Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa da Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyar Harshe, Jami’ar Jahar Kaduna ta shirya a kan Daidaitacciyar Hausa da Ƙa’idojin Rubutu da Fasahar Shirya Ƙamus da kuma Ƙalubalan da Suke Fuskanta a Cikin Ƙarni Na 21. Wanda aka gudanar a Zauren Lacca Na Tsangayar Fasaha da ke Jami’ar Jahar Kaduna, daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Nuwamban shekarar 2019.
Gudummawar Turawa
Wajen Samuwa Da Ginuwar Ƙa’idojin Rubuta
Hausa
Dr.
Adamu rabi’u bakura
08064893336
Tsakure
Rubutu wani salo ne na zayyana wasu alamomi
a kan wani abu mai bagire da za su waƙilci Magana. Ana iya
kallonsa a matsayin wani nau’i na kwaikwayon Magana wadda ake furtawa da fatar
baki. Akwai waɗansu ‘yan
bambance-bambance tsakaninsa da maganar fatar baka. Bambancin kuwa shi ne, naƙaltar ƙa’idojin rubutu,
rashin sanin ƙa’idar rubutu yana haifar da sauya ma’ana da rage wa
matanin da aka rubuta kima. Yayin da aka tashi rubuta wata maganar fatar baki,
dole ne a kula da wasu lafuzzan sautukan harshe tare da ƙoƙarin nuna su a rubuce
domin sadar da saƙo mai ma’ana. Hakan ba zai tabbata ba sai ta hanyar
fahimtar dokokin rubuta harshe. Rubutun Hausa, tamkar rubutun kowane harshe ne, yana da ƙa’idoji waɗanda tilas ne mai
rubutu ya kiyaye su muddun yana buƙatar isar da saƙo mai ma’ana.
Fahimtar haka ya sa Turawa suka haɗu suka shata ƙa’idojin rubuta Hausa
da haruffan boko. Harshen Hausa da al’ummar Hausawa sun amfana, saboda hakan ya
taimaka wajen cigaban harshen Hausa da kyautatuwar martabarsa. Ba don Turawa
ba, da ɗora wa boko harsashi
a Hausa ya yi wuya. Turawan mishan da ‘yan leƙen asiri da
ma’aikatan hukuma da ‘yan mulkin mallaka, sun taimaka wa rubutun Hausa har ya
sami kansa a matsayin da yake a yau. Sanin haka ne ya sa wannan maƙala ta ƙuduri aniyar komawa
fagen tarihi domin zaƙulo rawar da Turawa suka taka wajen shimfiɗa harsashen ginin ƙa’idojin rubutun
Hausa, musamman hanyoyin da suka bi wajen mayyaze wasu sautukan Hausa da babu a
harshen Ingilishi. Ko ba komai Hausawa sun ce, waiwaye adon tafiya.
1.0
Gabatarwa
Harshen Hausa ya fi kowane harshe da
ke sararin wannan duniya sauƙin sarrafawa. Domin lafuzzan haruffan
boko da ake rubuta Hausa da su, ba sa sauyawa kamar yadda wasu harsuna kan
sauya. Misali a rubutun Hausa lafazin harafin g ba ya sauyawa, kamar
yadda yakan sauya a Ingilishi, inda yakan koma lafazin /j/ kamar a Kalmar Germany. Haka kuma a
harshen Hausa ba a gutsure ƙarshen kalma wajen karatu tamkar yadda
yake faruwa a harshen Larabci, a inda ake rubuta BINTU a karanta shi da
lafazin BINT. Irin wannan sauƙin ne ya sa Turawa
suka duƙufa suka koyi harshen har suka yi ƙoƙarin shata masa ƙa’idojin rubutu domin
cimma wata ɓoyayyar manufarsa.
Rubutu da maganar baki sun sha bamban. Hasali ma dai rubutu wakiltar maganar
baka yake yi. Don haka ne suka yi tunanin tsara wasu ƙa’idojin da za su
taimaka wa masu karatu saurin fahimtar abin da aka rubuta. Fahimtar haka ne ya
sa aka ƙudurin aniyar komawa cikin fagen tarihi domin lalabo irin
rawar da Turawa suka taka wajen aza harsashen gina ƙa’idojin rubutun
Hausar boko. Shi ya sa aka sanya wa maƙalar suna: Gudummawar
Turawa Wajen Samuwa Da Ginuwar Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Takardar ta kawo
ma’anonin tubalan ginin taken maƙalar tare da bayyana
nau’o’in gudummawar da Turawan suka bayar kamar : Schon da Robinson da Hanns
Vischer da Bargery da R. M. East wanda ya kai gwauro ya kai mari don ganin
Hausa ta sami daidaitacciyar hanyar rubutu. Kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya.
