Ticker

6/recent/ticker-posts

Addini Da Yaƙar Ta’addanci Da Tabbatar Datsaro: (Duba Cikin Gudummuwar Malaman Ƙasar Zamfara)

 Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na zangon karatu na farko a shekara ta 2020 a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Tarayya ta Gusau, a ƙarƙashin Jagorancin Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza shugaban Sashen, a ɗakin taro na Tsangayar Fasaha.

carbi

Addini Da Yaƙar Ta’addanci Da Tabbatar Datsaro: (Duba Cikin Gudummuwar Malaman Ƙasar Zamfara) 

Dr. Adamu rabi’u bakura

arbakura62@gmail.com

08064893336

Tsakure

Fahimtar abubuwan da suka shuɗe ta kowace fuskar fannonin rayuwar ɗan Adam abu ne mai matuƙar amfani ga ita kanta rayuwar. Wannan ne ya sa masana tarihi ke iƙirarin cewa cewa duk wanda bai san abin da ya wanzu (faru) kafin haifuwarsa ba, zai kasance tamkar jinjiri har abada, domin zai zamanto da ilimin abin da ya sani ko ya gani, ba tare da fahimtar musabbabin wanzuwar abin ba. Shi tarihi yakan ɗauki fuskoki mabambanta, kamar na ƙasa ko al’umma ko addini ko managartan shugabanni ko adabi da sauran dangogin lamarin ilimin rayuwar zaman duniya. A waɗannan fannoni tarihi yana  amfani wajen ilmantar da al’umma nau’in cikin da jiya ta ƙunsa, domin ba da damar sanin abin da yau za ta haifa da kuma irin daraja ko ƙaskanci abin da aka haifa ɗin zai samu a cikin rayuwa. Ganin cewa a farfajiyar ƙasar Hausa an yi wa tarihi riƙon sakainar kashi, alhali kuwa ta hanyarsa ne za a iya tsinkayo abubuwan da suka faru a baya don ƙoƙarin daidaita muhimman abubuwan da ake fuskanta, ta yadda za a ci moriyar managarciyar rayuwa mai ma’ana. Wannan ne ya sa wannan maƙala ta ƙuduri aniyar komawa cikin tarihi don zaƙulo irin rawar da malamai magabata suka taka wajen samar da tabbatuwar tsaro da bunƙasar garuruwan farfajiyar ƙasar Hausa, da musabbabin ƙulluwar dangantakar malamai da sarakuna da sanadiyyar bayyanar tashin hankali a far fajiyar daular Zamfara. Takardar za ta bayar da haske game tushen taɓarɓareawar zaman lafiya a Najeriya ta Arewa da yadda lamarin ya haɓaka har zuwa yau. Ƙarshe za a kawo tashi faɗin da malaman addinin Musulunci ke yi don ganin an samu zaman lumana.

1.0 Gabatarwa

            Babu wani abu da zai inganta a farfajiyar wannan duniya ta mu, dole sai tare da muhimman abubuwa guda uku. Irin waɗannan abubuwa kuwa sun haɗa da, ilimi, hanyar samun isassshen abinci da kuma hanyar tsaron zaman duniyarmu. Saboda kowane abu da ke cikin wannan duniya, in har ya kasance babu tsaro yana da abin da zai iya lalata shi ya ɗaiɗaita shi. Don haka ashe ke nan ya zama wajibi kuma haƙƙinmu mu tashi tsaye mu yi namijin ƙoƙari da ƙwazo fiya da na magabatanmu, domin zamani ya juya. Dole ne mu bi hanyar zamani mu tsare kanmu ga kowane irin al’amarin da ba zai kawo alheri da zaman ƙasashenmu cikin kwanciyar hankali da lumana ba. Kuma mu sani cewa a waɗannan rukunnan yankuna na ƙasar Hausa, an yi mazaje masu dabarun tsare ƙasashensu, da kishin ƙasarsu tare da biyayya ga shugabanni domin samun cikakken tsaron da zai wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Da ba don su ba, da yanzu ƙilan mun kasance a yankin nahiyar ƙasashen Amurka ko Saliyo a sakamakon harin kamen bayi da ya raba uba da ‘ya’yansa ko mata da mijinta. Irin wannan ɗanyen aikin da ya auku a wannan nahiyar, ya ƙasura ne a sakamakon irin alfanun da ƙasashen Turai suka dinga samu a wanncan zamanin.

Tubalan Ma’anonin Taken Ginin Maƙalar

1.1 Addini

            Ita ma asalinta balarabiyar kalma ce. Tana cikin jerin kalmomin suna jinsin namiji. Kalmar na ɗauke ma’anar: Hanyar bauta wa Ubangiji (BUK, 2006:3). Shi kuwa Garba (1990:3) cewa ya yi: Bangaskiyar kasancewar ikon da ya fi na duniya. A ma’anarsa ta biyu kuwa ya fassara kalmar ne da cewa: Hanyar ibada.

1.2 Yaƙa

            Kalmar yaƙi  na nufin kai wa abokan gaba faɗa. A wata ma’anar an fassara ta da cewa: Yin  hidimomi na kauce wa abin da ba shi da kyau, kamar yadda Abubakar (2015:494) ya bayyana. Su kuwa BUK (2006:477) sun fassara ta ne da cewa: Far wa wasu da yaƙi.

A wannan fagen kalmar na ɗauke da ma’anar irin ayyukan kai da kawon da malamai suka gudanar a ƙoƙarinsu na ganin al’ummar wannan jahar sun sami dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali. Sun aiwatar da wannan aikin ne ta hanyar amfani da nassin Alƙur’ani da Hadisan Annabi S.A.W. da Ijma’in Malamai. Waɗannan abubuwan su ne suka kasance makamansu na yaƙin.

1.3 Ta’addanci

            Ta’adda, kalma ce da ke cikin jerin suna na mace, jam’i kuwa “ta’addodi ko ta’addoji. Kalmar na kunshe da ma’anar: “ Mugun aiki musamman na haddasa ɓarna”. Yayin da aka yi wa kalmar ɗafa-goshin Ɗan-, sai bayar da Ɗan ta’adda, wato mutum mai aikata ɓarba kamar lalata abubuwa ko kisa da sauransu don bambancin ra’ayin siyasa ko addini. Kalmar ta’addanci kuwa tana daidai da kalmar “ta’adi”. Ita kuwa kalmar “ta’adi” tana nufin ɓarna ta ganganci ko cuta ko lalata, kamar yadda BUK (2006:416) ya nuna. Shi kuwa Abubakar (2015:449) ya nuna cewa kalmar “ta’adi” na cikin jerin suna jinsin namiji, jim’I kuwa “ta’adda”. Kalmar na ɗauke da ma’anar “ Yin ɓarba”. Lalata abu da sani. A ma’anarsa ta biyu kuwa cewa ya yi: Ji wa wani ciwo a faɗa ko wajen aikata laifi.

            Ke nan ta’addanci shi ne, duk wani nau’in aikin tashin hankali da ɗan Adam zai aiwatar don biyan wasu muradun kansa ko iyayen gidansa ta hanyar zubar da jinainan al’umma ko lalata dukiyoyinsu ko cin irlinsu.

1.4 Tabbata

            Kalmar tabbata tana cikin jerin kalmomin aikatau. Tana ƙunshe da ma’anar kasancewa. A wata ma’anar kuwa an bayyana ta da Halin dindindin babu ƙarewar lokaci (Abubakar, 2015:449).

            Yayin da (BUK, 2006:417) ya fassara ta da cewa, kasancewa cikin rashin shakka a kan wani abu.

            Daga waɗannan ma’anonin ana iya cewa kalmar tabbata na nufin samar da wani yanayi na dindindin, wato mai ɗorewa ba tare da yankewa ba, ballantana a yi zullumin aukuwar wani abu.

1.5 Tsaro

            Tsaro kalma ce da ke cikin jerin suna jinsin namiji. Kalmar na ƙunshe da ma’anar kare jama’a daga abin da zai cuce su. Wato ba da cikakkiyar kariya ga mutane ko gari ko ƙasa da dukiya da rayuka baki ɗaya.

1.6 Gudummawa

            Gudummawa kalma ce bahaushiya da ke cikin jerin sunaye jinsin mata. Ana faɗar ta da “gudunmawa” a karin harshen Sakkwatanci da na Kananci da kuma Zazzaganci, kuma akan furta ta da lafazin “gudunmuwa” a karin harshen Kananci, kamar yadda Bargery (1993:402) ya nuna. Shi kuwa Abraham (1975:337) ya nuna cewa a karin harshen Sakkwatanci ne ake faɗar ta da lafazin “gudunmowa”, wato akan sa wasalin “o” a gaɓa ta uku maimakon wasalin “u” da wasu karin harsuna ke amfani da shi. Har ila yau Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero (2006:171) ya nuna ana furta gaɓa ta uku da wasalin “a” ko “o” misali gu-dum-ma-wa. Kalmar gudummawa tana ɗauke da ma’anar taimako na aiki ko kuɗi ko abinci ko sutura ko wani abu. Kuma daidai take da agaji ko ceto daga wahala kamar yadda Garba (1990:4) ya bayyana.

