Ticker

6/recent/ticker-posts

Tasirin Sarkanci Kan Kayan Kamun Kifi Na Ƙabilun Nupe Da Jukun

 Sarkanci is an age long Hausa craft that is primarily concern with artisanal fishing which provides the much needed protein that the human body requires for its growth and development. Allah in His infinite bounties has enriched some part of Hausa land with quite a number of water bodies. These are in the form of rivers, lakes, streams, dams and ponds. There is abundant fish species stocked in these water bodies and a substantial number of people are engage in harnessing the fish resources. Due to the pattern of their occupation, the Sarkawa, a professional fishing people are migrants in nature as they move from one water body to another in search of livelihood. In the course of their migration, they move along with their local fishing gears. The host community tends to copy and learn from them a lot of water rituals, including the production and use of certain fishing gears. It is in the light of these that this paper wishes to discuss how Sarkanci has made impact on fishing among the Nupe and Jukun tribes most especially in the use of Hausa fishing gears and other water rituals.

kamun kifi

Tasirin Sarkanci Kan Kayan Kamun Kifi Na Ƙabilun Nupe Da Jukun

DR. MUSA FADAMA GUMMI
Email: gfmusa24@gmail.com
Phone No.: 07065635983

Tsakure

Sarkanci sana’a ce ta kamun kifi wadda wani rukuni na al’ummar Hausawa ta daɗe tana aiwatarwa a matsayin hanya ta neman abinci. Sana’ar tana samar da kifi, wata halittar ruwa da take ƙunshe da sinadarai da jikin Ɗan’adam yake buƙata domin ginuwa da inganta lafiyar jiki. Allah a cikin nasa iko ya albarkaci ƙasar Hausa da albarkatun ruwa kamar gulabe da tafukka da ƙoramu. A cikin wannan ruwa, Allah ya rayar da kifi nau’uka daban-daban. Saboda waɗannan albarkatu da Allah ya huwace wa ƙasar, ya sanya waɗansu jama’a suka duƙufa wajen tatsar albarkatun ruwa na ƙasar. Dalilin yadda yanayin sana’arsu ke gudana, Sarkawa mutane ne masu yawan yin ƙaura daga wannan wuri zuwa wancan domin aiwatar da sana’arsu. Wannan ne ya sanya duk inda suka tafi, suna zuwa ne tare da kayan aikinsu da kuma irin fasaharsu ta kamun kifi. A wuraren da suka yi ƙaura, masu masaukinsu kan koyi waɗansu abubuwa daga wurinsu kamar kwaikwayon kayan aikinsu da kuma waɗansu al’adu na ruwa kamar tsaraka. A kan haka ne wannan muƙala ta ƙuduri yin waiwaye domin ƙyallaro irin tasirin da sana’ar Sarkanci take da shi a tsakanin ƙabilun Nupe da Jukun musamman yadda suka kwaikwayi wasu daga cikin harkokin kamun kifi daga wajen Sarkawa.

