Ticker

6/recent/ticker-posts

Kalubale Wajen Koyar Da Harshen Hausa A Makarantun Firamare Da Sakandare A Nijeriya: Gyara Kayanka Bai Zama Sauke Mu Raba Ba

Takarda Wadda Aka Gabatar A Taron Ƙara Wa Juna Sani Na Ƙasa, Wanda National Hausa Language Forum, Burkina Faso ta Shirya, a Ouagadougou, Daga Ranar 27 zuwa 28 ga Watan Maris, 2020.

makaranta

Ƙalubale Wajen Koyar Da Harshen Hausa A Makarantun Firamare Da Sakandare A Nijeriya: Gyara Kayanka Bai Zama Sauƙe Mu Raba Ba

Zainab Umar Saleh

Sashen Nazarin Harshen Hausa, Kwalejin Shari’a ta Aminu Kanu, Jihar Kano.
08065463288
Email: uzainab928@gmail.com

Da

Ibrahim Baba (Nayaya)
M.A Hausa (Literature) Student, Department of Nigerian Languages and Linguistics, Bauchi State University, Gaɗau.
07066366586, 08125351694
ibrahimba182@gmail.com

 

Tsakure

Harshen Hausa harshe ne mai cin gashin kansa a tsarin koyarwa cikin wannan Ƙasa ta Nijeriya, wannan ya sanya aka same shi cikin harsunan da aka yarda a koyar da su a dukkanin makarantun dake faɗin Ƙasar nan, sai dai makarantun da aka keɓanta da koyar da harkokin kiwon lafiya ko ayyukan fasahar ƙere-ƙere. A makarantun sakandare da firamare kuwa, harshen ya zama tilas ga kowane ɗalibi koda kuwa yana ɓangaren kimiyya da fasaha ne; idan a sakandare yake. Tare da wannan muhimmanci nasa, da yadda yake yalwatacce kuma sananne a tsarin koyarwa, harshen na samun tasgaro da ƙalubale a mafi yawan makarantun sakandare da firamare ta fuskoki da dama. Wannan takarda, ta bibiyi ire-iren waɗannan ƙalubale tare da bayyana su, sannan ta hakaito hanyoyin fita daga waɗannan ƙalubale a faɗin Jihar Yobe, musamman Ƙaramar Hukumar Nguru. Wannan aiki ya gudana ta hanyar tuntuɓa, karance-karance da ziyartar makarantu da bibiyar ɗalibai a matakan firamare da sakandare.

1.0 Gabatarwa

           Ko shakka babu, harshen Hausa na daga cikin harsunan da ake nazarta a matakai na ilimi daban-daban, harshe ne da ake yalwata ilimi a cikinsa dubi da bambance-bambance na ɓangarorinsa. A ƙananan makarantu na firamare da sakandare ma ba a bar Hausa a baya ba, domin tana cikin harsunan da ake koyar da su a matsayin darasi mai zaman kansa, wannan ta sanya ake samar masa da malaman da suke koyar da shi a matakin makarantun firamare da sakandare. Mafi yawan malaman da suke koyar da harshen Hausa; su ma sun karanci Hausa ne a matakin difloma, N.C.E, digiri na ɗaya, da na biyu da na uku. Amma da yawa cikin masu karantar da Hausa a makarantun firamare da sakandare; ba su wuce matakin digiri na farko ba. Amma akan samu waɗanda ba su karanci harshen Hausa ba a kowane mataki na karatu, amma sai ba su su rinƙa koyar da harshen Hausa. Karantar da harshen Hausa daga malamin da bai karance shi ba, yakan kawo babbar matsala a fagen koyon Hausa, musamman ganin yadda ake yi game da harshen cewa kowa ma yana magana cikin sa, don haka kowa zai iya karantar da shi. Sai dai abin da  ba a sani ba, ‘Ba a nan take ba, an danne bodari ta ka’. Domin a wannan aiki, za a ga illar da hakan yake haifarwa a tsarin koyar da harshen Hausa.

