Takardar da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa mai taken: Zamfara Kingdom: Social and Political Transformation from 14th Centuary to Date. Organized by Faculty of Arts and Islamic Studies Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, 25th – 28th February, 2020, at Usmanu Danfodiyo University Auditorium, Sokoto
ZAMFARA
A DIWANIN NARAMBAƊA
(Ibrahim Buhari Maidangwale Abdulƙadir Narambaɗa Tubali 1810-1960)
Aliyu Muhammadu Bunza
Professor of Hausa Cultural Studies
Department of Languages and Cultures
Faculty of Arts and Humanities
Federal University Gusau
Gabatarwa
Zamfara daula ce gawurtacciya daga cikin gawurtattun daulolin ƙasar Hausa.[1]
Haka kuma, tana daga cikin daulolin farko da tarihin Bahaushe, da ƙasar Hausa, ba ya
kammala sai da ita. Wata daɗaɗɗiyar al’adar mazauna
duniyar mutane ta shahara da ita ita ce, “waƙa.” A ƙasar Hausa, duk abin da ya ɓace wa Bahaushe cikin waƙa ana iya tsintarsa. Don haka, na zaɓo wani babban goga, daga cikin gogaggun mawaƙan Zamfara Ibrahim Buhari
Maidangwale Abdulƙadir Narambaɗa Tubali,[2]
domin mu karanci daular Zamfara cikin diwanin manyan waƙoƙinsa. Ga yadda na fasalta ɗan abin da na kalato cikin diwanin malamin kiɗa Narambaɗa.
Kadadar Bincike
Daular Zamfara faɗi gare ta, kuma al’ummomi sun yi sarƙeƙeniya a cikinta. Narambaɗa Malamin mawaƙa
ne da har yanzu ba a haƙiƙance yawan waƙoƙinsa ba.[3]
Bincikena zai tsaya ga waƙoƙin da ya yi wa sarakunan da ke
daular Zamfara kawai. Ko a cikin waƙoƙin zan fi lura da gutsattsarin ɗiyan waƙa da suka ambaci Zamfara ko da wani suna nata na daban. Bugu da ƙari, zan fi mai da
hankali ga ɗiyan waƙar da suka taɓo tarihin da ya shafi Zamfara. Abin kula a nan, takardar ɗan share fage kawai za ta yi, don tarnaƙin da aka saka na yawan
shafukan da aka ƙayyade.
Dabarun Bincike
Kan takardar wannan bincike shi ne Narambaɗa. Wannan ta tilasta, sauraron waƙoƙinsa musamman waɗanda suka shafi Zamfara da masarautunta fiye da shirin
(20). Bayan
haka, aka yi yaɓi da tattaunawa da wasu daga cikin sarakunan masarautun, da aka ayi wa waƙoƙin, da wasu ɗiyansu, da wasu daga cikin masu riƙe da wasu sarautu, da
fadawa, da kaɗan daga cikin na bayan fage masu
sha’awar Narambaɗa. Ala tilas, aka sake laluben wasu ayyukan ilmi da aka yi kan Zamfara da waɗanda suka shafe ta musamman Nadama,
(1977) da Mahdi, (1968, 1975) da Alƙali, 1968 da Last, (1969) da wasu muhimman
wallafe-wallafe, domin kwakkwahe riwayoyin Narambaɗa.
Matsayin Adabi a Nazarin Tarihi
Na zaɓi in yi garkuwa da adabi domin ƙyallaro wani tarihi daga
cikin diwanin tarihin Zamfara. Na zaɓi yin haka domin babu wani tarihi a duniyar mutane da aka rubuta wajen
taskar adabin mutanen da ake rubutu a kansu. Adabin baka a wajen masana tarihi
irin su Muhammadu Bello,[4] A.
H. Car,[5]
Abdullahi Smith,[6]
M. G. Smith[7]
M. Adamu,[8] Y.
B. Usman,[9] M.
Hisket,[10]
M. Last,[11]
Samaldone,[12]
P. J. Shea,[13]
J. Paden,[14]
sun tabbatar da cewa da tsohon zuma ake
magani. A adabin waƙa, ba a rasa cikas na kambama da kushewa, da ƙage da ƙaƙale, da tabbataccen kwanan wata da
sauransu,[15]
Waɗanan cikas ko rubuce-rubucen ilmi na
masana ba su tsere musu ba. Tarihin gidansu kowa da abubuwan da aka riska a
baka ne aka taskace shi, aka adana shi. Daga cikin sassan adabin baka, waƙa da karin magana da
kirari su ne mafi ingancin taskokin taskace tarihi waɗanda gobara, da ambaliya, da sata, da salwanta, ba su
cika yi wa ta’adi ba.
Wane ne Narambaɗa?
Cikakken sunansa Ibrahim Buhari Maidangwale, Abdulƙadir Narambaɗa Tubali. Mahaifinsa tafiyayye ne daga ƙasar Maraɗi(?). Mahaifiyarsa daga gidan Makaɗan Badarawa aka auro ta, sunanta Riba. Bai gaji kiɗa daga uba ba, ga uwa ya gada. A al’adance, sunansa Karen
Makaɗa.[16]
Ya fara kiɗin noma da kokuwa, ya koma kiɗin sarauta. Ya yi wa masarautar Isa da Gobir da Ƙaura da Moriki da Zurmi
da Gusau da Kwatarkwashi da Tsafe da sauran ƙananan masarautunsu waƙoƙi da yawa. Idan aka tattara waƙoƙinzasu fiɗaribiyar
(500)[17], amma shahararsa ta zarcesauran makadan fada a ƙasar Hausa. Fadar Isa ta Fulani yake yi wa waƙa, amma bai hana ya yi wa fadar
Gobir da sarakunanta waƙoƙi ba. An haife shi a wajajen 1890, ya rasu a shekarar 1963. Ya rasu yana ɗan shekara 73 a duniya. Ya fara waƙa da shekara 40. Ya shekara 33 yana
waƙa. Ya fara waƙa da cikakken hankalinsa ya mutu cikakken dattijo. Ba a sa ran zantukanƙarya su bazu a waƙoƙinsa. Don haka, yana zama wata hujja ga tarihi ya ce:
Jagora: Na bar ƙarya ko ina kiɗi
: Na wuce ƙarya ko ina kiɗi
: Nai sittin saba’in nika
hwaɗa[18]
: Mai saba’in yai ƙarya
Yara : Ana ta zunɗenai
:Ko yaran da ag garai
: Duk warwatse masa sukai
: Shina yawo shi ɗai ɓaro-ɓaro
Gindi : Ya ci maza ya kwan shina shiri
: Uban zakara dodo na
Alhaji
Dalilin yi masa suna Malamin kiɗi, bai taɓa barin sharholiyar waƙa ta
shi zage-zage ko cin fuska, ko batsa, ko kambamar zulaƙe ba[19]Ɗan dalilina ke nan na shiga diwanin waƙoƙinsa in lalubo tairhin Zamfara.