1.1
Gudummawa
Gudummawa kalma ce bahaushiya da ke
cikin jerin sunayen jinsin mata. Ana faɗar ta da “gudunmawa” a karin harshen
Sakkwatanci da na Kananci da kuma Zazzaganci, kuma akan furta ta da lafazin
“gudunmuwa” a karin harshen Kananci, kamar yadda Bargery (1993:402)
ya nuna. Shi kuwa Abraham (1975:337) ya nuna cewa a
karin harshen Sakkwatanci ne ake faɗar ta da lafazin “gudunmowa”, wato akan sa
wasalin “o” a gaɓa ta uku maimakon
wasalin “u” da wasu karin harsuna ke amfani da shi. Har ila yau Ƙamusun
Hausa
na Jami’ar Bayero (2006:171) ya nuna ana furta gaɓa ta uku da wasalin “a” ko “o” misali
gu-dum-ma-wa. Kalmar gudummawa tana ɗauke da ma’anar taimako na aiki ko kuɗi ko abinci ko sutura
ko wani abu. Kuma daidai take da agaji ko ceto daga wahala kamar yadda Garba
(1990:4) ya bayyana.
1.2
Turawa
Ita kuma Kalmar “Turawa”, jam’i ce
ta kalmar Bature ko Baturiya. Wannan kalma tana cikin jinsin suna na namiji.
Turawa suna ne da ake kiran ‘yan asalin ƙasashen Yammacin duniya
da ake yi wa laƙabi da Turai waɗanda ke amfani da harsunan Turanci a matsayin
harshen uwa, musamman Ingilishi na ƙasar Ingila, kamar yadda Ƙamusan Hausa (2006:41) da Webster (1990:428) da Macmillan
(2007:501) suka nuna.
1.3
Samuwa
Kalmar “samuwa” kuwa tana nufin
tabbatar da abu a hannun mutum ko al’umma. Ita wannan kalma an fito da ita ne
daga kalmar “saamaa” wadda ke iya ɗaukar wasalin “e” ko “i” ko “o” ko “u” a gaɓar ƙarshe. Misali;
saamee, saami, saamoo, saamuu, Ƙamusun Hausa (2006:385).
Wannan kalma ce da ke cikin jerin
kalmomin da ke nuna aiki, wato fi’ili. Kuma tana ɗaukar ɗafa ƙeya, wanda hakan ya
bayar da kalmar “samuwa”, wato an yi mata ƙarin “wa” a ƙarshenta.
1.4
Ginuwa
Ginuwa kuma kalma ce da aka samar
daga kalmar “gina”, mai ɗauke da ma’anar ƙaga wani abu. Ita
wannan kalma tana cikin sahun kalmomi da ke nuna aiki, wato fi’ili. Haka kalmar
tana iya ɗaukar wasalin “e” ko
“o” ko “u”. Ita ma tana ɗaukar ɗafa-ƙeya, wanda hakan ya
samar da kalmar “ginuwa”. A Hausance kalmar ƙaga na ɗauke da ma’anar ƙirƙiro ko samar da wani
abu ko gano wani sabon abu kamar yadda Ƙamusun Hausa (2006:165)
ya bayyana.
1.5 Ƙa’idoji
Asalin wannan Kalmar balarabiyar
kalma ce da aka samo daga Kalmar Larabci, wadda Larabawa ke kira da suna ƘA’IDATUN ana kuma taƙaita ta zuwa ƘA’IDA a harshen Larabcin.
Ta hanyar taƙaitawar ce Hausawa suke amfani da Kalmar, Kalmar ƘA’IDA (Ƙaa’idaa) tana cikin
jerin sunayen kalmomin Hausa jinsin mata, jam’i kuwa ya kasance ƙa’idoji ko ƙa’idodi. Kalmar na ɗauke da ma’anoni
daban-daban da suka haɗa da:
Doka – Wannan kalma
na nufin umurnin hukuma, jam’i kuwa a ce
dookooki.
Iyaka – Marabar wani
abu da wani abu.
Tsari – Daidaitawar
abubuwa ko kuma shiryiwarsu.
Kyakkyawar ɗabi’a, kamar yadda
BUK (2006:274) ya bayyana
1.6 Rubutu
Ita wannan kalma bahaushiyar kalma
ce wadda ke cikin tsarin kalmomin suna jinsin maza, jam’i kuwa shi ne rubuce-rubuce.
Kalmar na ɗauke da ma’anar: Zana
wasu alamomi a kan takarda ko wani abu mai bagire domin sadar da Magana wadda ɗan-adam ya fi faɗin (furta) ta da fatar
baki a ji da kunne, kamar yadda Yahaya (1988:1) da Bunza (2002:1) da BUK (2006:374)
suka nuna.
1.7 Ma’anar Ƙa’idajin Rabutu
Ƙamusai da dama sun
bayyana ma’anar ƙa’idar rubutu (orthography) gwargwadon fahimtarsu, kamar
yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya:
Webster (2000: 834) ya bayyana
ma’anar da cewa: Wata fasahar rubuta kalmomi ne ta amfani da haruffan da suka
dace bisa daidaitaccen tsari. A ma’anarsa ta biyu kuwa, cewa ya yi: hanya ce da ake amfani da ita wajen wakiltar
sautukan lafuzzan furucin harshe a rubuce ko kuma ta hanyar buga wasu sanannun
alamomi. Ba nan kawai ya tsaya ba, ya ma nuna cewa, wata hanyar nazari ce da ta
danganci haruffa da rubutun kalmomin harshe.
Yayin da Kamusan Macmillan
(2007:1058) ya bayyana ma’anar da cewa: A nazarin ilimin harshe ƙa’idar rubutu na
nufin wani salon tsarin rubutu ne da ake amfani da shi wajen rubuta haruffan
harshe.