1.1 Ma’anar Koyarwa

           Masana sun yi ƙoƙari wajen bayyana ma’anar koyarwa, amma yawancin ma’anonin da suka bayar saƙon yana komawa kan abu guda ne. Misali, Zarruƙ (1979:1) ya bayyana ma’anar koyarwa da cewa, “Hulɗa tsakanin mutum da mutum. Kuma ana yin hulɗar ne don a kawo canje-canje cikin abin da mutum ya sani, ko wanda ya yarda da shi. Hulɗa dai ita ce zuciyar aikin, canjin halayen mutum kuwa shi ne manufarsa. Sannan kowa ya san ba a hulɗa sai da mutane; watau aƙalla sai an samu mutum biyu sun sadu da juna tukuna”.

           Adeyeni (1985) a cikin Gambo (1998:3), ya ce, “Koyarwa wata tsararriyar hanya ce da malami ke bi wajen gwada wa ɗalibai abubuwan da ba su sani ba su koya su kuma yi amfani da shi a rayuwarsu ta yau da kullum”.

           Idan muka kalli waɗannan ma’anoni guda biyu, za mu ga aikin koyarwa shi ne aikin nuni ko gyara tsakanin mutane wanda ke farawa daga mutum biyu, wato mai koyo da mai koyarwa, har zuwa adadin mutanen da aka tsara za a koyarwa ko za a iya sanya su a gaba domin a koyar musu da dukkanin hanyoyin da suka dace da al’ada da ɗabi’a ta yanayin al’ummar da ke wurin kuma ba ta ci karo da yanayin al’adu da ɗabi’unsu ba, ko kuma amintaccen tsarin da zamani ya kawo.

2.0 Koyar Da Harshen Hausa A Makarantu

           Harshen Hausa na daga cikin harsunan da ake koyarwa a matakin makarantun firamare da sakandare, mafi yawan tsarin koyar da harshen akwai shi a rubuce cikin manhajar koyarwa kamar yadda Hukuma ta tsara. A tsarin koyarwa, kowane aji yana da nasa abin da ake koyarwa, wanda wani ke bin wani; har a kai ga abin da za a koyar a firamare, haka abin yake ga koyarwa a sakandare. A tsarin koyarwa, ana duba matakin karatun kowane ɓangare, wato ana yi duba ga abin da ya cancanta a koyar wa ‘yan firamare, da kuma abin da ya dace a koyarwa ‘yan sakandare; wanda ci gaba ne ga na ‘yan firamare.              

2.1 Masu Koyar Da Harshen Hausa

          Masu koyar da harshen Hausa a kowane mataki na makarantu daidai suke da masu koyar da kowane darasi, domin su ma malamai ne da suka karanci harshen Hausa a matakai daban-daban na ilimi, imma difloma ce, ko N.C.E ko digiri ko sama da waɗannan. Amma idan aka yi duba ga makarantun firamare, za a iske mafi yawan masu koyar da Hausa ba su fice masu difloma ko N.C.E ba, sai ɗaiɗaiku cikin waɗanda suka yi digiri. Wannan ya sanya duk makarantar da ta yi wannan dace da waɗanda suka kai wannan mataki, to za ka samu ɗaliban suna da ƙoƙari wajen fahimtar darasin Hausa; saboda waɗanda suke karantar da ita, sun karance ta kuma suna karantar da ita bisa ƙa’ida da tsari amintacce.

          Amma a wasu makarantun, za a iske ana bai wa waɗanda ba su karanci Hausa ba su karantar da ita. Wannan kuwa na da alaƙa da raina darasin ta yadda ake ganin kowa ma zai iya karantar da Hausa, ko kuma domin rashin malaman Hausa ko kuma rashin kayan aiki. Wannan ya sanya za a ga ɗaliban ba sa fahimtar komai, a wani lokacin ma su ɗauki darasin Hausa a matsayin lokacin koyar da labarun tatsuniyoyi ko hira.

