Ticker

6/recent/ticker-posts

Matakan Wayewa a Cikin Wasan Raha : Nazarin Wayewa Da Matakanta A Fim Ɗin Idon Ƙauye

 Tsakure: Wayewar mutum da fahimtar rayuwar duniya da abubuwan da ta ƙunsa kan faru ne a matakai daban-daban na rayuwa ba a lokaci ɗaya ba. Kuma abubuwan da kan haifar da irin wannan wayewar akan ci karo da su ne a lokuta mabambanta na zamantakewar rayuwa.Wannan maƙala ta ƙudiri aniyar nazartar wasu matakan wayewa ne (Agents of Socilization) na rayuwar Ɗan Adam, waɗanda masana ke ganin ta kansu ne akan bi domin samun ingantacciyar wayewa na zamantakewar duniya. Tare da fahimtar matsayin mutum, gami da iya samun dama na bayar da gudummuwa wajen inganta rayuwar al’ummar da mutum ke ciki. Maƙalar ta yi ƙoƙarin nuna yadda fina finan Hausa ke bin waɗannan matakai ne wajen ganin an samar da canji a rayuwarmutum daga rashin wayewa zuwa wayewa. Maƙalar ta ɗauki fim ɗin IdonƘauye netayiƙoƙarin nuna yadda rayuwar Indo ta canza sakamakon ɗorata da aka yi a kan waɗannan matakai. Maƙalar ta ƙoƙarta ƙwanƙwance wasan IndonƘauye inda daga ƙarshe ta nuna yadda waɗannana matakai na wayewa da suka haɗa da dangi (family), da tsara ko sa’annai (peer group), da makaranta (school), da addini (religion), da kuma horaswa (training)suka tasirantu a rayuwar tauraruwar fim ɗin ( Indo). Da kuma yadda bin su ya canzata ta wayegaba ɗaya kamar ba ita ba.

Matakan Wayewa a Cikin Wasan Raha: Nazarin Wayewa Da Matakanta A Fim Ɗin Idon Ƙauye

 Rabiu Bashir

Deparment Of Nigerian Languages And Lingustics,

Kaduna State University

rabiubashir86@gmail.com

08035932193/08094378162

1.1 Gabatarwa

Wasan kwaikwayo hanya ce da akan bi domin a nishaɗantar gami da ilmantar da al’uma a kan wasu abubuwa na rayuwar yau da kullum. Sau tari akan gina wasan kwaikwayo nedomin ganin an faɗakar da mutane akan wani abu da yake da muhimmanci domin su rungumeshi, ko kuma wani abu wanda bashi da kyau domin a guje masa. Inda akan kwaikwayi yadda wani ya aiwatar da irin wannan abin mai kyau, sannan a nuna wata nasara da ya samu. Ko kuma a nuna yadda wani ya aiwatar da wannan abin mara kyau, sannan a nuna mummunan sakamakon da ya tsinci kansa a ciki.A ƙalla kwai nau’o’in wasan kwaikwayo daban daban da suka haɗa da wasan raha, da wasan ban tausayi da kuma wasan tir madalla.

Masana ilmin ɗabi’ar Ɗan Adam sun tabbatar da cewa akan haifi yaro ne babu komai na ilmi a cikin ƙwaƙalwarsa, amma a hankali yakan koyi abubuwa na zamantakewar rayuwa daga wurin al’ummar da ya taso ya ga kanshi a ciki, har ya zamanto yana iya gane abubuwan da ake so ya aikata da kuma waɗanda ba a so ya yi. Kuma daga waɗannan abubuwan da ya koya ne zai gina tashi rayuwar har ya zamanto ya iya tantance matsayinsa da kuma irin gudummuwar da zai iya ba al’umar tasa. Haka kuma sun tabbatar da cewa irin wanna ilmin na wayewa da zamantakewar rayuwa ba abu ne da mutum zai iya koyoa lokaci guda ba, watau zai ci gaba da koyonsa ne iya tsawon rayuwarsa. Har wa yau masana irin su Hastings da Miller da Kahle da kuma Zahn-waxler (2014), sun tabbatar da cewa a kwai a ƙalla matakai ko hanyoyi na wayewa (Agents of Socialization) guda shida ko biyar waɗanda mutum kan bi ta kansu domin ya samu ingantacciyar wayewa gami da fahimtar rayuwar duniya. Waɗannan matakai sun haɗa da dangi, (family), da sa’anni ko tsarraki (peer group), da makaranta (school), da addini (religion), da kuma horaswa (training).

Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin nuna yadda fina-finan Hausa ke bin waɗannan matakai ne na wayewa domin ganin an canza rayuwar mutane daga duhun kai zuwa wayewa. Maƙalar ta ɗauki wani fim ne na wasan raha mai suna IndonƘauye,inda ta nazarci yadda aka sarrafa waɗanna matakai daban-daban don ganin an inganta rayuwar tauraruwar wasan ta hanyar wayar da ita daga tantagaryar baƙauyiya zuwa wata gogaggiyar ‘yar birni.

Fim ɗinIndonƘauye, ya ƙunshi wasa ne na raha wanda ya kawo rayuwar wata cikakkiyar baƙauyiya mai suna Indo. Wadda aka haifa kuma ta taso a ƙauye. Amma daga bisani ta koma birni da zama sakamakon auren zumunci wanda kakkarsu ta yi wasici tun tana da rai, kuma iyayensusuka cika mata burinta suka ƙulla,inda ta auri ɗan ƙanin mahaifiyarta mai suna Nura. Duk da kasancewar Indo wata ballagaza ko a cikin ƙauyawa, hakan bai hana ta waye ba, ta koma ƙyanƙyasasshiyar ‘yar birni a sakamakon ɗorata bisa kan waɗannan matakai na wayewa da mijinta yai ƙoƙarin yi.

2.1Waiwayen Wasan Raha da Wayewa

Kamar yadda aka bayyana tun a farko, cewa wasan IndonƘauye wasa ne na raha wanda aka shirya domin a nishaɗantar da masu kallon fina-finan Hausa, amma duk da haka yana ƙunshe da ilmantarwa mai tarin yawa wadda idan aka bi hanyoyi da matakan da wasan ya samar mutum zai tsinci kansa cikin wayayyun mutane wanda zai iya amfanar da rayuwarsa har kuma ya amfanar da ta wani.

Kamar yadda Aminu (2013) ya nuna, masana na ganin cewa Frye (1957), ne mutum na farko da ya fara daddale matsayin wasan raha a rayuwa baki ɗaya. Masanin ya bayyana cewa a kwai wasan raha na dauri, sannan a kwai kuma na zamani, sannan ya nuna cewa babbar manufar raha ita ce daidaita tunanin al’umma. Shi kuwa babban masanin falsafan nan Aristotle (1952) na ganin cewa babbar manufar wasan raha itace kwaikwayon rayuwar al’umma, musamman marasa galihu, domin a daidaita tunaninsu. Har wa yau dai Aristotle (1952) da Boulton(1960) da Preminger (1965) da Cuddon (1977) da Wilson da Golfarb (2000) da kuma Abrams da Harpham (2009) duk su haɗu a kan cewa wasan raha shi ne wasan da ake shirya shi musamman domin a samar da nishaɗi da annashuwa da manufar gyara a cikin al’umma. Sai dai a yayin da Aristotle yake ganin cewa makamashin nishaɗin da ke cikin wasan raha kan kasance munin halitta ne da nakasa waɗanda ba sa cutar da ‘yan wasa, inda su kuma su Preminger (1965) da Cuddon (1977) na ganin cewa ba lallai ne sai mummuna ko nakasasshe ne zai bayar da dariya ba, har kura-kuran rayuwa na yau da kullum kan iya zama hanyoyin haifar da nishaɗi da ban dariya. Su kuwa su Abrams da Harpham (2009), sun ƙara ne da cewa munanan ɗabiu’n ‘yan wasan raha su ne kan haifar da nishaɗi a madadin damuwa a zukatan ‘yan kallo. Bugu da ƙari Baldick (2004), ya yi ƙoƙarin bambance wasan raha da na ban tausayi, inda ya ce wasan raha baya ga nishaɗi da yake sa wa, ya fi kusa darayuwar mutane ta yau da kullum. Sannan ya jaddada cewa wasan raha yana ƙarewa gwarzon wasan ne da farin ciki da nishaɗi ba kamar wasan ban tausayi da yake ƙarewa gwarzon wasa da baƙin ciki ba.