1.0 Gabatarwa

 Sana’ar Sarkanci sana’a ce da ba ta gudana sai inda wadatar ruwa na gulbi ko tafki ko ƙorama yake, musamman inda ake samun wadatar halittar kifi a ciki. Sana’ar ta dogara sosai kan yin amfani da kayan aiki daban-daban. Kayan aiki na gargajiya da ake amfani da su wajen kamun kifi sun haɗa da koma da kalli da taru da unduruttu da gura da tsattsara da mashi da zago da gora da jirgi da dai sauransu. Sana’ar Sarkanci ba ta tsaya ga kamun kifi ba kawai, ta haɗa har da kambaɗar dabbobin ruwa kamar dorina da kada da ayyu da tsari da yuma da dai sauransu. Ana kama waɗannan halittu na ruwa ne domin abinci da kuma kasancewa ana amfani da wasu sassa na jikinsu wajen harhaɗa magungunan gargajiya na waraka daga cututtuka da kuma na biyan wasu buƙatun rayuwa. Sarkawa mutane ne da suka ƙware kan sha’anin ruwa kuma ba su da wata sana’a da ta shige kamun kifi da farautar ruwa. Hasali ma Sarkawa ko noma ba sa yi in dai akwai wadatar kifi. Idan har noman ya kama su, ba ya wuce noman shinkafa da suke yi a cikin fadamun da suke aiwatar da sana’arsu ta kamun kifi. Sarkawa mutane ne masu yawan yin ƙaura daga wannan shiya zuwa waccan inda ake samun wadatar ruwa da za su iya aiwatar da sana’arsu a ciki. A kan haka ne ake tarar da cewa ba a ƙasar Hausa kawai ba, a kowane yanki na arewacin Nijeriya da ma wasu sassa na Afirka ta yamma ana samun Sarkawa zaune a wuraren da ake kamun kifi. Wannan halayya tasu ta ƙaurace-ƙaurace ya sanya suka yaɗa fasahar wasu daga cikin kayan aikinsu na kamun kifi, da waɗansu al’adu na kamun kifi a tsakanin wasu al’ummomi da ke maƙwabtaka da ƙasar Hausa. A wannan fage ne wannan muƙala take son ta yi waiwaye domin ƙyallaro yadda Sarkanci ya yi naso a cikin sana’ar kamun kifi a al’ummomin Nupe da Jukun. Kafin yin haka, ya dace a duba asalin kalmar Sarkanci da abin da take nufi.

2.0 Tushe Da Ma’anar Sarkanci

 Bisa asali, kalmar Sarkanci ba bahaushiya ba ce. Asalinta daga kalmar ‘Sorko’ ne, wata al’umma ta daular Sanwai (Songhai). Al’ummar Sorko mutane ne da suka shahara matuƙa ga sha’anin su (kamun kifi) a kogin Kwara wanda ya ratso ƙasashe da dama na yammacin Afirka. Sana’ar su ce ta kawo wannan al’umma ta Sorko a daular Kabi. Sannu a hankali sai wannan al’umma ta ‘Sorko’ ta saje da al’ummar da suka tarar a Kabi (Alkali, 1969:29-30).

 Domin a Hausantar da wannan kalma ta ‘Sorko’ an yi mata kwaskwarima ta hanyar cire wasalin ‘o’ a gaɓar farko aka musanya shi da wasalin ‘a’, wataƙila domin a sami sauƙin furuci. Haka ma an yi mata ƙarin ɗafa goshi na ‘ba’ ta yadda za a sami sunan wanda ya fito daga wannan al’umma ta ‘Sorko’, kafin daga bisani ma’anar ta sauya zuwa ga duk wani mai gudanar da sana’ar. An kuma cire wasalin ‘o’ na ƙarshe, aka musanya shi da wasalin ‘e’, aka sami “Basarke”. Dangane da suna na sana’ar kuwa tushen kalmar ne Ɗsarkɗ aka yi wa ƙarin ɗafa ƙeya na ‘nci’ aka sami kalmar ‘Sarkanci.’[1]

 Bisa ma’ana, masana sun tofa albarkacin bakinsu dangane da abin da suke ganin ake nufi da sarkanci. Bargery, (1933:92) a ƙamusunsa, ya bayyana wanda ake kira basarke. Daga wannan kalma ta basarke za a iya tantance ma’anar kalmar ta sarkanci. A cewarsa,

 Basarke shi ne masunci ko mai fito da kwale-kwale.

