Ticker

6/recent/ticker-posts

Masarautun Zamfara A Waƙoƙin Narambaɗa

Narambaɗa basaraken mawaƙi ne kuma Malamin waƙa. Mawaƙin Masarautar Isa ne, kuma shahararre a ƙasar Hausa. Masarautun Zamfara da yawa sun sami shiga cikin waƙoƙinsa daban-daban. A taskar waƙoƙinsa, ya taskace makaɗan masarautun, kuma ya yi ɗan sharar fage ta yadda na bayan fage zai iya ya harari matsayinsu da darajarsu. A waƙoƙin da suka taɓo Moriki, Ƙaura, Zurmi, Gusau, Tsafe, Bunguɗu, Maradun da Kwatarkwashi, akwai abubuwan tsinta da yawa ga ɗaliban nazarin Hausa. Burin wannan bincike shi ne ya ƙyallaro yadda makaɗa Narambaɗa ya rambaɗo su da yadda ya kalle su a waƙoƙinsa. Wannan bincike gabatarwa ce ga mai son ya san masarautun Zamfara da matsayinsu a daular Sakkwato.

Masarautun Zamfara A Waƙoƙin Narambaɗa

  

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

GSM NO. 07032567689

E-mail: aliyurabiu83@gmail.cim

 

1.0  Gabatarwa

 

Mulkin jama’a abu ne da Allah (SAW) ke zaɓen wanda yake so ya bai wa shi, wanda ga alamu zai iya tafiyar da jagoranci na gari. Sarauta a ƙasar Hausa abu ce da ke da asali da muhimmanci ga zamantakewar al’ummar Hausawa tun fil’azal. Irin wannan tsari na shugabanci ya sa al’ummar Zamfara suke bugun gaba da samun sarakuna masu ƙwazo da kamala da jajircewa wajen tabbatar da mulkin adalci a tsakanin al’ummarsu. Saboda haka, wannan salon mulki ya jawo hankalin maƙaɗa Narambaɗa da sauran makaɗa daban-daban su riƙa rera waƙoƙi don kambama sarakunan bisa ga irin salon mulkinsu. Don haka wannan takarda za ta mai da hankali ga waoƙin sarautun Zamfara a bakin Narambaɗa dangane da kwarjininsu ta fuskar yaƙi da ilimi, da adalci da kuma bunƙasa ko faɗaɗa masarautunsu ta fuskoki daban-daban.

 

1.1 Manufar Bincike

Manufar wannan maƙala ita ce ta yi tsokaci dangane da masarautun Zamfara da tasirinsu ga samar da tsaro da zaman lafiya a yankin jihar Zamfara tun a lokaci mai tsawo da ya shuɗe. Za a ga irin tasirin da waƙoƙin Narambaɗa suka yi wajen fito da kwarjini da ƙwazon da Sarakuna suka nuna ga ɗaukaka darajar masarautun Zamfara ta fuskar yaƙe-yaƙe da samar da tsaro da sauran nasabobi.

 

1.2 Dabarun Bincike

An bi hanyoyi daban daban wajen binciken littattafan tarihi waɗanda masana da manazarta suka yi domin kafa hujjoji ga abin da wannan takarda take magana a kai. An ziyarci ɗakunan karatu domin samun ƙarin bayani game da tarihin Zamfara da masarautun gargajiya da kuma shi kansa Narambaɗa mawaƙin waɗannan masarautu.

 

1.3 Nasabar Yaƙi

A ɓangaren zamantakewar al’umma, yaƙi na ɗaya daga cikin fitintinun da ke tarwatsa jama’a su bar mazauninsu na asali su koma wani wurin zama da za su sami kwanciyar hankali; su gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba.

 

Haka kuma yaƙi abu ne da sarakuna ke amfani da shi wajen faɗaɗa masarautunsu da mamaye ƙasa mai faɗi a yankin masarautarsu. Sarakunan Zamfara sun shahara wajen irin wannan matsayi domin bunƙasa tattalin arzikinsu da kuma faɗaɗa ƙasarsu. Wannan ya sami asali ne tun daga burbushin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo wanda ya yi fama da Gobir a lokacin da yake jihadin jaddada addinin musulunci. Sarakunan Bukkuyum da Talata Mafara da Bakura suna daga cikin sarakunan da suka taka rawa wajen baiwa Shehu Ɗanfodiyo gayon baya ga samun nasarar rushe Daular Gobir (Johnston, 1967).