Wayewa kamar yadda Ƙamusun Wikifidiya(2017), ya bayyana ita ce hanyar koyo da koyarwa na abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum waɗanda suka haɗa da al’ada da tsarin zamantakewar al’umma, waɗanda ta su ne mutum zai iya kasancewa cikakken wayayye wanda ke da al’adunsa, sannan yake samun dama ya bayar da gudummuwa, ya kuma yi mu’amulla irin ta zamantakewa a tsakanin al’umma. Ya ƙara da cewa wayewa ta ƙunshi hanya ce ta ilmantar da mutum a kan muhimman abubuwan da rayuwa ta ƙunsa kamar ɗabi’u masu kyau da al’adu da kuma abubuwan da al’ummar suka aminta da su. Kuma ta wannan hanya ne mutum zai waye ya saje tare da sabawa da dukkan al’adun al’ummar da yake ciki. Ƙamusun ya ƙara da cewa duk wannan wayewar da fahimtar al’amura rayuwa na faruwa ne ta hanyar bin matakai daban-daban. Sannan ya kawo matakan wayewa waɗandayace ta kan su ne akan bi a canza ɗabi’ar mutum har kuma ya zama mai amfani a cikin al’ummarsa. Matakan wayewar da ƙamusun ya jero sun haɗa da dangi da tsara ko sa’o’i da makaranta da kafofin yaɗa labarai da kuma ƙungiyoyi.

Su kuwa wasu masana ilmin zamantakewar Ɗan’adam da suka haɗa da Bowles, da Samuel, da Herbert Gintis (1976), da kuma Kohn, shi da Melvin L (1977), sai kuma Crampton da Thomas (2002), duk sun yi ittifaƙin cewa wayewa cekan taimakawa mutum ya iya mu’amala kyakkyawa a duniyar da ya tashi, har ya samu damar iya amfani da kayayyakin amfani na yau da kullum, sannan kuma ya iya sanin al’adu da abubuwan da addini ya aminta da suda kuma waɗanda ba a aminta da su ba a cikin al’ummar da yake. Haka kuma sun tabbatar da cewa wayewar na faruwa ne ta hanyar bin matakai mabambanta da suka ƙunshi dangi ko iyali wanda ya haɗa da mahaifi da mahaifiya da ‘yan uwa da kakanni da kuma sauran dangi waɗanda su ne ke fara koyawa yaro abubuwan da ya kamata ya sani, inda za su nuna masa yadda zai yi amfani da abubuwa kamar na tufafi da kayan cin abinci da sauransu. Sai kuma tsarrarki waɗanda suka haɗa da sa’o’i na shekaru da kuma waɗanda suke a matsayi ɗaya, waɗanda za su rinƙa yin wasanni tare, inda daga nan ne yaro zai koyi ƙa’idoji na wasanni, da kuma yin abu daki- daki. Kuma hakan zai ci gaba da faruwa har zuwa girman yaro. Sai kuma makaranta, inda a nan ne yaro zai iya koyon abubuwa da yawa waɗanda zai gina rayuwarsa a kai. Sai addini wanda shi kuma zai koya wa mutum sanin yadda addininsa yake tare da nuna masa kayayyakin da suka shafi addinin da sanin yadda zai yi mu’amala da su kamar littafai na addini da kuma sanin muhimmancin wurin bauta. Sai kuma kafofin yaɗa labarai waɗanda sukan taimaka matuƙa wurin wayar da kan mutane ta hanyar kawo labarai na ilmantarwa da kuma masu sa nishaɗi gami da faɗakarwa a kan rayuwar yau da kullum.