Idan basarke shi ne masunci ko mai kamun kifi, to ke nan kalmar sarkanci na nufin sana’ar su.Wannan ma’ana tana da naƙasu domin kuwa sarkanci bai tsaya ga su ba kawai. Sarkanci, baya ga kamun kifi, ya kuma haɗa da farautar dabbobin ruwa kamar kada da ayyu da dorina. Ya haɗa da ba da magani na iskokin ruwa, da cizo ko sukar wata dabba ta ruwa da ma sauran cututuka na ruwa. Ba wannan kaɗai ba, sarkanci ya ƙunshi ba sana’ar kamun kifi muhimmnci fiye da kowace irin sana’a, rani da damina. Tare da haka, ga kuma zancen ƙwarewa kan sana’ar.

Alkali, (1969) ya bayyana abin da yake gani ake kira sarkanci a inda yake cewa

 Tun farkon ƙarni na goma sha tara (19) kalmar sarkanci ta ɗauki

 ma’anar ƙwarewa kan sana’ar su, don haka duk bakaben da ke

 yin wannan sana’a ake kiransa Basarke.(Alkali, 1967:30)

 Wannan ma’ana da Alkali ya kawo ta yi daidai don kuwa ba kowane masunci ne ake kira Basarke ba. Basarke masunci ne ƙwararre, wanda ba ya da wata sana’a da ta shige ta su, rani da damina. Irin wannan masunci ne za a tarar yana iya sarrafa ruwa da ma halittun da ke cikinsa ta duk yadda yake so. Ta fuskar ba da magani kuwa, Basarke ba kanwar lasa ba ne.

Da wannan, ana iya cewa sarkanci kalma ce da ke nufin sana’ar kamun kifi da duk abubuwan da ke tafiyar da ita kamar ƙwarewa a kanta da iya sarrafa ruwa da halittun cikinsa da kuma ba da taimako na cututukan da ake samu a ruwa da ma ba da taimako dangane da haɗurra da ake iya samu a ruwa.

3.0 Tasirin Sarkanci A Kan Kamun Kifi A Nupe.

 Nupe ƙabila ce da aka fi samu a ƙasar Bida da Agaye da Lapai da Katcha da sauran wasu garuruwa da ƙauyuka a cikin jihar Neja, da Wasu sassa na jihar Kogi, kamar Lokoja. Ƙasar Nupe tana nan shimfiɗe a inda gulbin Kaduna ya yi magama da Kogin Kwara. A galibin wuraren da Nufawa suke zaune a Jihar Neja da ma wasu yankuna da sassa da ke maƙwabtaka da Neja, inda ake samun al’ummomin Nupe, ana samun wadatar ruwa na gulabe da ƙoramu da tafukka. Hasali ma, kogin Kwara da ya shigo cikin Nijeriya ta wajajen Bahindi a jihar Kebbi, ya ratso ta Yawuri ne. Daga nan ya bi ta wajajen Agwara a jihar Neja. Kogin ya isa yankin Bussa da Katcha, sannan ya yi magama da Kogin Binuwai a wajajen Lokoja. Baya ga wannan, shahararriyar madatsar ruwan nan mai samar da wutar lantarki wa Nijeriya tana Kainji ne a cikin jihar Neja. Albarkar ruwa da Allah ya shimfiɗa a ƙasar Nupe ne ya sanya wani sashe na al’ummar Nupe suka rungumi sana’ar Kamun kifi sosai. Wannan ne ya sanya Sarkawa suke yin ƙaura daga yankin Kabi zuwa ƙasar Nupe domin neman abinci ta hanyar sana’arsu da aka san su da ita, wato kamun kifi. A cewar Sulaiman, (2001:33) tun gabanin shekara ta 1879 ake samun Sarkawa daga masarautar Gwandu masu zuwa ci-rani na kamun kifi a wajajen Lokoja. Tun Sarkawa kan je su dawo gida bayan waɗansu watanni a can, sannu a hankali wasu Sarkawan sun yi kaka-gida a can. Yin tattaki a Katcha da ƙauyukanta zai tabbatar da irin yadda Sarkawa suka yi kaka-gida a ƙasar Nupe musamman ƙauyen Ndalada da kewayensa. Hasali ma Sarkin Bankwai na Katcha, Alhaji Sule Sarki, Basarken ƙasar Jega ne ta jihar Kebbi. Unguwar Sabongari a Katcha, kusan a rukunin mazaunanta Sarkawan da suka fito daga ƙasar Kabi ne suka fi rinjaye.