 

Idan muka koma kan masarautun Moriki da na Ƙaura da sauransu za mu fahimci cewa waɗannan masarautu su ne cibiyar masarautun Zamfara da suka ƙarfafawa jihadin ɗaukaka addini a ƙasar Hausa. Saboda haka ne makaɗa Narambaɗa ya fifita su a cikin waƙoƙinsa don ya nuna irin ɗaukakar da Allah ya yi masu a fagen mulki. Makaɗa yana cewa a wannan bauti kamar haka:

Jagora:            “Moriki Ƙaura da Zurmi duk maganar ta zama ɗai

Amshi            Bunguɗu da Gusau, Kwatarkwashi ga ‘yan doto

Sun san Garba ɗan Hassan

Shi as shugabansu

Kai ab babban ɗa nai

Jagora             Magana taka ba a cewa ba daidai ba

Amshi            Nasabar Shehu ba ta ɗai da ta kakan kowa

(Bakandamiya Narambaɗa)

A cikin wannan baiti makaɗa Narambaɗa yana son ya danganta nasabar waɗannan sarakuna da ya ambada da ta Sarkin Gobir na Isa ne wanda ya samo asali daga Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Shi dai Narambaɗa mawaƙin fadar Isa ne, ga al’ada idan mawaƙi yana da Uban gidansa, to ba ya yi wa wani waƙa sai da izinin ubangidan nasa. Domin mawaƙi ya fita ya yi wa wani sarki waƙa ba da izinin Sarkinsa ba, to yana iya zama wata fitina saboda za a taras waƙar da ya yi ta fi ta uban gidansa. Haka kuma na iya zama sanadiyar rasa matsayinsa ga wannan fada ta uban gidansa. Narambaɗa fadar Isa yake yi wa waƙa a ƙarƙashin Sarakunan Gobir na Isa biyu, ya zauna da Tudu Muhammadu Na’ammani (1927 – 1935) da Sarkin Gobir Ahmadu Bawa (1935 – 1975). Narambaɗa ba shi da damar da zai yi wa wani Sarki waƙa face ubangidansa ya yarda da haka. Sannan idan ya tsara waƙa sai ya kawo wa uban gidansa ya gani, kuma shi Narambaɗa ya buɗa waƙar gaban Sarki ya jiya idan ba ta fi tasa ba (Bunza 2009).

 

Kamar yadda bayani ya gabata cewa; mawaƙa Narambaɗa ya ambaci sarakunan Zamfara bisa ga nasabar da suke da ita da daular Usmaniyya ta fuskar asali da yaƙe- yaƙe domin ya kambama su a idon jama’a su ɗauke su da daraja. Haka kuma su kalle su a matsayin adilan sarakuna. Saboda haka, irin wannan nasaba ta yaƙi ta bayyana ga sarkin Kuryar Dambo inda Narambaɗa ke yaba shi da kasancewar shi gwarzo a fagen yaƙi, misali.

Jagora:            Ai Kurya ta Dambo ce Makaru an nan

Amshi Zamfara babu ɓagare kama tai

Masu gari mazan gabas tsayayye

Sarkin Rwahi ya wuce a rammai

Jagora:            Ai da takobi da garkuwa da mashi

Amshi Mai sulke Dambo ho! Da Yaƙi

Kurya akwai mazan fada da arna

Masu gari mazan gabas tsayayye

Sarkin Rwahi ya wuce a rammai

(Narambaɗa: Masu gari mazan gabas tsayayye)

 

Waɗannan baituka biyu su suka tabbatar da bajinta da buwayar sarakunan Zamfara musamman a fagen yaƙi.

Misali yana cewa:

Jagora:            A runguma uban yaƙi

Amshi Mazan gabas da Sakkwato

Jagora:            Ba shawagi sa maza yawon duniya

Amshi Suna sai da abin hwaɗi ga ‘yan uwa

Jagora:            Mai halin mazan jiya

Amshi Ɗansanda mai Kwatarkwashi

                        (Narambaɗa: wakar mai kwatarkwashi)

 

Masarautar Kwatarkwashi ta yi fice a fagen yaƙi tun lokacin da aka haddasa wannan gari, ya ba da tasa gudummuwa wajen kawar da maƙiya a fagen yaƙi domin lokacin da jihadin Ɗanfodiyo ya yi tsauri masarautun Zamfara sun yi haɓɓasa a cikinsu har da Kwatarkwashi wajen faɗa da Gobir. Narambaɗa yana danganta Sarkin Kwatarkwashi da nasabar Sarkin Gobir na Isa, inda yake cewa a cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Kwatarkwashi Alu, yana cewa:

Jagora:            Da anka ce Alu as Sarkin gidan ga na taho

Amshi Yai halin mazan jiya

Amshi Ɗansanda mai Kwatarkwashi

 

Jagora:            Jikan Dabo mai Kwatarkwashi

Amshi Jikan kada gaƙe maza

Amshi Yai halin mazan jiya Ɗansanda mai Kwatarkwashi

Wato dai Alu Sarkin Kwatarkwashi Sarki ne wanda ya zama garkuwa a yankin gabas ga Sakkwato domin ya zama mai gaƙe maza idan sun taso ma garin Kwatarkwashi ba zai bari su isa can ba.