Idan muka dubi yadda masana suka
bayyana ma’anonin tubalan gini wannan maƙala a cikin ƙamusai da ita kanta
ma’anar ƙa’idar rubutu, za a iya
cewa a dunƙule: Wata daidaitacciyar hanya ce, da aka shata domin
sarrafa abjadin Hausa cikin kyakkyawan tsarin ginin kalmomin Hausa, bisa
dokokin haɗa kalma da kalma da raba su tare da ba kowane sautin furuci haƙƙinsa tamkar yadda
tsarin nahawun harshen ya tanada, domin sadar da sahihiyar ma’ana a rubuce.
2.0 Tarihin Rubutu Da
Gwagwarmayar Marubuta
Tun farkon zuwan Turawa a farfajiyar
Afirka ta Yamma a cikin shekarar 1773, suka soma tsintar kalmomi da zantuttukan
Hausa, suka tafi da su ƙasar Turai. Sun
rubuta su ne da harruffan Romawa (boko), kamar yadda Hair (1967:32) ya
nuna. A daidai wancan lokacin duk yadda kunnensu ya ji sautukan Hausar, haka
nan suka rubuta su.
Ƙasashe kamar Jamus da
Ingila su ne wuraren da aka fara ƙoƙarin daidaita
harruffan Romawa wajen rubuta harsunan Afirka, ciki kuwa har da harshen Hausa.
Wani masanin tarihin kalmomi da ke Jamus mai suna: Lepsius, shi ne ya fara
shirya wata hanyar rubutu a shekarar 1850, da aka kira: Daidaitaccen Abjadi,
kamar yadda Zarruk (1980:112) da Yahya(1988:74) da Bunza (2002:32) suka zo
da bayanin. Ta wannan hanyar rubutu ce, Turawan ƙasar Jamus da dama
suka aiwatar da rubuce-rubucensu masu ɗimbin yawa da suka danganci harshen Hausa da
adabinsa, kamar: James Frederick Schon da Prietzer da Miscich da George Reime
da Westerman da sauransu.
Yayin da aka karkato a ƙasar Ingila kuwa,
akwai masana kamar irin su: Farfesa Lee, da ya yi aiki a ƙarƙashin Ƙungiyar Gano Afirka,
waɗanda suka samar da
wani matani da suka kira da suna: Rubutun
Afirka. Daga cikin Turawan da suka yi amfani da wannan hanyar salon rubutu
babu kamar Rabinson da Bargery, tamkar yadda Hair (1967:40) ya ambata.
2.1 Gudummawar Schon
Schon mutumin ƙasar Jamus ne,
cikakken sunansa James Frederic Schon. Aikin Mishan ya kai shi Saliyo a wajejen
shekarar 1840. Bai taɓa saka ƙafarsa a farfajiyar ƙasar Hausa ba. Ya
koyi Hausa ne wurin Dorogu da Abega, wasu bayi da Barth ya tafi da su ƙasar Turai, kamar
yadda Yahaya (1988: 124).
Schon ya yi amfani da kusan haruffan
abjadin da ake amfani da su a wannan zamani wajen rubuce-rubucensa na Hausa, in
ban da ‘yan atishawa da ‘yan zoza da hamzatattu. Abjadin kuwa sun haɗa da: a, b, c, d, e,
f, g, h, I, j, k, q, l, m, n, o, p, r, s, t, u, v, w, y, z.
Kasancewar kunnen
Schon na Jamusanci ne, shi ya sa sautukan ‘yan atishawa kamar: c, j,
ts, sh, s, z da ‘yan zuz na Hausa kamar: f, fy, sh, h, s suka gagare shi rarrabewa. Wannan ne ya
haifar da hautsuna su.
Haka ya kasa tantance
hamzatattun baƙaƙe, wannan ne ya wanzar da rashin haruffan ɓ, ɗ, ƙ, da ‘y a
cikin abjadinsa. Wani lokacin yakan rubuta gb a madadin b. Ya
kuma kasa gane bambancin gajeren wasali da ɗauri. Wannan ne ya sa yakan rubuta baba a
wani wurin kuwa ya sa babba domin ya ɗauke su tamkar abu ɗaya ne. Wani lokaci
yakan rubuta dere wani zubin kuwa ya rubuta dare. A wasu wuraren
kuwa ya rubuta taffi da teffi a madadin tafi, kamar yadda
Newman (1974:3-4) ya nuna.
Schon ya bayar da
muhimmiyar gudummawa wajen aza harsashen ginin ƙa’idojin rubutun
Hausa, domin ana kyautata zaton cewa, shi ne Baturen farko da ya gabatar da
jerin haruffan Hausa da yadda ake amfani da su wajen gina kalmomin Hausa,
(Schon,1885:xi-xii). Hasali ma da aikinsa na Nahawun Hausa aka yi amfani wajen
koyar da Turawa ɗalibai harshen Hausa
a ƙasar
Turai, kamar yadda Bakura (2012:211) ya kalato daga Baldin (1977:9-10).