1.7 Malamai

            Kalmar malamai jam’i ce ta kalmar malami. Ita kuwa kalmar malami asalinta Balarabiyar kalma ce da aka samo daga kalmar Larabci wadda Larabawa ke kira MU’ALLIM da ke ɗauke da ma’anar malamin makaranta. Wato mai koyar da karatu da rubutu. Hausawa sun sake tsarin ginin kalmar ta dawo malami don ta dace da tsarin ginin kalmomin Hausa. Kalmar malami tana cikin jerin kalmomin suna jinsin namiji, jam’i kuwa malamai ko malumma a karin harshen Katsinanci, kamar yadda (Abraham, 1975: 650) da (BUK,2006: 328) suka nuna.

            Abubakar (2015:357) kuwa ya fassara ta da cewa, mutumin da ya koyi ilimin addinin Musulunci kuma ya sani sosai. A wata ma’anarsa da ya bayyana, kalmar na nufin: Dattijon mutum da ake ganin girmansa. A wata ma’anar kuwa cewa ya yi, kirari ne na ban girma ga wanda yake masani. Ya kuma nuna cewa kalmar na iya kasancewa, kirarin mutum da mutuncin iliminsa ko kyakkyawan halinsa. Daga ƙarshe ya fassara ta da cewa, maikoyarwa a makaranta.

            Ta waɗannan ma’anoni da masana suka bayar tare da la’akari da ma’anar luga za a iya cewa kalmar malamai  a nan tana nufin masana fannonin ilimin addinin Musulunci da suka duƙufa waje koyar da shi a tsakanin al’umma, kamar yadda wannan maƙala ta karkata. Amma a tsakanin al’ummar Hausawa da ma waɗanda suka shaƙu da su, kalmar na zaman laƙabi da nuna mutuntawa ga baƙo ko ɗan gari, wanda aka san sunansa ko wanda ba a san sunansa ba, malami ne ko kuma jahili. Ana laƙaba wa mutum kalmar malam ne don ana jin kunya ko nauyin faɗar sunansa gaya ba tare da an sakaya ba.

1.8 Ƙasa

            Ƙasa kalmar Hausa ce da ke cikin jerin suna jinsin mace, jam’i kuwa, ƙasashe ko ƙassai. Kalmar na ɗauke da ma’anar: “Wani yankin duniya wanda hukuma guda ke mulki”, kamar yadda BUK (2006: 278) ya bayyana. Shi kuwa Abubakar (2015:303) ya fassara kalmar da cewa: “Muhallin zaman jama’a a inda dagaci ko hakimi ko sarki ko mai mulkin siyasa yake shugabancin mazauna wurin”. A ma’anarsa ta biyu cewa ya yi: “Filin wuri da mutum ko iyali suka mallaka kuma ba wanda zai iya amfani da shi in har babu yarda ko amincewar mai shi ko masu shi”. Shi Garba (1990:96) ya fassara ta da cewa: “Sashen duniya wadda muke takawa da gini a kai”. A wata ma’anar kuma ya ce: “Yankin Mulki”.

            Ƙasa a nan tana nufin farfajiyar filin doron duniya da ɗan Adam ke iya rayuwa a cikinsa tare da gudanar da lamurransa ya yau da kullun.

1.9 Zamfara

            Zamfara bahaushiyar kalma ce da ke cikin jerin kalmomi jinsin mace. Kamal na nufin sunan ɗaya daga cikin sunayen jihohin Nijeriya a arewa wadda ta ƙunshi Gusau da Anka da Zurmi da Ƙaurar Namoda, kamar yadda BUK (2006:489) ya nuna. Shi kuma Abubakar (2015:511) cewa ya yi: “Ƙasar sarautar Zamfarawa, wato lardi mai Anka da Mafara da Gummi”. A ma’anarsa ta biyu kuwa ya ce: “Jahar mulki a cikin jihohin Najeriya, watau can kudu da Sakkwato, Arewa da Katsina”.  Idan muka dubi ma’anonin da Ƙamusoshin Hausa suka bayar, za a fahimci cewa, sun yi la’akari ne da harabar hajar tare da duban garuruwan da Zamfarawa ke sarauta, kamar: Anka da Gummi da Talata Mafara. Sai dai ba a ambaci wuraren Zamfarawa na asali ba kamar garin Dutsi da Jata da Kiyawa da tsohuwar Banaga da Zurmi duk daɗaɗɗun garuruwan Zamfara ne.  

2.0 Wanzuwar Tsaro A Tsakanin Al’umma

            Tsaro ya samo tushe ne tun lokacin da ‘yan Adam suka fara kafa mazaunai na dindindin a matsayin tunga da garuruwa har suka samar da shugabanni da za su yi musu jagaranci ta hanyar bayar da umurni da hani tare da hukunta wanda ya fanɗare. Ana cikin haka sai aka wayi gari wasu jinsin mutane na neman mamaye wasu, su handame musu mazauni tare da mayar da su ƙarƙashin ikonsu. Daga lokacin ne maganar tsaro ta soma tusgowa. Sai aka fara zagaye muhallai da ƙayoyi domin kariya daga farmakin ba zata ta haujen abokan hamayya. Yayin da aka samu bunƙasar tungaye suka koma garuruwa sai aka fara gina ganuwa domin samar da cikakken tsaron rayuwa da dukiya da kariyar mutunci tare da ɗorewar zuriya. Tun daga lokaci sai samar da tsaro ya zama wajibi domin shi ne ginshiƙin cigaban kowace al’umma da ke doron duniya. Kuma duk shugaba na gari mai kyakkyawan tunani, sai ya fara mayar da hankalinsa wajen lamarin inganta tsaro. Saboda sai da tsaro ne ake samun cigaba mai ma’ana.

            Tsaro yanayi ne da cikin shirin ko-ta-kwana, tare da samar da cikakkar kariyar al’ummar ƙasa, ba tare da jiran gawon shanu ba har sai bala’i ya far musu, sannan a yi fargar jaji. Yakan kuma kasance yanayin da hankullan al’umma ke kwance, suna cigaba da tafiyar da lamurran harkokinsu na rayuwar yau da kullun cikin kyakkyawan yanayin zamantakewa tare da rashi fargabar aukuwar wani aibu ba.

3.0 Bayyanar Malamai A Farfajiyar Ƙasar Hausa Da Tasirin Addu’a

            Bayan wafatin Manzon Allah S.A.W., sai sahabbansa suka yi azamar sadar da addinin Musulunci ga al’ummomi na kusa da na nesa. Bayan wucewar su, sai malamai suka ɗauki wannan nauyin, saboda su ne magada Annabawa, tamkar yadda Annabi S.A.W. ya bayyana. Sai dai Annabawa ba dukiya suka bari ba, sun bar ilimi ne, tun daga lokacin ne malamai suka duƙufa wajen shiryar da al’umma ga lamarin duniya da lahira.

3.1 Kafuwar Daular Sharifai A Ƙasar Zamfara

 Wani muhimmin abu da ya ƙara haɓaka sha’anin malanta da samuwar malamai ya cigaba da haɓaka sannu a hankali shi ne, samuwar Daular Sharifai a ‘Yandoto wadda ta zama matattara ta gaggan malamai masu ƙoƙari yaɗa ilimin addinin Musulunci, lamarin da ya haifar da yawaitar gogaggun malamai na kowane fannin a wannan nahiya ta jihar Zamfara. Ita wannan daular, Yahaya ɗan Nafsal- Zakiyya ɗan Aliyu Zainul Abidina ɗan Sayyidina Husaini ɗan Sayyidina Aliyu Ibn Abi Talibi daga wajen Nana Faɗima shi ya kafa ta. Sharif Yahaya ya kafa daular ne a ƙarni na takwas Miladiyya. Kuma yana ɗaya daga cikin malaman Imam Malik, wannan ya taimaka wajen ƙaƙa-gidan da Mazhabar Malikiyya ta yi a ƙasashen Hausa, kamar yadda Ibrahim (2009:16) ya nuna. Daular ta gudana har zuwa zamanin Shehu Usman Ɗanfodiyo.

