Citation: Sani A-U. & Jaja, M.B. (2019). Zamani Riga: Akalar Magungunan Gargajiya a Hannu Addini da Zamani. In The Nasarawa Journal of Humanities. Vol.7, Number 1&2, Pp. 257-268. ISSN: 1118-6887.
Abstract
The concept of medicine refers to any substance, which if taken or any act which if performed, cures or reduces the intensity of a sickness. On the other hand, the concept of sickness as used in the paper refers to any disease, unfulfilled need or a strong anxiety that courses unrest to an individual. The paper revisits the Hausa tradi-medical practices right from the origin of the word “magani” (medicine). Holding the Hausa popular saying “zamani riga” (citations change with time), the paper studies the influence of Islam and globalization on the traditional Hausa medicines. The paper also studies the merits and economic importance of such medicines. The findings of the research reveal that, despite their numerous importance, they have a number of disabilities. They include poor preparation procedures, storage as well as the usage. The paper lastly suggests that, government should design a special program to orient, support and modernize the Hausa tradi-medical practices.
Keywords: Medicines, Culture, Islam, Modernity
And
Muhamamad
Bala Jaja
Zamani
Riga: Akalar Magungunan Gargajiya a Hannun Addini da Zamani
(The Influence of Islam and Modernity on
the Hausa Tradi-medical Practices)
Tsakure
Magani ya shafi
duk wani abu da za a yi amfani da shi ko a aikata domin a samu sauƙi ko waraka
daga wata cuta. Idan aka ce cuta kuwa a nan, za ta iya kasancewa ta ciwo ko
wata damuwa ko buƙata da ta tsaya wa mutum a rai. An ɗora wannan bincike a kan
ra’ayin Bahaushe na “Zamani riga.” Binciken ya mai da hankali wurin waiwaye
dangane da magungunan Bahaushe na gargajiya tun daga kan hasahen samuwar asalin
kalmar magani. Daga nan sai aka duba
tasirin Musulunci da kuma zamani kan magungunan gargajiya na Bahaushe. Bayan haka,
takardar ta nazarci amfani da koma bayan da magungunan ke tattare da su.
Sakamakon na nuna cewa, ɗimbin amfanin magungunan gargajiya bai hana su samun
koma baya ba. Naƙasun da suke da shi ya danganci rashin ingancin hanyar
sarrafawa da adanawa da kuma amfani da magungunan. A bisa haka ne aka ba da
shawarar cewa gwamnati ta samar da shiri na musamman da zai samar da horo ga
masu ba da magungunan gargajiya tare kuma da ba su tallafi, duk dai don inganta
sha’anin maganin gargajiyar Bahaushe.
Muhimman Kalmomi: Magani, Gargajiya, Musulunci, Zamani
1.0 Gabatarwa
Fagen
ilimin magungunan gargajiya ya daɗe yana jan hankalin manazarta da marubuta. An
samu rubuce-rubuce masu ɗimbin yawa a wannan fanni. Hakan ba ya rasa nasaba da
matsayin magani ga rayuwar ɗan Adam. Neman magani abu ne na yau da kullum. Tuni
ya zama wani ɓangare na rayuwar ‘yan’adam baki ɗaya. Dalili kuwa shi ne, ba a
rayuwa ba tare da cuta ba. Cutar na iya kasancewa ta jiki ko ta zuciya, wacce
ake gani ko kuma wacce ba a iya gani.[1]
Zuwan
Musulunci da kuma zamananci sun yi tasiri kan lamarin magungunan gargajiya na
Bahaushe. Idan aka ce zamani kuwa, ana nufin rayuwar Bahaushe bayan cuɗanyarsa
da baƙin al’ummu musamman Turawa. Saboda haka, tasirin zamani kan magungunan
gargajiya na nufin ire-iren sauye-sauye da aka samu a sha’anin magani sakamakon
zuwan Turawa da kuma abubuwan da suka zo da su. Sannan ya haɗa da abubuwan da
suka shafi ilimin da Turawan suka zo da shi, wato boko. Shi kuwa zuwa Larabawa
(a cikin wanna takarda), kai tsaye an danganta shi da shigowar addinin
Musulunci. Takardar na da muradin waiwaitar lamarin maganin gargajiyar Bahaushe
domin duba inda aka taso, da wurin da aka kwana da kuma wurin da aka dosa.
1.2 Manufar Bincike
Manufar
wannan takarda ita ce bitar al’amarin magungunan gargajiyar Bahaushe tare da
ire-iren sauye-sauye da aka samu a wasu lokuta cikin tarihi. Aikin zai mai da
hankali kan:
i.
Bitar lamarin magungunan gargajiya ta
la’akari da sauye-sauye da aka samu sakamakon zuwan Musulunci da kuma tasirin
zamani.
ii.