Ƙasar Hausa a
Diwanin Narambaɗa
Tarihi da tarihihin ƙasar Hausa ya zo da abubuwa da
yawa. Tun daga tarihin Bayajida ya zuwa ga rubuce-rubucen masu jihadi da suka taɓo tarihin ƙasar Hausa da masarautunsu. Manyan ayyukan masu jihadi
sun haɗa da Rawdhatul Afkaari waj Tilaatul
Akhbaari fit Taarihil Bilaadil na AbdulƙadirƊantafa, da Infaƙul Maisuuri fi Taarihil bilad,na Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, da Ta’alimul Ikhwaani bil Umuuri
Allatii Kaffarnaa bihaa Mulluukus Sudan Wahum Muluuku Hausa, da Hukumul
Juhhal fi Biladi Hausa duk na Shehu Mujaddadi Ɗanfodiyo, sun ambaci ƙasarmu da sunan “ƙasar Hausa.: Daulolin da
suka taras a lokacin sun haɗa da Kano, Gobir, Zamfara, Kabi, Zazzau, Katsina, da Bauci. Suna kiran ƙasar Bilaadi Hausa, Sarakunan
Muluuku Hausa ko Muluukus Sudan. Abin nufi dai, Zamfara na daga
cikin ƙasashen da suka haɗa daulolin, kuma daular kanta ce.
A ɓangaren masarautun, da daulolin,
suna kiran kansu da sunayen daulolinsu, Daular Kano, Daular Katsina, Daular Kabi, Daular Zazzau, Daular Gobir, da Daular Zamfara.
Kasancewar mutanensu Hausawa, harshensu Hausa ya sa ake kiran daulolin “Ƙasar Hausa.” Bayan
jihadi, daulolin da ƙasashen da Fulani suka mamaye su ake kira da sunan “Hausa,” Zamfara na daga
cikinsu.[20]
A Diwanin Naramaɗa da kalmar “Hausa” ya yi amfani da
ita ga Daular Zamfara gaba ɗaya.[21]
Me ya sa haka? Domin kiyaye tarihi da sassauyawar zamunansa.
Zamfara ce Kadadar Hausa inji Narambaɗa
Narambaɗa na tare da tunanin Kabawa da ke da fahimtar duk ƙasar da ba ta Fulani ba, kuma Fulani ke mallakarta
sunanta “Hausa.”[22]
A diwanin Narambaɗa ya ambaci ƙasar Isa da Fulani ke mulki da sunan
“Sarkin Gobir Hausa.” Gobirawa da Kabawa da Zamfarawa ke da ƙasarsu. Zamfarawan Anka
(Wusake) suka fara zama Zamfara. Daga nan Gobirawa suka zo, bayansu Fulani suka
zo. Da aka ga Gobirawa sun fi yawa, aka naɗa wa Bafulatani rawanin Sarkin Gobir ta koma “Sarkin
Gobir na Isa[23].”
Diwanin Bakandamiya ta ambaci wannan a wurin da Narambaɗa ke cewa:
Jagora : Yau mai ashararu ya kaɗe
: Duniya ta yi mai hwashi
Yara : Ya san ba ƙwarjini ga mutanen Hausa
: Kowac ce shina iyawa ga
hili nan
: Sai ya ƙetare gidanai ba ban
kwana
Gindi : Gwarzon shamaki na Malam
toron giwa
: Baban Dodo ba a tammai
da batun banza
A nan, a garin Isa mai ashararu yake. Mutanen da aka ce ba a ƙwarjini gare su watau
“mutanen Hausa” mutanen Isa ne ko in ce Gobirawan Isa da Fulani ke mulki.
Makaɗa Narambaɗa ya ambaci babban birnin tarayyar Zamfara “Gusau” a
matsayin kadadar ƙasar Hausa. Daular Zamfara ta yi iyaka da Daular Zazzau, da Katsina. Can
kuma Zazzau da Katsina, sun yi iyaka da Daular Kano. Ita kanta Zamfara ta maƙwabci daular Gobir. Ga
yadda diwanin Narambaɗa ya warware batun:
Jagora : Tun dag ga Kaduna
Yara : Har Gusau ƙarewar Hausa
: Kowace shawara ta
labarin Turawa
: Amadu ba a yin ta sai ya
san hannunai
: Don kauƙoƙari garai da sanin hujjoji
Gindi : Gwarzon shamaki na Malam
toron giwa
: Baban Dodo ba a tammai
da batun banza.
Ke nan, Kaduna da
Zazzau da Kano da Katsinamakwabtasu asashen Hausa ne, kumaDaulolinƙasar Hausa, amma ba
“Hausa” ake ce musu ba. Hausa ita ce, Gusau da masarautun da ta yi wa cibiya. Dalilinmu a nan shi ne,
Zamfara ce ƙarƙashin Sakwkato, sauran daulolin cin gashin kansu suke. Zamfara da Gwandu da
ke cikin hamattan Fulani su ne “Hausa.”[24]
Sakkwato ce Cibiyar Hausa
A diwanin Narambaɗa, da Zamfara da Sakwkato duk abu ɗaya ya ɗauke su a matsayin “Hausa.” Diwanin
ya tabbatar
da Sakwkato ce cibiyar “Hausa” ƙasashen da ke amsa kiranta sau-da-ƙafa su ne “Hausa.”[25]
Zamfara ita ce babbar daular da ke ƙarƙashin Sakkwato. Gwandu wata ‘yar leza ce kawai.[26]
Diwanin Bakandamiya ya yi wannan fashin baƙin:
Jagora : An gamu Hausa kulluhin
jama’a duk an zo
Yara : Kamfunan ga arba’in da
bakwai duk sun zo
Jagora : Maiduka yah hito da shi da su
Gatau
..................................................................................
Gindi : Gwarzon shamaki na Malam
toron giwa
Baban Dodo ba a tammai da batun banza.
“Hausa” a nan ita ce “Sakkwato,” kamfuna arba’in da bakwai (47) Gundumomi
arba’in da bakwai na iyayen ƙasa arba’in da bakwai: Sakwkato, Zamfara, da Gwandu.
Makaɗa da ya wasa Sarkin Gobir Amadu cewa
ya yi:
Jagora: In an ce Isa, ba ka jin an ce, wani Sarki,
Yara: Ni ko duk Hausa, ba ka jin waƙa, bayan tau
Gindi : Gwarzon shamaki na Malam
toron giwa
Baban Dodo ba a tammai da batun banza.
Abin da makaɗa ke nufi da “Hasau: a nan, “Zamfara” da “Sakkwato” da sauran gundumomin da Sakkwato ta
mamaye. Narambaɗa ya tabbatar da haka a waƙar: “Ya ce maza ...”
Jagora: Ɗan mai Hausa bahago
Yara: Koma shirin daga na Alhaji
Gindi: Ya ci maza ya kwan shina shiri
: Uban bahago dodo na Ummaru
Sarkin Gobir Amadu Bawa ne ake cewa ɗan mai Hausa, wato ɗan Sarkin Musulmi ke nan. Sarkin Musulmi shi ne mai “Hausa” dukkanin ƙasashen da kakaninsu
suka mamaye, nan ne Hausa. Zamfara na
daga cikin babbar daular da Fulani suka mamaye.
Zamfara Rumbun Adabi
Daga cikin manyan diwanin makaɗa Narambaɗa Zamfara ita ce babban rumbun
adabin Hausa a duniya. Lallai biri ya yi kama da mutum, domin kashi 75-80 na
makaɗan Hausa Zamfarawa ne. Da za a bi
diddigin tarihi na tushen kowane Bahaushen makaɗi, da wuya Zamfara ba ta lashe kashi 90% ba.[27] Duniyar ilmi ta aminta da kasancewar taskar
adabi babban rumbu na ilmi da tarihin al’umma. Lallai yankin da duk aka fi
samun ma’abota adabi, musamman waƙa, nan ake sa ran a gano tushen masu harshen. Abin
mamaki, tunanin masu biyar diddigin asalin Hausawa da harshensu ya kasa ya ƙyallaro wannan
muhimmiyar kafa da Narambaɗa ya ƙyallaro kamar haka:
Jagora: Zamfara ba makaɗin da ka ja mini
Yara: Baya ga Jankiɗi sai ko Ɗandawo
Jagora/Yara: Sai Ɗandodo Alu mai taushi
Yara: Amma ba makaɗin gayya ba
Gindi: Gogarman Tudu jikan Sanda
: Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa.
A daular Zamfara, makaɗan fada da kowa ya san da ficensu su ne: Narambaɗa, Salihu Jankiɗi Aliyu Ɗandawo, da Ɗandodo Alu mai taushi. Da an ambaci waɗannan a waƙar fada an kai sin-wau-ra-takuri. Waɗannan su ne kan takarda. Makaɗa kai tsaye ya ce Zamfara bai ce “Hausa” ba domin a ganinsa
a nan ya san da cewa Zamfara ce mahaifar makaɗa, a nan aka turbuɗe cibiyar kiɗi. Da an ce, mawaƙi ba ya da kama a
Zamfara, to duk a daulolin ƙasar Hausa babu kamarsa. Dalili shi ne, Zamfara ce Makkan
makaɗa. Duk wurin da aka tsinci makaɗi a daulolin ƙasar Hausa ba zai kai Zamfara ba. Wannan abin kuwa, har
yau (2020) haka yake.
A babban gabatarwar da ya yi wa Bakandamiyarsa, ya tsaro baiwar da Allah ya
yi wa Zamfara da fitattun mawaƙa kamar haka:
Jagora: Kowaz za ka kallo ya karkaɗe kunnenai
Yara: Ga makandamiya za ni yi cikin manyan waƙoƙi
Jagora: Na jiya Jankiɗi
Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora: Na jiya Gurso
Yara: Yayi tai uwar waka
sainai tau
Jagora: Na jiya Akwara
Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora: Na jiya Ɗandawo
Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora: Na jiya Nagaya[28]
Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau
Jagora: Dodo Malawin waƙa Kundanmi Magajin Danbaidu
Yara: Ya yi tai waƙa sai nai tau
A cikin wannan ɗan waƙa ya ambaci fitattun makaɗan Sarakunan Zamfara takwas. Salihu Jankiɗi, Gurso, Akwara, Ɗandawo (ya yi wa Sarkin Gobir Isa waka), Nagaya, Dodo Malamin waƙa kundumi Magajin Ɗanbaidu, da Narambaɗa. A masarautar Ƙaura Narambaɗa ya ambaci wasu shahararru uku da
ba su fito a jereƙen Bakandamiya ba.
Jagora: Yanzu fa Ƙaura an ka yi Sarki,
Yara: Don na ji jawabin Gabci
Jagor: Na ji batun Ɗankyana da Kabshe
Yara: Kowa ka ba shi rabonai
Gindi: Shiri bajinin Mamuda
: Abu na Namoda shirarre.
A wannan diwanin, mun samu Gabci, Ɗankyana da Gabshe, sun kai su goma sha ɗaya (11). A wannan lokacin da Narambaɗa ke waƙoƙin, dukkanin daulolin ƙasar Hausa ba mai fitattun makaɗan fada uku (3). Ashe diwanin Narambaɗa ya ba da babban haske cewa, ya kyautu a fara tunanin
taskace mawaƙan daular Zamfara da waƙoƙinsu.
Masarautun Zamfara a Diwanin Narambaɗa
Diwanin Narambaɗa wani furen kallo ne ga biyar taliyon diddigin tarihin daular ita kanta.
