullahi Maƙarfi.
ɓ. Littafin
Mafarki na M.M. Kumasi.
ɓi. Motsi
Ya Fi Zama na Malam Aminu Kano, da sauransu. (Mukhtar, 2010:20).
2.3.5 Hukumar
Northern Nigerian Publishing Company NNPC
Wannan Hukuma an kafa
ta a shekarar 1960, kuma ta yi hoɓɓasa wajen samar da littattafai. Cikin
littattafan da ta samar sun haɗa da:
i. Nagari
Na Kowa (1959) na Jabiru Abdullahi.
ii. Tauraruwa
Mai Wutsiya (1969) na Umaru Dembo da sauransu. (Yahaya, 1988:213)
Bayan
haka, a cikin shekara ta 1981 wannan Hukuma ta sa gasar ƙagaggun labarai inda
ta buga uku daga cikin waɗanda suka yi nasara.
i. So
Aljannar Duniya (1980) na Hafsatu Abdulwaheed
ii. Ahmadi
Na Malam Amah (1980) na Magaji Ɗanbatta
iii. Mallakin
Zuciyata (1980) na Sulaiman Ibrahim Katsina.
Haka
kuma baya ga waɗannan kamfanoni da
hukumomi an samu wallafe-wallafe da dama a cikin shekarun 1970, misali:
i. Dare Ɗaya na Abdullahi Ka’oje wanda aka buga a shekarar 1973.
ii. Kitsen
Rogo na Abdulƙadir Ɗangambo wanda aka buga a shekarar 1978 da dai sauransu. (Mukhtar, 2010:20)
2.3.6 Hukumar
Al’adu Ta Arewa (Federal Department of
Culture)
Wannan Hukuma an kafa
ta a shekarar 1982. Ita ma ta yi ƙoƙari wajen samar da
littattafan ƙagaggun labarai, cikinsu akwai:
i. Turmin
Danya (1982) na Sulaiman Ibrahim Katsina.
ii. Tsumagiyar
Kan Hanya (1982) na Musa Muhammad Bello.
iii. Ƙarshen Alewa Ƙasa (1982) na Bature
Gagare.
iɓ. Zaɓi Naka (1982) na
Munir Mamman Katsina.
Baya
ga waɗannan, a shekarar
1984 wata al’adar rubuce-rubuce
na ƙaggagun littattafai ta sake kunno kai
wadda Malumfashi (1984) ya kira su da ‘Adabin Kasuwar Kano’, wato Kano Market
Literature a Turance. An samu wani jigo na soyayya wanda ya yi tasiri sosai da
sosai a cikin wannan adabin. Daga cikin waɗanda
suka
share fage akwai irin su littafin:
i. Rabin
Raina (1984) na Talatu Wada Ahmed.
ii. Soyayya
Gamon Jini (1986) na Ibrahim Hamza Abdullahi.
iii. In
Da Rai (1987) na Idris Imam.
iɓ. Budurwar
Zuciya (1987) na Balaraba Ramat Yakubu.
ɓ. Kogin
Soyayya (1988) na A.M. Zahraddeen.
ɓi. Idan
So Cuta Ne (1989) na Yusuf M. Adamu (Muktar, 2010: 21).
2.4 Kafa
Ƙungiyoyin Marubuta Ƙagaggun Labarai Na
Hausa
Bayan
ɓullowar Adabin
Kasuwar Kano a 1984, kamar yadda Malumfashi (1984) ya raɗa wa suna, sai ƙagaggun labarai suka
fara yawaita, musamman ma waɗanda suke da jigon soyayya. Wannan sai ya haifar da
kakkafa ƙungiyoyi na marubuta daban-daban. Mukhtar (2004:27), ya
jero ire-iren ƙungiyoyin da aka samar tun a wancan lokaci, cikinsu
akwai:
i. Ƙungiyar Raina Kama.
ii. Ƙungiyar Marubuta ta
Himma.
iii. Ƙungiyar Marubuta ta
Mikiya.
iɓ. Ƙungiyar Marubuta ta Ɗan haƙin da ka Raina.
ɓ. Ƙungiyar Marubuta ta
Soyayyar Zamani.
ɓi. Ƙungiyar Marubuta ta
Kukan Kurciya.
ɓii. Ƙungiyar Marubuta ta
Nijeriya (ANA) da sauransu.
Kafa waɗannan ƙungiyoyi ya haddasa
samuwar tarin marubuta mata da yawan gaske waɗanda littattafansu suka mamaye
kasuwannin ƙasar Hausa.