Bitar alfanu da kuma illolin da ke tattare
da amfani da magungunan gargajiya.
1.3 Ra’in Bincike
Bincike
ko nazari dangane da maganin kowace al’umma abu ne da ya shafi rayuwar al’ummar
gaba ɗaya. Bahaushe ya gama magana da ya ce: “lafiya uwar jiki.” Idan babu uwa,
lallai babu rabin zance domin ko a dara ma “fid da uwa ake.” Yayin da aka ɗaura
ɗamarar nazartar maganin gargajiya na Bahaushe, haƙiƙa an tunkari wani babban
ginshiƙi ne a rayuwarsa. Za a iya tabbatar da hakan yayin da aka yi la’akari da
cewa, nason magani ya mamaye al’ada da adabin Bahaushe baki ɗaya. Duk wani
motsinsa, sai ya sanya magani ciki. A bisa haka, za a ɗora aikin ne bisa
ra’ayin Bahaushe da ke cewa: “Zamani riga.”
Aikin
zai yi ƙoƙarin nazartar yadda rigar take lokacin da Bahaushe ke amfani da
magungunansa na gargajiya tsura. Sannan za a duba yadda ya ɗauraye rigar bayan
Musulunci ya riske shi. Daga ƙarshe kuma sai ya sauya wa rigar tasa fasali
domin dacewa da zamani bayan cuɗanyarsa da Turawa da kuma ƙarin ilimi da ya
samu sakamakon karatun boko.
Ma’anar Magani
Bunza,
(1990: 135) ya bayyana kirdadon samuwar kalmar magani da ya fi karɓuwa a
tsakanin masana Hausa a yau. Wannan ra’ayi ya yi daidai da ɗaya daga cikin
ra’ayoyin da suka shafi samuwar magani ga Bahaushe, wato ra’ayin gwadawa.
Ra’ayin na nuna cewa, kalmar magani ta samu ne a lokacin da Bahaushe ke ƙoƙarin
samar wa kansa magungunan cutuka daban-daban. Yayin da cuta ta samu, sai
Bahaushe ya tattaro ganyaye da saiwu da sassaƙe-sassaƙe domin gwadawa, har sai
ya samu wanda zai samar masa da waraka. Zai ɗauki nau’in sassaƙe ko saiwa ko
ganye (da makamantansu), sai kuma ya ce: “Ma gwada wannan mu gani.” Wato dai za
a gwada a gani ko za a dace?
Sannu
a hankali har aka gajarce furucin. Daga nan aka koma cewa: “Ma yi ma gani.”
Bayan tafiya ta yi tafiya ne kuma aka sake gajarce furucin zuwa: “Ma gani.”
Yayin da aka haɗe kalmomin guda biyu, su ke ba da sunan “Magani.” A bisa wannan
ra’ayi, kalmar ta “magani” gamin gambiza ce.
Ɗumbin
rubuce-rubucen da aka gudanar game da magunguna a matakin duniya da kuma ƙasar
Hausa ya sa akwai ma’anoni da dama da masana da marubuta suka samar. A
luggance, Bargery, (1933: 743) ya ce: “Magani yana nufin riga-kafi da kariyar
cuta.” A ɓangaren nazari kuwa, an samu marubuta da dama da suka bayyana ma’anar
magani.[2] Kusan da zarar an ambaci
kalmar magani, kowane Bahaushe ya san ma’anarta. Dalili kuwa shi ne, magani abu
ne da mutum ke cuɗanya da shi kullum. Gobir, ya bayyana ma’anar magani da cewa:
“Hanya ce ta kawar da, ko kwantar da, duk
wata cuta ta jiki ko ta zuciya, ko neman ɗaukaka, ko kariya daga makaru da jifa
da sihiri ko siddabaru.” Gobir, (2012: 224)
Wannan
ma’ana da Gobir ya bayar na nuni da cewa, ana neman magani ne domin ɗaya daga
cikin waɗannan dalilai:
a. Neman
waraka
b. Kwantar
da cuta
c. Neman
ɗaukaka
d. Neman
kariya
Lura
da wannan, akan nemi magani ne domin dalilai mabambanta. A wata ma’ana
makamanciyar wannan, Sarkin Gulbi, (2014: 5) ya ce:
Magani
shi ne duk wata hanya da za a yi amfani da ita domin riga-kafin cuta ko rage raɗaɗinta
ko ma a kawar da ita gaba ɗaya ko warwale wata matsalar rayuwa. Wannan hanya
tana iya kasancewa ta kimiyar zamani ko a gargajiyance, watau hanyar tsafi da
tsibbace-tsibbacen al’umma.