Narambaɗa ya yi waɗaiɗaikun Sarakunan Zamfara waƙoƙi ya kuma taskace fitattun garuruwan tarihi na Zamfara, a diwanin waƙoƙinsa. A riwayar bakandamiya akwai:
Jagora: Moriki Ƙaura da Zurmi, duk maganar ta zan dai
Yara: Bunguɗu sa Gusau, Kwatarkwashi, ga
‘Yandoto
Yara: Sun san Garba Ɗanhassan, shi yah hau gadon Hassan,
Jagora: Shi as shugabansu, kai ab babban ɗanai.
Yara: Komi kay yi ba a cewa, ba daidai ba
Jagora:Yara: Nasabar Shehu, ba ta ɗai da ta kakan kowa
Gindi : Gwarzon shamaki na Malam
toron giwa
Baban Dodo ba a tammai da batun banza.
Masarautun da suka bayyana a nan su ne: Moriki, Ƙaura, Zurmi, Bunguɗu, Gusau, Kwatarkwashi, da Tsafe. Bisa ga jereƙen Narambaɗa, a yanzu, duk waɗannan garuruwa manyan sarakuna gare su, masu sanda, kamar kowane babban
sarki, a daular ƙasar Hausa. Ashe gaskiyar Narambaɗa, “duk maganar ta zama ɗai.” Da an tura Isa Zamfara, babu mai hana a ba ta Sarki mai Sanda.[29]
Diwanin Narambaɗa ya taɓo wasu masarautu abokai, kuma masu
zumunta da Zamfara a wajen ƙasar Zamfara. Ya fito da ƙasashen da yake cewa: “Hausa” bisa
ga tarihin da ya tabbata yana cewa:
Jagora: Dubu ta kammala ga fadar Gwadabawa
: Kable da fadar Gwandu
Yara: Ga kuma Tangaza can ga Yabo
: Dange da Wurno da fadar
Sakwkato
: Dud dai Amadu ab babba ɗa
....................................................................
Gindi: Gogarma Tudu jikan Sanda
Maza su ji tsoron ɗan Maihausa
Jagora: Maradun, Raɓa, Dogon Daji
Yara: Sa Mafara da Gusau da Kadassaka
: Dud dai Amadu ab babban ɗa
: Ba ɗan tashi ka rama ne ba
: Giye tuda ka yi wa yaro
nisa
Gindi: Gogarman Tudu jikan Sanda
: Maja su ji tsoron ɗan Maihausa
Narambaɗa ya lissafo masarautu goma sha uku
da kowacensu na da alaƙar tarihi da Zamfara. Ya tsaro fadar Gwadabawa, Gwandu, Tangaza, Yabo,
Dange, Wurno, Sakkwato, Maradun, Raɓa, Dogon Daji, Mafara, Gusau, da Kadassaka. A tarihance, ya tsame sarautun da ake cewa “Hausa”, ya gwama da na Zamfara, domin
daidaita tarihi a gargajiyance. Dukkanin garuruwan na da ya ambata face ɗaya kacal a wannan ƙarni, duk sun zama ƙananan hukumomi, kuma garuruwansu ne cibiyar mulkin ƙananan hukumomin. Waɗanda suke cikin Zamfara su ne: Maradun, Mafara, Gusau da
Kadassaka. Gwandu tana cikin Kabi, daular Kabi tana da dangantakar tarihi da
Zamfara. Raɓa, Dogon Daji, Yabo, Tangaza, Dange,
Wurno da Sakwkato fitattun garuruwa ne a daular Sakkwato ta ƙarni na goma sha tara (ƙr. 19) su tarihi ke ce wa “Hausa.” Yabo na da sarkin
Kabi. Tangaza na da Gorzon.[30]
Makaɗa Narambaɗa ya harari wasu muhimman masarautun Zamfara da yake son
tairhi ya taskace su sosai yana cewa:
Jagora: Ga Ƙaura nan ga Zurmi can
: Yaro kauce Moriki ta
Yara: Mahammadu na na gidan Alu
: Manyan magabata sun hawo
Gindi: Ya ɗan girma ko ba a so
Maƙi gudu baban ‘yan ruwa.
Masarautun Ƙaura da Zurmi da Moriki manya ne ga tarihi, da yawan ƙasa, da yawan mutane, da tattalin
arzikin Zamfara. A fagen ilmi fitattu ne a Zamfara.[31]
Taskar Diwanin Gindin Waƙoƙin Masarautun Zamfara
Huskar abu ita ke sayar da shi. Ga al’adar diwanin waƙoƙin Narambaɗ tun a gindin waƙa za a gane dalilin da ya sa ya yi wakar. Gindin waƙar/Waƙoƙin Narambaɗa wani madubi ne na ƙyallaro tarihin masarautar da irin ƙwazonmazajen da take
hannunsu. Ga wasu daga ciki domin a tantance manufar wannan fasali:
Gusau: Mai Gusau Rabakaya, ba a kai maka wargi,
: Mai rabo da yawa,
ganda’aren Sarkin Gobir
Gindin ya fito da sarauta da shimfiɗa mulki, na a ji iko, a ga iko. Don haka aka ce: “ba a kai maka wargi.”
Kwatarkwashi: Yai halin mazan jiya
: Ɗansada mai Kwatarkwashi
Kiɗan yaƙi ne zangabur kuma ƙumshiyar waƙar ta tabbatar da haka.
Mazan jiya gawurtattun mayaƙan da.
Tsafe: Gagarau mai buge kangara Ali ‘Yandoto,
: Ba ya son wargi ba a kai
masa batun banza.
Kiɗin yaƙi ne ƙiri-ƙiri da ƙwazo ƙunshiyar waƙar ta tabbatar da himma da zimmar yaƙi. Buge kangara hana tawaye.
Kurya: Masu gari mazan gabas tsayayye
: Sarkin Rwahi ya wuce a
rammai
Kiɗin yaƙi ne ƙarara. An ce, har rawar yaƙi Narambaɗa ke yi in kiɗin kurya ne. Mazan gabas mayaƙan gabas ga Sakkwato.
Shinkafi: Ibrahim na Guraguri mai Shinkahi bajinin zagi
: Mu dai Allah ya bar muna
kaya.
Bajinin zagi bajinin jagora, a fagen yaƙi su ke gaba ba ja baya.