3.0. Zubin Wasan IndonƘauye

Zubin wasan ya fara ne da nuno Nura (Ali Nuhu) a mota yana waya da budurwasa inda yake gaya mata ya sauka lafiya, daga nan sai aka nuno shi da iyayensa suna yi masa barka da dawowa daga Turai (ƙasar waje), inda suka shirya cin abinci. A wurin cin abincin ne sai mahaifin Nura ya kama kuka, da aka tambaye shi dalili sai ya ce mahaifiyarsu ta bar masu wasiya cewa su haɗa zumunci na aure tsakanin ‘ya’yanshi da na yayarsa, don haka tunda Nura ya gama karatu sai ya je ƙauye ya auri Autar Guggu wadda ita kaɗai ta rage. Da fari Nura ya nuna rashin amincewarsa, amma da babansa ya matsa sai ya ce ya yarda zai je ya ganta. Daga nan sai aka nuno Indo tana cin gyaɗa tana ta santi a ƙauye, inda aka gaya mata yayanta (Nura) ya zo daga birni, don haka ta ruga gida don ta ganshi. An nuna Nura sun yi Magana da Guggo ya shaida mata abin da ya kawo shi inda ta nuna murnarta, sai dai Nura ya kawo hanzarinshi na cewa yana da wadda yake so ya aura. Guggo ta gaya masa bai isa ba sai ya auri Indo domin su sami damar cika wasicin da mahaifiyarsu ta yi musu. An nuna Nura da Indo a cikin motarsa suna hira, inda yake lallashinta da tace bata son shi, saboda yana da wadda yake son zai aura. Indo ta ƙi amincewa da shawarar Nura inda ta dage ita tana son shi kuma sai ta aure shi.

An nuna Nura da Indo sun yi aure kuma suna zaune a birni, sai dai Indo tana fuskantar ƙalubale na zaman birni domin ita ta saba zaman ƙauye ne, don haka bata iya komai ba hatta masai ba ta iya amfani da shi ba. Nura ya yi ta ƙoƙarin nuna wa Indo yadda ake amfani da abubuwa daban daban na gidan da suke zaune kamar ɗakin girki da yadda za ta yi amfani da kayan ciki, da kuma kunna kayan kallo da sauransu. An kuma nuna yadda Nura ya sa Indo a makaranta duk domin ganin ta waye. Da farko Indo ta ƙi amincewa, amma da mijnta ya lallasheta sai ta haƙura. Sai aka nuna Indo ta yi ƙawaye da dama a makarantar wanda hakan ya sa ta koyi abubuwa daga gare su. Haka kuma an nuna yadda Nura ya ɗaukowa Indo malamin addinin wanda zai koya mata yadda abubuwa na addinin musulunci suke kamar yadda ake tsarki da alwala da kuma sallah.Daga nan sai aka nuna yadda Nura ya kai Indo wajen wata mai horaswa duk domin ƙoƙarinsa na ganin ta waye. Inda aka nuna su a wurare daban- daban tana koya mata abubuwa na zaman takewa kamar iya cin abinci, da iya tafiya a matsayinta na mace, da magana irin ta mata, da kuma karatu da rubutu. Sai kuma aka nuna Indo ta dawo a mota inda take tambayar mai gadi ko “Sweet heart” ɗinta yana nan? An nuna Indo suna hira da mijinta a matsayin wayayyiya, har tana yi masa turanci, inda a ƙarshe take tambayrsa me yake so ta dafa masa? Shi kuma ya amsa mata da cewa indai abinci nata ne duk abin da ta dafa zai ci.A ƙarshe taraka shi ya hau mota tana gaya mishi da Allah kada ya daɗe da harshen Ingilishi.