 

Kotorkoshi gari ne mai dogon tarihi, wanda ya samu asali daga wani jarumin mayaƙi kuma maharbi da ya fito daga Katsina mai suna Mangul. Tun a cikin ƙarni na (14) kimanin shekaru (611). Aminu (2018).

 

Narambaɗa yana danganta Sarkin Kotorkoshi da nasabar Sarkin Gobir na Isa ta fuskar Jaruntaka.

 

Wato makaɗa Naramɗa yana nufin Alu Sarkin Kotorkoshi Sarki ne wanda ya zama garkuwa a yankin gabacin Sakkwato, domin ya zama mai gaƙe maza idan sun taso ma garin Kotorkoshi ba zai bari su iso can ba. Masarautar Kotorkoshi ta yi fice a fagen yaƙi tun lokacin da aka assasa ta, garin ya taka muhimmiyar rawa wajen kawar da maƙiya a fagen yaƙi a lokacin da jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya yi tsauri, tsakaninsu da Gobirawa. Narambaɗa ya yabi Sarkin Kotorkoshi da irin wannan nasaba ta yaƙi.

 

1.4 Ƙaura 

Masarautar Ƙaura Namoda ta yi fice ainun wajen dattako da sanin ya kamata da tsare amana da iya tafiyar da mulki ta fuskoki daban-daban. Masarautar Ƙaura Namoda a ƙarƙashin mulkin Muhammadu Namoda ta yi ƙoƙarin kare martabar Birnin Zurmi daga hare-hare da yaƙe-yaƙe na gobirawa da Adarawa da Ɓurmawa da Zamfarawar Kiyawa da Sauransu. Namoda ya kafa mazauninsa a wani dausayi na Ƙoramar Fafara, inda a nan ne Namoda ya dinga kai yaƙe-yaƙe na Musulunci har zuwa Birnin Alƙalawa, daga bisani kuma Muhammadu Namoda ya sake ƙarawa gaba inda ya kafa wani mazauni kudu daga inda yake a dai-dai gulbin gagare wanda ake kira Ƙauran Namoda a halin yanzu (Gusau 2015). Saboda haka makaɗa Narambaɗa ya yabi Sarkin Ƙaura a kan bajinta da dattako da riƙon amana da gaskiya inda yake cewa:

Jagora:            Da samin Dattako da girma

Amshi Da tsaron aikin ga na zamani

Jagora:            In dai ba ka koma Isa ba

Mai Ƙaura babu awa tai

Amshi:           Shirin bajirin Mamuda

Abu na Namoda tsayayye

 

A nan makaɗa Narambaɗa yana son ya nuna irin kwarjinin Sarkin Ƙaura Namoda da dattako da riƙon amana ga jama’arsa. Wannan shi ya sa masarautar Ƙaura Namoda ta yi tashe har Narambaɗa ya ambace ta a tsarin waƙoƙinsa na masarautun Zamfara.

 

1.5 Nasabar Ilmi

Hausawa na cewa “Nazango moriyar ka da nisa” Wato ilmi kenan. Ilmi shi ne ginshiƙin samun nasarar kowane irin abu da aka sa a gaba. Da ilmi ake samun ɗaukaka da imani da tsaron amana da mulkin adalci. “Yandoto cibiya ce ta ilmi wace ta yi tasirin gaske wajen bunƙasar ilmi a masarautar Tsafe da jihar Zamfara da kuma ƙasar Hausa baki ɗaya. A cikin bakandammiya. Narambaɗa ya yi shagube ga al’umma a kan muhimmancin ilmi inda yake cewa:

Jagora:            Ai kyau Mafarauchi ya ɗau kare ya kiyayo ya hi

Shi ɗan Malam ya kama littafi ad daidai

Amshi Sai zuba waƙa nikai kamar alfa zazi

(Narambaɗa: Bakandamiya)

 