Shanawa: Gishimin Haliru uban zagi na Malam Isa
: Gagarau jikan Shehu Iro
toron giwa
Kiɗan yaƙi ne ciki da waje. Ƙunshiyar waƙa ya ƙara tabbatar da gindin.
Gagarau an gagari abokan yaƙi.
Maradun: Ya buwayi maza ginshiƙin tama na Amadu
: Moyi ƙigudu ɗan Sanda mai halin mazan jiya
Tun a ɗan waƙa na farko an fito da jigon waƙar wato kiɗan yaƙi ne na tashi tsaye, a fuskanci masu son karɓar fansa. Ginshiƙin tama ba ya turuwa ba ya kauruwa, tirƙashi!
Da waɗannan ‘yan misalai bakwai za mu fahimci cewa, daular Zamfara ta yi yaƙe-yaƙe da yawa. Gindin waƙoƙin masarautunsu na nuna, ga aƙidar Zamfarawa raggo, tanfaski,
matsoraci, ba zai sarauce su ba. Gindin waƙoƙin kaɗai, wata taska ce daga cikin manyan taskokin diwanin
adana Zamfara a cikin waƙoƙin Narambaɗa.
Ƙyallaro
Jaruntakar Zamfarawa a Fagen Artabu
Narambaɗa makaɗin sarauta ne. Sarautun ƙasar da yake yi wa waƙa watau ƙasar Isa sun sha
gwagwarmayar yaƙe-yaƙe na jahiliyya da na jihadi. A farfajiyar daular Zamfara, babu wata
masarautar da ba ta yi yaƙin cikin gida da wajen gida ba.[32]
Nason wannan gwagwarmayar a fili yake idan muka karanci kirarin yaƙi da jaruntaka da
diwanin Narambaɗa ya taskace a diwanin Kwatarkwashi:
Jagora: A runguma uban Yari
Yara: Mazan gabas ga Sakwkato
Jagora: Ba shawagi sa maza yawon duniya
Yara: Suna sai da abin hwaɗi ga ‘yan uwa
Gindi: Yai halin mazan jiya
: Ɗan Sanda mai Kwatarkwashi
“A runguma” kalmar yaƙi ce, ta tunkarar abokin gaba gaba-da-gaba, komai taka zama ta zama. A
fagen yaƙi sun sa maƙiya shawagi, da dawara, suka bar wa na baya abin faɗi/kunya. A masarautar Shinkafi akwai irin wannan jirwayi:
Jagora: Gadan-gadan na Sambo na Aisa
Yara: Gaƙe maza uban Turawa
Jagora: Riƙa da gaskiya Ibrahim
Yara: Mai taimakonka Allah na nan,
Jagora/Yara: Zan ka wa maza gurnani
Gindi: Madogara na Malam Iro
: Uban Yari mai gidan
Shinkahi
Kalmar “gadan-gadan” kirari ce mai nuna fuskantar abu da anniya ba da wasa ba. A fagen daga
tana nuna a yi taho-mu-gama mai rabon ganin baɗi ya gani. Idan gumurzu ya yi gumurzu a fagen yaƙi, zancen magana ba ta
taso ba, sai dai gurnani. Gaƙe maza, a takura su a hana su zuwa gaba bale baya.
A fagen yaƙe-yaƙen ƙasar Hausa, Zamfarawa suka fara
shimfiɗa buzun artabu gabanin Gobirawa su
zo. Idan Narambaɗa na kiɗin yaƙi yakan gabatar da Zamfara a irin wannan gaɓa.
Jagora: Zamfara sun san kana Isa
: Gobir sun san kana Isa
: Amadu miƙe ƙafafunka zauna daidai
Jagora/Yara: Magana ce ta Sarkin Musulmi Sa Bubakar
Yara: Sun sani Hausa
Gindi: Amadun Bubakar gawarzon Yari
: Dodo na Alƙali
Sarki Amadu ake yabo da fama, amma da aka zo ga zancen yaƙi dole aka lalubo “Zamfara” gabanin Gobir domin Gobirawa Zamfarawa suka
taras a ƙsar Zamfara.
Wasannin Motsa Jiki
Kowace al’umma ta duniya tana da wasannin da take tarbiyantar da yaranta,
domin sa musu nagarta da himma, da ɗebe tsoro, da jiran ko ta kwana. A ƙasar Hausa, manyan wasannin da ake ɗora yara a kai su ne, kokuwa da dambe. A diwanin Zamfara
waɗannan wasanni biyu wani babban jigo
ne a waƙoƙin fada. Makada
Narambada ya ce:
Jagora: Bamin[33]
kokawwa bai iya ba,
: Shi aka shammata
kodayaushe
Yara: Ga wata kokuwwa an wuce da shi
Jagora/Yara: Ƙarsanai[34] kakkaɓe mishi ƙasa
Gindi: Ibrahim na Guraguri
: Mai Shinkahi bajinin
zagi
: Mu dai Allah ya bar muna
kaya
A cikin waƙar “ya ci maza...” Narambaɗa ya kawo zancen dambe a matsayin jarunta da iya yaƙi, ya ce:
Jagora: Uban zakara mugun madambaci
Gindi: Ya ci maza ya kwana shina shiri
: Gamda’aren sarkin Tudu
Alu
Wasan dambe da kokuwa su ne wasannin ƙasar Hausa na motsa jiki. A Zamfara su ne fitattun
wasanni musamman idan aka dubi dangantakar Katsina da Zamfara da Maraɗi ta ɓangaren Katsinar Laka.[35] A
da, babu garin da babu fagen dambe,babu garin da babu runji Hausa, duk wurin
da runji suke ana samun wasar dambe. Shaharar Shagon Mafara[36]
ba ɓoye take ba a farfajiyar ƙasar Hausa:
Sana’o’in Zamfarawa
A tsarin shimfiɗar da Allah Ya yi wa Zamfara, ƙasar sana’o’in more wa rayuwa ce. Manyan sana’o’in
Zamfara su ne, noma da su, da fatauci. A farfajiyar ƙasar Hausa, waɗannan su ne manyan sana’o’in Bahaushe a ko’ina yake. A waƙar Sarkin Shinkafi
Ibrahim Narambaɗa ya taskace noma kamar haka:
Jagora: Kowane ɗan sarki son shikai shi zan sarki