 Duk lokacin da Sarkawan suka bar gida da nufin zuwa kamun kifi a ƙasar Nupe, sukan yi haka ne tare da kayansu na kamun kifi. Ba wannan kaɗai ba, dabarunsu da dama al’adunsu duk sukan yaɗa su a tsakanin al’ummomin da ke yi masu masauki a can. Wannan ba ƙaramar rawa ya taka ba wajen sadar da kayan aikin kamun kifi na Sarkawa ga ƙabilar Nupe masu masaukinsu. Misali na fasahar kayan aiki da Sarkawa suka yaɗa ko Nupe suka kwaikwaya daga Sarkawa ya haɗa da :

3.1 Gura

 Wani kayan kamun kifi ne da ake saƙawa ta hanyar amfani da sayun itaciyar goriba da giginya. Ana saƙa raga ce wadda za a shirya ta zama tarko mai ɗan tsawo da faɗi da wata ‘yar farfajiya daga cikinta, wadda idan kifi ya shiga a ciki zai kasa fita domin bakin da akan yi mata matsattse ne daga ciki. Ana haƙa wannan kayan kamun kifi ne a gulbi daidai da inda ake samun madawayi. Haka ma ana haƙa ta a wurin da aka yi tariya ta shinge ko ganuwa a cikin ruwa. Gura tana da inganci sosai wajen kama nau’ukan kifaye daban-daban. Saboda ingancin da take da shi ne wajen kamun kifi ya sanya masunta na ƙasar Nupe suka kwaikwaye ta a wurin Sarkawa kuma suke kiranta da suna guran Sarkawa (Reed da Wasu, 1967:170)

3.2 Mali

 Kamar gura, mali ma tarko ne na kamun kifi wanda ake saƙa shi da zare domin samar da raga wadda za a lulluɓa ta jikin wasu ‘yan tsumangi na itacen gyayya ko geza, waɗanda aka tanƙwara su, suka yi siffa shigen akurkin kaji. Ana yi wa mali ‘yan kafofi na zagai (‘yar raga da ake saƙawa da zare) guda biyu ko uku waɗanda suke da ɗan faɗi a waje amma matsattsu daga ciki ta yadda duk kifin da ya shiga ciki ba zai iya fita ba. Fasahar yin wannan kayan kamun kifi ta samo asali ne daga ƙasar Mali. Ta shigo ƙasar Hausa ne sakamakon ƙaura da masunta kan yi zuwa ƙasar Mali da kuma yadda masuntan Mali kan shigo ƙasar Kabi da nufin kamun kafi. Gura mali ta shigo a yankin Kabi ne a wajajen shekara ta 1980 (Alhaji Garba Nda, Sarkin ruwan Yawuri da Agwara, hira ranar 05/03/2011).

Sannu a hankali wannan kayan kamun kifi ya sami karɓuwa a wajen masuntan wannan ƙasa har Sarkawa Hausawa suka yi mata suna gurar mali suka kuma yaɗa ta a tsakanin al’ummar Nupe da suke cuɗanya da su. Sarkawan ba su yaɗa wannan fasaha ba sai bayan da suka yi mata kwaskwarima ta ƙara inganta ta fiye da yadda suka same ta a wurin mutanen Mali. Kwaskwarimar da suka yi mata shi ne saka mata zagai[2] wanda aka saƙa shi da zaren siliki, saɓanin yadda ‘yan Mali suke yi mata zagai na ragar koma wadda kamfani suka buga. Baya da wannan, haka ma Sarkawa sun daɗa inganta amfani da gurar mali ta hanyar ɗaura igiya mai ƙwari domin a gicciye ruwan gulbin da za a haƙa gurar malin. A kan wannan igiya ne za a ɗaura duk malin da aka haƙa a wannan ruwa. Ana yin haka ne domin guje wa ruwan gulbi mai ƙarfi da zai iya kwashe gurar ya yi gaba da ita. Wannan fasaha ta samu karɓuwa ga Nufawa kuma suna amfani da wannan kayan kamun kifi sosai a ƙasarsu.[3]

3.3 Buzun Mali

 Buzun mali kamar gurar mali take sai dai ita buzun mali tana da farfajiya biyu ne ba ɗaya ba irin na mali. Ita ma raga irin ta koma ce ake lulluɓa wa waɗansu tsumangi da aka tanƙwasa su, suka yi siffa shigen akurkin tsuntsaye. Buzun mali farfajiya biyu take da shi. Ta samo asali daga wata ƙabila ta Mali da ake kira ‘Buzo’ Wannan al’umma sun shahara matuƙa ga sha’anin kamun kifi a kogin Kwara da fadamar da ta raɓi kogin. Sarkawa Hausawa sun kwaikwayi wannan kayan kamun kifi ne daga wannan al’umma suka kuma yaɗa ta a tsakanin masunta na ƙasar Nupe. Kayan kamun kifin ya sami karɓuwa ne saboda fa’ida da kuma ingancinta wajen kamun kifi idan aka haƙa ta a ruwa.

3.4 Gyandi

 A bisa ma’ana, wannan na nufin addu’o’i na surkulle waɗanda Sarkawa kan yi domin neman biyan wasu buƙatu nasu waɗanda suka jiɓinci harkar ruwa. Da yawa-yawan al’adu daban-daban waɗanda Sarkawa kan aiwatar musamman ma dai na waibuwa a ruwa duk akan aiwatar da su ne ta hanyar haɗa addu’o’i na surkulle da wasu tsatsube-tsatsube. Al’adun sun haɗa da tsaraka da ɗaurin ruwa da ƙulle ruwa da kwance ruwa da dai sauransu. Tsaraka ana yin ta ne domin neman sa’a da nasara na a kama kifi irin wanda rayuwa take muradi. Ɗaurin ruwa kuwa ana yin sa ne domin a nemi tsari daga kowane irin haɗari da ka iya faruwa a cikin ruwa. Ana ɗaure miyagu kamar kada da miyagun Iskoki da duk wata halitta da ka iya cuta wa masunci a yayin da yake cikin ruwa. Ƙulle ruwa kuwa ana yin sa domin a yi wani mugun ƙulli don hana wani abokin adawa ya yi nasara, a hana kama kifi a cikin ruwa. Kwance ruwa ana yin sa domin a warware wani mugun ƙulli da aka yi da nufin a hana abokin adawa samun nasara ta hanyar hana ya kama kifi. Waɗannan duk sihirce-sihirce ne na Sarkawa.

 Cuɗanya tsakanin jama’a da al’ummomi ba ta ƙarewa har sai an sami wani ya koyi wani abu daga wurin wani. Cuɗanya da ke gudana tsakanin Sarkawa da Nufawa kan haifar da tasiri mai yawa ta haujin koyon gyandi da sihiri. Al’ummar Nufawa, haƙiƙa sun tasirantu da mu’amaloli na Sarkanci da suka wakana a tsakanin su da Sarkawa. Da dama daga cikin Nufawa sun amfana matuƙa ta fuskar koyon addu’o’i da gyandi daga wurin Sarkawa.[4]