A
taƙaice duk wani abin da zai hana jin daɗi da walwala da nishaɗi da gudanar da
rayuwa yadda ya kama, to sunansa cuta. Hanyar da ake bi domin kawar da shi (Ko
kuma abin da ake amfani da shi domin kawar da wannan cuta) shi ake kira magani.
2.1 Hasashen Samuwar Magani
Masana
ba su samu matsaya guda ba dangane da asalin samuwar magani ga ɗan’adam.
Kasancewar haka bai zama abin mamaki ba idan an yi la’akari da cewar magani abu
ne da ɗan’adam ya fara cuɗanya da shi tun farkon samuwar cuta gare shi. Cuta
kuwa, babu wani lokaci a tarihin ɗan’adam da ba ta wanzu ba. A nan za a kawo
wasu daga cikin ra’ayoyi ko hasashe dangane da asalin samuwar magani:
2.1.1 Gwaji
Masu
wannan ra’ayi sun tafi kan cewa, ɗan’adam ya samu magani ne ta hanyar gwaji.
Kamar dai yadda aka bayyana a sama (ƙarƙashin samuwar kalmar magani), magani ya
samu ne ga mutum ta hanyar gwadawa. Yayin da cuta ta samu, sai a yi ta gwada
hanyoyi da abubuwa daban-daban har dai sai an dace an samu waraka.
2.1.2 Dabbobi da Tsuntsaye
Wannan
ra’ayi ya tafi kan cewa, an gano magunguna ne daga dabbobi da tsuntsaye. Idan
wata dabba ba ta da lafiya, akan iya fahimtar hakan ta hanyar rashin walwala da
za a lura da ita daga gare ta. A irin wannan yanayi ne masu kiyon dabbobin ke
lura da ire-iren ganyaye da ciyayi da dabbobin ke ci. Lokacin da dabba ta samu
sauƙi, sai ɗan’adam ya kimanta nau’ukan ganyaye da ta ci. Ta haka ne zai yi ƙoƙarin
haɗa nau’ukan ganyayen tare da amfani da su yayin da makamanciyar cuta ta same
shi. Ra’ayin na ganin cewa, wannan shi ne farkon samuwar magani.
2.1.3 Iskoki
Ra’ayin
nan ya tafi kan cewa, iskoki su ne silar samuwar magani ga ɗan’adam. Iskoki na
da ɗimbin ilimi dangane da magungunan cutuka daban-daban. Yayin da suke son
wani daga cikin mutane, sai su samar da ilimin magani gare shi. Wani lokaci
kuma ɗan’adam ne ke neman huwacewar magani ta hanyar fara hulɗa da iskoki.[3]
2.1.4 Ilhami
Wannan
shi ne ra’ayin da Bunza, (1990: 136) ya fi aminta da shi. Ra’ayin ya tafi kan
cewa, Ubangiji ne ke saukar da ilimin magani ga ‘yan’adam a matsayin ilhami.
Yayin da mutum ba shi da lafiya, zai samu ilhami, misali: “Ka yi amfani da
ganye kaza da sassaƙe kaza.” Yayin da ya gwada wannan magani, sai kuwa a dace.
Daga nan zai ci gaba da amfani da wannan nau’in magani tare da sanar da sauran
jama’a. A fahimtar wannan ra’ayi, a haka ne aka samu magunguna daban-daban.
Idan
aka duba sosai, za a tarar da cewa dukkanin ra’ayoyin hasashe ne kawai na
ilimi. Al’amarin samuwar magani abu ne mai dogon tarihi. Ayad, (2008: 18) ya
nuna cewa, an fara amfani da maganin garganiya tun shekaru 1,000 kafin hijira.
Ya ce:
The
Greek Hippocrates is considered to be the father of ‘traditional’ western
medicine. He lived around 1,000 year before Hijrah or 400 year before the birth
of Jesus (BC), and built his medical practice on observation and experience
using the natural world as a teacher that helped him to better understand how
healing is achieved. (Ayad, 2008: 18)
Fassara
An ɗauki
Bagirken nan Hippocrates a matsayin baban ‘maganin’ gargajiya na yammaci. Ya
rayu kimanin shekaru 1,000 dubu kafin hijira, wato shekaru 400 kafin haihuwar
Annabi Isa (BC). Ya gina binciken maganinsa kan lura da yanayi da kuma kaifin
nazari. Ya ɗauki duniya a matsayin malama da ke taimaka masa wurin fahimtar
yadda ake samun waraka.
A
ra’ayin wannan bincike, ya fi kyau a ce “ɗan’adam ya fara ƙoƙarin nema wa kansa
magani tun lokacin da ya fara cin karo da cuta a duniya.”
