Hausa language and most Hausa people are geographically found in the north western part of Nigeria and the southern part of Niger republic around MaraɗI, Ƙonni, Damagaran etc. This region falls within the Sudan savannah belt and the Sahel, a region that records low amount of rainfall which is below 100 cm annually. Coupled with the high poverty level in the region, there is the occurrence of famines from time to time. ‘Yar Gusau occurred in 1943, ‘Muɗa’ in 1953 and in the year 1973, the was region was afflicted with yet another famine called ‘Bankaura’. Another food shortage coined ‘Yar Buhari occurred in 1985. This plague continued to afflict the area once in almost every decade.
Nason Yunwa a
Cikin Adabin Baka na Hausa
DR. MUSA
FADAMA GUMMI
Email: gfmusa24@gmail.com
Phone No.: 07065635983
Tsakure
Adabi madubi ne ko hoto na rayuwar al’umma.
Abu ne da ya game dukkanin rayuwar al,umma musamman fasaharsu, da hikimominsu.
Fasahohi da hikimomin al,umma kan haɗa da maganganun hikima kamar kirari,
da take, da habaici, da gugar zana, da baƙar
Magana, da Karin Magana, da tatsuniyoyi, da labarai, kai har da uwa uba, waƙa. Waɗannan
wasu ne daga cikin rassa na adabin baka.Yunwa kuwa wani hali ne na rashin
wadataccen abinci, mai gina jiki, ga yawancin jama’a na wata al’umma.Ƙasar Hausa ta sha fama da lamarin
yunwa a lokuta daban-daban da suka gabata. Misali, ‘yar Gusau yunwa ce da ta
addabi wani sashe na ƙasar
Hausa a shekara ta 1943. An yi fama da yunwar Muɗa
a shekara ta 1953. Yunwar Bankaura kuwa a shek arar 1973. ‘Yar Buhari, ta faɗawa ƙasar
Hausa ne a shekara ta 1984. Nufin wannan muƙala ne ta yi tsokaci kan yadda lamarin yunwa ya yi naso a
cikin adabin baka na Hausa, musamman yadda ya kutsa a cikin labarai, da
tatsuniyoyi, da Karin Magana, da almara, da kirari, da kuma waƙa ta baka.
1.0 Gabatarwa
Hausawa mutane ne da suke zaune a wani sashe
na Nijeriya wato Arewa maso Yamma, da kuma wani sashe na Kudancin ƙasar Nijer. Wannan yanki da Hausawa
suke zaune ya faɗo ne a Sahel, wuri mai fama da
matsalar ƙamfar ruwan
sama daga lokaci zuwa lokaci, da kuma yankin Sabana ta Sudan, wanda ke maƙwabtaka da yankin Sahel. Sakamakon ƙamfar ruwan sama da yankin kan samu,
da kuma matsanancin talauci da ya yi wa yankin katutu, ya sanya wani lokaci
yunwa kan addabi mutane daga lokaci zuwa lokaci. Ana iya hasashen cewa bayan
kowace shekara goma sai an sami aukuwar yunwa ko ƙarancin abinci a wannan yanki. Yunwa da talauci ɗanjumma ne da ɗanjummai. Wanzuwarsu ko kasancewarsu a
tattare da al’umma kan jefa ta cikin wani hali mawuyaci da mutane kan tagayyara
a kuma galabaita. Idan lamarin ya ta’azzara, har ‘yan mace-mace akan samu a
cikin al’umma musamman dangane da ƙananan
yara da tsofaffi.
Ganin cewa haƙiƙa
wannan lamari kan auku a cikin wannan al’umma ta Hausawa wadda take al’umma ce
mai hikima da basira tare da zalaƙa,
ake ganin ya kyautu a yi waiwaye a cikin adabin baka na wannan al’umma domin a ƙyallaro yadda lamarin na yunwa ya yi
tasiri ko yadda yunwa ta shiga, ta kuma bazu a cikin adabin na baka. Ƙudurin wannan muƙala ne ta kalli yadda yunwa ta kutsa a
cikin adabin baka na Bahaushe musamman abin da ya shafi labarai da tatsuniya,
da almara, da Karin Magana, da kirari, da kuma waƙar baka waɗanda suke rukunai ne ko sassa na
adabin baka.
1.2 Ma’anar Adabi
Kalmar Adabi, kamar yadda masana irin su Dangambo
(1984:1), da Umar (2003) suka bayyana, ta samo asali ne daga kalmar Larabci
watau ‘Adab’. A lokacin jahiliyya kalmar tana nufin ‘walima’ ko ‘liyafa.