3.2 Zuwan Malamai A Ƙasar Hausa da Tasirin Addu’a

            Tawagar malamai Wangarawa daga Mali ta mutane arba’in sun sami zuwa Kano a zamanin mulkin Sarkin Kano Yaji 1349-1384. Manyan ayarin su haɗa da Abdur-Rahman Zaite da Mandawari da Shehu da Limamin Jujin ‘Yan Loba da kuma Limamin Maɗatai.  Sun gabatar masa da maganar addinin Musulunci, sun ko yi sa’a sarkin ya karɓe su hannu biyu, ya kuma amince ya karɓi Musuluncin. Aka naɗa Mandawari Limamin gari, Zaiti kuwa aka naɗa shi Alƙali, Gurdumus Limamin Sarki, yayin da Lawan ya zama Ladanin Sarki, kamar yadda Ibrahim (2009:38) ya nuna. Sarki Yaji ya yi wa al’ummarsa umurni da yin sallah, aka kuma gina masallaci, kowace ƙabila ta yarda tana salla, sai ƙabilar Gazargawa kaɗai suka ƙi yarda da yin salla. Sai suka rinƙa zuwa masallacin suna shafa najasa. Yayin da lamarinsu ya tsananta, sai aka sa Ɗanbayi da rundunarsa suna gadin masallacin tun daga magariba har zuwa safe; amma mutanen ba su daina sa wa masallacin najasa ba. Malamai suka shawara, suka ga babu maganin abin sai addu’a, suka taru a masallacin suka yi addu’a, Allah kuwa ya karɓi addu’arsu. Shugaban mutanen ya makance, sauran duk wanda ya taɓa zuwa wurin ya sa najasa sai ya makance shi da matarsa (Dokaji, 1978:15) da (Waya,2000:6). Haka a zamanin Sarkin Kano Kukuna, sai sha’anin sarautarsa ya fara rawa, sai ya nemi Limamin ‘Yandoya aka yi masa wani dafa’i aka binne a Zauren Kuka da Zauren Turaki da Turakar Kano domin duk wanda ya sarauci Kano kada a cire shi, komai tsawon lokaci (Dokaji, 1978:26).

A zamanin Sarkin Kano Alwali, ɗansa da ake kira Ɗanmama da ke riƙe da sarautar Ciroman Kano, ya yi hawa tare da baradensa, ya tafi Gwale wajen gonakin Malam Abdullahi Suka, sai dawakansa kakkarya amfanin gonar malamin. Da malamin ya ga abin da Ciroman ya yi masa, sai ya yi addu’a a kan kada Allah ya ba yaron nan gadon sarautar ubansa. Shi ke nan tun daga wancan lokacin duk wanda aka yi wa sarautar Ciroman Kano, ba a taɓa ganin wanda ya sami sarautar Sarkin Kano ba, sai Sarkin Kano Abdullahi Bayero ɗan Abbas abin ya warware, kamar yadda Dokaji (1978:28) ya nuna. Tun daga wannan lokacin ne Kanawa ke riƙe da malamai, kuma ba sa wasa da addu’a a cikin kowane lamari.

            Fahimtar irin tasirin da malaman addinin Musulunci ke da shi a fannonin lamurran duniya da ma na gobe ƙiyama, ya sa sarakuna da jinin sarauta kusantar malamai domin samun damar biyan buƙatunsu na ƙoƙarin samun shiga gidan sarauta ko kuma samun galabar murƙushe abokan adawarsu ko maƙwabtansu ta yadda za su dawo ƙarƙashin ikonsu. Sakamakon irin wannan mu’amala ce aka sami gwarzaye a farfajiyar ƙasar Hausa, kamar irin su Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo da sauransu.

Yawaitar Zuwan Malamai da Bunƙasar Ilimi

            An sami yawaitar shigowar malamai a ƙasar Hausa a mabambantan lokutta wanda hakan ya haifar da haɓakar ilimin addinin Musulunci da yawaitar masana a farfajiyar ƙasar Hausa. Misali a zamanin mulkin Sarkin Kano Yakuba 1452-63 miladiyya, waɗansu Fulani suka shigo ƙasar Hausa suka kawo fannonin ilimi na Tauhidi da na Lugga. A wajen ƙarshen ƙarni na goma sha biyar wasu manyan shaihunnai sun ziyarci ƙasar Hausa. Malaman sun haɗa da Malam Abdur Rahman Al-magili da Abdur Rahman Al-SuyuɗI; sun je har Kano a lokacin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa 1463-99 miladiyya da kuma Sarkin Katsina Ibrahim Maje 1494-1520 miladiyya. Waɗannan malamai sun kafa makarantu sun koyar a garuruwan Kano da Katsina, sun kuma kawo littattafai na koyon addinin Musulunci; bugu da ƙari sun taimaka wa sarakuna wajen tafiyar da mulki bisa ƙa’idar shari’ar Musulunci, kamar yadda Dokaji (1978:24) da Ibrahim (2009:39-40) suka bayyana.

Kuma malamai suka cigaba da zuwa Kano ɗin. Misali, a zamanin Sarkin Kano Kisoki 1509-63 wasu baƙin Shaihunnai suka dinga zuwa Kano suna kawo sababbin littattafai. Waɗannan malaman sun haɗa da:

·         Malam Sheihu Batunashe wanda ya zo da littafin Ashafa

·         Shaihu Abdussalam wanda ya kawo littafin Madauwana Jami’ussagir

·         Usman Sidi Ahmad Shaihin ɗariƙar Ƙadiriyya

·         Malam Mahaluf Ibn Ali Al-Balbali.

Ganin  yadda addinin Musulunci ya fara ƙasaita, sai Sarkin Kano Abubakar Kada 1563-73 ya gina wani soro da ake kiraq Zauren Fagaci a gidansa don koyar da ilimin addinin Musulunci.

Bayan da addinin Musulunci ya zauna da gindinsa sosai a ƙasashen Hausa, sai malaman da suka kawo addinin suka shiga koya wa Hausawa karatu da rubutu na Larabci domin su san yadda za su karanta Alƙur’ani da sauran littattafan koyon addinin Musulunci. Sakamakon koyon karatu da rubutun ne ya wanzar da samuwar shahararrun malamai a ƙasar Hausa ciki kuwa har da ƙasar Zamfara. Irin waɗannan malai sun haɗa da:

·         Malam Abdullahi Suka wanda ya kasance mutun na farko da ya soma fahimtar ciki da wajen littattafan Hadisai Ingantattu guda shida. Ya kuma wallafa ƙasida mai suna: “Adiyyatul-Mudi” mai baiti dubu da ɗari biyar.

·         Malam Ɗammarina wanda ya yi sharhin littafin Ishiriniya ta Alfazazi. Aikin nasa yana ƙunshe da shafi dubu.

·         Malam Ɗammasani wanda ya wallafa littafin  Annafhatul Ambariyya sharhin Ishiriniyya da Buzugus-Shamsiyya sharhin Ishimawi. Kamar yadda Talata Mafara (2004: 2-3) ya nuna.

An kuma samu malamai da dama kamar Malam Haruna da Malam Umar ɗan Muhammad Attarwadi da Malam Jibrila ɗan Umar da Malam Kabara da Shehu Usman Ɗanfodiyo da Malam Abdullahi Gwandu da Malam Shi’itu ɗan Abdur-Ra’uf da Malam Muhammadu Na-Birnin Gwari da sauransu, kamar yadda Dokaji (1978: 22) da Galadanci (1982:87) da T/Mafar (2004:2-6) da Ibrahim (2009:26-39) suka zo da bayanin.

            Wani muhimmin lamari game da malamai da bunƙasar addinin musulunci wanda tarihi ba zai bari a manta da shi ba, shi zuwan Shehu Magili Kano, wadda ta kasance tamkar sharar fage ga dubban Larabawa da suka riƙa zuwa Kano don harkar kasuwanci da sha’anin malanta (Dokaji, 1978:23). A lokacin Almagili da shugaban Wangarawa suka haɗu da Sarki Rumfa aka roshe wajen bautar tsafi a Kano, aka kuma gina masallacin Juma’a sannan kuma aka kafa makarantar Islamiyya a Kano, tare da sa malamai su riƙa koyar da addinin Musulunci, kamar yadda Waya (2000:13) ta bayyana.

4.0 Rabe-Raben Malamai A Ƙasar Hausa

            Dazarar an ce malami a ƙasar Hausa, ba abin da zai faɗowa mutum a rai sai, wanda ya kasance masanin Alƙur’ani mai tsalki, da ilimin furu’a, da shari’ar Musulunci,  da balaga da sauransu, kuma yake karantar da shi ilimin na addinin Musuluncin. Sauyawar zamani da gurɓacewar zukatan al’umma da nau’o’in burece-buracensu ya haifar da samuwar rukunonin malamai a farfajiyar ƙasar Hausa kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya.