3.1 Jigon wasan IndonƘauye

Jigon wannan wasa shi nenuna muhimmancin yi wa iyaye biyayya a kan duk abin da suka umarci mutum matuƙar bai saɓa wa shari’a ba. Haka kuma a nuna cewa duk wanda ya bi umarnin iyayensa zai dace da farin cikin rayuwa komai tsawon lokaci. Hakan ya fito ƙarara a cikin wasan, a inda aka nuna Alhaji na jaddada cewa dole ne sai Nura ya auri Indo, domin ya samu damar cika umarnin da mahaifiyarsu ta yi na haɗa auren zumunci a tsakanin iyalansa da na ‘yar uwarsa koda kuwa bayan rayuwarta ne. Haka kuma itama Guggo ta jaddada wannan zance na ganin ta yi biyayya da umarnin mahaifiyarsu.

Har wa yau jigon wasan ya ƙara fitowa, a inda aka nuna Nura ya yarda ya auri Indo duk da cewa yana da wadda yake so zai aura, kuma gata bata wayeba kamar wadda yake so ya aura ɗin. Amma haka nan ya yi biyayya ga iyayensa ya aureta duk da cewa ba ƙaunarta yake yi ba, sai don ganin ya yi biyayya tare da cika umarnin iyayensa.

Haka kuma an ƙara bayyanar da jigon wasan a inda aka nuna Indo ta waye, ta zama kamar kowacce mata ‘yar birni, har ta kasance abin alfahari kuma mai faranta rai a wurin mijinta wadda ba ya so ta yi nesa da shi, duk kuwa da cewa da ba ita cezaɓinsa ba a farko domin ba ita ya so ya aura ba. Sannan kuma jigon wasan ya ƙara fitowa a inda aka nuna Nura yana godewa Allah yana kuma nuna jin daɗinsa da Allah ya bashi iko ya yi wa iyayensa biyayya ta hanyar auren Indo, wadda a farko ba itace zaɓinsa ba. Amma gashi yanzu yana matuƙar ƙaunarta har yana jin ba ya so ta yi nesa dashi.

4.1. Matakan Wayewa a Cikin WasanIdonƘauye

Bayaga nishaɗantarwa da wannan wasa na IndonƘauye ke ƙunshe da shi, wasan ya sarrafa matakan wayewa daban-daban domin ƙoƙarin ganin an nuna yadda taurarruwar wasan ta bi ta kansu kafin ta kai ga ta waye, ta kuma kasance kamar kowanne mutum a cikin al’umma wanda ka iya bayar da tasa gudummuwar a tsarin zamantakewar rayuwa. Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin fito da waɗannan matakai da yadda aka yi amfani da su a cikin wasan, tare da bayyana su a fili ta yadda za a iya fahimta har kuma a amfana daga gare su. Matakan da aka yi amfani das u a cikin fim ɗin sun haɗa da:

4.1.1Iyali: Iyali kamar yadda Bargery da kuma Ƙamusun Bayero suka bayyana shi ne dangin mutum, wanda ya ƙunshi mai gida da matansa da kuma ‘ya’yansa da sauran ‘yan uwa na kusa. Samuel da Herbert (1976), kuwa cewa suka yi iyali shi ne matakin wayewa na farko wanda mutum ke bi ta kai, wanda ya ƙunshi uwa da uba da ‘yan uwa da kakanni da kuma sauran dangi, waɗanda su ne ke fara koya wa yaro abubuwan da ya kamata ya sani na rayuwa, kamar yadda mutum zai yi amfani da abubuwa na yau da kullum kamar sutura da wurin zagayawa da kumayadda zai yi hulɗa da sauran jama’a tare da iya tantance matsayin kowa ya gane iyaye da yayye da malamansa da sauransu.

Wannan mataki na wayewa (iyali), ya bayyana a cikin wasan IdonƘauye, tare da taka rawa matuƙa a cikin rayuwar tauraruwar wasan wajen wayar mata da kai don ganin ta fahimci rayuwa, inda tun sanda Nura ya je ƙauye da niyyar ganinta, Guggo (mahaifiyar Indo) take yi mata faɗa da cewa ta rinƙa natsuwa a duk abin da take yi sannan ta sani Nura yayanta ne kuma ya zo ne ya ganta domin shi za ta aura, sannan ta umarce ta da ta yi wanka tare da kwalliya ta iske shi a waje. Haka kuma bayan Indo ta je wurin Nura ta shiga motarsa sai ta koka da cewa motar ta cika sanyi, har take tambayarsa ko hunturu ya ɗebo musu daga birni, shi kuma sai ya mata bayani da cewa iyakwandishina ce ya kunna wadda ita ce ke sanyaya motar. Haka kuma bayan an nuna cewa an ɗaura auren Indo da Nura, an nuna tauraruwar a cikin gidan aurensu tana barci, ga shara nan ta zubar a ko ina, sannan ta yi bayan gari a masai irin na zamani har ya cika, saboda bata iya amfani da shi ba. Amma bayan mijinta ya dawo sai take gaya masa cewa masan ya cika ne sai an nemo mai yashewa, inda shi kuma ya yi mata bayani da cewa ba cika ya yi ba, sannan ya nuna mata yadda za ta rinƙa yi mafani da shi nan gaba. Haka kuma an nuna “Yaya Nura” yana ƙara yi mata bayani a kan yadda abubuwan da ke amfani da wutar lantarkikamar su radiyo mai hoto da kayan girki na gidan suke, domin ta san yadda za ta sarrafa su tare da gujewa haɗarin wutar wanda kan iya kai mutum ga rasa rayuwa. Haka kuma an nuna yadda Guggo ke yi wa Indo bayani da cewa ba komai ba ne ake faɗa a gaban mutane, a lokacin da take gaya mata cewa tana da ciki. Waɗannan misalai ne na yadda aka nuna irin yadda iyali ke taka rawa wajen wayar da kai ga mutum domin ya fahimci wani abu na rayuwa wanda bai sani ba, waɗanda za a iya kafa hujja da su daga cikin wasan.

4.1.2Tsara: Tsara ko sa’a kamar yadda Bargery da Ƙamusun Bayero suka bayyana shi ne wari, ko jerin mutane da suke dai-dai da juna ta fuskar shekaru ko matsayi ko kuma arziki. Yayin da su kuma Hebert da Samuel (1976), suka bayyana cewa tsara ya ƙunshi mutane ne da shekarunsu da kuma matsayinsu na rayuwa yake dai-dai da juna. Sun ƙara da cewa wayewa a tsakanin tsararraki kan fara ne tun daga yarinta a inda yara ke nuna wa junansu dokoki da ƙa’ida ta yadda ake aiwatar da wani wasa tare da sanar da su hikimomi da dabaru na zaman rayuwa. Wannan mataki ya bayyana a cikin wasan IndonƘauye tun a farko-farkon wasan, inda aka nuna tauraruwar wasan (Indo) a ƙauyensu tare da wata ƙawarta mai tallan gyaɗa suna hira ta bata gyaɗa tana ci har da yi mata kirari, inda daga nan ne har ta ke gaya mata ta ga yayan nan nata na birni (Nura) ya zo a mota.Haka kuma an nuna Indo a mastayin ɗaliba acikin ‘yan uwanta ɗalibai suna wasanni irin na motsa jiki tare da waƙe-waƙe irin na yara wanda yake ɗebe musu kewa tare da samun buɗewar ƙwaƙwalwa. Haka nan kuma an nuna wata cikin ‘yan ajin su Indo ta na gaya mata ta zo su tafi gida a mota, inda ita kuma take gaya mata cewa a ƙafa za ta tafi, sai ƙawar tata ke gaya mata cewa za ta ɓata fa kasancewar ba ta san gari sosai ba. A wani wurin kuma an nuna Indo a cikin yaraɗalibai ‘yan uwanta suna yin labarai a tsakaninsu, har wani yaro yana roƙonta ta sam masa mangwaron da take sha, inda ta hana shi yake ce mata rowa dai babu kyau, kuma za a rinƙa ce mata marowaciya. Har wa yau an nuna wata ɗaliba tana gaya wa Indo cewa ta dena cin abinci a cikin aji domin ba ɗabi’a bace mai kyau. Haka kuma an nuna Indo da ƙawayenta suna wasanni irin nasu na mata. A irin wannan mataki yaro kan koyi abubuwa da yawa waɗanda za su sa ya waye tare da koyon abubuwa na zamantakewa kamar yadda ya faru da Indo.

4.1.3Addini:Addini kamar yadda Ƙamusun Bargery da na Bayero suka bayyana, shi ne hanyar da ake bi domin a bauta wa ubangiji.Shi kuwa Bunza (2013), ya bayyana addini ne a matsayin yadda da umarni, da kuma hani da horo. Sannan ya ƙara da cewa addini ya shafi miƙa wuya ga abin bauta, ita kuma bauta itace yin ɗa’a kan hani da horo. Addini na da matuƙar muhimmanci a matsayin mataki na wayewa, domin yakan kasance ne hanya da ake nuna wa mutum abubuwan da addininsa ya amince da su da kuma waɗanda bai amince da su ba. Haka kuma a matakin addini ne ake nuna wa mutum yadda zai bi ya aiwatar da wata bauta domin neman yardar ubangiji, tare da sanar da shi abubuwa muhimmai da addinin ya zo da su. An yi amfani da addini a matsayin matakin na wayewa a cikin wasan IndonƘauye, inda aka nuna Nura ya ɗauko malami na musamman na addinin musulunci domin ya koyawa matarsa ilmi da dokokin addinin, sannan yake sanar da shi cewa matar tasa ba ta san komai ba na daga addinin, don haka zai fara mata karatu ne tun daga farko. Nura ya nuna wa malamin cewa yana so ne a koya wa matar tasa yadda ake yin alwala da yadda ake yin wankan tsarki da kuma yadda za ta yi sallah. Waɗanda a iya cewa su ne abubuwa na farko-farko da ya kamata kowane musulmi da ya fara koyon addinin musulunci ya sani. Haka kuma an nuna Nura yana gaya wa Indo cewa zai sa ta a makarantar Islamiyya domin ta sami ilmin addinin musulunci. Sannan ya jaddada mata cewa wajibi ne a duk abin da mutum zai yi ya san ilmin addininsa domin da haka ne zai san yadda zai bauta wa ubangijinsa. Har wa yau an nuno malam yana yi wa Indo bayani dangane da abin da ya shafi salla da kuma irin matsayinta a addinin musulunci, wadda ya ce ita ce mafi girman ibada a wurin ubangiji, kuma idan ta inganta ana sa rai dukkan ayyuka na bauta su inganta. Sannan ya ƙara mata da cewa ita kuma salla ba a yin ta sai da tsarki na jiki da kuma na tufafi.

4.1.4 Makaranta :Makaranta wuri ne da ake zuwa domin a koyi ilmin haɗe da tarbiyya. Makaranta a matsayin wani mataki na wayewa takan kasance ne wuri da za a koya wa yaro abubuwa na karatu da rubutu da kuma ilmi na zamantakewar rayuwa, tare da koya masa tarbiyya ta girmama na gaba da shi, gami da ladabi da biyayya. Haka kuma a makaranta ne ake koya wa yaro yadda zai yi mu’amala da mutane wajen haɗuwa a aiwatar da wani abu da zai inganta rayuwar al’umar da yake ciki. Kuma a makaranta ne yaro kan koyi iya tsara abubuwa da kansa.An yi amfani da makaranta a cikin wannan wasa a matsayin mataki da za a iya bi domin a wayar da wani mutum. An nuna haka tun a lokacin da Nura yake lallashin Indo da ta yi haƙuri ta je makarantar da zai sa ta, har yake gaya mata cewa zai sa ta a makarantar ne saboda ta samu ilmi na yadda za ta kula da kanta ta iya tsafta, ta kula da ‘ya’yanta ta kuma kula da gidanta da kyau. Bayan Indo ta shiga makaranta an nuna malamin ajinsu yana gaya wa sauran ɗalibai da su rinƙa girmama Indo saboda ta grime su, kuma duk abin da ba ta sani ba su koya mata. Sannan ya gaya wa Indo cewa idan aka kawo mutum makaranta to dole ne ya kasance mai biyayya duk girmansa. Baya haka kuma an nuna ɗalibai a cikin aji malama na koya musu karatu, inda ta tambaye su sunan gwaiba da mangoro da kuma kankana da Ingilishi, wanda hakan ya sa Indo ta samu ƙaruwa na sanin sunayen abubuwa da harshen Ingilishi kamar yadda aka nuna ta tana biyawa mijinta. Har wa yau an nuna Indo malamanta sun kirata suna yi mata faɗa cewa ba kowacce maganace ake yi da yara ba, kuma ta sani ta girmi sauran yaran da take tare da su. Hakan ya faru ne saboda an same ta tana ba ɗalibai ‘yan uwanta labarin irin yadda maza da mata ke zaman aure a tsakaninsu. An nuna Indo ta je gidan shugaban makarantarsu tana ɗibar mangwaro, inda ya yi mata nasiha da cewa ta dena ɗibar abin da ba a bata ba, yin haka kuma sata ne, don haka idan tana buƙatar mangwaron sai ta tambayi iyalinsa domin su bata.

4.1.5. Horaswa: Horaswa ya ƙunshi nuna wa mutum wani abu domin ya koya ya kuma iya ta hanyar nanata masa abin a kai- a kai, har ya kai ga ya iya abin yadda ake buƙata. Horaswa ya kasance a matsayin mataki na ƙarshe da aka bi a cikin wannan fim domin ganin an canza tare da inganta rayuwar Indo. Nura ya bi shawarar abokinsa ne inda ya ɗauki Indo ya kai ta wurin wata mai horaswa ta musamman (Meenat), domin ganin ta koya mata abubuwa na rayuwa a matsayinta na mace domin ta waye, wadda ta ja ta a jiki sosai tare da koya mata yadda za ta yi abubuwa na cikin gida kamar su girki da gayara gida, da tafiya irin ta mata da sarrafa kayayyakin zamani da iya tuƙin mota da kuma uwa uba iya karatu da rubutu tare da iya magana cikin harshen Ingilishi, waɗanda duk an nuna tauraruwar a wurare daban-daban tana koya daga mai horas da ita.

5.1 Kammalawa

Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin fito da yadda wannan wasa ya sarrafa matakan wayewa ne domin ganin an canza tare da inganta rayuwar tauraruwar wasan daga cikakkiyar baƙauyiya wadda ke da yawan wauta ga kuma jahilci zuwa wata wayayyiyar mai ilmi wadda za ta iya amfanar da kanta har kuma ta iya inganta rayuwar waninta. Saboda haka an ga yadda wasan IndonƘauye, wanda yake wasa ne na raha ya yi ƙoƙarin nuna matakai daban-daban na rayuwa waɗanda za a iya bi ta kansu domin a sauya rayuwar mutum ya zama ya san abin da ya dace da kuma wanda bai dace ba, sannan ya zama ya iya kyautata rayuwar al’ummar da yake ciki ta hanyar bayar da gudummuwar da ta dace. Ire-iren matakan da wannan maƙala ta duba tare da fito da yadda aka yi amfani da su a cikin fim ɗin sun haɗa da iyali, da tsara, da makaranta, da addini, da kuma horaswa, waɗanda sai da aka ɗora tauraruwar wasan a kan kowanen su, kafin daga bisani rayuwarta ta canza tare da inganta zuwa matar da mijinta ke ƙauna da kuma alfahari da ita.

Manazarta

 

A tuntuɓi mai takarda domin samun manazarta.

Post a Comment

0 Comments