3.0 Ƙalubalen Da Harshen Hausa Ke Fuskanta A Makarantu

          Halima (2011:384) ta bayyana cewa, za mu iya cewa an yi wa aikin koyar da Hausa riƙon sakainar kashi, kai ba ma koyarwa ba, shi kansa malamin Hausa da koyon Hausa da ma nazarinta wasu ba su ɗauke shi da muhimmanci ba. Wataƙila wannan ita ce babbar matsalar farko. Muna iya cewa alama wannan duhu ne yake dukan duhu. Dalili shi ne, waɗannan matsaloli da ake fuskanta dawurwura suke yi a tsakanin al’ummar Hausawa da kuma hukumomin ilimi da jihohin Arewacin Nijeriya. Saboda haka, a nan Gizo ke saƙarsa, a wannan kogon matsalolin suka maƙale, sai kame-kame ake yi.

         A wannan gaɓa, za mu bayyana ƙalubalen ta hanyar rukunoni na jama’a daban-daban, wanda ta nan za mu gane inda matsalar ta fi ƙarfi da kuma samar da hanyoyin da za bi domin magance waɗannan matsalolin.

3.1 Ƙalubale Daga Gwamnati/Hukumomin Ilimi

          Ƙalubale na farko da wannan bincike ya gano, ƙalubale ne daga gwamnati da hukumomin ilimi, domin su ne suke da hanyoyin tsara ko gyara harkar koyar da Hausa wadda kowa zai bi ba tare da an samu wata matsala ba. Idan kuwa har an samu wata matsala, to su suke da alhakin ɗaukar dukkanin wani mataki na magance faruwar hakan a gaba. Daga cikin matsalolin da gwamnati ko hukumomin ilimi suka haifar akwai:

3.1.1 Rashin Kayan Aikin Koyarwa Na Hausa

          Kamar yadda Taiwo (1985:32) ya bayyana cewa, babu wata koyarwa a duniya da za a yi ta ba tare da kayan aiki ba, wannan koyarwar kuwa ta shafi makarantun firamare da sakandare, su kuwa kayan aikin sun shafi koda kuwa littafin da za yi amfani da shi ne wajen ɗaukar muhimman batutuwan da ake son koyarwa. Ba ya ga littattafai, akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata a ce an gabatar da su a zahirinsu ga ɗalibai, kamar ganguna; idan ana koyar da su abin da ya shafi kaɗe-kaɗe, ko launuka; idan ana koyar da su abin da ya shafi launi, ko kitso, ƙunshi, shigar al’adu ko tufafin ma’aurata; yayin da ake koyar da su al’adun aure. To duk waɗannan gwamnati ba ta aika wa makarantu, kamar yadda su ma hukumomin ilimi ba sa nemar wa makarantu su tura musu domin a koyar da Hausa. 

3.1.2 Rashin Aiki Da Manhaja Da Sabunta Littattafan Hausa

          Manhaja ita ce kundin da ake tsara dukkanin abin da za a koyar da ɗalibai a kowane mataki na karatu. (Madugu, 2000:69). Sau da dama ba a tantance manhajar Hausa kamar yadda ba a fiye sabanta ta ba; musamman ta firamare, idan kuwa an sabanta ta; to zai yi wuya ka ga ana aiki da ita a ƙananan makarantu. A yayin wannan bincike, kaso 67 cikin ɗari na alƙaluman lissafi, sun bayyana cewa mafi yawan makarantu ba sa amfani da manhaja yayin darasin Hausa, kawai dai suna amfani da littattafai ne irinsu: ‘Koyon Hausa Sabuwar Hanya’, ‘Mu Koyi Karatu’, ‘Mu Yi Ta Karatu’, ‘Makarantar Malam Mamman’ ko ‘Inna Da Baba’, waɗanda yawancinsu an wallafa su ne a kafin shekarar 1990, ko bayanta da kaɗan. Cikin wannan bincike, kaɗan ne aka samu suna amfani da Tsanin Hausa na Kamilu Ɗahiru Gwammaja wanda aka yi bugunsa na farko a shekarar 2005.

