Takardar Da Aka Gabatar A Wurin Bikin Karrama Haziƙan Marubutan Da Suka Samu Nasarar Lashe Gasar Marubuta A Matakai Daban-daban, Wanda Ƙungiyar Marubuta Littattafan Hausa, Wato Hausa Authors Forum, Reshen Jihar Kano Ta Shirya, Ranar Lahadi 29 Ga Watan Disamba, 2019, A Ɗakin Taro Na Laburaren Jihar Kano.
Marubuci
Ɗan Baiwa: Rubutu Da Marubuci A Fuskar
Masu Mulki Da Al’umma
NA
Ibrahim Baba (Ibrahim
Garba Nayaya)
Shugaban Ƙungiyar
Inuwar Marubuta ta Jihar Yobe (Yobe Authors Forum), Nguru Writers’ Association of Nigeria (NWAN).
07066366586,
08125351694.
Instagram: ibrahimgarbanayaya
E-mail: ibrahimba182@gmail.com
1.0 Gabatarwa
Babban abin da yake jagorantar
rubuce-rubucen littattafan Hausa ita ce fasaha, domin da ita ce marubuta suka bambanta
da sauran gama-garin jama’a. Tare da wannan fasahar tasu, sukan samu matsaya
mabambanta a wurin jama’a, kowa da irin kallon da yake musu. Amma rubutu, abu
ne da yake fito da kyawun al’umma ta zama tamkar fuskar kyakkyawar budurwar da
take da dogon hanci da idanu farare abin so ga kowa. Haka rubutun marubuta yake
a tsakankanin al’umma, wannan sai ya sanya marubutan sun samu ƙauna da soyayyar
al’umma. Babu yadda za a yi rayuwa ta yi wa kowa daidai yadda yake so, wannan
ya sanya a gefe guda za a ga akwai masu nuna ƙiyayya ga marubuta,
wannan kuma shi ke sanya rayuwa ta yi kyau; amma ga wanda ya fahimce ta.
2.0 Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Littattafan Ƙagaggun
Labarai Na Hausa
Tarihin kagaggun littattafai bai daɗe ba sosai idan aka
kwatanta da tarihin samuwar wakokin baka da kuma rubutattu. Waƙoƙi sun samu kulawa tun
shigowar Musulunci ƙasar Hausa, da yake an yi amfani da su wajen yaɗa addinin Musulunci,
su kuwa ƙagaggun lattattafai sai bayan da Turawa suka shigo ƙasashenmu na Afrika
ta Yamma ne suka fara samuwa.
Yawancin rubuce-rubucen da Turawa
suka yi ba na ƙagaggun littattafai ba ne. Littafin da Schon J.F. ya
rubuta mai suna Farawa Letafen Magana Hausa, shi ne littafin Hausa na farko na
zube cikin boko, kuma duk rubuce-rubucen da Turawan suka yi babu wanda ya yi
kama da ƙagaggun labarai wato Noɓel, sai dai a bugun ƙarshe a shekarar
1886, ya tabo tatsuniyoyi. Kuma yawancin littattafan na yaɗa addinin Kiristanci
ne.
Amma rubuce-rubucen zube na ‘yan ƙasa ya samo asali ne
sakamakon kafa Hukumar Talifi ta Arewa (Northern Literature) a shekarar 1933,
inda ta sa gasar rubuce-rubuce ga ‘yan Ƙasa, inda suka samar
da littattafai guda shida kamar haka:
1. Ruwan Bagaja na
Abubakar Imam 1935
2. Gandoki na Bello
Kagara 1935
3. Jiki Magayi na
Tafida Umar da Dr. R.M. East 1935.
4. Idon Matambayi na
Muhammadu Gwarzo 1935.
5. Shehu Umar na
Abubakar Tafawa Balewa 1935.
6. Iliya Danmaikarfi
na Ahmadu Ingawa. 1968. (Gidan Dabino, 2010:2-3).
Bayan samar da waɗancan wallafe-wallafe
a mataki na farko na ‘yan ƙasa, an ci gaba da samun wasu,
musamman ta hanyar hukumomin da aka rinƙa kakkafawa da kuma
kamfanoni har zuwa wajajen shekarar 1980, wato lokacin da aka fara samun ɓulluwar wani salo na
rubuce-rubucen littattafan ƙagaggun labarai, saboda dalilai na
sauyin zamani da ɓulluwar baƙin al’adu da kayan
zamani zuwa ƙasar Hausa. (Nayaya, 2019:2).