2.5 Wasu Cikin Littattafan Ƙagaggun Labarai Na
Hausa da Marubutunsu a Yau
Nayaya
da Baba (2018:54) sun haƙaito ire-iren littattafan ƙagaggun labarai na Hausa, cikin waɗannan litattafan akwai:
i. In
da Alƙawari (1992) na Bala Anas Babinlata.
ii. Duniya
Sai Sannu (1997) na Ado Ahmad Gidan Dabino, MON.
iii. Mafarkin
Khadija (2014) na Maimuna Idriss Sani Beli.
iɓ. Rayuwar
Bilkisu (2016) na Ayuba Muhammad Ɗanzaki.
ɓ. Firgita
Samari (2005) na Kabir Yusuf Anka.
ɓii. Amon
‘Yanci (2013) Halima Ahmad Matazu.
ɓiii. Jarrabi
(2014) na Abubakar Auyo.
ɗ. Me
Zan Yi Da Ke (2016) na Maryam Rabi’u
Ado.
ɗi. Marubuciya
(2019) na Jiddah Haulat Nguru.
ɗiii. Rumaisa
(2014) na Fauziyya D. Suleiman.
ɗiɓ. Adon
Dawa (2011) na Jamila Umar Tanko.
Idan
an dubi waɗannan littattafai, za
a ga mafi yawan jigonsu ya karkata ne a kan soyayya (duk da akwai waɗanda ba jigon soyayya
suke ɗauke da su ba),
wannan shi ya ƙara tabbatar da sauyin jigo da aka samu tsakanin wallafe-wallafen baya, da waɗanda
suka tsiro daga shekarar 1984, da kuma waɗanda
ake haifa a yanzu. Wannan kuwa na da alaƙa da yanayin da aka samu na sauyin zamani da kuma wanzuwar
baƙin al’adu a cikin al’adun Hausawa.
2.6
Marubuta Ƙagaggun Labaran Hausa
Kafin mu kawo marubuta ƙagaggun labarai na
Hausa, ya kamata mu bayyana ma’anar marubuci. Nayaya da Baba (2018:53) sun
hakaito ma’anar marubuci daga masana. Misali, Wikipedia ta bayyana da cewa,
"Marubuci shi ne wanda yake amfani da rubuta kalmomi ta hangar mabambantan
salo da dabara domin sadarwa ta hanyar hikimarsu". A wani wurin kuma, ta
bayyana da cewa, "Marubuci shi ne mai shirya mabambanta ayyukan adabi da
rubutun hikayoyi kamar rubutattun labaru, gajerun labarai, tatsuniyoyi,
wasanni, tsara labarai, insha'i da kuma rahotanni da labarai, da muƙalu waɗanda suka yi dai-dai
da ra'ayin jama'a. Rubutun marubuta ana buga shi a ɗaukacin wuraren watsa
labarai".
Collins English Dictionary ta
bayyana da cewa, "Marubuci shi ne wanda yake rubuta littattafai, labarai,
da muƙalu a matsayin aiki".
Kafar bayanai ta Difference
Between ta bayyana marubuci da "Shi ne wanda yake rubuta littafi, muƙala, da kuma dukkanin
akin adabi".
Shi kuwa Gidan Dabino
(2006:1) ya bayyana marubuci da,
"Marubuci shi ne wanda ta hanyar amfani da fasahar rubutu yakan ƙirƙiri wani yanayi na
gaske ko na almara ko tunani ya kuma yi amfani da shi don gina wasu mutane da
abubuwa wadanda yake amfani da su don isar da sako ga al'ummar da ke karatun
rubutunsa. Shi wannan sako ana tsara shi ne ta hanya ta musamman mai cike da
hikima da hazaka don isarwa a saukake, kamar ta hanyar yin amfani da haruffa
zuwa kalmomi zuwa jimloli zuwa siɗarori da shafuka har zuwa cikakken
littafi".
Nayaya
da Baba (2018: 55) sun jero wasu daga cikin marubutan ƙagaggun labarai na
Hausa. Misali;
i. Bilkisu
Ibrahim Nabature.
ii. Zuwaira
Isa.
iii. Fauziyya
D. Suleiman.
iɓ. Hadiza
Nuhu Gudaji.
ɓ. Naja’atu Haruna Saleh.
ɓi. Muhammad
Lawal Barista.
ɓii. Maryam
Kabir Mashi.
ɓiii. Abubakar
Auyo.
iɗ. Nura
Sada Nasimat.
ɗ. Zaidu Barmo Katsina da sauransu.