2.2
Gudummawar Charles Henry Robinson
Robinson
haifaffen garin Ingila ne. Yana ɗaya daga cikin ‘yan ƙungiyar Hausa, wadda
aka kafa a shekarar 1890. Ƙungiyar ce ta ɗauki nauyin turo shi ƙasashen Afirka. Ya
zauna a Libiya inda ya koyi harshen Larabci da Hausa, wannan ne ya ba shi damar
naƙaltar
rubutun ajamin Hausa. Wannan ne ya ba Robinson damar sanin hamzatattun baƙaƙen Hausa, ya yi ƙoƙarin rarrabe su. Ana
kyautata zaton shi ne ya fara yin ɗigagga a ƙarƙashin haruffa kamar: b.
da d. da kuma k. . Sai dai ba ko’ina
yake yin ɗigon ba. Saboda
tasirin da rubutun ajamin Hausa ya yi masa, domin su kansu masu rubutun ajamin
Hausa, sukan rubuta harafin ƙan mai ruwa (ق) wani zubin su rubuta kaulasan
(ك) dalilin
haka ne Robinson ya rubuta karami maimakon k.arami ( ƙarami) ya kuma rubuta k.aratu
maimakon karatu.
Abin tambaya
a nan shi ne, daga ina Robinson ya samo wannan fasahar saka ɗigagga a ƙasan hamzatattun
haruffa? Shin shi da kansa ya ƙago ko ilhami ya samu? Ko kuwa
kwaikwayon fasahar ya yi?
Amsar waɗannan tambayoyi ita
ce, muna sane da cewa, ya koyi harshen Hausa da Larabci a ƙasar Libiya. Ita kuwa
Hausar da ya koya, ya koye ta ne daga wasu malamai ko almajirai da suka fito
daga ƙasar Hausa. Wannan ne ya ba shi damar naƙaltar ajamin Hausa,
ta hanyar karatu da rubutun ajamin ne ya mayyaze hamzatattun sautuka. Har ya yi
ƙoƙarin kwaikwayon
hanyar da Malam Shi’itu Ɗan Abdur-Ra’ufu ya yi amfani da ita a littafinsa mai suna
: JADDIL- AJIZ waƙaƙƙe na fiƙihu. Ana kyautata
zaton cewa, malamin ne na farko da ya fara sanya ɗigagga a saman wasullan sama na
haruffa dal (د ) da ba
(ب ) da kaulasan ( ك ) domin su bayar da
sautukan ɓ da ɗ da kuma ƙ. Daga nan ne
Rabinson ya ciranto wannan fasahar. Shi kuma sai ya sanya musu ɗigaggan a ƙasan haruffan b da
d da kuma k, na haruffan Romawa waɗanda ke da muryoyin sautuka ɗaya da makamantansu
na Larabci, domin su bayar da sautukan ɓ da ɗ da ƙ. Daga wannan za a
iya fahimtar cewa, Robinson ya gina ƙa’idojin rubutu
Hausar boko a bisa tsarin rubutun ajamin Hausa. Saboda haka ne Robinson ya gaza
cim ma Schon a fagen raba kalmomin Hausa.
Robinson ya bayar da gagarumar
gudummawa a wannan haujin, musamman ida aka yi la’akari da talife-talifensa a ɓangaren Nahawu da
adabin Hausa, waɗanda ya yi amfani da
su wajen koyar da Turawan Mishan harshen Hausa a Jami’ar Ingila a ƙarshen ƙarni na goma sha tara
(19) don su sami damar yaɗa addinin mishan a ƙasar Hausa, kamar
yadda Bakura (2012:155) ya nuna. Da wannan aikin ne Turawan da suka biyo
bayansa suka sami hasken kwaikwayon yadda Hausawa suka alamta sautukan muryoyin
Hausa a tsarin rubutun ajamin Hausa.
3.0
Tunanin Samar Da Sigar Abjadin Sautukan Hausa Daga Abjadin Ingilishi A Nijeriya
Bayan samuwar makarantun boko da yaɗuwar ilimin zamani da
ƙaruwar
yawan ɗalibai da ke shiga
makarantun a sassa daban-daban da ke farfajiyar Nijeriya Ta Arewa. Babbar
matsalar da ta fara fuskantar ma’aikatar ilimi ita ce ta ƙarancin littattafan
karantawa a makarantun. Wannan ne ya sa a daidai lokacin da Hanns Vischer ya
tafi London hutu a shekarar 1911, ya gudanar da tarurruka da masu ruwa da tsaki
wajen tafiyar da harkokin mulkin mallakar ƙasar Hausa, domin
ganin an samar da littattafan karatu a Makarantar Nasarawa kafin ƙarshen hutun, saboda
shiga sabuwar shekarar karatu a cikin watan Oktoba na shekarar 1911, wato bayan
sallah ƙarama (Graham, 1966:83). Babbar matsalar da ya fara
fuskanta, ba ta wuce ta rashin takamaiman abjadin da za su mayyaze saututtukan
harshen Hausa a cikin sigar rubutun Hausar Boko ba (Graham,1966:83).
A sakamakon fahimtar da ke akwai na
cewa, abjadin Ingilishi bai ƙunshe da wasu sautukan Hausa, ya sa
tun a cikin watan Afirilu na shekarar 1910, Bishop Tugwell ya bayar da shawara
ga Hesketh Bell da ya ƙaddamar da wani kwamiti da zai ƙunshi mutane kamar
Miller da Bargery da Vischer da H.R. Palmer da E.J. Arnett, domin su tattauna
game da matsalar wasu sautukan harshen Hausa da yadda za a magance lamarin.