          Idan ka koma ta fuskar makarantun sakandare kuwa, nan ma za ka iske mafi yawa suna amfani ne da littattafai irin su: Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa (1987), Darusan Hausa (1992) da makantansu. Haka wajen nazarin littattafan zube, da na wasan kwaikwayo, su ma ba a canjawa, domin har yanzu ana amfai ne da ire-irensu: Ruwan Bagaja (1933), Shehu Umar, Tauraruwa Mai Wutsiya (1969), Tabarmar Kunya (1968), Zamanin Nan Namu (1970), Wasan Marafa (1949) da Waƙoƙin Hausa (1957) da sauransu wanda yanayin zamanin da aka rubuta su ya bambanta da wannan zamani.

3.1.3 Rashin Shirya Wa Malaman Hausa Tarukan Bita

          Kusan kowane sashe na malaman firamare da sakandare ana shirya musu tarukan bi-ta ko ƙara wa juna sani, amma ban da malaman Hausa, zai yi wuya ma ka ji an ce an shirya bi-ta ga malaman Hausa a kan tsarin koyar da Hausa ko a kan bin da ake karantarwa; kamar yadda ake shiryawa sauran malaman da suke wasu sassa. Wannan ya sanya su kansu malaman Hausa suke guduwa zuwa wani sashe domin su samu a tura sunayensu cikin waɗanda za su je wannan taron bi-ta la’akari da ɗan abin da ake samu daga waɗanda suka shirya wannan taro.

3.1.4 Rashin Ɗaukar Ƙwararrun Malaman Hausa

          Hausa tana fama da rashin ƙwararrun malamai ta la’akari da yadda ɗalibai ba sa samun gogewa. Domin idan har akwai gogaggun malamai kuma ƙwararru, to za su yi amfani da hikim da gogewarsu wajen karantar da ɗalibai; koda kuwa suna da ƙarancin kayan aikin koyarwa.   

3.1.5 Mayar Da Darasin Hausa Koma Baya Da Rashin Ba Shi Muhimmanci

          Ko shakka babu, darasin Hausa ba shi da wani muhimmanci a wurin shugabanni da Hukumar Ilimi, wannan ta sanya ba a sayan kayan koyar da Hausa da shiryawa malaman Hausa tarukan bi-ta kamar yadda muka bayyana a sama.

          Ta fuskar jarabawa ma, akan samu wannan ƙalubalen, domin ba a ba ta muhimmanci koda ta fuskar tsaro ne a yayin rubuta ta; imma  jarabawar kammala karatu ce ko kuma ta sauyin aji ce. Shi ya sa za ka ji ana cewa, ‘Cin ki banza; barinki banza’, ko kuma ka ji an ce ‘Gida da masallaci’, wato Hausa da Islamic Studies.      

3.1.6 Raina Malaman Hausa Da Nuna Musu Wariya

          Malamin Hausa mutum ne maras gata koda ta fuskar gwamnati ce ko kuma Hukumar Ilimi, domin za ka iske ba a martaba shi ko nuna kulawa irin yadda ake nunawa ga malaman da suke koyar da English, Maths, Primary Science da sauransu.

3.2 Ƙalubale Daga Shugabannin Makaranta

          Akwai ƙalubale mai yawa da Hausa take samu daga wurin shugabannin makarantu. Daga cikin ƙalubalen akwai:

3.2.1 Rashin Girmama Malaman Hausa

          A ɗabi’ar ɗan’adam; yana son girmamawa, amma malamin Hausa ba ya samu wannan girmamawar a wurin da yawa daga cikin shugabannin makarantu. Wannan ta sanya koda malamin ya nemi a kawo wasu kaya domin yin darasi, za ka ga ba a kawowa, sannan idan ya nemi ɗalibai su sayi wasu takardu; shugabannin ba sa bayar da goyon baya, domin suna ganin Hausa ce ba ta da wani muhimmanci.