: Sai in ba ta samuwa
: Ta tabbata ko ban hwaɗi ba
: In gandu[37]
yas samu ya hi gamana.[38]
: Ibrahim na Guraguri
: Mai Shinkahi bajinin
zagi
: Mu dai Allah shi bar
manna kaya
Bazamfaren asali ba sai an yi mishi fashin baƙin kalmar “gandu” da “damana” ba
domin cikinsu ya tashi. Wannan ɗan waƙa zakara ne daga cikin zakarun ɗiyan waƙoƙin diwanin Narambaɗa. A fagen “Su” yana cewa:
Jagora: Da a ce gu gai da ɗan mai taru[39]
: Gara a ce mai taru
: Ƙwak kashe kihinai
: Sai shi nasa goranai[40]
: Na riƙa ka ga girma Audu ƙanen mai daga
: Kan da mu san kowa kai
mun ka sani Sardauna
Ƙwararrun masunta kawai suka san
“taru” da irin amfaninsa da matsayinsa a sana’ar “su.” Nasa kifi gora sai ‘yan
gado (sarkawa) ke fashin baƙinta. Idan muka duba waƙar da aka yi wa Alhaji Ɗandurgu Ƙaura da ambaton su
Alhaji Ɗanwawu tabbacin Zamfarawa a fagen fatauci gaba suke.[41]
Halayen Zamfarawa
Hausawa na cewa, kamar Kumbo kamar kayanta. Ga alama, halayen sarakunan
Zamfara, shi ne halayen talakawansu. Narambaɗa na kallon Zamfarawa mutane masu nagarta da ƙwazo. Mutane ne da ba sa
son ragganci da raggo da zauna gari banza. A Zamfara sata babbar abin kunya ce,
duk a cikin waƙoƙin masarautun Zamfara da Narambaɗa ya yi, babu ko wuri ɗaya da ya zargiwani ɗan sarki da sata, ko
bafaden sarki, ko ‘yan adawar sarki. Don haka, ko’ina aka
ga ɓarawo a Zamfara baƙo ne, tafaffe ne, in ga
uba in ga kaka. Da wuya a samu Bazamfare wawa, shi ya sa ake zargin su da yawan
ruhi har da kirarin: “galma uwar ruhi.”[42]
Narambaɗa ya ɗan gutsuro haka a waƙar Magajin Shinkafi Ibrahim yana
cewa:
Jagora: Haba! Ba su amana
Bas su da Allah
Jagora/Yara: Komi suka yi, ya sani
: Munahukkai ku bi sannu
“kar” shika gani
Gindi: Ibrahim na Guraguri
: Mai Shinkahi bajinin
zagi
: Mu dai Allah shi bar
muna kaya
Mai wayo da wawa, ba a shan inuwa ɗaya. Magaji Ibrahim “kar” yake gani, watau kansa garas yake, sai dai ya yi
ruhi don kunya, amma ba don bai gane ba. A masarautar Ƙaura wayon Zamfarawa ya fito ɓaro-ɓaro a faɗar Narambaɗa:
Jagora: Gidan ga mutum huɗu ba su arauta,
: Da samɓalto da satoto
: Shi wanga na ukku ƙazami
Jagora/Yara: Na cikon na huɗunsu hawa’i
Gindi: Shiri bajinin Mamuda
: Abu na Namoda shirarre
Sambalto babban wawa ke nan. Satoto ya fi sambalto haukar wauta.[43]Ƙazanta ba a san ta ga
masu wayo ba, ga ƙauyawa da wawaye aka san ta. A
riwayar Narambaɗa na huɗu shi ne “hawa’i” ɗan iska ko shashasha
ko mahaukaci. Ba a shashasha sai wawa.
Sakamakon Bincike
Na zaɓi gogaggen makaɗin fada ɗaya, domin ya jagorance ni ga karatun daular Zamfara. Wanda na zaɓo, a wajen uba Babarbare ne, a wajen uwa Bazamfare. A
al’adance, Karen Makaɗa ne ya san sarauta ya san makaɗanta.[44]
Uban gidansa Bafulatani ne Batoranke, amma kuma ya yi wa Gobirawa da Zamfarawa
da Zagezagi da Katsinawa waƙa. Yadda Narambaɗa ya kalli Zamfara na tace shi kamar haka:
1.
Waƙa wata babbar taskar tarihi ce, da
za a ce Salwantarta kamar salwantar tarihi ne da kyawawan al’adun al’umma.
Taskace waƙa, taskace tarihi ne, dole a tashi tsaye. Narambaɗa ya tabbatar da kasancewar waƙa diwanin tarihi.
2.
A farfajiyar ƙasar Hausa, Zamfara ta
fi kowace daular daga cikin daulolin ƙasar Hausa takwas (8)[45]
yawan mawaƙan baka. Narambaɗa ya tabbatar, dole mu yi binciken mafari.
3.
Manyan rubuce-rubucen da
aka yi kan Zamfara na Infaƙui Maisuri, Rahoton Jamusawa, Last, (1968) Adamu (1968),
Alƙali, (1968), Nadama, (1972), babu wanda ya taskace Zamfara sosai, tare da
hujjoji, kamar Narambaɗa. Da za a kalli mawaƙan masarautun Zamfara daban-daban da abu ya fi haka.
4.
Na gano cewa, masarautun
Anka da Gummi ba su bayyana a diwanin Narambaɗa ba. Wannan na buƙatar sabon bincike ko don fitaccen karin maganan da ya
game duniya na “Gummi ta gamu da Anka.”
5.
Babban cikas da masana
tarihi (History) da walwala (sociology) da Ilimin Al’adau (Anthropology) ke
fama da shi, shi ne, rashin sanin ilmin da ke ƙunshe cikin adabin bakanmu, musamman
waƙoƙin bakanmu. Wanda duk ya jahilci
adabinmu, ya jahilci sanin al’adunmu da tarihinmu, da addininmu da wayewarmu.
6.
Binciken da aka yi
barkatai kan Zamfara, sun manta da gurbin
mawaƙa cikin tarihin Zamfara, shi ya sa suka bar muhimman kusurwowi da yawa, da
ba su toshe ba.
7.