An samu maganganu da dama daga
masana daban-daban game da samuwar Adabin Kasuwar Kano, ko kuma sajewar
littattafan Hausa zuwa ga komawa ga abin da Malumfashi (1984) ya kira da Adabin
Kasuwar Kano. Amma a taƙaice, ga abin da Mukhtar (2010:21) ya bayyana, “A cikin
shekarar 1984 ne wata al'adar rubuce-rubuce ta ƙagaggun littattafai
ta kunno kai wadda aka sa wa suna Adabin Kasuwar Kano, a Turance " Kano
Market Literature". An sami wani jigo na soyayya inda ya yi tasiri sosai
da sosai cikin wannan adabin. Daga cikin waɗanda suka share fage akwai irinsu:
-Rabin Raina, littafi na ɗaya (1984) na Talatu
Wada Ahmad
-Soyayya Gamon Jini (1986) na Ibrahim Hamza
Abdullahi.
-In Da Rai (1987) na Idris ImamImam.
- Buduwar Zuciya (1987) na Balaraba
Ramat Yakubu.
-Kogin Soyayya (1988) na A M.
Zahraddeen.
-Idan So Cuta Ne (l989) na Yusuf M.
Adamu”.
Daga cikin abin da ya gabata, za mu
fahimci Adabin Kasuwar Kano ba wata gamammiyar ƙungiya ba ce ko wata
hukuma da aka yi taro aka sanya mata wannan suna, sunan ya biyo bayan la'akari
da Adabin Kasuwanni makamantansa ne ya samar da shi, wannan ya sanya Malumfashi
(1994) da ya kira shi da wannan suna. Kuma shi Malumfashin ya yi haka ne daga
abin da ya gani masu kama da juna tsakanin littattafan da irin waɗanda aka samar a
Kasuwar Onisha wanda ake kira Adabin Kasuwar Onitsha, kuma irin haka ne ga abin
da ya wakana ga abin da ake kira da Adabin Elizerbert da na Kitsh na Jamus.
(Nayaya, 2018:55).
2.1
Wane ne Marubuci?
Masana sun bayyana ma’anar marubuci
ta fuskoki mabambanta, misali: Wikipedia ta bayyana cewa, "Marubuci shi ne
wanda yake amfani da rubuta kalmomi ta hanyar mabambantan salo da dabara domin
sadarwa ta hanyar hikimarsu". A wani wurin kuma, ta bayyana da cewa,
"Marubuci shi ne mai shirya mabambanta ayyukan adabi da rubutun hikayoyi
kamar rubutattun labaru, gajerun labarai, tatsuniyoyi, wasanni, tsara labarai,
insha'i da kuma rahotanni da labarai, da muƙalu waɗanda suka yi dai-dai
da ra'ayin jama'a. Rubutun marubuta ana buga shi a ɗaukacin wuraren watsa
labarai".
Collins English Dictionary ta
bayyana da cewa, "Marubuci shi ne wanda yake rubuta littattafai, labarai,
da muƙalu a matsayin aiki".
Kafar yaɗa bayanai ta
Difference Between ta bayyana marubuci da "Shi ne wanda yake rubuta
littafi, muƙala, da kuma dukkanin aikin adabi".
Shi kuwa Gidan Dabino (2006) ya bayyana marubuci da, "Marubuci shi ne
wanda ta hanyar amfani da fasahar rubutu yakan ƙirƙiri wani yanayi na
gaske ko na almara ko tunani ya kuma yi amfani da shi don gina wasu mutane da
abubuwa wadanda yake amfani da su don isar da sako ga al'ummar da ke karatun
rubutunsa. Shi wannan sako ana tsara shi ne ta hanya ta musamman mai cike da
hikima da hazaka don isarwa a saukake, kamar ta hanyar yin amfani da haruffa
zuwa kalmomi zuwa jimloli zuwa siɗarori da shafuka har zuwa cikakken
littafi".
Nayaya (2018:53), wajen taƙaita waɗannan ma’anonin, sai
ya ce, “Marubuta su ne ire-iren mutanen da suke sarrafa fasaharsu wajen ƙago ko gyara wani
labari da ya afku ko ake jin zai iya afkuwa a rayuwar jama’a, domin faɗakarwa da yin
hannunka mai sanda, shin su ɗin za su samu wani abu ne ko a’a”.
2.2
Wasu Cikin Marubuta Litattafan Hausa
Baya ga bayanan da suka gabata,
yana da kyau a bayyana wasu cikin marubuta littattakan Hausa a matsayin misali.
Daga cikin marubuta akwai:
-Ado
Ahmad Gidan Dabino - Ɗan Azumi Baba
-Bilkisu
Ibrahim Nabature
-Fauziyya D. Suleiman
-Ruƙayya Abdullahi
Dangado -Kabir Yusuf Fagge
Anka
-Maimuna
Idriss Sani Beli -Ayuba Muhammad Ɗanzaki
-Abubakar
Auyo
-Hadiza Nuhu Gudaji
-Amina
Dauda Abubakar
-Naja'atu Haruna Saleh
-Maryam
Kabir Mashi
-Jiddah Haulat Nguru
-Maryam
Rabi'u Ado
-Muhammad Lawal Barista
-Sadiya
Garba Yakasai -A'isha
Abdullahi Bagwanje, da dai sauransu.