3.2.2 Rashin Bayar Da Darasin Hausa Ga Wanda Ya Karance Ta

          Hausawa na cewa, ‘A rashin uwa; akan yi uwar ɗaki’. To fagen koyarwa ba a la’akari da hakan, bal ma a wani lokacin akwai uwar, amma sai ka ga ana ƙoƙarin yin uwar ɗakin, ko ma ka ga an yi uwar ɗakin. Za ka iske ga malamin da ya karanci Hausa, kuma yana da ƙwazo, amma ba za a ba shi ya koyar ba, sai a ba shi Ciɓic Education, Social Studies ko Islamic Studies, idan ya so sai a ɗauki malamin da bai kai shi ƙwazo ba, ba shi da ƙwarewa ta fuskar Hausa, sai a ba shi darasin a ce shi zai koyar da Hausa.

3.2.3 Rashin Sanya Darasin Hausa A Muhimmin Gurbi A Jadawalin Shiga Aji

          Sau da dama za ka ga an mayar da darasin Hausa ƙarshen lokaci, wato dab da za a tashi, a wannan lokaci kuwa ɗalibai sun gama galabaita, kowanensu na marmarin tafiya gida sakamakon gajiya ko yunwa; ta yadda cikkunansu ke kiran ciroma. To a irin wannan yanayi babu yadda za a yi darasi ya samu gurbin zama a zukata ko ƙwaƙwalen ɗalibai walau manya ne ko ƙanana; sai ɗaiɗaiku.

3.2.3 Nuna Wariya Ga Malaman Hausa

          A tsakanin shugabannin makarantu, wasu daga ciki kan nuna wariya tsakanin malaman da suka karanci Hausa kuma suke koyar da ita, da waɗanda suke koyar da wani darasin da ba Hausa ba. Wannan ta sanya koda wani ɗan kuskure aka samu, an fi ƙarfafa na malaman Hausa a kan na wanda ba Hausa suke koyarwa ba, har ma su akan yi musu afuwa a nan take.

          A gefe guda kuwa, idan malaman Hausa suka nemi kafa wata ƙungiya irin wadda tsarin ilimi ya aminta a kafa a makaranta domin kaifafa tunani da samar da wani yanayi na sanya gasa tsakanin malamai, za ka iske ba sa bayar da goyon baya.

3.3 Ƙalubale Daga Malamai

          Malamai a junansu suna haifar da babbar matsala a tsakaninsu wanda wannan shi ma babban ƙalubale ne. Daga cikin irin ƙalubalen da ake samu ta ɓangaren malamai akwai:

3.3.1 Rashin Mutunta Malaman Hausa

          Malaman da suke koyar da darusan kimiyya, fasaha, yanayi, harkar gona da ilimin sanin halittu ko Turanci, za ka iske ba su fiye  ɗaukar malamin da yake koyar da Hausa da muhimmanci ba, bal ma a wani lokacin sukan ɗauke shi a matsayin abokin tsokana, wannan kuwa koda a cikin ɗalibai ne. Hakan ta sanya za su iya gaya wa malamin Hausa dukkanin kalmar da suka ga dama idan wani saɓani ya ɗan gitta tsakaninsu.

3.3.2 Nuna Wa Ɗalibai Karantar Hausa Ɓata Lokaci Ne

          Sau da dama za ka iske malaman da suke koyar da wani darasi da ba Hausa ba, suna ɓata malaman Hausa a gaban ɗalibai ko kuma su nuna wa ɗaliban yin karatun Hausar ma asarar lokaci ne.

3.4 Ƙalubale Daga Malaman Hausa

         Bahaushe kan cewa, ‘Da ɗan gari kan ci gari’, kuma ‘Sai bango ya tsage; ƙadangare ke samun wurin shiga’. Wannan magana haka take, domin mafi yawan wasu ƙalubalen da ake samu a cikin makaranta game da Hausa suna samo asali ne daga malaman da suke karantar da Hausa. Daga cikin ƙalubalen da ake samu daga wurinsu akwai:

3.4.1 Rashin Ɗaukar Darasinsu Da Muhimmanci

          Mafi yawan malaman Hausa ba sa ɗaukar darasinsu na Hausa da suke koyarwa da muhimmanci, a wasu lokutan ma za aka iske suna jin kunyar su ce Hausa suke koyarwa. Wannan kuwa ba ƙaramin ƙalubale ba ne, domin ba yadda za a yi su karantar da ɗalibai yadda ya kamata dubi da yadda su ma ba son abin da suke koyarwar suke yi ba. Da wuya ka ji su sun zauna suna tattauna wasu muhimman batutuwan da ake koyarwa a Hausa, ko ƙara wa junansu sani.

3.4.2 Rashin Zurfafa Bincike

          Aikin koyarwa dole sai da bincike ta hanyar karance-karance da sayen litattafan da za su taimaka masa wajen ƙara wa kansa sani da zurfafa iliminsa. Har wa yau, zai yi wuya ka ga malamin Hausa yana da niyyar ci gaba da karatunsa a mataki na gaba domin karantar Hausa, in dai a matakin firamare ne ko sakandare sai ɗaiɗaiku. Domin waɗanda suka karance ta ɗin ma, suna ganin sun karance ta ne ala dole, amma ba wai domin sun so ba.

3.4.3 Rashin Kafa Ƙungiyoyin Hausa (Hausa Kulob) A Makarantu

          Kafa kulob-kulob a makarantu abu ne da yake jan ra’ayin ɗalibai kuma yake sanya musu son harshen da ake amfani da shi. To a yankunanmu, babu ire-iren waɗannan kulob ɗin da aka buɗe domin raya harsunan Hausa a makarantu. Ire-iren waɗannan kulob ɗin ne ke shirya tarukan Makon Hausa domin raya al’adu da harshen Hausa a makarantun sakandare da na sama da su, musamman a wasu jihohin da suke wannan Ƙasa.

3.4.4 Rashin Sabunta Tunani Da Sanya Al’amura na Zamani A Yayin Koyarwa

          Hausawa suka ce, ‘Zamani riga; kowane da irin tasa’. To a nan ba a samun sauyi ta fuskar koyar da Hausa, ba a sanya al’amuran zamani, ba a yin amfani da kayan zamani koda kuwa a cikin manhaja ne. Wannan ta sanya ɗaliban ba su san abubuwa da dama ba, domin rashin kyakkyawar fassara ko rashin kwatanta wasu abubuwan al’ada ta hanyar amfani da abubuwan zamani.

3.4.5 Rashin Gogewa Ta Musamman

          Himma ba ta ga rago’ in ji ‘yan magana. Akan samu rashin gogewa ga kaso mai yawa daga cikin malaman da suke koyar da Hausa a matakin firamare ko sakandare. Wannan kuwa ya biyo bayan wasu cikin abubuwan da suka gabata, ko dai ba su karanci Hausa ba, ko kuma suna karantar da ita ce tilas, domin ba darasin da za su iya koyarwa.

3.4.7 Rashin Kai Ɗalibai Yawon Gane Wa Idanu Wasu Muhimman Abubuwan Da Aka Karanta A Aji

          A tsarin koyarwa, akwai kai  ɗalibai yawon gani da idanu kan abin da aka koyar musu a cikin aji. A darasin Hausa, ba a ɗaukar ɗalibai domin kai su ire-iren wuraren tarihi ko wasu sana’o’i na gargajiya, malami mai ƙoƙari ne kaɗai yake nuna wa ɗalibai hotunan wasu abubuwa, kamar su ganguna, tukwane da wanin waɗannan.

3.5 Ƙalubale Daga Ɗalibai

          Ɗalibai a nasu matakin, su ma suna da nasu gudumawa wajen haifar da wasu matsalolin da ake samu. Daga cikin ƙalubalen da ake samu ta fuskar ɗalibai musamman waɗanda ke sakandare akwai:

3.5.1 Zuga A Junansu

          Sau da dama ɗalibai kan zama a junansu suna tattauna irin abin da suke son zama idan sun kammala karatunsu, wannan ya sanya za ka ji mafi yawansu suna mayar da hankali ne kan son zama likita, ko ma’aikacin jirgin sama, ko dai wani babba a wata ma’aikatar tarayya. Kaɗan ne cikin ɗalibai ke marmari ko burin zama malamai; su ɗin ma ba za ka ji sun nuna sha’awarsu ga zama malaman Hausa ba. Idan an samu wani ɗalibi/ɗaliba ya/ta nuna sha’awar son karantar Hausa ko burin zama malamin Hausa, to za ka ji sauran ɗaliban suna zuga shi/ta cewar me zai/za ta yi da Hausa? Ai karantar Hausa shiririta ce da ɓata lokaci. Irin wannan zugar kuwa, takan yi tasiri a zukatan da yawa cikin ɗalibai har ta kai ga sun haƙura da wannan buri da yake ransu.

3.5.2 Fahimtar Lokacin Darasin Hausa A Matsayin Lokacin Hira Da Wasa

          Duk lokacin da malamin wani darasi ya shiga aji, za ka iske ɗaliban sun nutsu tare da mayar da hankali a kan abin da ake koyar musu. Amma ga darasin Hausa; abin ba haka yake ba, domin sau da dama za ka iske wasu ɗaliban sukan guje wa darasin Hausa; musamman idan ya kasance malamin na da doka da bibiyar komai, idan kuwa malamin maras tsawatarwa ne, za ka ga ajin ya zama tamkar kasuwa a ranar jajiberen sallah.

3.6 Ƙalubale Daga Iyaye

          Iyaye suna da rawar da suke takawa imma wajen kawo wa darasin Hausa cikas ne ko kuma wajen ciyar da shi gaba. Cikin irin ƙalubalen da ake samu ta fuskar iyaye akwai:

3.6.1 Rashin Bayar Da Goyon Baya Ga ‘Ya’yansu Masu Son Karantar Hausa

          A matakin sakandare imma ƙarama ce ko babba, iyaye ba sa bayar da goyon baya ga ‘ya’yansu da suke nuna sha’awarsu ga darasin Hausa. Sau da dama iyaye ba sa ɗaukar ɗansu ko ‘yarsu da suka yi ƙoƙari a darasin Hausa a matsayin abin birgewa da so. Za su iya bayar da kyauta ga ‘ya’yansu da suka yi bajinta a wasu darusa, amma ban da Hausa.

3.6.2 Rashin Bincikarsu Darasin Hausa

          Daga cikin abin da yake ƙara ƙoƙarin ɗalibai akwai binciken da iyaye suke musu game da darusan da aka koya musu a makaranta. A irin wannan binciken, za ka iske iyaye ba su fiye bincikar ‘ya’yansu abin da aka koyar musu a Hausa ba, domin su a wurin su; yin ta da barinta duk ɗaya.

3.6.3 Rashin Ganin Muhimmancin Malaman Hausa

          A duk lokacin da iyaye suka ziyarci makarantun da ‘ya’yansu suke karatu, za ka ga suna nuna farin ciki ga malaman da suke koyar da darusan kimiyya ko Turanci, a daidai lokacin da ba sa nuna irin wannan fara’a ga malaman da suke koyar da darusan Hausa, har ma idan malamin mai bin aikinsa da bibiyar ayyukan ɗalibai da yi musu horo kan sakacinsu ne, to iyaye akn ji haushinsa.

3.6.4 Ƙin Saya Wa ‘Ya’yansu Takardun Hausa

          Kusan kowane darasi ƙunshe yake da littattafan da ake karantawa, musamman a matakin sakandare, ko kuma ƙananan littattafan da ake koyarwa na koyon rubutu na Hausa ko harufa. Za ka iske iyaye ba su damu da su saya wa ‘ya’yansu ire-iren waɗannan littattafai ba; duk kuwa da ƙarancin kuɗaɗen da ake sayar da su. Amma ga wasu darusan, za ka iske iyaye na gaggawa wajen sayen littattafai da sauran kayan da za su taimaka wa ‘ya’yansu su koyi waɗancan darusa.