Haka ma tana nufin halin ɗa’a, fasaha ko ƙwarewa.
Daga bisani kalmar ta ‘Adab’ ta ɗauki wata ma’ana ta dukkan abin da aka rubuta na waƙoƙi
da labarai game da harshen Larabci. Ga dukkan alamu da wannan ma’anar ce kalmar
ta shigo cikin Hausa. Kalmomin Hausa ba su faye ƙarewa da baƙi
ba kamar yadda su ke ƙarewa
da wasali. Domin wannan ararriyar kalma ta dace da kalmomin Hausa sai aka saƙala mata wasali a gaɓar ƙarshe,
ta koma Adabi. A yanzu idan aka ce Adabi to ana nufin dukkan wani zance na
hikima da aka yi da harshen Hausa, wato sarrafaffen harshe da ya ƙunshi wata hikima ta musamman mai
bayyana rayuwar al’umma, (Umar, M.B. 2003). A taƙaice ke nan adabi shi ne madubi ko hoton rayuwa na
al’umma. Idan aka dubi abin da masana suka faɗa
dangane da ma’anar adabi, to kuwa ana iya bayyana cewa adabi abu ne da ya game
dukkanin rayuwar Bahaushe musamman fasaharsa da hikimominsa na baka da na rubuce.
Fasahohin nasa na baka ka iya haɗawa da maganganunsa na hikima kamar
kirari da take da habaici da gugar zana da baƙar magana da karin magana da waƙa da dai abubuwa makamantansu. Haka
kuma yana iya ƙunsar taɗoɗinsu da labarai da hikiya da almara da
tatsuniyoyi da sauransu. Wannan wasu ne daga cikin misalai na abubuwan da
adabin baka ya ƙunsa.
1.3 Ma’anar Yunwa
Masana daban-daban sun yi ƙoƙari
a wurare daban-daban, su bayyana abin da ake kira yunwa. A ƙamus na Longman cewa aka yi yunwa ita
ce tsananin rashin abinci ga jama’a masu yawa.
A cikin kundin Encylopidae
Brittanica, cewa aka yi yunwa ita ce matsanancin ƙarancin abinci a wani yanki ko
wata ƙasa
baki ɗaya, wanda ke sa a tagayyara
har ma da mace-mace.
Watts,
(1983:1) cewa ya yi yunwa tana nufin wani bala’i da kan shafi al’umma, wadda ke
haddasa ƙarancin
abinci ta yadda jama’a masu dama za su tagayyara.
Umar,
(1992:5) gani yake cewa yunwa ita ce matsanancin ƙarancin abinci. Watau mutane su rasa
abincin da zai wadace su.
Malumfashi,
(2002), cewa ya yi wasu za su ce ai ba komi ba ne yunwa face zafin ciki da
mutum kan ji idan bai ci abinci ba, ko rashin isasshen abinci mai sa ƙoshin lafiya. Haka ne amma
yunwa ta wuce nan. Duk wanda ya ɗauki
yunwa a matsayin rashin cin abinci ko ramewa saboda rashin ƙoshi to bai fahimci yunwa sosai
ba. A ganinsa yunwa ta haɗa da
talauci da fatara.
A tawa fahimtar, idan Bahaushe ya ce
yunwa to tana iya ɗaukar ɗaya daga cikin ma’anoni biyu. Na farko
dai tana nufin zafin cikin da mutum kan ji idan bai ci abinci ba na wani ɗan lokaci, ko da kuwa yana da abincin.
Ma’ana da zarar mutum ya ji yana matuƙar buƙatar abinci to kuwa yana jin yunwa.
Irin wannan yunwa ta yi daidai da abin da wani mawaƙin noma ya ce a wata waƙa tasa.
Jagora: Hunger
is very danger
If you are feeling hunger
It will make you anger.
Yara: Wai yunwa bala’i ta
In yazzan kana jin ta,
Zahin rai take sa wa.
(Alh.
Sani Da’aino Gyalange Waƙar Salihu Maibuhu).