4.1 Malaman Sunna

            Su ne waɗanda ke da ilimin addinin Musulunci gwargwado, kuma sun duƙufa wajen yaɗa shi ba dare ba rana a tsakanin al’umma, ba tare da neman lada daga kowa ba sai daga wajen Allah. Suna da taƙawa da natsuwa da tsantseni da gudun abin duniya. Ba sa zuwa gidan kowa don neman wani abin hannun mutane. Hasali ma ba sa tsoron faɗar gaskiya game da komai da kowa. Ba su damu da fushin mai fushi ba a fagen bayyanar da gaskiya.

4.2 Malaman Bidi’a

            Wannan rukuni, suna da ilimin addinin Musulunci tare kuma da karantar da shi ga al’umma. Sai dai suna da  kwaɗayin abin da ke hannayen jama’a tare da tsananin son tara abin a cikin zukatansu. Hasali ma sun fi kowa iya tawilin abin da zai wanzar da biyan buƙatun zukatansu da na irin waɗanda suke kwaɗayin samun wani romon duniya daga haujinsu. Nau’in waɗannan malamai sun fi siffantuwa da tsananin son yin zari da ƙage da kinibibi iri-iri da yaudara da rashin amana, duk mai mulki nasu ne.

4.3 Malaman Tsibbu

            Wannan rukunin malamai, sun fi mayar da hankullansu wajen bayar da magani da rubutun sha ko duba (bugun ƙasa) domin bayyana wa masu hulɗa da su, alheri ko cutar da za ta same su. Sukan aikata naƙulƙula ta hanyar surkulle da amfani da wasu ayoyin Alƙur’ani domin cutarwa zuwa ga wasu. Wasu daga cikinsu ba su yi zurfi a fagen ilimi, ammfa sun koyi hisabi wanda ya ba su damar iya duba.

5.0 Darajojin Malamai A Ƙasar Hausa

            A ƙasar Hausa, malamai suna suka tara, domin sun bambanta dangane da bambanci iliminsu da muƙaminsu da fannin da suke koyarwa da nau’in ɗalibansu, kamar yadda za a gani daki-daki.

5.1 Shehun Malami

            Shi ne malamin da ya ƙware tare da shahara a fagen fannonin ilimin addinin Musulunci, har ma wasu malamai na kusa da na nesa na zuwa wajensa domin ɗaukar karatu. Wanda ya kai wannan mataki za a tarar gogagge ne a fagen rayuwar duniya. Wato ya sha ruwa, yawan shekarunsa na rayuwar duniya da ɗinbin iliminsa kan taimaka wajen ɗora ɗalibansa a turba madaidaiciya.

            Yayin da mutum ya mallaki ilimi mai zurfi, ya kasance yana aiki da shi tare da tsananin tsoron Allah har cikin zuci ga natsuwa da gudun duniya da lizimtuwa ga ibada, har yakan iya nuna abin mamakin da ba kowane Musulmi zai iya yin sa ba. In mutum ya kai wannan matsayi ke nan an yaye masa kashfi. Sakamakon haka ne akan ce wane waliyyi ne.

5.2 Malaman Zaure

            Su ne waɗanda ke karantar da manyan littattafan ilimin addinin Musulunci. Wato su ne manyan ɗalibai ke ɗaukar karatu wurinsu, kimanin ɗaliban kulliyya a tsari karatun zamani. Duk da haka, za a tarar cewa, a wani sashen makarantar ana koyar da karatun allo a ƙarƙashin kulawar wani daga cikin ‘ya’yan malamin ko wani daga cikin almajiransa na kusa.

5.3 Malaman Allo

            Su ne waɗanda ke karantar da al’umma karatun allo. Mafi yawan lokutta, su kansu malaman allo sukan kasance almajirai ne na wani malami. Sau da yawa bayan an tashi makaranta, sukan ɗauki littattafansu su tafi wajen malaminsu su ɗauki karatu.

5.4 Alaramma

            Wannan wani rukunin malamai ne na mahaddatan Alƙur’ani mai tsalki. Suna rubuta Alƙur’ani da ka ba tare da sun duba ba. sun san tsarin surorin Alƙur’ani daki-daki, da zarar ka furta wata aya, za su iya bayyana maka surar da take.

5.5 Malaman Gafaka

            Su ne malaman da ke yawo da almajiransu daga wannan gari zuwa wancan. Irin waɗannan malamai sun dogara ne ga sadakar da ake ba su tare da hidimar da almajiransu ke yi musu.

6.0 Ayyukan Malamai A Ƙasar Hausa

            Tun farkon fara bayyanar malamai a farfajiyar ƙasar Hausa, sun rungumi aikin nan da suka gada daga Annabi S.A.W. kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya.

6.1 Karantarwa

            Muhimmin aikin da malamai suka sa a gaba shi ne yaɗa addinin Musulunci tare da koyar da dokokinsa. A ƙasar Hausa, malamai ne ke koyar da al’umma karatun Alƙur’ani da furu’a da da sauran fannonin abubuwan da suka danganci hukunce-hukuncen shara’ar Musulunci. Su ke shiryar da al’umma zuwa ga tafarkin Ubangiji, da yadda ake kaɗaita Allah da koyar da hanyoyin gudanar da kyakkywar mu’amala da ke wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Su ke bayyana yadda ake gudanar da ayyukan ibada kamar: Tsarki da alwala da salla da azumi da zakka da aikin Hajji. Sukan yi albishir da shiga Aljanna ga wanda ya yi kyakkyawan aiki a zamansa na rayuwar duniya, tare da gargaɗi game da azabar wuta mai raɗaɗi ga wanda ya yi mummunan aiki a zamansa na rayuwar duniya.

6.2 Alƙalanci

            Malamai masu taƙawa da tsoron Allah da aka tabbatar da adalcinsu, su akan naɗa a matsayin Alƙalai a farfajiyar ƙasar Hausa. Haka lamarin ya soma tun farkon zuwan Musulunci a ƙasar Hausa, musammam a garuruwan Kano da Katsina da Zazzau a mabambantan lokutta. Bayan bayyanar Shehu Usman Ɗafodiyo da tabbatuwar Daular Usmaniyya, wadda ta haifar da samuwar malamai a matsayin jagororin daular. Samun wannan kyakkyawan yanayi ya sa manyan sarakunan daular suka kasance manyan alƙalan majalisun ɗaukaka ƙara na kowace masarauta. Manyan sarakunan sun yi ƙoƙarin nannaɗa alƙalai a yankuna daban-daban da ke faɗin lardunan masarautarsu. Yayin da mai ƙara bai gamsu da hukuncin alƙalin yankinsu ba, sai ya ɗaukaka ƙararsa zuwa majalisar sarkin yanka na ƙasarsu. Haka lamarin ya cigaba da tafiya har zuwa samun ‘yancin kai. Ta wannan hanya ana iya cewa, malaman wancan ƙarni suka tabbatar da zaman lafiya.

6.3 Limanci

            Kasancewar sarakuna malamai, shi ya ba su damar jagorancin sallar juma’a a garuruwansu. Misali a Kano, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 1, wanda ma idan yana huɗuba ba wuya ya yi kuka, saboda tsoron Allansa da irin tsawatarwar da ta ƙunsa (Sufi, 1993). Sakamakon yawaitar hidimomin al’umma da ke wuyansu, sukan zaɓo wasu malamai da aka tabbatar sun cika sharuɗɗan limanci, su naɗa su domin su waƙilce su.

6.4 Shawara

            Malamai masu basiri da hangen nesa ga kuma tsoron Allah da taka tsantsan da gudun duniya su ne suka kasance mashawarta ga sarakuna. Saboda haka ne ake samun malamai a fadodin sarakunan ƙasar Hausa a matsayin mashawarta ga sarakunan. Wannan ya samo asali ne tun daidai lokacin da addinin Musulunci ya samu karɓuwa a tsakanin sarakunan ƙasar Hausa. Misali Kano a lokacin da Wangarawa suka isa birnin Kano. A Zazzau kuwa iri wannan dangataka ta haifar da wanzuwar gidan sarautar Mallawa da saurasu. A Gobir irin haka ya wanzu tsakanin Shehu Usman Ɗanfodiyo da Bawa Jangwarzo (Tsiga, 1985: 17-19).

7.0 Matsayi Malamai A idanun Al’umma

            Al’ummar ƙasar Hausa sun ba malamai babban matsayi, sakamakon tawali’un malaman da tsoron Allansu da taka-tsantsan da suke da shi ga lamurran duniya tare da ƙoƙarin kiyaye dokokin Allah sau-da-ƙafa. Irin wannan tsalkin zuciya da cikakken imanin malaman da ƙoƙarin cin halat ya sa addu’o’insu sukan kasance abubuwar karɓa cikin sauri fiye da waninsu. Fahimtar haka ya karkato da hankullan al’umma zuwa gare su ta fuskar neman kusanta da su domin samu addu’o’insu, don neman tsari daga abokan gaba ko samun zaman lafiya, ko ƙarin haɓakar arziki, ko neman lafiyar jiki da makamantansu.

8.0 Tasirin Zamani Ga Rayuwar Malanta

            Sauyawar zamani ya haifar da wanzuwar sauye-sauyen al’amurran da suka jiɓinci malanta a ƙasar Hausa. Abu na farko da ya fara sauyawa shi ne, ita kanta niyyar ta neman ilimin addinin Musuluncin, domin ana nemansa ne ba don a san Allah da yadda za a  bauta masa ba ne, sai don neman tara abin duniya ta kowane hali. Ba kamar lokuttan da suka shuɗe ba, lokacin da ake neman ilimi don a san Allah haƙiƙanin saninsa da yadda za a bauta masa. Lokacin da malamai ke taka tsantsan wajen hulɗa da mutane don gudun hulɗa da ɓatagari.

            Sauyawar zamani da manufar da ake neman ilimin addinin Musulunci sun sa an fara samun wasu masu da’awar malanta suna mu’amala da ‘yanfashi da ɓarayi da ‘yandaudu, da karuwai, da ɓarayin zaune, ta hanyar ba su miyagun asiran da ke jefa al’umma baki ɗaya ga fushin Allah. Wasu lokuttan irin waɗannan malamai har sukan ƙarfafa satar dukiyar hukuma, ta hanyar bayar da fatawoyi masu take: “A ci ban da ɓarna”, musammam ma ga waɗanda ke wawurar dukiyar hukuma suna kai musu har gida.

9.0 Dalilan Dagulewar Tsaro A Najeriya Ta Arewa

            Ba yadda za ayi a magance matsala face sai an bi diddigin gano tushen matsalar, sanna ne za a iya gane hanyar kawar da ita. A sakamakon nazari da tunani mai zurfi tare da duban tarihi da yadda al’amurra ke guda a yanayin da muke ciki. Za a iya cewa taɓarɓarewar lamarin tsaro a Najeriya ta Arewa ya samo tushi ne tun bayan da aka samu ‘yancin kai. Samun ‘yancin kai a shekarar 1960 wanda ya wanzar da shigowar mulkin jamhuriya ta farko a Arewacin Najeria. Babu ko tababa, shigowar mulkin siyasa ba ƙaramar koma baya ya haifar ba ta haujin cikakken ikon da sarakunan yankin ke da shi a kan masarautunsu, wanda suka samo tun lokacin kafuwar Daular Usmaniyya wadda aka kafa bisa harsashin addinin Musulunci.

            Kafin lokacin siyasa, baƙo ba zai zauna a cikin hurumin wani sarki ba, sai da izinin sarki. Yayin da aka ba shi izinin zaman gari, izinin na iya kasancewa na wucin-gadi. Idan wani mugun hali ya bayyana ƙarara na baƙon, kai tsaye sai sarkin garin ya kore shi daga ƙasarsa. Sarakuna kan yi haka ne domin tabbatar da cikakken tsaro a hurumin ƙasashensu.

            A cikin shekarar 1962, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Jahar Arewa, ya gabatar da wata dokar da ta kafa Gwamnatin Yanki wato Pronincial Government wadda ta samar da kwamishinoni a dukkan faɗin yankuna 13 da ke Jahar Arewa, waɗanda suka kasance ‘yan siyasa ne jagororin mulkin yankunan da aka tura su. Hasali ma sarakuna kamar Sarkin Musulmi Sir. Abubakar III da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da Shehun Barno, da Sarkin Zazzau da Sarkin Gwandu, duk za su rinƙa amsar umurni daga kwamishinonin yankunansu (Ibrahim, 1999:56). Wannan lamarin ba ƙaramin zubar da martabar iyayen al’umma da tarnaƙi gare su da kuma ayyukansu na kare al’umminsu ya haifar ba.

            A cikin shekarar ne aka sake kafa wata doka ta haƙƙin mallakar ƙasa, wadda ta karɓe dukkan ilahirin haƙƙin kula da filaye da dazuzzuka daga hannun sarakuna aka mayar da ikonsu ga shugaban gwamnatin Jahar Arewa, wato Sardauna wanda ya kasance jagoran gwamnatin.

            Tun daga wannan lokacin, a hankali sai sarakuna suna ta rasa ikon da suke da shi a tsarin gudanar da gwamnatin En’e da suka samu tun zamanin Turawa. A wancan zamanin, haƙƙin kula da doka da kiyaye bin doka da gudanar da harkokan shara’a bisa adalci, abubuwa ne da suka tattara a wuyan Manyan sarakunan ƙasar nan. Kuma su ke da haƙƙin kafa dokoki game da al’amurran da za su wanzar da jin daɗi tare da walwalar al’ummomin da ke farfajiyar masarautunsu. Kundin tsarin dokokin En’e (N.A.) na shekarar 1943 ya ba sarakuna damar tsara ‘yandokan hukumar En’e, tare da kafa  ɗakunan shara’a. haka kuma a ƙarƙashin doka ta shekarar 1933 mai lamba ta 44 wadda dokar majalisa ta 1945 lamba ta 1 ta yi wa kwaskwarima, kuma kundin tsarin dokokin En’e na shekarar 1948 doka mai lamba ta 36 ta ɗora alhakin gudanar da shara’a da ɗakunan shari’u da ke faɗin masarautunsu, kamar yadda Yahaya (1950:1) ya bayyana.

            Sarakuna a daidai wancan zamanin saboda kasancewar su malamai ne a fannoni daban daban na addinin Musulunci, sun mayar da hankullansu wajen tabbatar da bin dokoki tare da kiyaye tsare-tsaren hukuma na gudana daidai babu tangarɗa a duk faɗin lardunansu. Don haka ne aka ɗora musu alhakin sake tsare-tsaren ‘yandokan En’e da kula da lamurransu tare da sanya idanu a kan yadda suke gudanar da ayyukansu. Wannan tsarin ya taimaka wa ‘yandoka wajen samun ƙarfin guiwar tafiyar da ayyukan da aka ɗora musu, na kare aukuwar aikata laifuka tare da  bankaɗo maɓarnata, da murƙushe hargitsin da ke iya tasowa a tsakanin al’ummar masarautar. Kuma ‘yandokan ne ke da haƙƙin kula da tsaro da kariyar rauwa da dukiyar al’ummar masarautar, kamar yadda Yahaya (1950:2) ya nuna.

Ɗaukar Aikin ‘Yandoka

            Kafin bayyanar siyasa, sarakuna ke da alhakin zaɓar waɗanda za a ɗauka aikin ‘yandoka. Duk wanda za a ɗauka aikin akan yi ƙwaƙƙwaran bincike dangane da halayyarsa da ta zuriyarsa, idan an sami labarin wanda ya taɓa sata ko wani mummunan hali daga cikin zuriyarsu, ba za a ɗauke shi ba. Akan sanya sashen ‘yandoka a ƙarƙashin kulawar Wakilin ‘Yandoka, wanda yakan kasance jami’in tuntuɓa ga Waziri a wasu masarautu. A wancan zamani, ‘yandoka ba su da bariki, suna da masaukai ne awasu sassa daban-daban da ke cikin birni. Sarakuna na amfani da ‘yandoka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Ta amfani da su ne, sarakuna ke hana sace-sace da fashe-fashen gidajen al’umma da wasu nau’o’in ta’addanci a tsakanin al’umma. Su ke yin gadin dare (sintiri da dare) domin murƙushe masu aikata miyagun laifuka a garuruwa, kamar yadda Ɗalhatu (2002:272) ya nuna.

Ɗakunan Shari’a

            Sarakuna su ke da haƙƙin zartar da wasu hukunce-hukunce da suka danganci dokokin shara’ar Musulunci da kuma na al’ada. Ɗakunan shari’a kamar na Sarkin Musulmi, da Sarkin Kano, da na Sarkin Zazzau, da na Sarkin Gwandu, da Borno da Katsina da Bauci da sauransu, su ne ɗakunanan shari’a na ƙoli a kowace masarauta. Suna da ƙarfin zartar da hukuncin kisa idan laifi ya tabbata da ƙwararan hujjoji da cikakkiyar shaida ko shaidu.

            Kafin bayyanar mulkin kai, kowace babbar masarauta tana da kotun ƙoli. Babban sarkin shi ne babban alƙali tare da maƙarabansa. Sai dai duk da haka a duk msarauta akwai Alƙalin Alƙalai. Misali a Masarautar Zazzau ga yadda tsari kotun ya kasance a shekarar 1937 kamar haka:

1.      Sarkin Zazzau             Malam Jafaru                                              shugaba

2.      Ma’ajin Zazzau         Ibrahim Bagudu                                memba

3.      Alƙalin Zazzau         Muhammadu Lawal                                    memba

4.      Galadiman Zazzau  Alh. Hayatuddeen                           memba

5.      S/Ruwan Zazzau     Malam Sanusi                                               memba

6.      Malam Ibrahim Ɗan Makama Ahmadu                           memba

7.      Malam Suleiman (council secretary)                                             magatakardan kotun.

Ƙararrakin da aka ɗaukaka ne daga wasu garuruwa iyayen ƙasa ake kaiwa gaban majalisar sarkin.

    An fara rage musu iko ne lokacin da aka ɗauke ɗakunan shari’a da ‘yansanda da gidajen yari (kurkuku, ko jaru, ko gidan kaso) daga ƙarƙashin kulawarsu. Wannan lamari ya wanzu ne a wajejan shekarun 1960 ne. A cikin shekarar 1976 kuma aka kwace musu iko gaba ɗaya, aka maye gurbin gwamnatin En’e (N.A.) da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi. Daga wannan lokacin sarakuna ba su da cikakken ikon akan ƙasashensu, sun zama shugabannin jeka-na-yi-ka kawai. Wannan ba karamar matsala ba ce. Sakamakon haka ne aka yi ta samun rikice-rikice ba iyaka a wannan yankin. Misali rikicin maitatsine a shekarar 1980, ‘yanfashi da makami suka rinƙa cin karensu ba babbaka. Sai aka rinƙa samun rikice-rikice a sassa daban-daban da ke wannan yanki. Misali a Rikicin Bakalori a yanki Bakura da Maradu, da naTafawa Ɓalewa da Zangon Kataf waɗanda suka yi sanadin salwantar dukiyoyi da rayukan al’umma. A cikin shekarar 2009, sai ‘yan Boko Haram suka bayyana, inda suka girgiza al’ummar wannan ƙasa. Daga nan kuma sai aka tsunduma a cikin wani yanayi na garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa tare da satar bisashen al’umma. Za a ga cewa, an yi hasarar dubban rayukan al’umma da dukiya mai ɗimbin yawa ba don komai ba sai don son zuciyar wasu ‘yan tsiraru daga cikin al’umma.

Dalilan Taɓarɓarewar TsaroA Jahar Zamfara

            Bayyanar mulkin siyasa ya taimaka matuƙa wajen lalacewar tarbiyyar matasa a wannan jahar, musamman ta fuskar shaye-shayen abubuwan da ke sa maye. Duk da kasancewar an jaddada gudanar da shara’ar Musulunci, amma wannan bai hana maƙaraban shayar da matasa abubuwan da ke sa maye ba. Alhali kuwa sun san yin haka haramun ne. Ana yin haka ɗin ne domin cimma wata manufa ta siyasa. Da nau’in irin wannan matasan ne ake amfani wajen gallaza wa abokan adawar siyasa na cikin gida ko na wata lemar siyasa ta daban. Irin waɗannan ‘yanbangar siyasar ne akan tura su kasha wasu ‘yan siyasar da ake jin za su iya kawo cikasa ga wasu ko wani. A bayyana yake ƙara, an sha ganin irin waɗannan matasan suna aikata ayyukan ta’addanci a tsakanin jama’a ba tare da hukuma ta ɗauki mataki ba. An sha kisan bayin Allah a sakamakon bambancin siyasa, a rasa wanda ya aikata. Hasali ma irin waɗannan ‘yan bangar siyasar suna samun kuɗaɗen da suka wuce misali a shekarun da suka shuɗe. kuma das u aka yi yaƙin neman zaɓe,wanda suke cike da burin za su dara idan aka yi nasara. Sai lamarin ya zo musu ba yadda suka zata ba. Duban irin sauyin da ya faru gare su, shi yasa al’umma ke has ashen cewa irinsu ne suka tare a dawa suna gudanar da ta’addaci tare da abokansu da ke zaune a cikin birane da ƙauyuka suna aika musu da rahotannin mutane akai-akai don neman kuɗin fansa. Wannan lamarin ya zama ruwan dare zagaye duniya. Allah ne kawai zai tsalkake ‘yan siyasar wannan jahar daga zargin mutane, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ba irin waɗannan mutane wasu muƙaman siyasa. Wani lamarin da ya ƙara sa su zama abin zargi bai wuce yadda aka rinƙasa saka Alƙur’ani Mai tsalki cikin shadda ba, hasali ma zaɓe na ƙaratowa, lamarin sai ƙara ta’azzara yake. Idan kuwa abubuwa irin waɗannan na faruwa a jahar da ake da’awa da ta shara’a, ai dole ne al’umma su girbi abubuwan da suka shuka.      

Gudummuwar Malaman Ƙasar Zamfara

            Tun lokacin ɓarkewar yaƙin basasa na biyu da ya auku, malamai suke tsaye ga yin addu’o’in samun zaman lafiyar wannan yanki da kuma ƙasa baki ɗaya, a duk lokuttan da aka kammala sallolin farilla guda biyar da ake aiwatarwa kowace rana. Ba nan kaɗai ake aiwatar da irin waɗannan addu’o’in ba, har da wuraren taron ɗaurin aure ko zanen suna ko naɗin sarauta ko  wata walima. Irin waɗannan addu’o’i da malamai suke aiwatarwa ba ƙaramar garkuwa ba ne wajen yaƙar ta’addanci a tsakanin al’umma.

Masarautar Bakura

            Yayin da lamarin rashin tsaro ya yi ƙamari wasu masarautu sun yi ƙoƙarin kiran tarurrukan malamai da limamai domin tattaunawa game da matakan da ya kamata a ɗauka don maganin matsalar ɓarayi da ta kunno kai da kuma satar shanu. Miasli a Masarautar Bakura, Sarkin Ɓurmin Bakura ENGR. Bello Sani, ya kira taron malamai da limaman da ke farfajiyar masarautarsa, inda ya nemi shawara game da hanyar da ta dace a bi domin maganin bala’in da ke tunkarar al’ummar masarautar da jaha da kuma ƙasa baki ɗaya. Malaman suka tsayu a kan cewa, yayin da bala’i ya kunno kai irin wannan, ba wata hanyar da ta dace sai a fuskanci lamari addu’a. Masanan sun shawarci sarkin da ya bayar da umurnin yin amfani da masallatan juma’a a riƙa yin addu’o’i a ranakun Alhamis da Juma’a bayan sallar asuba a sauke Alƙur’ani a duk sati. Yayin da shi kansa Sarkin Ɓurmin Bakura ya bayar da gudummuwar Ƙur’anai guda sittin a raba a manyan masallatan juma’a da ke garuruwan uwayen ƙasa da zawiyyoyin da ke faɗin masarautar (Sulaiman,2020).

             Kwamitin Da’awa na Ƙaramar Hukumar Mulki ta Bakura, sun zagaya saƙo da lungu da ke yankin domin wa’azin wayar da kan al’umma dangane da muhimmanci tsaro a yankunansu da kuma illar zubar da jinin al’umma da salwantar da dukiyarsu ba bisa haƙƙin shara’ar Musulunci ba. Masanan sun faɗakar da al’ummomin cewa,  wajibi ne kowane musulmi ya kasance wakilin jami’an tsaro a cikin yankinsu, ta hanyar sanya ido a kan irin nau’o’in mutanen da za su yi hulɗa da su. Yayin da suka ga baƙuwar fuska wadda ba a san matsayinta a cikin al’ummarsu ba, sai a hanzarta kai rahoto wajen jami’an tsaron yankin don binciken matsayinsu a yankin.

            Masu wa’azi a masallatan juma’a da ke faɗin masarautar kuwa, suna faɗakar da masallata game da irin gudummawar da ya kamata su bayar wajen  kawar da ta’addaci tare da samar da tsaro da hanyoyin kare kansu. Malaman sun samar da wasu addu’o’i ga al’ummar masarauta waɗanda za su dinga karantawa domin neman kariya ga ƙasashensu da jaha da kuma ƙasa baki ɗaya. Misalan addu’o’in su ne kamar haka:

 

بسم الله الر حمن الرحيم                                 

يس والقرءان الاحكيم .(1000) تبت يدآ أبى لهب .(1000) إنك لمن المرسلين.(1000)ماأغنى عنه ماله وماكسب .(1000), على صراط مستقيم.(1000), سيصلى نارا ذات لهب.(1000),تنزيل العزيز الرحيم.(1000), وامرأته                                                     حمالةالحطب.(1000),لتنذرقومامآأنذر ءاباؤهم فهم غافلون.(1000), فى جيدها حبل من مسد.(1000)

بسم الله الرحمن الرحيم                   

لقد جآءكم رسول من انفسكم عزيز عليه ماعنتم حريص عليكم بالمومنين رءوف رحيم. فإن تولوا فقل حسبي الله لا إله الاهوعليه توكلت وهو رب العرش العظيم.(41)        

بسم الله الر حمن الرحيم                        

اللهم اقطع أجل أمل معتدين وشتت اللهم شملهم وأمرهم,وفرق جمعهم, واقلب تدبيرهم, وبدل أحوالهم , ونكس أعلا مهم, وأكل سلا حهم , وقرب آجا لهم, ونقص أعمارهم, وزلزل أقدامهم, وغير أفكارهم, وخيب آمالهم, وخرب بنيانهم, واقلع آثارهم حتى لا تبقى لهم باقية ولا يجدوا لهم واقية, واشغلهم بأبدانهم وأنفسهم, وأبدهم بصواعق انتقامك, وابطش بهم بطشا شديدا,وخذهم أخذاعزيزا,إنك على كل شىءقدير, ولاحول ولاقوة إلابالله العلى العظيم. اللهم لا نمنعهم ولا نرفعهم إلابك, اللهم إنا نجعلك فى نحورهم, ونعوذبك من شرورهم,يامالك يوم الدين إياك نعبد, وإياك نستعين عليهم, فدمرهم تدميرا. وتبرهم تتبيرا فاجعلهم هباء منثورا, آمين                  

اللهم من أرادنا والإسلام والمسلمين بسوء اوشرٍ فاضربه بسيف انتقامك القاتل, وارمه رمية تصيب منه المقاتل, وأذقه وبال امره عاجلاًغيرَ آجلٍ, اللهم اقمع بأسهُ, وَاعقدْلسانه, وألجمْ فاهُ, واحْبِس يديْهِ, وَحُلْ بينناو بينهُ كيف شئتَ و أنَّى شئتَ, بِقُوَّتك ياقوىُّ يا متينُ, اللهم اجعله عبرة للحاضرِ والبَاد, فإنك أنت المَليكُ المقتدر القا هرُ فوق العبادِ.                     

اللهم كن لبِلادِ الإسلامِ والمسلمين حافظًا من مكرِ كُلِّ ماكرٍ, وفُجُورِ كلِّ فا جرٍ, وغدرِ كلِّ غادرٍ, وحسدٍ كلّ حاسدٍوحا قدٍ, و ظلمِ كلِّ ظا لمٍ, وفسادِ كلِّ فاسدٍ, وشما تة كل شا متٍ وعداوةِ كلِّ عدوِّ, ومن كلِّ سوءٍ و شرٍّ, ومن كلِّ بلاءٍ و مرضٍ وضرٍّ, و نجنا والمسلمين اجمعين من جميع المهالك والمضارِّ والمعاصى والحرام والضلال, يا شديدَالمحال, يا من إليه المرجعُ والمآلُ. اللهم عليك بكلِّ من يؤْذِى المسلمين.           

اللهم احفظ بلادنا من شر الكوارِثِ والزلازِلِ والسُّيُولِ والبراكتن و جميع البلايا, وثبِّتْ الأرض من تحت اقدام المسلمين, وزَلْزِلِ الأرض من تحت أقدام أعداء المسلمين. اللهم زلزل الأرض من تحت اقدام الكافِرِين بقوَّتك يا قوِيُّ يا متين, يا خير السائلين,يا حرْزَ الضعفاءِ والمساكينَ.                 

            Ganin irin muhimmiyar rawar da malaman ke takawa ne, kwamitin tsaro na Ƙaramar Hukumar Mulki ta Bakura ya sanya malamai cikin kwamitin a matsayin masu bayar da shawara ga babban kwamitin tsaro wanda Masarautar Bakura da Ƙaramar Hukuma suka kafa.

Kwamitin Malamai Na Jaha

            Ganin yadda lamarin tsaro ya taɓarɓare a wannan jaha har abin ya kai lahaul wa la ƙuwati, al’ummomi daga kowane lungu sai koke suke, musamman a Masarautar Ɗansadau, inda aka sami asarar ruyukan al’umma. Wannan lamarin ya haifar da canjin yawu a tsakanin tsohon ɗan majalisar tarayya Sanata Sa’idu Muhammad Ɗansadau da tsohon gwamnan Alh. Abdul’Aziz Yari Abubakar. A sakamakon haka ɗin ne aka gayyato wani mai asirin kama ɓarayi da ake kira Ali Ƙwara domin ya bayar da tasa gudummuwa. Ya zo ya kuma yi aikinsa na wani ɗan lokaci. Ya yi kuma nasarar kama maɓarnatan da jami’in ‘yansada da ke kula da makamai na rundunar ‘yansanda ta jahar Zamfara, amma tun daga lokacin da kafafen ‘yaɗa labarai suka bayyana lamarin ba wanda ya ƙara jin komai.

Ayyukan Kwamitin Malamai

            Gwammanati ta kafa kwamiti, wanda aka kira kwamitin sasantawa tsakanin rikicin manoma da makiyaya a ƙarƙashin shugabanci marigayi Malam Abubakar Tureta. Kwamitin ya yi duk abin da ya kamata ya aiwatar. Kasancewar kwamitin na malamai ne, ya samu karɓuwa da amincewa a tsakanin al’ummomin da lamarin ya shafa. Kwamitin ya samu ganawa da waɗanda aka zalunta da ma azzaluman. Saboda irin yadda al’umma ke mutunta malamai da harka malanta, har ‘yanta’addan sun bayyana wa kwamitin, kanwa uwar haɗin rikice-rikicen da yadda suke ruruta wutar fitinar da alfanun da suke riska sakamakon ta’addanci. Malaman sun rubuta cikakken rahotonsu mai ɗauke da bayanan waɗanda ake tuhuma, sun kuma danƙa rahoton domin ɗaukar mataki na gaba. Sai dai maimakon a binciki waɗanda ake tuhumar, sai gwamnatin ta roshe kwamitin, ta sake kafa wani kwamitin aka kuma sanya mutanen da ake tuhuma cikin kwamitin. Wannan shi ya haifar da watsewar kwamitin (Kanoma,2019). Malamin ya ƙara da cewa:

                        Lokacin da aka yi wannan kwamiti, kasancewar an ce zama na malamai

                        ne, to irin haɗin kan da al’umma suka bayar, abin za ka sha mamaki! Da jami’an

                        tsaro da masu ɓarnar. A lokacin da anka haɗa rahoton farko aka mika ma Gwa-

                        mna. To matsalar da anka samu, da anka haɗa rahoton nan na farko har anka

                        miƙa ma Gwamna, ya je ya aje bai ma karanta ba.

Malamin ya cigaba da cewa, suna jiran gwamna ya kira su, amma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Har Malam Abubakar Tureta ya hasal, ya ce masa haka mutumin nan zai muna. Malamin ya ƙara da cewa:

                        Mun gano asalin abubuwan, masu yi, da hanyar da za a bi a magance,

                        ga hanyar da kuma su za a haɗa su Fulani da manoma duk a haɗe su,

                        ga ɓarayi, a ci nasara a kai. Masu ɗaukar fansa, da masu koke-koken

                        ga koken da su Fulani su ka yi. Kuma ga lokacin da an kai ƙarshen

                        matsalar!

            Bayan sun bayar da rahoton farko duk da kasancewar suna sane da irin halin ko oho da aka yi game da ƙoƙarin da suke yi na yaƙar ta’addanci cikin ruwan sanyi ta hanyar lalama, sai suka cigaba da aiki ba kama hannun yaro. Sun sami damar haɗa rahoto na biyu. An yi ƙoƙarin a zauna ba a sami zaman ba, sai ran da Gwamnatin Tarayya ta naɗo wani kwamiti da ta turo, sai aka ce yaya za yi, daga ƙarshe sai aka gabatar da rahoton da kwamitin malamai suka rubuta. Yayin da kwamitin Gwamnatin Tarayya ya karɓi rahoton ya duba, sai suka ce da gwamnati ta yi aiki da rahoton ai da tuni an kawar da matsalar (Kanoma,2019).

            Malamin ya tabbatar da cewa, suna cikin tafiyar da aikinsu sai wasu suka yi wani kwamiti na daban, amma suka buƙaci malamin da ya ba su kwafen rahotonsu, haka su ma ‘yansanda sun karɓi kwafen rahoton. Sai lamarin ya kusan zama kamar ana wasa da hankalin al’umma ne. dalili kuwa shi ne, duk wurin da malamai suka tafi, sai bayan sun bar garin sai wani kwamiti na daban ya ziyarci muhallin, akwai garin da kwamitin na biyu ya tafi mutane ishirin kawai suka halarci zamansu. Ke nan wannan lamari yana buƙatar ayar tambaya. Tambayar kuwa ita ce: Me ya sa duk gari ko ƙauyen da malamai suka kai wa irin wannan ziraya al’umma na yi musu lale-marhaba, yayin da kwati na biyu in je bai ganin kowa sai waɗanda zuwansu wurin ya zama dole? Amsar tambayar a bayyane take, domin al’ummomin ba su da tabbas tare da shakku da ke cikin zukatansu game da kwamitin (Kanoma,2019).