5.0 Abin Da Bincike Ya Gano

          Baya ga bayanai da suka gabata a wannan bincike, binciken ya gano wasu cikin ƙalubalen da ake samu yayin koyar da harshen Hausa a makarantun firamare da sakandare, waɗannan ƙalubalen kuwa sun samu ne ta fuskoki da dama kamar yadda binciken ya lalubo. A binciken, an gano inda matsala ta farko ta samu; wato matsala daga wurin gwamnati ko hukumar ilimi, ta yadda ita ce mataki na farko wajen gyara ilimi ko lalata shi. To a binciken an ga yadda sakaci da rashin ko in kula ga harshen Hausa yake fuskanta daga gwamnati ko hukumar ilimi. Binciken ya sake gano ƙalubale na biyu ya fito daga shugabannin makarantu ne a mataki daban-daban, la’akari da bambance-bambancen makarantu. A binciken an gano malaman da suke koyar da Hausa ma suna da nasu kaso na haifar da wannan ƙalubale, kamar rashin bincike da ƙamatar koyar da Hausa bisa tsari da kuma rowar maki a yayin gwaji ko jarabawa. Har wa yau, binciken ya gano wani ƙalubale daga rukunin iyayen yara, ta yadda rashin kulawarsu ga darasin Hausa ke kawo cikas da matsaloli. Binciken dai ya gano wani ƙalubale daga wurin ɗalibai da kuma malamai a junansu, ta yadda suke kyarar malaman da suke karantar da harshen Hausa da kuma nuna musu wariya ko bambanci.     

           Idan har waɗannan bayanai da suka gabata su ne abin da bincike ya gano, ke nan an samu hanyoyin fita daga ƙalubalen muddin aka ɗabbaka waɗannan shawarwari. Shwarwarin kuwa sun haɗa da:

a. Ɗaukar ƙwararrun malaman Hausa a matakan firamare da sakandare, waɗanda su ne za su zama tsani ga koyar da harshen Hausa a makarantu.

b. Samar da kayan aikin koyarwa da zamanantar da tsarin koyar da Hausa.

c. Shirya tarukan bita ga malaman Hausa da suke makarantun firamare da sakandare.

d. Tura malaman Hausa ƙaro karatu da kuma bibiyarsu a makarantun.

e. Samar da sabuwar manhaja da sauya takardun zamani.

f. Kafa ƙungiyoyin raya harshen Hausa a makarantun firamare da sakandare

g. Sanya darasin Hausa a jerin darusa masu muhimmanci.

h. Gina ɗakunan amon sautuka da gwaje-gwaje na Hausa da adana kayan al’adu na Hausawa.

i. Sanin muhimmancin abin da ake karantawa daga malaman Hausa da Samun mutuntaka tsakanin malamai.

j. Kafa hukuma a ƙarƙashin ma’aikatun ilimi mai kula da al’amuran koyar da Hausa, (Hausa Board).

6.0 Kammalawa

          Daga cikin abin da ya gabata a wannan bincike, an bayyana ma’anar koyarwa sannan aka ɗora bayani a kan koyar da harshen Hausa a makarantun firamare da sakandare. A cikin nazarin, an bibiyi ƙalubalen da yake kan darusan Hausa a makarantun firamare da sakandare ta fuskoki da dama, ta fuskar gwamnati da hukumar ilimi, ta fuskar shugabannin makarantu, ta fuskar malaman da suke koyar da wasu darusa waɗanda ba Hausa ba, ta fuskar malamn da suke karantar da Hausa, ta fuskar ɗalibai da kuma iyayen yara. Takardar, ba ta tsaya hakaito matsaloli kaɗai ba, sai da ta bibiyi hanyoyin da ake kyautata zaton matuƙar an bi su; to ko shakka babu za a fita daga cikin waɗancan ƙalubale na matsalolin da suka yi wa darasin Hausa katutu a makarantun firamare da sakandare.

 

Manazarta

Tuntuɓi masu takarda.

Post a Comment

0 Comments