4.0 Tasirin Sarkanci Kan kamun Kifi A Ƙabilar Jukun

 Jukun ƙabila ce da cibiyarta take a Wukari cikin jihar Taraba, a yankin arewa maso gabas na Nijeriya. Wannan ƙabila ta daɗe tana hulɗa da al’ummar Hausawa shekaru aru-aru da suka shuɗe. A wani ƙauli masana tarihi sun sanya ƙasar Jukunawa wato Kwararafa ɗaya daga cikin banza bakwai. Welmers, (1968) na ganin cewa Hausawa ne suka saka wa wannan ƙabila suna Jukun, su kuwa suna kiran kansu da suna Apa. Wani rukuni na al’ummar Jukun da ake kira ‘Wanu’ masunta ne kuma suna zaune a gaɓar kogunan Binuwai da Kwara. Wanu, ana samun su warwatse a jihohin Benue da Nassarawa baya ga inda cibiyarsu take wato Taraba. Waɗannan Jukunawa masu kamun kifi suna cuɗanya ƙwarai da gaske da Sarkawa waɗanda suka yi ƙaura zuwa ƙasarsu domin aiwatar da sana’ar kamun kifi a can. Sarkawan da suka fito daga yankin Kabi a lardin Sakkwato kan yi ƙaura zuwa yankunan da Jukunawa suke zaune musamman a wajajen Ibbi da Jalingo inda suke aiwatar da su a gulaben Talla da Bantajo (Kamba Musa Argungu, hira ranar 23/04/2012).

 Cuɗanya a tsakanin Sarkawa da Jukunawa masu kamun kifi ta yi ƙwari sosai har ta kai Jukuwan suna kwaikwayon waɗansu daga cikin kayan kamun kifi irin na Sarkawa waɗanda su Jukunawan ba su da su. Sun kwaikwayi waɗannan kaya ne sakamakon la’akari da suka yi da cewa, kayan kamun kifin na Sarkawa suna da inganci sosai wajen kama kifi. Sarkawa Hausawa ne suka tafi da fasahar saƙa gura da kuma amfani da ita wajen kama kifi a ƙasar Jukun. A wurin Hausawa ne Jukunawa suka kwaikwayi dabarar saƙa wannan kayan kamun kifi. A harshensu na Jukun, suna kiran kayan kamun kifin, wato gura da suna ‘agura’ (Obande da Wasu, 2010:183).

5.0 Sakamakon Bincike

 Sarkawa mutane ne da suka shahara matuƙa a sha’anin kamun kifi. Sana’arsu kan sa su yin ƙaura daga wannan wuri zuwa wancan. Dalili kuwa shi ne duk inda suka fahimci akwai ƙarancin ruwa sakamakon fari, ko kuwa akwai ƙarancin halittar kifi a cikin ruwa, sukan yi ƙaura zuwa inda suke ganin akwai wadatarsa. A cikin irin wannan ƙaurace-ƙaurace nasu, sukan tsallaka har a wasu ƙasashe na yammacin Africa, kamar Mali. Wannan ya haifar da yaɗa fasahohin gargajiya na kayan kamun kifi da dabarun kamun kifi. Wannan ne ya haifar da samuwar kayan kamun kifi kamar gurar mali da buzun mali.

Sarkawa Hausawa ne suka yaɗa fasahar saƙa gura ga ƙabilun Nupe da Jukun. Ƙabilar Nupe sun koyi amfani da dabarar haƙa gurar mali da buzun mali daga wajen Sarkawa. Sun kuwa yi haka ne bayan sun yi la’akari da ingancin waɗannan kayan kamun kifi wajen biyan buƙatar masunta.

Ba ta fuskar kayan kamun kifi kawai ba, cuɗanya tsakanin Sarkawa da waɗannan ƙabilu ta haifar da yaɗuwar waɗansu al’adu da suka jiɓinci kamun kifi kamar addu’o’i da gyandi waɗanda a al’adance, sai da su harkar kamun kifi ke gudana a bahaushiyar al’ada.Waɗansu Nupawa ga misali sun tasirantu da al’adu na ɗaurin ruwa da tsaraka da kwance ruwa da dai sauransu, daga wajen Sarkawa Hausawa.