Ɗaya ma’anar kuwa ita ce hali na matuƙar ƙarancin abinci ga mafi yawan jama’a na wata al’umma wanda
ke sa a tagayyara, wani lokaci har da mace-mace. Irin wannan bala’i na yunwa ya
yi daidai da abin da wani mawaƙi
yake cewa:
Jagora: “Rani wanga ya yi rani
Ya sa maza lage,
Tafiya wagga ta yi nisa
Ta sa maza gaba
Yunwa wagga ta yi yunwa
Ta ba mu arkane
Ga mata da ‘yan ɗiya
Ka ji ƙatonta ya yi lalata
Ya ba ta wuri
Yara: Ya
tcere yana ta kai nai”.
Watau ke nan yunwa iri biyu ce, akwai ta al’ada wadda aka saba da ita yau da kullum da kuma ta bala’i wadda kan sami al’umma lokaci-lokaci.
Yanzu ya kamata a kalli yadda lamarin
yunwa ya kutsa cikin adabin baka na Hausa.
1.4 Labari
A tsawon lokaci, Hausawa suna da hanyoyi
na gargajiya waɗanda suke bi domin samun nishaɗi. Ɗaya
daga cikin hanyoyin samun nishaɗi a wurin manya shi ne ba juna labarai
na ban dariya, ko ta’ajibi, ko tausayi, wani lokaci ma labarun masu ban haushi.
Wani sa’ili akan ba da labarai ne na yaƙe-yaƙe, musamman na gwarzaye da suka rayu a
wani shuɗaɗɗen lokaci. Daga cikin ire-iren labaran
akwai wanda ke da tasirin yunwa a cikinsa.
Misali akwai wani labari da aka ce
zamanin yunwa wani magidanci ya fita neman abinci tun da safe. Ya yi ta ƙoƙarin yawace-yawace a dawa ko zai sami
ko ɗan ganyen da zai kawo wa
iyalansa su dafa to amma har yamma bai sami komai ba sai ganyen tafasa ɗan kaɗan. Mutumin ya kawo ‘yar tafasar a gida
domin a dafa a ci. Aka dafa tafasar, ‘ya’yansa suka ci tare da mahaifiyarsu
amma maigida bai samu ba saboda ƙarancin ganyen. Da maigida ya dawo daga
hira yana zaton zai sami tafasar ya ci, sai uwargida ta sheda masa cewa sun
cinye sarai. Maigida sai ya haƙura ya kwanta a cikin halin jin yunwa.
Da dare ya raba, uwargidan da yake tana da ɗan ƙoshi sai ta buƙaci maigida ya biya mata buƙata irin ta mata da miji. Da ta
tashe shi, ta ɗauko
hannunsa ta ɗora a kan al’aurarta, sai
maigida ya tashi, ya zabura da azama ya ce “Eh! Tafasa ce?
1.5
Tatsuniya
Tatuniya bisa ma’ana labarai ne da mutane ke ƙirƙirowa cikin azanci don su tarbiyantar da ‘ya’yansu da
kuma cimma wasu buƙatoci dangane
da al’umma ( Koko,2009:2). Galibi labaran na baka ne don haka a ka ake adana su
amma duk da haka an rubuta wasu a litattafai.
Akwai waɗansu tatsuniyoyi a cikin Littafi na
Tatsuniyoyi na Hausa wanda Frank Edgar ya rubuta a shekara ta 1911. A cikin
littafin akwai tatsuniyoyi har guda uku waɗanda
aka gina su bisa tubalin yunwa. A labarin farko, wani malami ne da matansa biyu,
da aka yi wata yunwa ba su samun abinci sai kaɗan kaɗan, malamin ya kira matarsa ɗaya wadda yake so ya ce da ita mu kama
kishiyarki, mu ba ta wani ganye ta ci ta zama akuya mu sayar da ita mu sayi
abinci, haka kuwa aka yi. Wannan tatsuniya tana nuni ne ga irin yadda ake kama
bisashe ko dabbobi ana sayarwa domin a sami kuɗin sayen abinci. Sauran tatsuniyoyin
guda biyu duk makamantan wannan da ta gabata ne.
1.6
Kirari
Kirari a cewar Kafin Hausa, (1997:99) shi ne
kalma ko kalmomi da akan faɗe su da wani salo na musamman don
kambama ko zuga ko girmama mutum ko wani abu.
Yunwa aba ce da ta daɗe tana addabar mutane don haka tana da
nata kirari da ake yi mata. Dubi wani kirari da ake yi wa yunwa.
“Allah tsare mu da yunwa mu dinga nisa da ita.
Ta bahuwa mai mahurin ƙarfe,
Sa dogo rama, sa gajere faɗin kai
Kisan ki ba jini sai hamma.