Wannan ya sa Hesketh Bell ya yi na’am da shawarar, tare da ƙudurin jinkirta buga
littafin da Hanns Vischer ya rubuta mai suna Hausa Primer , sai bayan kwamitin ya zauna, sun cimma matsaya game
da sigar abjadin sautukan Hausa da za a yi amfani da su (C.M.S.,1910/(N.N.)No.37).
3.1 Gudummawar
Turawan Mishan
‘Yan Mishan sun haɗu a Lakwaja suka
gabatar da buƙatarsu ta a samar da wani tsayayyen abjadin da zai samar
da wasu sautuka na harsunan Hausa da
Nufanci da Yarabanci da kuma harsunan da ke Lardin Binuwai. Harshen Hausa yana
da haruffa 29, idan aka cire harafin “q“ da “x” a matsayin haruffan da suka
amince a yi amfani da su wajen rubuce-rubucen adabin mishan (C.M.S.,
1911/N.N.).
3.2 Gudummawar Hanns
Vischer
Hanns Vischer, shi ne mutun na farko
a farfajiyar Nijeriya Ta Arewa da ya fara shata ƙa’idojin rubutun
Hausar boko. Ya tsara su ne a daidai lokacin da yake riƙe da muƙamin Daraktan Ilimi a
Nijeriya Ta Arewa. Ya rubuta maƙala da ya kira da suna: Rules
For Hausa Spelling, wadda aka buga a farkon shekarar 1912. Sai dai Yahaya
(1988:126) ya ambaci Rules For Hausa Spelling a matsayin littafi ba maƙala ba. A tsarin
abjadin Vischer an kawo haruffa 28 ne kawai, yayin da aka cire haruffan “ c” da
“q” da “v” da kuma “x”.
Visher ya nazarci matsalolin rubutun
Hausa da na nahawunsa, a cikin wannan maƙalar tasa ya yi
magana a kan baƙaƙe da wasulla da auren wasali kamar “ au”, da “ ai” da
wakilin suna da zagi da yadda ake samar da jam’i da lokuttan aikatau. Haka ya
bayyana cewa duk kalmomin Larabci da ake amfani da su a cikin harshen Hausa da
suka danganci addini da shari’a za a rubuta su kamar yadda ake furta su da
Hausa. Sunayen Larabci kuwa za a juya su ne kamar yadda suke. Yayin da kalmomin
Ingilishi kuwa sai a fassara su zuwa Hausa (Vischer, 1912:3) da (Graham,1966:84)
da (Zarruk,1980:116-7).
Vischer, ya cancanci laƙabin Ɗanhausa, domin
sautukan harshen Hausa ba su kuɓuce masa ba. Ya bayyana irin kalmomin da suka kamata a haɗa da waɗanda suka kamata a
raba. Hasali ma, ba inda abjadinsa ya bambanta da na wannan zamanin sai a waɗannan muhallai:
1- Amfani da harafin ch
a madadin c misali, ya rubuta mache a madadi mace
2- Ya kasa bambanta y
da ‘y.
3- Ya yi amfani da ɗigagga a ƙarƙashin hamzatattun baƙaƙe. misali: b. d.
k. a madadin ɓ ɗ ƙ. Sai dai an sami saɓani a wannan Haujin,
domin Yahaya (1988:126) cewa ya yi Hanns ya sauya alamar nan ta yin digo da
almar yi wa harafi alamar hamza. Misali: b. a rubuta shi haka ‘b wato ɓ , d. a rubuta ta haka: ‘d wato
ɗ, yayin da k.
za a rubuta shi haka: ‘k wato ƙ. Ya kuma nuna cewa
da ƙa’idojin
ne Bargery ya yi amfani wajen rubuta ƙamusunsa.
4- Yakan sa ɗauri a muhallin da
babu ɗauri. Misali: barra
a madadin bara.
5- Harafi r da ke
ƙarshen
Kalmar nasaba ko haddasau yakan saje da baƙin da ke biye da shi.
Misali: rigad da a madadin rigar da, ko fitad da a madadin
fitar da.
6- Ya yi amfani da karan
ɗori a sashen farko na
tagwan Kalmar da ke sarrafuwa. Misali: ɗan-uwa; ‘yan-uwa. Su
kuwa kalmomin da ake maimaitawa,sai a haɗe su ba za a sa musu karan ɗori ba. Misali: saƙesaƙe a madadin saƙe-saƙe.
3.3 Gudummawar George
Parcy Bargery
George Parcy Bargery ya bayar da
tasa muhimmiyar gudummawa wajen kyautata ƙa’idojin rubutun
Hausar Boko ta hanyar yi wa abjadin Hausa wasu gyare-gyaren da yake ganin sun
dace da harshen Hausa. Daga cikin waɗannan gyare-gyaren da ya aiwatar sun haɗa da:-
-
Watsi
da tagwan harafin “ ch” ya ɗauki “ C”. Sai dai ya amince da
harafin “ sh” da “ ts”, a fagen ɗauri ne kawai yake amfani da “ –ssh”
da “ –tts”, ba “-shsh” da “ –tsts” ba.