Wannan baiti yana bayyana muna darajar ilmi ga masarautu wanda ya sa masarautar Tsafe ta shiga cikin tsara a fagen jajircewa ga neman ilmi. Haka ya sa sarkin Tsafe ‘Yandoto Ali ya taka rawa ga harkar ilmi a masarautarsa; inda Narambaɗa ke cewa a cikin waƙarsa:

Ko ɗan Malami da yay yi karatu

Yaƙƙi biyat nassi

Yaƙ kiɗe baƙi

To Allah yana watse kayanai

(Narambaɗa: Gagarau mai buge kanfara Ali Yandoto)

 

Saboda haka aiki da ilmi ya ɗaukaka masarautar Tsafe, wannan ya sa darajar Masarautar Tsafe ta samu ɗaukaka a idon duniya a lokacin Sarkin Tsafe Ali ‘Yandoto.

 

1.6 Nasabar Mulkin Adalci

Adalci shi ne bai wa kowa ‘yanci da ya kamata a ba shi, wato a bai wa mai gaskiya, gaskiya, shi kuwa maras gaskiya a hukunta shi. Irin wannan mulki na adalci shi ne ya ƙara ɗaukaka darajar Sarakunan Zamfara a Idon duniya (Dangulbi 2013). Makaɗa Narambaɗa ya tabbatar da wannan zance a cikin waƙarsa inda yake cewa:

Jagora:            Sarkin Ƙayan Maradun ba kama na ba shi

Amshi Komai za ya yi da gaskiya yakai

Jagora:            Ya buwayi maza ginshiƙin tama na Amadu

Amshi Garba ƙi gudu ɗan moyi

Amshi Mai halin mazan jiya

(Narambaɗa: Waƙar Sarkin Ƙaya Maradun)

 

Jagora:            Ya shirya zama da ku mutanen kudu,

Amshi:           Duk ku kiyaye halinai

 

Jagora:            Ba ya ce ma baranai

Amshi Tahi samo man rance

Jagora:            Ba ya cewa

Amshi Yau wane ina kai ma malka

Jagora:            Babu mai tsira wargi

Amshi:           Yaji tsoron ɗamri nai

Jagora:            Mai Gusau raba kaya

Amshi Ba a kai maka wargi

Jagora:            Mai rabo da yawa

Amshi Gamda aren Sarki Gobir

(Narambaɗa: Waƙar Sarkin Gusau)

 

Abin nufi a nan, Narambaɗa yana ƙoƙarin nuna nasabar mulkin adalci ga waɗannan masarautu guda biyu masu alaƙa ta jinni ga gidan mujaddadi Usmanu Ɗanfodiyo. Bugu da ƙari, masarautun Zamfara sun zama abin koyi ga sarakunan ƙasar Hausa ta fuskar adalci da riƙon amana.

 

1.7 Nasabar Tsaro

Tsaro shi ne kula da shige da ficen al’umma a ƙasa ko a yanki, kuma wannan tsaro shi ne tushen samar da zaman lafiya. Hausawa sukan ce “Zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki”, wasu kuwa sun ce “Ko Sarkin ma ya fi”. Idan babu zama lafiya to kuwa ba za a samu cikakken haɗin kai ba tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulki (Talakawa).

 

Masarautun Zamfara suna iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun sa ido ga masarautunsu don su hana shiga da fice a masarautunsu ba bisa ƙa’ida ba. Samun haka ya sa sarakunan ƙasar Zamfara suka zama masu bin doka da oda ga hukumomi da suka naɗa su domin tabbatar da ingantaccen tsaro. Makaɗa Narambaɗa yana cewa:

Jagora:            Gadan – gadan na Bawa na Aisa,

Amshi Gaƙe maza uban Turawa

Jagora Madogara na Malam Iro uban Bawa

Amshi Mai gida Shinkafi

 

Jagora:            Riƙe da gaskiya Ibrahim

Amshi Mai taimakonka Allah na nan,

Jagora/Amshi Zan ka wa maza gurnani

(Narambaɗa: Waƙar Sarin Shinkafi)

 

1.8 Naɗewa:

Kamar yadda muka yi bayani a kan matsayin Sarakunan Zamfara a bakin Narambaɗa, mun ga irin gudummuwar da Sarakunan Zamfara suka bayar ta fuskar yaƙi da ilmi da adalci da tsaro da sauransu. Wannan ya yi sanadiyar samun ɗaukakar su a idon duniya, saboda tun farko an san Zamfarawa da zama lafiya wanda shi ya haifar da bunƙasar tattalin arziki da kyakkyawar mu’amala tsakanin masarautun Zamfara da maƙwabtansu.

 

Manazarta

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments