Akwai masu ganin bai kamata a kira Hausawa da suna ƙabila ba, sai dai a ce, su taro ne na ƙabilu daban-daban da suka cuɗanya da juna, kuma suka taru suna magana da harshe ɗaya. Ita kanta kalmar Hausa a wurin Bahaushe tana nufin harshe. Saboda akan ji y ace: “ ban ji wannan Hausar ba”. Wato bai gane wannan yare ke nan. Ko kuma ya ce: “ ya ji wata Hausa”. Wato ya ji ana magana da wani harshe, ko gwalangwanto.
Ginuwar Ƙagaggun Labaran
Kallon Da Bahaushe ke Yi Wa Wasu Ƙabilu
Dr.
Adamu rabi’u bakura
08064893336
1.0 Tsakure
Ana iya kallon kalmar Hausa a
matsayin suna na harshe, kuma masu wannan harshe su ake kira Hausawa. Su
al’ummar Hausawa ba su ɗauki kansu ƙabila ba, don kuwa a
gurin su duk wanda ba Bahaushe ba ne, shi suke kira ƙabila, ko kuma
bagware, tamkar yadda Larabawa suka ɗauki duk wanda ba Balarabe ba a matsayin
Ba’ajame (Baubawa). Masana da dama sun bayyana Ƙabila da cewa: “
Al’umma ce mai asali ɗaya da yare ɗaya da kamannu (ƙirar jiki) kusan ɗaya da al’adun
gargajiya iri ɗaya da ra’ayin zaman
duniya (falsafa) ɗaya, da sauran
irinsu. Kuma lallai ne cikin wannan al’umma kowa yana da’awar shi ɗan ƙabilar ne (Adamu,
19787) da (Adamu, 1997) da (Aamu,2011) da (Kwakwachi,2010).
Akwai masu ganin bai kamata a kira
Hausawa da suna ƙabila ba, sai dai a ce, su taro ne na ƙabilu daban-daban da
suka cuɗanya da juna, kuma
suka taru suna magana da harshe ɗaya. Ita kanta kalmar Hausa a wurin Bahaushe
tana nufin harshe. Saboda akan ji y ace: “ ban ji wannan Hausar ba”. Wato bai
gane wannan yare ke nan. Ko kuma ya ce: “ ya ji wata Hausa”. Wato ya ji ana
magana da wani harshe, ko gwalangwanto.
Sau da yawa akan sami ɗan haifaffen ƙasar Hausa, a tambaye
shi ƙabilarsa, zai ce shi Bafillace ne ko Babarbare ko Banufe,
amma bai san ko zo-in-kashe ka ba. Haka ana samun wasu jisin mutane zaune tare
da wasu ƙabilun da ba sa jin Hausa, waɗanda harshen ƙabilun ya yi tasiri
gare su, bas a jin Hausa, amma duk da haka suna da’awr su Hausawa ne. Misali, Abakwa Riga na Wukari
da Takum na Lafiya. Wannan kan faru ne a sakamakon cuɗanya da auratayya.
Wannan maƙala ta ƙuduri aniyar gabatar
da ƙwarya-ƙwaryar bayanai game
da yadda Bahaushe ya ƙaga labaran raha game da wasu ƙabilu da zama tare ya
haɗa shi da su. Ya gina
labarin ne a sakamakon fahimtar wasu daga cikin halayen ƙabilun. Sai dai muƙalar za ta taƙaita ne kawai a kan
al’ummomi kamar Fulani, Buzaye, Nupawa, Yarbawa da Inyamurai tare da bayar da
haske game da sanadin haɗuwar Hausawa da su.
2.0 Gabatarwa:
Mafi yawan Hausawa musulmi ne, waɗanda yawancin
al’adunsu sun dogara ne a kan yadda Musulunci ya yi tanadi. Sai dai ɗan abin da ba a rasa
na daga al’adun gargajiya, musammman ta haujen Maguzawa. Ta fuskar mu’amala da
iyaye ko dangi ko abokai ko shugabanni ko maƙwabta ko wanin waɗannan, yawanci ana
gudanar da su ne kamar yadda addini ya tanada.
A sakamakon irin tasirin da addinin
Musulunci ya yi a rayuwar Bahaushe Musulmi, shi ya wanzar da zaman lumana a
tsakaninsa da sauran jinsin ƙabilu da zaman tare ya haɗa su. Sakamakon
wannan zama ne, har Bahaushe ya sami damar fahimtar halayen ƙabilun, musamman na
wauta, son abin duniya, rowa, ƙazanta da sauransu. Fahimtar irin waɗannan halayyar mutane
shi ya bayar da damar samar da labarai da suka dace da halayen ƙabilun, ya riƙa bayarwa da niyyar
tsokana don a yi dariya.
3.0 Haɗuwar Hausawa Da
Fulani :
Fulani, mutanen Fula ne, suna zaune
a ƙas
ashe kamar Mali daSenegal. Fulani nau’i biyu ne, Fulanin daji ( Bararoji) da
Fulanin Soro. Fulanin daji su ke kiwon shanu. Suna yawo daga wannan wuri zuwa
wancan domin neman makiyaya da rowan sha saboda dabbobinsu. Su kuwa Fulanin
Soro rukuni - rukuni ne da suka haɗa da: Torankawa da Sulluɓawa da Jahunawa da
sauransu. Ana kyautata zaton sun fara zuwa ƙasar Hausa zamanin
Sarkin Kano Yakubu wanda ya yi mulki a tsakanin shekarar 1452-1463 (Ibrahim,
1970:103). Fulanin daji a koyaushe suna cikin jeji, babban abin da ke haɗa su da Hausawa shi
ne kasuwanci, wato cinikin mai da nono ko shanu da kanwa da gishiri da
sauransu.
Fulanin Soro kuwa suna zaune cikin
garuruwa suna karatu da karantarwa. Daga cikin sun e aka sami Malam Musa
Jakollo kakan Shehu Usman Ɗanfodiyo wanda ya zauna a Birnin Ƙonni da ke cikin ƙasar Gobir a wancan
zamani (Ibrahim,1970) da (T/ Mafara,1999) da ( Wazirin Sakkwato). An sami
muhimmiyar alaƙa tsakanin Hausawa da Fulani bayan kammala jahadin Shehu
Usman Ɗanfodiyo, wanda ya yi sanadin mayar da ragamar mulkin ƙasar Hausa a hannun
Fulani har zuwa farkon ƙarni na ishirin lokacin da Turawa suka ƙwace mulki daga
hannun Fulani. Irin wannan zama na masu riƙe da mulki da waɗanda aka ƙwace wa mulki, ya
wanzar da kusanta ta ƙud-da-ƙud da hulɗa tsakanin Bahaushe
da Bafillatani da ta haifar da raini a tsakaninsu. Kuma ita ta ba Bahaushe
damar fahimtar halayen Bafillatani musamman wajen wauta da rashi wayewar kansa,
har ma yake ganin Bafillatani a matsayin sakarai maras wayon zaman duniya. A
kan haka ne Bahaushe ya gina labarai don ya nuna wautar bafillatani kamar haka:
3.1 Ƙagaggen Labari Game
Da Fulani
“ Wai wani Bafillatani ne, rowan sama ya
dake shi, ga sanyi, ga dare.
Sai ya zo ya sami mafaka. Ya tarar
an hura wuta, ana gasa gyaɗa. Da
Gyaɗa ta gasu, aka ba Ɗanfulani ya ci sai y
ace, “Mhm”! Aka ce, “yaya
dai Ɗanfulani?” Sai ya ce
“ Ai mu oya, wallahi ko lahira wuta muka zaɓa
da kwandon gyaɗa”.
4.0 Haɗuwar Hausawa Da
Buzaye
Azbinawa suna zaune tare da Bugaje
(Buzaye) a bakin saharar yashi arewa da ƙasar Hausa. Buzaye
kuwa asalinsu bayin azbinawa ne (Ibrahim, 1970). Dukkansu suna Magana da harshe
ɗaya ne, suna da
al’ada iri ɗaya. Suna ado da baƙaƙen tufafi ba ka raba
su da naɗa rawani a kowane
lokaci
Azbinawa da Buzaye sun fara cuɗanya da Hausawa tun
kusan lokacin da aka kafa ƙas ashen Hausa bakwai. An ce shekarar
da su Bagauda suka sara Kano tare da manya-manyan gonaki, kasancewar wurin sabo
ga kuma taki mai yawa, sai Allah ya ba su amfanin gona mai yawa. Da shekara ta
zagayo sai aka yi yunwa mai tsanani wadda ta shafi kusan dukkan sassan ƙasashen Hausa har ma
da ƙasar
Azbin. Wannan yunwa ta haifar da kwararar mutane zuwa Kano, don su sami abinci.