Kammalawa

 Sana’ar Sarkanci sana’a ce da take wakana sosai ƙasar Hausa albarkar ruwa da halittun cikinsa da Allah ya shimfiɗa ya kuma rayar a ƙasar Hausa. Albarkar ruwa da ake samu a ƙasar Hausa ya taimaka wajen yawaitar jama’a da tsugunar da su a cikin ƙasar. Al’ummar ‘Sorko’ wata al’umma ce daga Sanwai da suka yi hijira zuwa Kabi kuma zuwansu ya daɗa inganta sha’anin kamun kifi a ƙasar Hausa. Sakamakon yawace-yawacen da Sarkawan kan yi a ciki da wajen ƙasar Hausa ya ƙara buƙasa sha’anin kamun kifi musamman a tsakanin ƙabilun da Sarkawa kan baƙunta. Wannan muƙala ta tabbatar da yadda waɗansu kayan aikin Sarkanci suka sami karɓuwa ga al’ummomin Nupe da Jukun. Kayayyakin da suka sami karɓuwa su ne gura da gura mali da buzun mali. Haka ma wannan bincike ta tabbatar da cewa wasu Nufawa sun tasirantu da wasu al’adu na sarrafa ruwa daga wajen Sarkawa. Waɗannan al’adu sun haɗa da addo’o’i da gyandi da suka jiɓinci tsaraka da ɗaurin ruwa da sauransu.

Duk inda aka sami cuɗanya tsakanin al’ummomi daban-daban, haƙiƙa sai an sami musayar fasaha da aro na kayan aiki tsakanin al’ummomin. Wannan muƙala ta yi waiwaye ne kawai kan tasirin da Sarkanci ya yi a kan sana’ar kamun kifi a tsakanin ƙabilu Nupe da Jukun. Nan gaba, cikin yardar Mai duka, an ƙuduri lalubo irin tasirin da wasu al’ummomi maƙwabtan Hausawa suka yi a cikin sha’anin kamun kifi na Hausawa da yake Bahaushe na cewa, ‘akwai ruwa a ƙasa sai in ba a tona ba’.

 Manazarta

Tuntuɓi mai takarda.



[1] Domin ƙarin bayani kan yadda ake yi wa kalmomi ɗafe-dafe don sauya ma’anarsu sai a duba Abubakar, A. (2001) An Introductory Hausa Morphology. Faculty of Arts, University of Maiduguri, Nigeria. Shafi na 23 – 27.

[2] Alhaji Garba Nda, Sarkin Ruwan Yawuri da Agwara ya tabbatar man da cewa Sarkawa Hausawa suka yi wa gurar mali ƙarin inganci na saka mata zagai da aka tufƙa da zaren siliki da kuma ɗaura a jikin igiya. Wurin su ne Nufawa suka koyi wannan fasaha.

[3] Malam Mustafa Yunusa a wata hira da na yi da shi a ƙauyen Kiho kusa ga Ndalada a ƙasar Katcha ta jihar Neja ya tabbabatar da cewa Nufawa sun koyi saƙa da kuma amfani da gura wajen kamun kifi da hannun Sarkawa da suka fito daga Lardin Sakkwato musamman ƙasar Kabi da Gwandu. An yi wannan hira ne ranar Talata 05/06/2011.

[4] Wani Banufe, Mustafa Yunusa na ƙauyen Kiho kusa da Ndalada, ƙasar Katcha ta jihar Neja ya tabbatar mani da cewa haƙiƙa ya amfana da hulɗarsa da Sarkawa domin an taɓa ƙulle masa ruwa ya yi kimanin sati biyu bai kama ko kwaɗo ba. A wurin wani Basarke da ya fito daga ƙasar Kabi ya sami gyandin da ya warware masa wannan matsala. Tun daga wannan lokaci bai koma fuskantar irin wannan jarabta ba. Ya kuma faɗa cewa ya koyi addu’o’i masu yawan gaske wajen Sarkawa daban-daban.

Post a Comment

0 Comments