-
Amfani
da waƙafi a gaban hamzatattun baƙaƙe a maimakon ɗigagga da ake sawa a ƙarƙashin baƙaƙen, misali: ‘b
, ‘d , k’
-
Rashin
nuna alamar tsawon wasali, sai wurin da ake jin mai karatu zai ruɗe. Idan haka ya zama
wajibi, sai a yi layi a saman wasalin kamar a wannan misali: “ ko ya aike ni ba
na je ba.”
-
Rashin
rarrabewa tsakanin ra-kaɗe da ra-buge. Ba kuma
za a sa wata alama da za ta bambanta “n” ‘yar hanƙa da ‘yar hanɗa ba.
Kusan za a iya cewa, abjadin Bargery
ya fi kusanta da kuma dacewa da lafuzzan Hausa fiye da na sauran da suka gabace
shi. Haka ƙa’idojinsa na raba kalmomi sun fi na sauran, kamar yadda
Zarruk (1980:117-8) ya bayyana.
Bayan wannan sahihiyar hanya da aka
fara bi don ganin an samar da ingantaccen harsashen ginin ƙa’idojin rubutun
Hausa, an kuma yi ƙoƙarin kafa wasu hukumomi a cikin gida da ƙasashen Turai da aka ɗora wa alhakin
kyautata ƙa’idojin da kuma haɓaka shi. A ƙasashen waje hukumar
da aka ɗora wa wannan aiki
ita ce Hukumar Ƙasa Da Ƙasa Ta Nazarin Harsuna Da Al’adun
Afirka:-
3.4
Gudummawar Hukumar Ƙasa Da Ƙasa Ta Nazarin
Harsuna Da Al’adun Afirka
(International
Insitute Of African Languages And
Cultures).
Bincike ya tabbatar da kafuwar
wannan hukuma a cikin watan Yuni na shekarar 1926, a ƙarƙashin jagorancin
Frederick John Dealtry Lugard. Hukumar ta ƙunshi ‘yan majalisar
gudanarwa mutun goma sha biyar (15). Hukumar tana tattare da ƙungiyoyi 28 da ke
sha’awar nazarin al’amurran da suka danganci Afirka, da ke da wakilai a ƙasashe goma a cikin
nahiyar ta Afirka, tare da ƙungiyoyin mishan daban-daban da suka
haɗa da Forotastan da
kuma Roman Katolika (International Institute, 1928:10).
An kafa wannan hukuma ne domin ta
samar da bayanai da suka danganci al’ummomin nahiyar Afirka. Ta bayar da
shawarwari tare da tallafi ga Turawa da ke tafiyar da wasu ayyuka na musamman a
wasu sassan Afirka, da kuma bayar da gudummawa a kan sha’anin binciken kimiyya
da ilimin halayyar al’adun ɗan-adam da kuma ilimin harsuna.
Hukumar ta sha alwashin danganta duk
wani sakamakon binciken da aka aiwatar, da rayuwa ta haƙiƙa da ta shafi al’ummomin
Afirka ta yadda binciken zai amfani jami’an mulkin mallaka da na sashen ilimi
da na ɓangaren ma’aikatar
lafiya da masu kula da jin daɗin walwalar al’umma da Turawa ‘yan kasuwa da ke zaune a
nahiyar Afirka (Lugard, 1928:2). Domin ganin ta cimma burinta, hukumar ta samar
da mujalla guda biyu, ɗaya an yi mata take: African Studies, wadda ta ƙunshi nazarce- nazarcen
ƙwararru
a kan wasu fannoni da suka keɓanta ga hukumar. Mujalla ta biyu kuwa an yi mata laƙabi da: African Documents, wannan mujalla ta ƙunshi ƙasidu da rubutattun
matani, waɗanda aka samu a
rubuce ko ta hanyar shifta daga ɗan Afirka, aka kuma fassara shi cikin
harsunan ƙasar Turai. Irin waɗannan bayanai sun ƙunshi labarai da waƙoƙi da wasan kwaikwayo
da kacici-kacici da karin Magana da tarihi da wasu hanyoyin gudanar da al’adu
da ke ɗauke da bayanai
nau’i-nau’i da suka haɗa da tsarin sarautun
al’ummomi da al’adunsu da hikayar mafari da kuma uwa-uba, lamarin addini.
Muhimmin aikin farko da hukumar ta
fara sa wa a gabanta bayan da aka kafa ta shi ne, ƙoƙarin samar da
daidaitaccen ƙa’idojin rubuta harsunan ƙasashen Afirka, wanda
ya kwashe shekaru ba tare da haƙa ta cimma ruwa ba. Duk da haka
Farfesa Westerman ya yi namijin ƙoƙarin shata wata ƙa’ida ta gaba ɗaya da ta shafi
rubuta harsunan Afirka, ciki kuwa har da harshen Hausa, bayan ya sami damar
ganawa da ƙwararru da dama, kamar yadda Lugard (1928) ya nuna.
Sakamakon samuwar wannan hukumar
ce da ayyukan da ta zartar ya haifar da
wanzuwar gasar farko da ta samar da littattafan gasa kamar:
1. Hausa Stories na
H. G. B. Nuhu.
2. Hausa Stories na
Malam Dodo.
3. Zaman Dara na Malam
Ahamet Mettenden.