3.0 Nazarin
Kura-kurai A Wasu Littattafan Ƙagaggun Labarai Na
Hausa
Babu shakka littattafan ƙagaggun labarai na
Hausa cike suke da kura-kurai ta fuskoki da dama, samuwar waɗannan kura-kuran kan
juya saƙon da aka nufa, ko kuma a kasa fahimtar abin da ake son
bayyanawa. Misali, idan aka zo rubuta waɗannan jumlolin:
Ba shi ya ci (giɓe
him let him eat), ko
Bashi ya ci (He was credited).
Ya ƙi ya je (He refuse to
go), ko Yaƙi ya je (He went for a war).
Ta kai ya wuce (He
passed through it), ko Takai ya wuce (Takai has passed).
Kusato (Come
close), ko Ku sato
(Go and steal).
Ka bari ya shiga (Let him enter), ko Kabari ya shiga (He entered graɓe).
Da wa ya raba? (With
whom he distributed?), ko Dawa ya raba (He distributed some corn). (Nayaya da Baba, 2018:53).
Idan aka lura da waɗannan misalai da ke
sama, za a ga haɗe kalma a yayin
rubutawa ko rabewa shi ne zai bayyana ma’anar abin da ake son faɗi. To idan aka yi
kuskure wajen rubuta abin dab a shi ake nufi ba, to ma’anar ce za ta sauya zuwa
wata ma’ana wadda ba ita aka nufata ba. Akwai kuma kalmomin da wasu jimlolin da
tsarin sauti ko hawa da sauƙar muryya ne yake tantance su, sai a
fahimci abin da ake son nufata. Misali:
Mace= A mace na ganta
jiya.
Cuta= Cuta ta kama
shi.
Wuri= Kowa ya zo da
wuri.
Tasa= Tasa ya bayar.
Shayi= Ina shayinka?
Sauke= Allah ya sauƙe ta lafiya.
Wata= An ga wata.
Nasara= Nasara ya
samu. (Na-Sara).
Fashi= Sun yi
fashi. (Baba, ba a buga ba).
A wannan nazari, an taƙaitu zuwa ga
kura-kurai guda biyar, wanda duk abin da ake magana a kai, to misalinsa kawai
za a nuna koda akwai wani kuskure a nan.
3.1 Rashin Sanya Alamomin Kyautata Rubutu
Babu shakka rashin sanya alamomin
kyautata rubutu bisa ƙa’ida kuskure ne wanda hakan kan haifar da gushewar saƙon da marubuci yake
son isarwa a littafinsa. Alamomin kyautata rubutu sun haɗa da: Aya, Waƙafi, Karan-Ɗori, Alamar Motsin
Rai, Alamar Tambaya, Ruwa Biyu, Waƙafi Mai Ruwa, Zarce,
Baka Biyu da sauransu. Ga wani wuri da ba a sanya su ba:
Rahma tace dan wannan me saukine ga dady
yana zuwa ai sai
mutambayeshi.....................
(Tababa na 1, Shari na 21,
na A'isha Abdallah Bagwanje).
Cikin wannan misalin da ya gabata, ba
a sanya alamomin zancen wani. Ga yadda rubutun ya kamata ya kasance:
Rahma
ta ce, "Dan wannan me sauƙi ne, ga Daddy
yana zuwa, ai sai mu tambaye
shi....................".
Kamar yadda wasu lokuta ba a sanya
alamomi a muhallansu, haka kuma a wasu wuraren ma ana sanya su alhali bai
cancanci a sanya ba. Misali:
Tsabar haushi ma ta rasa me za
ta ce masa ta ji daɗi.
Wato ma abin haka ne, ka-fin bikin
ba abin da bai
ce mata ba akan shi ba abinda ya
shalle shi da auren
haɗa wani kin zuwa
zance. Namiji ke-nan....
(Aaliyah na Azeezah Idris Gombe, shafi
na 225).
A nan, ba a sanya alamar Karan-Ɗori a tsakanin waɗannan kalmomi ‘kafin’
da ‘ke nan’, kamar yadda Marubuciyar littafin ta sanya. Sannan a shafin dai,
akwai inda ta rubuta ‘ya ce’, sai ta sanya Karan-Ɗori a tsakani kamar
haka ‘ya-ce’,
wanda duk
waɗannan kuskure ne.
3.2 Haɗe Kalma ko Rabawa a Muhallin da Bai Dace Da
Yin Hakan Ba
Haɗe kalma a muhallin
rabewa, ko rabe kalma a muhallin haɗewa na daga cikin kuskuren marubuta a yau,
hakan kuma na sauya ma’anar kalma ko kuma ma a kasa fahimtar saƙon da marubucin yake
son isarwa. Ga misali:
Bayan da na dawo ne Hajiya ta
saka muka fara jin
gidan rediyo, fara jin da mu kai shi ne wai anyi hatsari
a can Katsina mota biyu sun haɗu…..
(Sauyin Allah na Raihanat
Aliyu S.Rafi Azare, shafi na 25).
A nan, an haɗe kalmomin nan,
maimakon ‘anyi’
maimakon ‘an yi’.
A Hausa, akwai (W) iri biyu, jakada
da ɗafa ƙeya. Cikin su kowacce
akwai yadda ƙa’ida ta bayar a rubuta. Ita ɗafa ƙeya (W), tana zuwa a
jikin kalmar da aka yi wa ɗafin, yayin da jakada (W) take zuwa a rabe. Ana rarrabe
‘jakada w’ da ‘ɗafa ƙeya w’ da cewa shi
kullum ɗauke yake da karin
sautin ƙasa (\) kuma ba ya iya ɗaukar ɗafi ko a raɓa masa wata ƙwayar ma’ana.
(Yakasai da Mu’azu, 2010). Misali:
i. Usman ya tsone wa Ali idanu.
ii. An cuna wa ɓarawo kare.
iii. Na saya wa Sadiƙ keke.
To amma idan ‘w’ ta zo a matsayin ɗafa ƙeya ko gaɓar kalma, musamman ga
kalmomin aikatau, ana haɗe ta da kalmar da ta
zo da ita. A nan kalmar tana tashi ne a matsayinta na aikatau ta koma suna ɗan aikatau. Misali:
i. Yana sayarwa idan
ana buƙata.
ii. ‘Yan tawaye sun
daɗa kutsawa.
iii. Maryam tana
rubutawa da kyau. (Sa’id, 2004:13-14, Wurma, 2005:89-90)
Amma da yawa cikin marubuta ba sa
la’akari da muhallan bayyanar su. Ga wani misali:
..., amma ban nunawa Johara na ji haushin abinda ta
faɗa ba, muka ɗan yi hirar mu ba yabo ba fallasa,
sannan na yi mata sallama ta taho gida.
(Jininmu Ɗaya na Abida
Muhammad).
Amma
bisa ƙa'ida, ga yadda ya kamata ya kasance:
..., amma ban nuna wa Johara
na ji haushin abin da ta
faɗa ba, muka ɗan yi hirar mu ba yabo ba fallasa,
sannan na yi mata sallama ta taho gida.
3.3 Rashin Kula Da
Inda Ake Tashi Da Babban Harafi
Akwai wurare da wajibi ne a tashi da
babban harafi, misali inda aya ta bayyana da kuma duk inda aka samu sunan yanka.
A wasu lokutan marubuta ba sa la'akari da waɗannan wurare, maimakon ƙaramin harafi; sai su
rubutu da ƙaramin harafi, wanda kuma ƙa'ida ita ce farawa
da babban harafi. Misa, duk inda Aya ko
Alamar Tambaya ko Alamar Motsin Rai ko Alamar Zancen Wani suka fito, to harafin
farkon da zai zo, babba ne. Ga wani misali:
Ɗayan ya ce, “alhaki
dai ba a kanmu yake ba, yana
wuyan waziran da suka sa muka aikata haka.”
(Tekun Labarai na ɗaya, 2015, shafi
na78. Ɗanladi Z. Haruna).
A nan, farkon kalmar da ta zo a
cikin wannan alama, babba ya kamata ta zo, saɓanin yadda Marubucin ya rubuta.
Haka zalika, dukkanin sunan yanka
ana rubuta harafin farko ne da babban harafi, amma za ka iske wasu cikin
marubuta na farawa da ƙaramin harafi. Misali:
Sai
dai ni na kasance mai murna. na gane
cewa Muhammad
(S.A.W) annabi ne.
(Ɗan Musulmi 2014 na
Rahma Abdulmajid)
A nan wurin, an samu kura-kurai
guda biyu, amma wanda muke magana a kansa shi ne tashi da babban harafi a sunan
yanka, to a nan, Annabi yana komawa kan Muhammad (S.A.W), ke nan ya kamata ya
zama kamar haka:
Sai dai ni na kasance mai murna. na gane
cewa Muhammad (S.A.W) Annabi ne.
Ga wani misali:
Hadiza ta harare ta ta ce, "a'a kin
manta Allah
Talatu ba na son rainin
wayo, malam Balaraben
me, Me zanci da shi?"
(Babban Dare na 1,
na Amina Dauda Abubakar).
Maimakon haka, ga yadda ya dace a
rubuta:
Hadiza ta harare ta ta ce,
"A'a kin manta Allah
Talatu ba na son rainin wayo, Malam Balaraben
me, me zan ci da shi?"
3.4 Hargitsa Kalmomin Dirka
Kalmomi ne ‘yan ƙanana waɗanda suke taimaka wa
jimloli su dire sosai da sosai. Kalmomin dirka da aka fi sani, su ne: ‘ne’ da
‘ce’ da ‘ke nan’.
A Hausa, ba a liƙa wa kalmomin dirka
kowace irin kalma walau a gaba ko a baya. Duk inda suke, suna fitowa ne su kaɗai. Ga misali:
ni ne amma ba nine ba
ke ce amma ba kece ba
ke nan amma ba kenan ba (Wurma, 2005:63).
Marubuta da dama ba sa la’akari da
muhallan sanya waɗannan kalmomi na
dirka, wato su na sanya su a hargitse ko kuma su haɗe su da kalmar da ta
zo kafinta. Misali:
Alhaji ya ce, “Ba ita bane gata
nan”.
(Sauyin Allah na Raihanat
Aliyu S.Rafi Azare, shafi na 27).
A nan, an samu kura-kurai guda
biyu, na farko dirka ‘ce’ ya kamata a sanya maimakon ‘ne’, na biyu kuma sai aka
haɗe su, wanda a rabe ya
kamata su a rubuta su.
In ba wata mai matsayi bace sai kaga ana yi maka
Kallon biyu ahu.
(In Da Alƙawari, shafi na105,
na Bala Anas Babinlata).
Idan an lura, za a ga kalmomin ‘ba’
da ‘ce’ ba a haɗe ya kamata su zo ba,
kamar yadda kalmomin ‘ka’ da ‘ga’ su ma ba a haɗe suke ba.
A wasu muhallan kuma za a ga
marubuta kan sanya dirka, jinsin namiji a muhallin da jinsin mace za a sa wa.
Misali:
Shekarata goma sha huɗu amma idan kika ganni sai ki ce
‘yar
shekara sha bakwai ne,…..
(Sauyin Allah na Raihanat Aliyu
S.Rafi Azare, shafi na 26).
3.5 Sanya Alamar Hamza A Muhallin Da Ba Nata Ba
Alamar Hamza waƙafi ne da ake sanyawa
a saman gaɓar kalma (ba a ƙasa ba) domin rabawa
tsakanin gaɓar da ta ƙare da wasali da kuma
maƙwabciyarta
da ta farad a wasali (ba a amfani da wannan alama a farkon kalmar da ta fara da
wasali). Ana amfani da wannan alama ne saboda dalilai biyu: Na farko domin nuna
cewa ba ɗaurin wasali ko
tsawon wasali ake nunawa ba, na biyu kuwa domin sauƙaƙa furuci. (Bunza
2002:184-186). Misali: Ma’ana, da’awa, mu’amala, a’a, ba’a, mu’amala, ɗa’a, Sa’adatu,
Mu’azu, ɗabi’u.
Marubuta ba su fiye kula da
muhallan wannan alama ta Hamza ba, hakan ya sanya suke sanya ta inda bai dace
ba. Misali:
“Student lafiya ba’a zo an ɗauke ki bane?”.
(Sauyin Allah na Raihanat
Aliyu S.Rafi Azare, shafi na 5).
4.0 Kammalawa
Cikin abin da ya gabata a
wannan takarda, an bayyana ma’anar ƙagaggun labarai, taƙaitaccen tarihin
samuwarsu, wasu cikin marubutansu da wasu cikin littattafan ƙagaggun labarai na
Hausa. A cikin takardar, an kawo wasu jimloli masu ma’ana mabambanta domin
fayyace misalai, sannan aka bayyana yadda ma’anar kowace daga ciki. A takardar,
an zaƙulo wasu misalai daga cikin litattafan ƙagaggun labarai na
Hausa, sannan aka bayyana yadda ya dace su kasance a matsayin daidai. Lalle
kula da kiyaye waɗannan ƙa’idoji na rubutu zai
sanya rubuce-rubucen litattafan ƙagaggun labarai na
Hausa su ƙara armashi. Ke nan, mayar da hankali ga kiyaye waɗannan ƙa’idoji wajibi ne ga
marubuta da masu aikin ɗab’in littattafai na
Hausa.
MANAZARTA
Tuntuɓi masu takarda.
1 Comments
Wannan aiki ya ƙayatar matuƙa, da fatan Allah ya ba mu ikon amfani da gyararrakin da muka koya a ciki.
ReplyDeleteSani Adamu Faskari
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.