Wani abin la’akari, mafi yawan
marubuta littattafan ƙagaggun labarai na Hausa, ba Hausa suka karanta ba, ƙila ma ba su haɗa layi da darasin day
a shafi Hausa ba, walau a babbar sakandare har zuwa manyan makarantu. Misalai
na nan da dama, daga ciki: Marubucin littafin Idan So Cuta Ne, wato Farfesa
Yusuf M. Adamu malamin Nazarin Labarun Ƙasa ne (Geography),
Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, (Mass Commuhaka abin yake har zuwa yanzu wanda ga
misali nan a nan gabanmu ga wadda ta samu nasarar zuwa ta ɗaya.
2.3 Misalan Littattafan Ƙagaggun Labarai Na
Hausa
Nayaya da Baba
(2018:54) sun haƙaito ire-iren littattafan ƙagaggun labarai na Hausa, cikin waɗannan litattafan akwai:
i. In da Alƙawari (1992) na Bala
Anas Babinlata.
ii. Duniya Sai Sannu (1997) na Ado Ahmad
Gidan Dabino, MON.
iii. Mafarkin Khadija (2014) na Maimuna Idriss
Sani Beli.
iɓ. Rayuwar Bilkisu (2016) na Ayuba Muhammad
Ɗanzaki.
ɓ. Firgita Samari (2005) na Kabir Yusuf
Anka.
ɓii. Amon ‘Yanci
(2013) Halima Ahmad Matazu.
ɓiii. Jarrabi (2014) na Abubakar Auyo.
ɗ. Me Zan Yi Da Ke (2016) na Maryam Rabi’u Ado.
ɗi. Marubuciya (2019) na Jiddah Haulat
Nguru.
ɗiii. Rumaisa (2014) na Fauziyya D. Suleiman.
ɗiɓ. Adon Dawa (2011) na Jamila Umar
Tanko.
3.0 Marubuta A Idon Masu Mulki Da Al’umma
Marubuta wasu keɓantattun mutane ne da
suke rayuwa a tsakankanin al’umma suna masu hidimta wa al’umma ta hanyar
sarrafa basira da hikima gami da fasahar da Alllah huwace musu. Har wa yau, ta
wannan hanya ce suke taimakon kansu da taimakon al’umma wajen wasu ɗawainiyar da suka
shafi kuɗi. Saboda wannan
muhimmanci nasu, sai ya kasance suna da matsaya a idanun al’umma, sawa’un masu
mulki ne ko kuwa ɗaiɗaikun mutane ne cikin
masana da ɗalibai da sauran
gama-garin mutane cikin masu karanta littattafan marubuta.
3.1 Marubuta A Idon Masu Mulki
Masu mulki a nan, sun ƙunshi dukkanin ayarin
da suke riƙe da madafun iko; musamman a ƙololuwa, wato
jagorancin jama’a. Waɗannan rukuni na
mutane sun ɗauki marubuta da
muhimmanci dubi da yadda suke karrama ɗaiɗaikunsu da lambobin yabo da kambunan
girmamawa. Har wa yau, waɗannan mutane sukan
bai wa marubuta dukkanin gudumawar da suka nema domin gabatar da muhimman
taruka na marubuta. Tare da wannan muhimmanci nasu, sukan samu wasu matsaloli
na rashin kyakkyawan tallafi wajen yin ɗab’in littattafansu, hakan ya sanya ake samun
yawaitar waɗannan littattafai
suna yawo a soshiyal mediya, domin ba a samu an buga su an fitar da su kasuwa
ba. Ke nan, idan dad a masu mulki za su ware wani ofishi domin yin wannan aiki,
da harkar rubuce-rubuce za ta ƙara ɗaukaka.
A taƙaice dai, marubuta
littattafan Hausa suna da wata daraja ta musamman a idanun shugabanni, domin ƙoƙarinsu na seta
rayuwar al’umma da ɗora ta a kan tsari
mai kyau.
3.2 Marubuta A Fuskar Al’umma
Al’umma a nan, na nufin dukkanin
jama’a, musamman masu karanta littattafan Hausa da waɗanda ake karanta musu
da waɗanda suke kallon masu
karatun. A wannan ɓangare akwai matsaya
guda uku:
i. Waɗanda ke karanta
litattatafan Hausa kuma suke samun nishaɗantuwa daga littattafan. Ire-iren waɗannan mafi yawa ‘yan
mata ne masu shekarun tsaka-tsaki, sai matan auren da ba su jima a gidajen aure
ba, sai kuma manyan mata; wato matan alhazai ko kuma hajiyoyi. Galibi irin waɗannan mataye sun yi
nutso cikin karance-karancen waɗannan litattafai, wannan ta sanya lokacin da guguwar
karanta littattafanan Hausa ta kunno kai a wasu gidajen radiyo a ƙasar Kano, suka mayar
da hankali wajen sauraron radiyo, har ma ɗalibai mata sukan tafi makarantunsu da ƙaramar radiyo ko waya
domin sauraren wannan shiri na karatun littattafan Hausa.