Narambaɗa ba sarauta kaɗai ya taskace a Zamafara ba. Ya taskace tarihinta, sana’o’inta, halayenta
mutanen daular da gudummuwarsu.
Naɗewa
Bisa ga abubuwan da diwanin Narambaɗa ya taskace kan Zamfara, akwai buƙatar zurfafa bincike a kan sauran masarautu gaba ɗaya. Sauƙin mawaƙa ga hardacewa, wata babbar taska ce ta adana tarihi a ka. Da za a bi mawaƙan Zamfara daban-daban,
a taskace waƙoƙinsu, masana za su samu taskar baje kolin bincike, da za a gina gawurtaccen bincike da zai amfani kowa da kowa. Duk wani cikas mai tsentsenin binciken tarihi zai hanga a waƙa, akwai shi cikin
kowane tushe daga cikin tussan adana kayan bincike da tarihi. Za mu iya cewa,
mafi yawan abubuwan da Narambaɗa ya taskace a diwanin waƙoƙinsa, fiye da ƙarni ɗaya, yau sun wakana gaban idanunmu.
Wannan wata hujja ce ta cewa, tarihinmu, da al’adunmu da halaynemu, da Turawa,
da Larabawa da Fulani suka taskace, dole a tashi tsaye a yi musu gyaran fuska,
bisa ga abubuwan da muka tabbatar cikin adabinmu, na kunne ya girmi kaka. Babu
tarihin da ba kunne ya girmi kaka ya haifar da shi ba. Babu mai nuna gidansu da
hannun hagu. Bakin wani ba ya suɗe wa hannun wani
miya. Babu wanda ya cancanta ya ba da labarin abu kamar wanda aka yi tare da
shi, ko gaban idonsa domin gani ya kori ji. Rubuce-rubucen Larabawa, da Turawa
da Fulani, a kan Hausawa da ƙasar Hausa, ya tabbatar da bukatar bita a yau. Babu wai, da dahuwa, da banda, da tuya da suya duk gashi ya fi su sanin asirin wuta. Babu mai rubuta daidaitaccen tarihin Bahaushe fiye da
Bahaushe.
Manazarta
Adamu, M. (1968) “Yawuri in the 19th
Century”, M.A Dissertation: Zaria. Ahmadu Bello University.
Adamu, M. (1978) Hausa
Factor in West African History. Zaria. Ahmadu Bello University.
Alkali, M. B. (1968) “Hausa Community in Crisis.
Kebbi in the 19th Century”. Zaria. Ahmadu Bello University.
Auta, A. L. (1986) “ Gudunmawar Wa}o}in Maka]an Baka Dangane da
Adana Tarihi”, Kundin M. A. Kano. Jami’ar Bayero.
Bello, M. (n.d) Infa}ul Maisuri. Rubutun Hannu.
Bunza A. M. (1998) “ Na}alin Diddigin Jirwayen
Rayuwa Cikin Falsafar Luguden Kalmomin Wa}o}in Hausa”. Ma}ala.Sakkwato: Jami’ar
[anfodiyo.
Bunza A. M. (2009) Naramba]a. Lagos: Ibrash
Publishers.
Bunza A. M. (2015) “ Hyperbole as the Peak of
Stylistic Adorment in Hausa Oral Songs,” Paper Presented at the 3rd
Annual Conference and 12th
NFS Congress organized by the Nigerian Folkloric Society, Center for the research in Nigerian Languages. Kano: Bayero University.
Bunza A. M. (2019)” Wane ne Naramba]a? Lead Paper on
Life History Wisdom and Contributions of Ibrahim Naramba]a to Hausa Studies.
Organized by Center for the research in Nigerian Languages.
Translation and Folklore 15-17 September 2019. Kano: Bayero University.
Bunza A. M. (2020) “ Citation of Naramba]a
(1810-1960). Delivered on the occasion of the 24th Convocation
Ceremony of University of Abuja and the Conferment of Honorary Degree (Doctor
of Literature) on Ibrahim Buhari
Maidangwale Abdul}adir Naramba]a Tubali (1810-1960). Held at the University’s
Convocation Centre, on Saturday 15th Feb, 2020.
Car, A. H. (n.d)What
is History?
[angambo, A. (1979) “ Use of Kirari and Taakee in
Hausa Oral Praise Songs. (Shata, Naramba]a and Sa’idu Faru)”, Nigeria Magazine
128-9:89-99.
Furniss, G. (1999) Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa. London: Edinburgh
University Press.
Gusau, S. M. (1987) Jerin Wa}o}in Ibrahim Naramba]a Tubali. Kano: Jami’ar Bayero.
Hiskett, M. (1975) History of Hausa Islamic Verse. London: SOAS.
Last, M. (1969) Sokoto
Caliphate. Ibadan: Unversity Press.
Marwick, A. (1989) The Natureof History. (Third Edition) London: The Macmillan Press.
Mukhtar, I. (1984) “Nahawun Wa}a: Yanaye-yanayensa
da Sigoginsa Cikin Rubutattun Wa}o}i”. Kundin M. A. Kano: Jami’ar Bayero.
Nadama, G. (1977) “The Rise and Collapse of Hausa
States: A Social and Political History of Zamfara”. PhD Thesis. Zaria: Ahmadu Bello University.
Paden, J. (1986) Ahmadu
Bello The Sardauna of Sokoto: Values and Leadership in Nigeria. London:
Hodder and Stough.
Samaldore, S. (n. d) Warfare in Sokoto Caliphate.
Shea, P. J. (1986) “The Development of an Export
Oriented Dyed Cloth Industry in Kano”. PhD Thesis. Madison: Unversity of
Wisconsin.
Smith, A. (1987) A
Little New Light . Zaria: ABU Press.
Smith, M.G (1960)
Government in Zazzau (1800-1950). London: Oxford University Press.
Sodangi, B. A. (1979) “ Naramba]a da Wa}o}insa”.
Kundin digirin Farko. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Udu, A. (1972) “Comparison of Naramba]a and Aliyu
[andawo”. B.A Project. Zaria: Ahmadu Bello University.
Usman Y.B. (1981) Transformation of Katsina. Zaria: Ahmadu Bello University.