(Umar, 2003:79).
Kusan duk yunwar da aka yi a lokuta daban-daban da suka
gabata gwargwado kowace tana da kirarin da ake yi mata. Yunwar Hamada da aka yi
a wajajen shekara ta 1927 ana yi mata kirari kamar haka:
Ta malam ba ki da daɗi,
Sa maza barin gari ba su shirya ba
Mata ‘yan gata! Yau ga mata shiga dawa ba su
shirya ba
Sa ɗan’uwa
rufe ɗaki saboda ɗauraye
Ta malam sa ginar gidan tururuwa.
Wani misali na kirari da ake yi wa wata yunwa da ta
gabata shi ne wanda ake yi wa yunwar Banka4ura wadda aka yi a shekara ta 1973.
Bankaura mai bankar ƙatti
Ta banki Bala da Bawa kai har ma Balki
Ta banke su Tanko mai kayan ƙore.
Baya ga kirarin da ake yi wa yunwa, ana samun wasu mutane
masu yi wa kansu kirari su saka turken yunwa a ciki misali:
Sai ni ɗan
gidanmu ƙanen
wana,
Na Shehu wanda ba ya wasa da ciki
Allah tsare mu da yunwa mu dinga nisa da ita.
Wasu misalai na kirarin da ake yi wa yunwa su ne:
i)
Yunwa
mai mai da yaro tsoho.
ii)
Yunwa
a ba ki a huta.
iii)
Yunwa
maganin mugunyar dafuwa.
iv)
Ƙishirwa
ba ruwanta da wargi, karɓar rangwama sai yunwa.
v)
Gani
ba ci ba ne; da gani ci ne da Karen gidanmu ba shi kwana da yunwa.
vi)
Baƙin dare a kwana da yunwa, baƙar safiya a tashi da yaƙi.
vii)
Gwazama
ciyawar doki in yaƙi-ci ya kwana
da yunwa.
viii)
Itatuwa
abincin giwa in ta ƙi ci ta kwana
da yunwa.
1.7
Almara
Almara musamman irin ta kacici-kacici
ta ƙunshi faɗin
wani zance a cikin hikima inda za a buƙaci
mai sauraro ya gano abin da ake nufi da zancen, ya kuma faɗa. Misali:
Almara: Ƙulunƙulufita? Amsa: Gauta.
Akwai almara irin wannan inda yunwa ita ce ginshiƙi. Misalansu ya haɗa da:
i)
Tsumangiyar
kan hanya fyaɗe yaro fyaɗe babba.
Amsa: Yunwa
ii)
Gari
ɗaka yara kwana da yunwa
Amsa: Hauɗi
1.8 Karin Magana
A cewar Umar
(1987) Karin Magana wata dunƙulalliyar
jimla ce mai sassa biyu da ta ƙunshi
zunzurutun ma’ana idan aka yi bayani. Karin Magana wani muhimmin rukuni na
adabin baka da yunwa ta yi naso a cikinsa ta kuma taimaka wajen ginuwarsa da
bunƙasarsa. Dalilin wannan zance shi ne
cewa ana samun karin magana masu ɗan dama waɗanda aka gina su bisa tafarkin yunwa. Misalin waɗannan karin magana sun haɗa
da:
i)
Barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa
ii)
Ba a bar wa mayunwaci tsaron tuwo
iii)
Sa zuciya ga ci shi ke kawo yunwa
iv)
Komi tsananin yunwa ba a miya da anza
v)
Da wasa da yaro gara kwana da yunwa
vi)
Wanka da gari ba ya maganin yunwa sai
an sha
vii)
Daren tuwo ba kwana da yunwa ba ne
1.9
Waƙar Baka.
Waƙar baka bisa ma’ana wani zance ne na hikima ko Magana
wadda ake shiryawa ta hanyar tsara kalmomi zaɓaɓɓu kuma zaunannu, a rera su gutsure-gutsure cikin azanci
da salon armashi, tare da yin kiɗa da amshi don a isar da saƙo.
Waƙoƙin baka na Hausa suna da yawa da kuma
ire-ire ko nau’o’i. Akwai waƙoƙin sarauta da na jama’a da na maza ga
kuma waƙoƙin sana’a. A cikin ire-iren waɗannan waƙoƙi ana samun ɓirɓishin yunwa. Akasari an fi samun yunwa
ta yi tasiri sosai a cikin waƙoƙin noma. A cikin waƙoƙin
na noma ana samun turke na yunwa. Irin waɗannan turke na yunwa da ake samu a
cikin waƙoƙin na noma ne za a duba.