Don haka a wurin waɗannan makaranta,
marubuta na da matuƙar daraja da ƙima a idanunsu, har
ma suna ganin daina yin rubuce-rubuce kan iya jefa su cikin wani kogin dab a
zai ɓulle da su ba. Idan
kuwa wata musifa ta samu wani/wata marubuci/marubuciya, sukan damu matuƙa, har ma su ji kamar
su abin ya sama. Yayin da suke matuƙar jin daɗi da farin ciki a duk
lokacin da abin farin ciki ya samu marubuta.
ii. Kaso na biyu, su
ne masu karantawa idan sun samu, a gefe guda kuma suna ganin baiken marubutan.
Don haka, marubuci kan iya zama mai daraja a idanunsu, a wani lokaci kuma ya
zama akasin haka. Irin waɗannan mutane, ba su
da wata alƙibla guda ɗaya da suke kan ta. Su dai idan sun samu su
karanta, su yaba, ko su kushe. Ba kasafai suka fiye damuwa da halin da marubuta
ke ciki ba, walau mai kyau ne ko akasin haka.
iii. Wannan kaso, su
ne waɗanda kwata-kwata sun
tsani marubuta, ba sa son su ji ko ganin ayyukan marubuta, domin sun ɗauki harkar ɗab’i a matsayin
shiririta da ɗirkaniya da rashin
aikin yi. Irin waɗannan nan, ba su da
wani aiki face zagi da kushe ga marubuta a kowane lokaci.
3.3 Marubuta A Idon Malamai, Manazarta Da Ɗalibai
Malamai su ne masu sanya ɗalibai yin nazarin
ayyukan marubuta, sawa’un su umarce su domin su ciro wani kuskure ne, ko kuma
su zaƙulo wani darasi ne da ke cikin littafin ko kuma su
waiwaici matsala ta ƙa’idojin rubutu. Haka zalika manazarta, aikinsu ne
nazartar ayyukan marubuta tare da sanya su a ma’aunai daban-daban. Manazarci
kan iya zaƙulo matsala a cikin littafi amma ba lalle ya iya kawo
mafita daga wannan matsala ba, domin wannan aiki sai wanda ya rubuta.
Ɗalibai kuwa, su ne
masu tsayuwa wajen nazartar waɗannan ayyuka na marubuta, hakan kuwa ba zai yiwu ba; har
sai sun tattauna da marubutan, domin mafi yawan nazari ba ya yiwuwa da littafi
kawai, dole sai an nemi marubucin littafin.
A wurin waɗannan ayari na
masana, marubuta na da muhimmiyar gudumawa acikin rayuwar al’umma, domin ta
fuskar nazarin nasu ne suke zaƙulo wasu sabbin ilimin da su kansu
marubutan ba su san as u ba. Don haka, su ma sukan bibiyi rayuwar marubuta da
son farin cikinsu, da kuma damuwa da damuwarsu.
5.0 Kammalawa
Kamar yadda waɗannan bayanai bayanai
suka gabata, babu tantama marubuta na da muhimmiyar rawa a cikin rayuwar
al’umma. Ke nan, kafa ofis domin ƙoƙarin tafiyar da
ayyukansu a gwamnatance abu ne da zai ƙara gyara wannan
harka. Sannan jami’o’i su zama mahaɗa ta waɗannan marubuta domin tattauna batutuwan da
suke addabar ƙasa gami da fitar da rubuce-rubucen da suka fi dacewa da
zamani. Misali, a irin wannan zamani, rubuce-rubucen da suka shafi haɗin kan ‘yan ƙasa, zaɓar shugabanni ba
domin kuɗi ba, sanya kishin
gari da yare da addini da al’adu, matsalolin shaye-shaye da barace-barace (duk
da an yi rubuce-rubuce a kai) rubutu ne da zai taimaki al’umma. Idan muka kalli
al’amari na jagoranci da siyasa, da ilimin matasa da zaman kash-wando, da
bangar siyasa, akwai buƙatar a samar da sabbi wallafe-wallafe waɗanda suka fi dacewa
da wannan zamani da irin alƙiblar da al’umma ke kai. Har wa yau,
malamai a manyan makarantu har ma da sakandare su mayar da hankali wajen sanya ɗalibai nazartar
ire-iren waɗannan
wallafe-wallafe, da kuma gabatar da jawaban fiɗar waɗannan litattafan a taruka mabambanta.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.