Cikin mutanen da suka yi ƙaura zuwa Kano har da Azbinawa da Buzaye (Ibrahim, 1970).
Da aka sami ƙoshi da yalwar abinci
a ko’ina, sai yawancin al’ummomin da suka zo Kano, suka koma ƙasashensu, amma su
Buzaye sai suka ƙI bin Azbinawa suka yi zaman su a Kura ta ƙasar Kano (Ibrahim,
1970). Kasancewar Buzaye gwanin ƙira da rinin baƙaƙen tufafi, sai suka duƙufa ga sana’arsu.
Wannan ya ‘yan’uwansu suka rinƙa zuwa Kano suna sayen baƙaƙen tufafi, ta haka
ciniki ya yi yauƙi har Hausawa suka tsunduma cikin safarar, suna kai hajar
baƙaƙen tufafi ƙasar Azbin.
Babbar hanyar nan ta ciniki ta da,
wadda ta tashi daga bakin kogin Bahar Rum ta ratsa ta hamadar yashi ta zarce
zuwa ƙas ashen Hausa, ta ƙara kawo cuɗanyar Hausawa da
Buzaye, domin hanyar ta ratsa garin Azbinawa. An yi amfani da ita wajen
fataucin bayi da wasu kayayyakin ƙasar Turai zuwa ƙasar Hausa. An ci
gaba da amfani da hanyar har bayan zuwan Turawa, musamman daga kudanci sahara
zuwa ƙas ashen Hausa, wajen cinikin gishirin mangul da manda da
kanwa da dabbobi. Buzaye su ne madugun wannan tafiya. Idan sun sayar da kayansu
sai su sayi baƙaƙen tufafi da goro su tafi da su ƙasarsu (1970).
Sakamakon wannan daɗaɗɗiyar mu’amala
tsakanin Hausawa da Azbinawa da Buzaye ta ba Bahaushe sararin fahimtar ɗabi’ar Buzu ta
tsananin son kuɗI, don haka ne
matansu kan tafi suna bin mutane suna cewa: “ Muna bara muna kitso muna
karuwa”. Wato a nan ida n sadaka ta samu ko kitso suna so, in
kuma akwai mai buƙatar su a shirye suke. Ta la’akari da wannan ne ya sa
Bahaushe ya tsara labari don ya nuna irin yadda yake kallon Buzu.
4.1 Ƙagaggen Labari Game
Da Buzu
“Wai wani Buzu ne cikinsa na ciwo,
shi kuma yana sayar da kanwa, sai aka
Ce, a nemo kanwa a jiƙa masa, sai ya ce a
je cikin kindinsa a saka sisin kwabo
a ɗauko kanwar a jiƙamasa”.
Ba nan kaɗai ta tsaya ba, domin
Bahaushe na kallon Buzaye a matsayin mutane marasa hankali, ga su da tsananin
wauta.
5.0 Haɗuwar Nupawa Da
Hausawa
Ƙasar Nupe tana gefen
Kogin Kwara da ke kan hanyar da Hausawa kan bi wajen zuwa fataucin goro a ƙasar Yarbawa. Hasali
ma an sami mu’amalar cinikayya a tsakanin Nupawa da Hausawa. Hausawa kan sawo
irin manyan rigunan nan da Nupawa ke ɗinkawa masu aiki da ake kira girken Nupe da
kwakwata waɗanda suke da farin
jinni a wajen Hausawa, musamman attajirai da sarakuna, ga kuma kayan ƙarau da manja da suke
samarwa. Irin waɗannan sana’o’i da
Nupawa suka ƙware, sun wanzar da kyakkyawar mu’amala a tsakanin su da
Hausawa (Tukur,1978), tun kafin zuwan Turawa.
Sakamakon jahadin Shehu, wani
muhimmin ne wajen ƙara kawo cuɗanyar Hausawa da Nupawa. Shi ne ma sanadin
zamansu a ƙarƙashin daula ɗaya, domin mafi yawan su musulmi ne( 1978).
Sakamakon wannan cuɗayyar har an sami ƙulluwar auratayya a
tsakanin Nupawa da Hausawa. A daidai shekarar 1807-1833 Sarkin Katsina Ummarun
Dallaje ya auri Banupiya wadda ta haifa masa ‘ya’ya kamar yadda (Tukur,
1991) ya nuna. Ana kyautata zaton irin
wannan dangantaka ta ɗan namiji da ɗan mace ita ta wanzar
da samuwar labaran raha a tsakanin Hausawa da Nupawa. Misali Bahaushe ya yi
nazari ya gane cewa, Banupe mutun ne mai maƙo, sai ya samara da
labarin dakon Banufiya.
5.1 Ƙagaggen Labari Game
Da Nupawa
“Wai Banufiya ce ta ɗora wa ɗandako kaya mai nauyi
ya kai mata gida. Ya
Kai kayan da ƙyar. Da aka sauke,
sai t ace da shi ya shiga rumfarta. A cikin
Rumfar ya shiga ɗaki. A cikin ɗakin (uwar ɗakan) ya duba ƙarƙashin gado
Akwai tukunya. Cikin tukunyar akwai
gwangwani, a cikinsa akwai ƙunshi
Leda ya ɗauko ya duba zai
tarar da ƙullin tsumma, ya kwance zai ga kwabo,
ya ɗauki ɗari ladan dakonsa”.
Ganin wannan wahalar
da zai sake sha wajen neman ladan dakon, sai ɗandakon ya ce ya yafe. Idan muka dubi
wannan labari za a fahimci an gina shi ne a kan fahimtar da ke akwai ta
mutsiltsila da tsananin matsolancin Banufe.
6.0 Haɗuwar Hausawa Da
Yarbawa
Ƙasar Yarbawa tana
kudu maso yamma da Kogin Kwara. Cinikin goro shi ne farkon abin day a haifar da
cuɗanya tsakanin Hausawa
da Yarbawa. Hausawa al’umma ce mai sha’awar cin goro, matansu kuma suna cin
hannun ruwa (goro mai yauƙi), wanda ba a samun su sai a ƙasar Yarbawa. Wannan
ne ya sa Hausawa tafiya ƙasar Yarbawa domin fataucin goro a ƙasa da kuma jakuna. Sun kira waɗannan ƙasashe da suna
“Gonja”. Wannan suna bai keɓanta a kan ƙas ashen Yarbawa ba,
har ya haɗa da ƙas ashen Ghana, domin
suna tafiya can wajen safarar goro.
Jahadin Shehu ya ƙara kawo cuɗanyatsakanin Hausawa
da Yarbawa. Shi ne sanadin zaman ƙasar Ilori da wasu
sassan ƙas ashen Yarbawa a ƙarƙashin daula ɗaya tare da
Hausawa(Ibrahim,1970). Irin wannan zaman tare ya ci gaba da wanzuwa har zuwa
kafuwar mulkin mallakar Turawan Ingila. Kafa mulkin mallaka ya ƙara haɗe ƙas ashen Yarbawa suka
kasance a ƙarƙashin ƙasa ɗaya da suna Nijeriya, wanda hakan ya ƙara haɓaka mu’amala tsakanin
Hausawa da Yarbawa. Irin wannan shaƙuwa ta tsawon lokaci
ta ba Bahaushe dama fahimtar halaye da ɗabi’un Yarbawa. Shi ya sa Bahaushe ke kallon
Bayarbe da wasu halaye da suka danganci tsattsauran ra’ayi da tsumulmula game
da kuɗI ko dukiya. Wannan
ya ba Bahaushe tsara labari domin ya shammaci Bayarbe a kan halayensa da ya
sani game da dukiya.
6.1 Ƙagaggen Labari Game
Da Bayarbe
“ Wai wani Bayarbe ne mai suna Baba
Alabi, ya yi adashi tare da Hausawa.
Sai Bahaushe ya karɓi kwasar farko. Ana
cikin haka sai kwasa ta zo ga Baba
Alabi. Da ya zo karɓar kuɗinsa, sai ya taras da
wanda ya ɗauki kwasar farko
ya mutu. Kowa ya ba shi zubi saura
na mamaci, sai aka gaya masa cewa, ya
mutu. Daga nan Baba Alabi, ya ce
kai! Wannan “ Filan ni”. Wai a nan yana
nufin bai tashi mutuwa ba sai da ya
karɓI kuɗin mutane? Don haka
shi bai yarda
ba.”
7.0 Haɗuwar Ibo ( Inyamuri)
da Bahaushe
Zuwan Turawan Mulkin Mallaka da
tabbatar kafuwar mulkinsu na ɗaya daga cikin sanadin cuɗayyar Hausawa da Ibo. Haka samuwar
hanyoyin sufuri kamar titunan matoci da layukan jirgin ƙasa da ta taso daga
Legas ta zarce zuwa Kano mai tsawon mil 704 wadda aka kammala a shekarar 1911.
Ita ma hanyar jirgin ƙasa da ta taso daga Port Harcourt zuwa Kano mai tsawon
mil 600 da aka sami kammalawa a 1926 ta taka muhimmiyar rawa wajen zama
sinadarin haɗuwar Bahaushe da Ibo
(Crowder, 1968). Hasali ma hanyoyin sun haɗa babbar cibiyar kasuwancin ƙasar Hausa da sauran
sassan manyan garuruwan da ke cikin Nijeriya. Irin waɗannan hanyoyi sun
taimaka matuƙa wajen cuɗayyar Hausawa da wasu ƙabilu, musamman ƙabilar Ibo da suka
taso daga garuruwa kamar Legas da Enugu da Ibadan suka zauna a wurare kamar
Kano da Zariya da Jos da Gusau da Sakkwato domin neman riba ta hanyar kasuwanci
(Osaghae, 1994). Ta wannan mu’amala ce Bahaushe ya fahimci cewa, baa bin da ya
fi ƙyama
a rayuwarsa irin kuturu, sai ya ƙirƙiro labarin hammer
Inyamiri.
7.1 Ƙagaggen Labari Game
Da Inyamiri
“ Wai wani inyamiri ne yana tsaye
bai san cewa, wani kuturu mai zubar
mugunya na tsaye a bayansa ba. Sai
Inyamiri ya yi hamma ba tare da ya
sa hannu ya rufe bakinsa ba. Ganin
haka sai kuturu ya cusa dugun hannunsa
a bakin Inyamiri, y ace, “shege,
kafiri, ba salati ba rufe baki”. Sai Inyamiri
ya rufe baki da dungun kuturu. Ba a
Ankara ba sai Inyamiri ya faɗI somamme,
aka yayyafa masa ruwa”.
8.0 Kammalawa:
Allah Ya yi wa ɗan Adam baiwa da
basiri da tunani ta yadda zai iya ƙwanƙwance abubuwa ta
kowace fuska ya same su. Wanna ne ya ba shi damar bayyana ra’ayinsa game da duk
wani abu da yake kusa da shi. Ba Bahaushe ne kaɗai ke da wannan sifa ba. Kowace
al’umma ma akwai yadda take kallon wata al’umma da zaman tare y agama su, da
yadda suka suka fahimci juna, fahimta mai kyau ko maras kyau ko da kuwa iyaye
ne, sai daikunya ko tsoro ko wani abu ya hana a bayyana. A sakamakon haka ne
aka kalato ire-iren labaran da Bahaushe ya ƙaga a kan al’ummomi
daban-daban da suka haɗa da: Fulani da
Buzaye da Nupawa da Yarbawa daga ƙarshe aka cika da
Inyamiri(Ibo). Sai dai idan aka nazarci irin waɗannan labaran barkwanci za tarar akwai
birbishin kishi a mafi yawan su. Wasun su an ƙaga su ne domin a
huce haushe. Misali, barkwancin da ke wanzuwa a tsakanin Bahaushe (kaɗo/ haɓe), an aiwatar da shi
ne a sakamakon haushin da Bahaushe ke ji na zafin Fulani sun ƙwace masa mulkin ƙasarsa ta haihuwa.
Shi ma sai ya samara da irin waɗannan labarai domin ya muzanta Fulani. Haka lamarin zai
kasance idan aka zurfafa bincike a kan labaran da aka gina game da sauran ƙabilu.
MANAZARTA
Tuntuɓi mai takarda
Masha Allah. Na ƙaru matuƙa.
ReplyDelete