4. Littafin Karatu Na
Hausa na Malam Bello Kagara.
5. Takobin Gaskiya na Malam
Nagwamatse Ɗan Alƙali Sakkwato, (Westerman,
1933:102-103). Sai dai ba a samu damar buga waɗannan littattafan ba.
3.5 Gudummawar Dr.
R.M. East
A daidai shekarar 1933, Bargery yana
ƙoƙarin famar kammala ƙamusansa, yayin da
Ministan Ilimi kuma Shugaban Ofishin Fassara, Dr. R. M. East yana azamar tsayar
da ƙa’idojin
rubutun Hausar boko. Ko da yake yana ƙudurin daidaita
rubutun Ofishin Fassara da na Bargery. A Ofishin Fassara ana amfani da harafin ch,
ana kuma saka wa hamzatattun haruffa ɗigagga a ƙasansu. Misalan wasu
jumloli daga cikin Ladabin Chiniki a Labaru Na Da Na Yanzu :
·
Ya
kamata ka d.ebe malafo ko lema.
·
In
ya karb.a maka ka shiga.
·
Sai
ka fara chinikin abin da ya kawo ka (1931:260).
Duk da haka sai da
East ya bayar da umurnin yin amfani da ƙa’idar rubutun
Bargery tamkar
Yadda yake, kamar
yadda Zarruk (1980: 118) ya zo da bayani.
Kasancewar Gwamnatin Jahar Arewa ta
naɗa kwamiti tun a cikin
shekarar 1932, wanda ya share kusan shekaru biyar yana kai da komawa kafin ya
cimma matsayar yi wa haruffan b da d da k kugiya ko lanƙwasa a samansu
maimakon ɗigaggan da ake yi a ƙasan haruffan. Domin
ganin an cimma gurin da ya sa aka naɗa kwamitin, takanas sai Dr. East wanda yake ɗaya daga cikin ‘yan
kwamitin, ya tafi Birnin Berlin da ke ƙasar Jamus, ya
tattauna da Shugaban Cibiyar Nazarin Harsuna Da Al’adun Ƙasashen Afirka, a
inda suka kai ga matsayar da a rinƙa rubuta ƙugiya a kan haruffan b
domin samar da sautin ɓ, haka harafin d
domin samar da sautin ɗ, da kuma harafin k domin
samar da sautin ƙ.
Yayin da East ya dawo, sai ya sanar
da Gwamnatin Jahar Arewa, aka aminta tare da bayar da sanarwar amincewa da waɗannan alamun sautukan
Hausa, a Mujallar Gwamnatin Nijeriya (Nigeria Gazett, Government Notice,
No.396, ta 24 ga watan Maris na shekarar 1938, kamar yadda Yahaya (1988:127) ya
zo da bayanin. Binciken Yahaya (1988:127) ya nuna cewa, R.C. Abraham ne farkon
wanda ya fara amfani da waɗannan sababbin alamomin sautukan haruffan wajen rubuta ƙamusansa mai Suna: Dictionary
of the Hausa Language wanda London University Press suka buga a cikin
shekarar 1946.
3.6 Gudummawar
Gwamnatin Nijeriya Ta Arewa
Duk da kasancewar akwai ƙa’idojin rubuta Hausa
da Gwamnati ta aminta a yi amfani da su, amma akan samu bambace-bambance wajen
yadda wasu ke rubuta Hausa, musamman a fagen haɗa wasu kalmomi da raba su. Ga kuma
kullun safiya harshen sai daɗa bunƙasa yake ta hanyar sababbin kalmomin
Turanci da ke shiga cikin harshen Hausa ba kama hannun yaro. Don a hanzarta
shawo kan waɗannan matsalolin da
ke barazana ga rubutun Hausar boko, sai wani ɗan Majalisar Wakilai ta Jahar Arewa da
ke Kaduna, da ke wakiltar Lardin Bauchi mai suna Malam Bawa Bulkacuwa, ya
gabatar da shawarar cewa, “ya kamata a ba Mai Girma Gwamna shawarar a kafa wata
hukuma da za a kira: Hukumar Harshen Hausa.
Sakamakon wannan buƙata ce da Malam Bawa
Bulkacuwa ya gabatar a zauren Majalisar Wakilai da ke Kaduna na kafa Hukumar
Harshen Hausa domin a daidaita ƙa’idojin rubuta harshen Hausa, sai
gwamnatin ta karɓi kiran, ta kuma kafa
hukumar da aka kira da suna: “Hausa Language Board” wato Hukumar Harshen
Hausa, a shekarar 1955 domin daidaita ƙa’idojin rubutun
Hausa. Hukumar ta yi ƙoƙarin tace kalmomin da harshen Hausa ya aro daga wasu
harsuna kamar Larabci da Turanci. Ta kuma gudanar da wasu ayyukan da suka
taimaka wajen kyautatuwar rubutun harshen Hausa.
Hukumar ta ɗauki ma’aikata da
dama, shahararru daga cikinsu sun haɗa da: Alhaji Isa Kaita da Alhaji Aliyu
Makaman Bida da Alhaji Tukur Sarkin Yawuri da Alhaji Abubakar Imam da Mr. C.