            Kamar yadda wannan maƙala ta kalato, a daidai lokacin da malamai za su sake mika wani rahoton, sai mutanen nan da suka kasance abin tuhuma ga malamai saboda hannun da suke da shi cikin ta’addanci, aka sanya su cikin kwamitin. Kuma gwamna da kansa ya ce ya jaddada kwamitin tare da su a matsayin ‘yankwamitin. Saka su kwamitin shi ya kawo ƙarshen aikin kwamitin, kamar yadda (Kanoma, 2019) ya bayyana.

Da gwamnati ta yi amfani da shawarwarin da ke ƙunshe cikin rahoton, da lamarin bai ta’azzara haka ba. A ƙoƙarin malaman na yaƙar ta’addanci da ya dabaibaye Jahar Zamfara, sun gabatar da maƙalu a tarukan faɗakar da al’umma da dama a cikin gida da kuma wajen jaha. Daga cikin irin waɗannan muƙalun da malaman suka gabatar sun haɗa da muƙalu masu take:

1.      Nauyin da Allah Ya Ɗora ma Shugabanni a Kan Harkokin Tsaro.

2.      Muhimmancin Zaman Lafiya da Cigaban Addini a Duniya.

3.      Illolin Ƙabilanci da Tasirin Ƙabilanci Wajen Haddasa Fitina.

4.      Gudummuwar da Kowa Zai Bayar Wajen Samar da Tsaro da Yaƙar Fitinoni.

5.      Illolin Garkuwa Da Mutane.

6.      Nauyin da ke Kan Jami’an Tsaro Wajen Tabbatar Da Tsaro.

Shawarar Malamai Ga Gwamnatin Jahar Zamfara

            A ƙoƙarin malaman Jahar Zamfara na yaƙar ta’addancin da jahar ke fama da shi sun shawarci gwamnatin jaha da aiwatar da wasu gyare-gyare a matakai da sassa daban-daban kamar haka:

Makarantu

            Kasancewar makarantu wurare ne na koyarwa tare da horar da ɗalibai ayyukan da za su yi wa al’umma amfani,  saboda haka ya kamata a cusa wa ɗaliban halaye na musamman da suka haɗa da:

*Tsoron Allah, da kishin ƙasa, da girmama iyaye, da na gaba, da hukuma, da gaskiya, da riƙon amana.

* Haka kuma, tawali’u da aiki tuƙuru da sadaukar da kai da tsabta da son juna duk abubuwa ne da suka wajaba a horar da ɗalibai su a duk faɗin makaratun jaha, ta hanyar tilasta darussan addinin Musulunci domin shi ke horar da zukatan ɗan Adam.

Shugabannin Makarantu

            Shugabannin makarantu da malamai, su ne aka ɗorawa alhakin koyarwa tare da gyara halayen ɗalibansu. Wajibi ne su kasance abin koyi ga ɗaliban. Su kuma zama masu kulawa da halin da ɗalibansu ke ciki tare da nuna damuwa game da cigaban ɗaliban. Hakan ba zai samu ba sai an horar da malamai masu tarbiyya da dattako waɗanda za su tafiyar da wannan gagarumin aiki tare da ba su haƙƙoƙinsa da kuma kyautata musu kamar yadda ya kamata.

Bayar DA Kyakkyawar Kulawa Ga Al’umma

            Wajibi ne gwamnati ta dubi buƙatar bayar da kulawa ta musamman wajen sake halayyar zamantakewar al’umma da ke zaune a ɓangaren birane da karkara domin dawo da ɗa’a tare da magance rashin aikin yi da rashin bin doka da taɓarɓarewar ɗabi’u da aikata munanan laifuka.                            Wajibi ne a bayar da kulawa ta musamman domin samar da tsaro mai ɗorewa da zai wanzar da zaman lafiya ta waɗannan hanyoyi:

·         Sake dawo da ɗa’a da daidaitawa a tsakanin al’umma, ta ba kowa haƙƙinsa.

·         Hana miyagun halaye.

·         Samar da cikakken tsaro a kowane lungu da saƙo da ke faɗin wannan jaha.

·         Ciyar da matasa gaba da samar musu ayyukan yi, tare da farfaɗo da cibiyoyin horar da matasa sana’o’in hannu a lungu da saƙo na wannan jahar.

·         Inganta makarantu da asibitoci, ta hanyar samar musu da wadatattun kayan aiki da kwararrun ma’aikata tare da ba ma’aikatan haƙƙoƙinsu kamar yadda doka ta tanada.

·         A taimaka wa ƙungiyoyin tsaro da ke gudanar da sintiri a garuruwa da kauyukan da ke faɗin wannan hajar.

·         A yi amfani da ƙwararrun malaman addinin Musulunci masu tsoron Allah da tamali’u wajen ilmantar da al’umma, muhimmancin neman ilimi da kawar da jahilci da wajabcin ɗaukar nauyin iyali da muhimmancin kula da cigaban jama’a. Su kuma faɗakar da jama’a muhimmancin kula da lafiya da tattalin arziki da haƙuri a lamarin rayuwa. Su kuma faɗakar da mata haƙƙoƙinsu da nau’in gudummuwar da za su bayar wajen tabbatar da tsaro a tsakanin al’umma. Su faɗakar da al’umma game da muhimmancin tarbiyyar ‘ya’yansu tare da ciyar da su daga abinci na halal.

·         A samar da hayoyin ayyukan da suka dace da mata.

·         A wayar da kan mata game da haƙƙoƙinsu.          

   Abubuwan Da Gwamnati ya Kamata ta Kawar

            Akwai abubuwa da dama, amman a nan ya kamata a duba a cikin sha’anin kasuwanci kamar:

·         Alguussu (maguɗi ko amaja).

·         Ƙarin farashin kaya ba tare da wani dalili ba, musamman a lokacin azumi.

·         Rashin amana a tsakanin abokan ciniki.

·         Ɓoye kayan masarufi.

·         Rashin taimakon juna a tsakanin ‘yankasuwa da kuma al’umma.

A aikin gwamnati kuwa akwai abubuwa da ke buƙatar kulawa ta hanzari kamar:

·         Rashin kyakkyawan shugabanci nagari.

·         Rashin bin ƙa’idar aiki, wato dokokin aiki da ƙa’idojin kashe kuɗaɗen hukuma.

·         Karɓar hanci da bayar da rashawa.

·         Magance hauhawar talauci a tsakanin ma’aikatan gwamnati, ta hanyar biyansu haƙƙoƙinsu bisa ga la’akari da yadda yanayin rayuwar al’umma ke tafiya ta yau da kullum.

Kammalawa

            Bisa ga abubuwan da suka gabata, an fahimci cewa tun daga lokacin da addinin Musulunci ya shigo ƙasar nan malamai ke kai da kawo wajen ƙoƙarinsu na faman yaƙi da abin da ke wanzar da ta’addaci wato jahilci da shi kansa ta’addancin ɗin. sakamakon haka ɗin ne a kwana a tashi har aka samu kafuwar Daular Usmaniyya. Daular ta samar da kyakkyawan tsarin shugabanci, wanda ya wanzar da kafuwar ɗakunan shara’a a duk faɗin daular. Irin waɗannan ɗakuna sun taka muhimmiyar rawa wajen yaƙar ta’addanci. Haka an ga irin yadda malaman jahar Zamfara suka bayar da muhimmiyar gudummuwarsu ta haujin wa’azi da gudanar da addu’o’i don ganin an kai ƙarshen wannan lamari. Akwai buƙatar kowa da kowa ya tsaya ya binciki irin miyagun ayyukan da yake aikatawa, ya tuba ya dawo ma turba ta gari. Ko za mu sami saukin wannan lamari. Wajibi ne ga masu riƙe da madahun mulki da su sanya tsoron Allah a cikin dukkan lamurran gudanar da ayyukan jahar nan. Su fa tuna akwai ranar da za su tsayu gaban mahaliccinsu su yi bayani dala-dala game da yadda suka tafiyar da wannan jahar. Adalcinsu ne zai kuɓutar da su. Daga ƙarshe ya zama wajibi a ba al’ummar Nijeriya ta Arewa cikakken ‘yancin da shari’ar Musulunci ta ba su, musamman Musulmi. A kuma yi tanadin da zai ba masu zaɓen sarki cikakken ‘yancin bin ƙa’idar da shara’a ta ɗora musu na zaɓen shgabanni kamar yadda addinin Musulunci ya sharɗanta. Yin haka zai taimaka a samu shugabanni masu tsoron Allah. Wanda hakan zai taimaka wajen daidaituwar lamurra.

Manazarta

Tuntuɓi mai takarda

Post a Comment

0 Comments