[1]Gawurtattun su ne Kano, Katsina, Kabi,
Zamfara, Zazzau, Damagaran, da Gobir
[2]A.M. Bunza, Narambaɗa, Ibrash,
Lagos, 2009
[3]A. M. Bunza, “Wane ne Narambaɗa?” Takardar Taron Ƙasa da Ƙasa kan Ibrahim
Narabaɗa Tubali, BUK, September 1th – 17th, 2019.
[4][4]Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, Infaqul
Maisuri.
[5]A. H. Car, What is History?
[6]Abdullahi Smith, A little more light
[7]M. G. Smith, Government in Zazzau
[8]Mahdi Adamu, History Factor in West
African History, ABU Press, 19
[9]Yusuf Bala Usman, Transfromation of
Katsina
[10]M. Hisket, History of Hausa Islamic
Verse, SOAS, London, 1975
[11]M. Last, Sokoto Caliphate, Longman, Ibadan,
1969
[12]S. Samaldone, Warefare in Sokoto
Caliphate
[13]J. Shea
[14]J. Paden, The Right Honorable Gentle
Man
[15]A. M. Bunza, Hyperbole
[16]Wajen uwa ya gaji kiɗa, makaɗan da suka
gaji roƙo wajen uba tobassansa ne. Idan ya riske su wajen waƙa zai karɓe duk
abin da suka samu. Da Kurna da Ɗandawo in sun ji Narambaɗa na cikin gari ba su
waƙa sai ya fice.
[17]
Hira da Alhaji Danyadodo Shinkafi, 2006.
[18]A wata riwaya an ce: “Nai sittin.” Yana
nufin ya sauke hizu sittin Alƙur’ani. A shekaru kuwa saba’in yake kwarare.Hira
da Sarkin Gobir na Isa Alhaji Nasiru a gidansa Sokoto. Laraba, 22/1/2020
Gudunmuwar Alƙali Muhammad Mudassir Hassan ce wani masani waƙoƙin Narambaɗa
kuma aminin Sarkin Gobir na Isa Alhaji Nasiru.
[19]Masana waƙoƙin Narambaɗa sun shaida cewa
ba a taɓa tsintar batsa ko ƙarya a zantukansa ba. Idan ya faɗi batu cikin waƙa
komai duhunsa, idan an yi taliyo za a ga haskensa.
[20]Hira da wani Hakimin garin Zazzagawa ta
daular Kabi a garinsu, a shekarar 2016.
[21]Takwarorinsa irin su Jankiɗi da Ɗan’anace
da Gambo duk “Hausa” suke kiran Sakkwato da Gwandu da Zamfara cikin waƙoƙinsu.
[23]
Hira da Murray Last, 2020.
[24]Domin sarakunan Fulani ake tura musu su
sarauci ƙasashensu, alhali ba Fulani ke da ƙasashen ba.
[25]A. M. Buna, “Sakkwato ce Tushen Hausa in
ji Narambaɗa,” takardar da aka gabatar, UDUS
[26]Gwandu a halin yanzu tana Jihar Kabi tana
da ƙananan hukumomi goma (10) daga cikin ƙananan hukumomi ashirin da ɗaya (21)
na jihar Kabi.
[27]A daular Zamfara akwai makaɗan Saurata,
Farauta, Fawa, Noma, Su, Tauri, Gayya, Sha’awa, Zari, Sata, Ban dariya,
Kuntugi, Garaya, Bori, duk wani nau’in kiɗa na gargajiyar Bahaushe akwai su a
Zamfara. A wakokin fada muna da Narambada Kurna, Makadan Maza, Kassu
Zurmi, Makadan Dambe, Dan’anace, Makadan Tauri, Garba Danwasa Gummi, Makadan
Noma, Amali Sububu d.s. Binciken da B.B.C ta yi wajajen (1997?) ya yi tsokacin
haka.
[28]A wata faɗa ualam ce: “Ai tun da Nagaya ya
i tai waƙa”
[29]Narambaɗa na cewa: “Sarkin Kudun Gusau
Allah dai ya cika ma burinka.” Wato ya riƙi Isa, ya koma ya riƙi Sakkwato. Isa
babban gari ne a daular Usmaniyya.
[30]A wajen Kabawa Yabo Hausa ce.
[31]Fitattun garuruwa ne na masu kuɗi da ilmin
addini da boko.
[32]Wannan ya tabbatar da ba ƙasar matsorata
ba ce.
[33]Ɗan koyo wanda bai iya abu ba
[34]Karsa shi ne mai rabon kokuwa a fagen
wasa. Idan fagen dambe ne a ce mishi “damazau”
[35]Zamfara yankin ‘Yandoto ita ce Katsinar
Laka
[36]Sunan Shago na yanka Abubakar Sunan
Mahiafinsa Abdullahi mutumin ‘Yarkahoji ne gabas da garin Rini cikin ƙasar
Mafara, Daular Zamfara.
[37]Babban gona na tarayyar iyali ko dangi
[38]Ƙaramar gona da ake ɗeba wa yara “kurga”
[39]Babban abin haƙon kifi ne masunta na da
sarauta “Taru”
[40]Faɗar “ya nasa” kan kifi ake fara nasawa
gora jiki ya bi.
[41]Fitattun masu fatauci ne a Gwanja da
ƙasashen ƙetare.
[42]Ni ban yarda ba, ai mai kunya ke rufi
domin gudun ya bayyana a yi abin a ji kunya. Wanda ba ya ruhi ai ba ya da
kunya.
[43]Samɓalto ya sha hura ta zuba a cikinsa sai
ƙuda/ƙuje ya sauka ya sha furar da ta zuba. Ganin haka, ya kira Satoto, ya ce:
“ya ɗauko kibiya ya harbe ƙudan.” Nan take Satoto ya aikata, samɓalto ya
baƙunci lahira. Da wanda ya yarda ya yi kisan kai, da wanda ya yarda aka
kasha shi, wane ne wawa ko mahaukaci? A ganina, su duka wawaye ne mahaukata ne.
[44]Karen makaɗa bayan hulɗa da sarakuna yana
hulda da mawaƙa. Ya tara abubuwa biyu ke nan.
[45]Daulolin takwas su ne: Kano, Katsina,
Kabi, Zamfara, Damagaran, Bauchi da Yawuri (Inji Mahdi Adamu Ngaski).
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.