Daga cikin muhimmancin waƙoƙin
noma akwai zaburar da manoma don su duƙufa
ku su himmatu ga aiwatar da sana’arsu ta noma. A cikinsu akan nuna cewa wanda
duk ya zama rago to kuwa zai fuskanci matsalar yunwa. Wannan ya ƙara sa ake samun turken yunwa a cikin
waƙoƙin
baka na noma.
A cikin wata waƙa
ta Amali Sububu yana cewa:
Jagora: Sarki ya yi doka a bar waƙar manoma,
In
ba mu garza su
Ba aiki sukai ba.
‘Yan amshi: Dan nan am mafarin hatsi su katse ma gwarza.
. (Makaɗa Amali: Sububu: “Mai batun yaƙi da sabra”).
Da zarar kuwa hatsi suka ƙare wa gwarzayen noma to yunwa ta yi
sallama ke nan. Da haka ne ake samun mawaƙan
ko makaɗan noma suna saka turken yunwa a cikin
waƙoƙin
nasu. Misali, a cikin wata waƙarsa,
Makaɗa Sani Ɗan’aino Gyalange yana cewa:
“Rannan da yunwa tah hita
Rannan da yunwa tah hito
Sai nig ga ta tare godabe
Kuma ga mutane nan tahe,
Kuma ga mutane nan tahe
Da masu gero sunka zo,
Tac ce ma mai gero wuce
Da masu maiwa sunka zo,
Tac ce ma mai maiwa wuce
Da masu dawa sunka zo,
Tac ce ma mai dawa wuce
Da masu wake sunka zo
Tac ce ma mai wake wuce.
Da masu rogo sunka zo
Tac ce ma mai rogo wuce
Dukkan manoma sun wuce,
Saura masu tallaz zamani
Da ɗan
akwaku nai riƙe,
Daga rosuman sai mai zobe,
Sai godilib, sai rosuman
Ran da ta tcinkai tahe
Sai taɗ
ɗauki
sanda tat tarai
Wada yag gani yab bakace
Yad ɗauki
sayyun kudaku
Sai nij ji yunwa tay ƙyaci,
Wallahi yaro ka kuru,
Inda da taba kat taran
In na yi ma mugun bugu,
Kowa bai hana ma faɗuwa
(Makaɗa Sani Dan’aino Gyalange: Waƙar Shehu Mai Sunar Hatsi).
A cikin ‘Waƙar Shehu mai sunar hatsi’ ta Makaɗa Sani Ɗan’aino
wani ɗan waƙa yana cewa:
Ga yunwa tai ma raggo baki ɗaya
Yunwa tai ma raggo baki ɗaya
Taz zaka tai yi ma ɗaurin
kurkutu,
Kowag ga shi sai ya ce kamun doguwa,
Kai ni ca nikai ciwo na yakai,
Ba ciwo ba ne yunwa ah haka,
Dut ta bi shi ta tsotce yai tsawo
Yara na yi mai waƙa ya hito,
Ga dogo kashin yunwa ya hito
Mai cin gujjiyar naira ya hito
Ko wata mai dawo ko mai gujjiya
Ko mai kudaku komai gwantale,
Kat ta bari ya sa hannunai ciki,
Don in tab bari kwashewa yakai,
Ko jiya na hwaɗi
dug gun ‘yan uwa
Kor rage ɗan
tuwon dawa ko hura,
Don Allah ya hirkai bakin gida
Dogo mai cikin ɗauka
ya hito
Baki ca kakai ramin kwakware.
(Makaɗa Sani Dan’aino: Waƙar Shehu Mai Sunar Hatsi).
Waɗannan
ɗiyan waƙa suna nuni ga yunwa irin ta yau da kullum wadda ke sa
mutum ya ji cikinsa na zafi, ga kuma matuƙar
buƙatar ya ci abinci.
Yunwa irin ta gama-gari wadda ke
aukuwa sakamakon rashin wadatacce ruwan sama a lokacin damina ko sakamakon fara
ko wani mawuyacin hali na talauci, kan samu ambato a cikin waƙoƙin
na noma. Akwai misalai a cikin waƙoƙin Makaɗa
Amali Sububu, kamar haka:
Jagora: “Rani wanga ya yi rani
Ya maza lage,
Tafiya wagga ta yi
nissa,
Ta sa maza gaba,
Yunwa wagga ta yi nisa,
Ta ba da arune
Ga mata da ‘yan ɗiya,
Ka ji ƙatunta ya yi lalata,
Ya ba ta wuri.