Sanderson da Alhaji Abubakar Dokaji da Alhaji Abdulmalik Mani da Malam Maigari
Yusuf da Mr. J. W. Court a matsayin sakataren hukumar.
Daga cikin ayyukan da hukumar ta
aiwatar sun haɗa da:
1. Tabbatar da littafin ƙa’idojin rubutun
Hausa mai suna: Rules For Hausa Spelling, tare da yi masa wasu
gyare-gyaren da suka suka shafi haɗa kalmomi da raba su. Misali: a riƙa raba lamirin mutum
da na lokaci kamar a irin waɗannan jumlolin:
·
Abin da su ke so ba Abin da suke so ba
·
Sa’ar da ya ke zuwa ba Sa’ar da yake zuwa ba.
Kalmomi irin su saboda
da kalmomin jama’u irin su koyaushe da kowane da ko’ina sun raba su kamar haka:
·
Ko yaushe ba koyaushe ba
·
Ko wane ba kowane ba
·
Ko ina ba ko’ina ba
·
Sabo da ba saboda ba
Haka sun zartar da
hukuncin haruffa za su daina sajewa a cikin kalmomi irin waɗannan:
·
duk da haka ba dud
da haka ba
·
ya fitar da mu ba ya fitad da mu ba
kamar yadda
Kirk-Green (1964:194) ya nuna. An ma buga gyare-gyaren da hukumar ta aiwatar
game da ƙa’idojin rubuta Hausa a Mujallar Gwamnatin Jahar Arewa,
wato Northern Nigeria Gazette, Northern Reginal Notice No.31 ta ranar 22 ga
watan Janairu, shekarar 1957, kamar yadda Yahaya (1988:129) ya bayyana.
2. An cimma matsayar yin
amfani da wasu kalmomin bayanin nahawun Hausa kamar:
·
Ismi ya koma suna
·
Fi’ili ya
koma abin da za a yi
3. An tsara littafi
wanda ya ƙunshi jerin kalmomin da harshen Hausa ya ara fiye da ɗari biyu da hamsin
(250) waɗanda aka kira da suna
Alphabetical List of Words Impoted into Hausa. Kamfanin ɗab’i mai suna: Baraka
Press ta buga a shekarar 1958, kamar yadda Yahaya (1988:129) ya nuna.
4. An tsara littafin keɓaɓɓun kalmomin Hausa, da
aka kira da suna Glosseries of Technical Terms. Wannan littafin yana ɗauke da kalmomi dubu ɗaya da ɗari ɗaya (1100) da suka
danganci keɓaɓɓun kalmomin da ake
amfani da su a sassan ma’aikatu daban-daban.
Wannan
ba ƙaramar
gudummawa ba ce ga harshen Hausa da su kansu al’ummar Hausa.
Domin irin wannan rawar da Turawa suka taka ta
taimaka gaya wajen taskace tarihi da fasahohin magabatanmu tare da ƙara wa harshen Hausa ƙima a idon duniya,
har al’ummomi daban-daban sun duƙufa a fagen
nazarinsa.
4.0 Kammalawa
Daga waɗannan bayanai za a
fahinci cewa, Turawa sun shata ƙa’idojin rubuta Hausar boko ne, domin ƙoƙarin samar da wasu
alamomin da za a rinƙa sa wa harruffan Romawa don su wakilci muryoyin harshen
Hausa. Saboda Hausa tana da sautukan da babu irin su a harshen ƙasashen Turai. Haka
sun yi ƙoƙarin samar da hanyoyin da za a riƙa haɗa harruffa ana gina
kalmomi da jumlolin Hausa da yadda za a riƙa rarrabewa tsakanin
kalma da kalma da hanyoyi da za a nuna wa mai karatu wurin tashi ko tsayawa ko
iƙirari
ko tambaya da sauransu. Abin kula a nan shi ne, sun aiwatar da haka ne domin
wasu manufofi nasu. Duk da haka sakamakon aikin ya haifar da bunƙasar harshen Hausa,
musamman idan aka yi la’akari da ayyukan da Turawa suka yi kamar: Hanns Vischer
da G.P.Bargery da R.M. East da R.C. Abraham da sauransu. Wannan takarda ta gano
tushen inda Robinson ya samo fasahar yi wa hamzatattun haruffa ɗigagga, wato daga
aiki Malam Shi’itu Ɗan Abdur-Ra’uf na Birnin Zariya. Bayan shuɗewar Turawan Mulkin
Mallaka, an samu wasu masana daga cikin Hausawa da ma masu sha’awar harshen
Hausa da suka ba da tasu gudummawa ta hanyar ɗorawa daga inda Turawan suka tsaya.
Masanan ne suka daɗa daidaita ƙa’idojin rubutun
Hausar book tare da inganta shi, duk kuwa da irin matsalolin da harshen ya rinƙa fuskanta a hannun
‘yan ƙasa, bayan gushewar Turawan Mulkin Mallaka. A sakamakon
irin yadda aka yi masa riƙon sakainar kashi, ta hanyar hana koyar da Hausa a
makarantun furamare da ke faɗin Arewacin Nijeriya. Akwai buƙatar a ba da himma
wajen binciken tsofaffin ayyukan magabatanmu da ke jibge a wuraren adana kayan
tarihi domin fito da fasahohin magabatanmu.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.