Ya tcere yana ta kainai”.
Baya ga salon mutuntarwa da ke cikin
wannan ɗan waƙa ta Amali, ana kuma nuna turken ƙaura a lokacin yunwa. A cikin wata waƙar, Amali yana cewa:
Jagora: Kun gani yunwag ga na sa,
Mutum ya yi zamne
jangwam,
Yana magana cikin
zuciyatai ba a sani ba,
Sai ka ji zuciya tai,
Tana mai ebe-ebe
“Ashe yunwag ga na sa,
mutum ya gaza da mata,
Ya sa a yi mai jiƙo,
Yara: Ba ya ce mata tashi ga shi
(Amali Sububu: Mai shirin yaƙi da sabra).
Waɗannan
ɗiyan waƙa guda biyu suna nuna irin yadda a lokacin yunwa mutum
kan lalace, ya yi jangwam, ya shiga cikin kogin tunani mai zurfi ta yadda
zuciyarsa za ta riƙa yi masa saƙe-saƙe. Ɗaya
ɗan waƙar kuwa yana ɗauke ne da turken rowa a zamanin
yunwa. Irin wannan hali na yunwa kan sa mutum ya kasa ɗaukar wani nauyi nasa na ba iyali abinci, yadda har zai
ci Garin kwaki ba tare da ya ba iyalinsa ba.
A cikin wata waƙar, Amali yana cewa:
Jagora:
Ku yi noma da gaskiya,
Yara:
Don Allah ku hwanshi kanku
Jagora:
Inda dai Yab Buhari ta,
Yara:
Kowa ba bari takai ba,
Jagora:
Yunwa ta taho da gorori,
Ta iske maza
Duk ƙaton
da taƙ ƙumai ga wuya,
Sai a shantala,
Yara:
Sai ya hurce kwantagora,
Jagora: Dan nan ta waiwayo,
Yara: Ta ga ƙaton
da bai ɗaga ba,
Jagora: In tak ƙumai
bugu
Yara: Wajjen yamma za ya sauka
Jagora:
Ga hwa kudun muna ta yi
Yara: Amma ba a yi arewa
Jagora: Har na arewa sun biyo hanya,
Sun ɓata
ƙasa,
Yara: Sai shayi sukai na gaske
Jagora:
Ni dai ban san na gaske ba,
Yara:
Sai na sa dawo ga baki,
Jagora:
Kowac ce na gaske ne,
Yara:
In dai ba dawo ba ƙyale”.
(Amali Sububu: Noma baya saka rama).
A waɗannan
ɗiyan waƙa, baya ga yadda mawaƙin ya yi amfani da salon mutuntarwa, ya bayyana turken ƙaura wadda jama’a kan yi a lokacin da
yunwa ta addabe su. A ci gaba da nuna irin wannan turke na ƙaura ne Amali Sububu yake cewa:
Jagora: Yunwa
ta ci Adarawa,
Sun yo ga Gobirawa,
An iske Zamfarawa,
An zan mutum guda,
Yara:
Kowa ba ka jin ba’a tai.
Jagora: Sada ina ba’a take
Yara: Ƙato
bai ci yar raga ba,
Jagora Garba ina batun raha,
Yara: Ƙato
bai ci yar raga ba.
(Amali Sububu: Noma baya saka rama).
Akwai tarin waƙoƙi
baka da dama waɗanda yunwa da lamarinta ya yi tasiri
ko naso sosai a cikinsu Waƙoƙin sun haɗa da na sarauta, da na jama’a, da waƙoƙin
maza,da na sana’o’in gargajiya na Hausawa.
1.10
Kammalawa.
Wannan muƙala kamar yadda aka gani ta yi tsokaci
dangane da yadda yunwa, wadda kan addabi mutane, ta yi naso ko jirwaye a cikin
adabin baka na Hausa. Adabi kamar yadda masana suka faɗa madubi ne na rayuwar al’umma to kuma da yake yunwa wani
al’amari ne da jama’a kan fuskanta lokaci-lokaci. Ashe ba abin mamaki ba ne don
lamarin yunwa ya fito ɓaro-ɓaro
a cikin adabin baka na al’ummar Hausawa kamar yadda wannan muƙala ta nuna.
MANAZARTA
Tuntuɓi mai
takarda.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.