2.3 Rabe-Raben Magungunan Gargajiya
A
mafi yawan lokuta, rabe-raben magungunan gargajiya na tafiya ne tare da
rabe-raben cututtuka. Dalili kuwa shi ne, cuta da magani tare suke tafiya.
Kamar yadda suke tare a zahiri, haka ma suka kasance a fagen nazari tare. Masana
da dama sun ba da rabe-raben magungunan gargajiya. Wani abin burgewa shi ne,
dukkanin ra’ayoyin na masana alƙibla guda suka dosa, amma ta fuskoki
mabambanta. Bunza, (1990: 154-141) ya raba magani zuwa manyan rukune guda biyu,
wato:
i.
Magungunan cutar jiki
ii.
Buƙatocin ɗan’adam
Gobir,
(2012: 167-170) ya raba cutuka zuwa manyan rukunai guda biyu, (i) Cutukan jiki
da kuma (ii) Cutukan zuciya. Lura da wannan rabo da ya yi, za a iya fahimtar
yana da ra’ayin cewa magunguna sun rabu zuwa gida biyu manya. Na farko shi ne magunan
cutukan jiki. Na biyu kuwa ya kasance magunan cutukan zuciya. Yayin da aka
nazarci waɗannan rabe-rabe, za a tarar ba su ci karo da juna ba. Cutukan zuciya
dai su ne buƙatocin ɗan’adam.
Kalmar
Bature ta medicine na da kamar sauƙi
wurin fassara. Idan aka zo fassarar kuwa, za a tarar da cewa abin ya wuce yadda
ake tsammani. Dalili kuwa shi ne, kalmar magani
gama-gari ce. Ta tattara dukkanin nau’ukan hanyoyin samar da waraka da suka haɗa
da na jiki da kuma na zuciya. Kowanne daga ciki kuwa yana da sunan da Hausawa
suka laƙaba
masa. Za a fi fahimtar yadda abin yake yayin da aka waiwaici rabe-raben
magunguna manya da ƙananan da ake da su.
Wannan
aiki ya yaba da hikimar da ke cikin dukkannain rabe-raben da masana suka bayar
kamar yadda aka zayyana a sama. Aikin ya gamsu da salon da Gobir, (2012: 242)
ya yi amfani da shi domin bayyana rabe-raben magani. Duk da haka, a ƙarƙashin
rukunin magungunan buƙatun zuciya,
wannan bincike ya
ɗan
sha bamban da ra’ayin Gobir. Takardar ta raba magungunan biyan buƙatun zuciya
zuwa Son kai da na sharri da kuma
na alkairi. Hakan ya zama saɓanin na
Gobir da ya kawo su a matsayin na alheri
da kuma na sharri.[4]
Ga yadda abin yake:
|
Misalai |
||||
Magani |
Cutuka
|
Jiki
|
Ciki
|
Sanyin
ƙashi Ƙurjin
hanji Ciwon
ƙoda Amosani
|
|
Waje
|
Gwaiwa Makanta Gyambo Karaya |
||||
Ƙwaƙwalwa
|
Taɓin
hankali Farfaɗiya Rawar
kai Mantau
|
||||
Kare
kai |
Sagau Tauri Zana Baduhu |
|
|||
Buƙatun
zuciya |
Alkairi |
Maganin
kasuwanci Tsaraka |
|||
Son
kai |
Bi-ta-zai-zai Soyayya Neman
mulki |
||||
Sharri
|
Kurciya Kashe
rai Firaƙi Gumuni
|
||||
|
|||||
|
Kwaikwayo Daga: Gobir,
(2012: 242).
Yawaitar
nau’ukan magani ba ya rasa nasaba da yawan da cututtuka suke da shi. Kowane
nau’in cuta na da irin nasa nau’in magani. Hanyoyin da ake samun cutuka sun
bambanta, haka ma hanyoyin samar da magungunan waɗannan cutaka. Misali, Harold
da wasu (1964: 203) suna da ra’ayin cewa:
It is
clear that becoming a mental patient is a socially structured event.
Fassara
A
bayyane yake cewa, ciwon hauka lamari ne na zamantakewa da ke ɗaukar tsawon
lokaci kafin tabbatuwa.
Wannan
fahimta na nuna cewa ciwon hauka ya shafi matsalolin zamantakewa da ke taruwa
su yi yawa a ƙwaƙwalwar ɗan’adam. Kenan dai, kafin a shawo kan wannan nau’in
cuta sai an bi kadun lamarin tare da gano inda bakin zaren yake tare da yi wa
igiyar tufka.
2.4 Masu ba da Magungunan Gargajiya
A
al’adance, akwai rukunin jama’a da Bahaushe ya riƙa a matsayin masu ba da magungunan
gargajiya. Gobir, (2012: 264-271) ya kawo masu ba da magungunan gargajiya a
Bahaushiyar al’ada, musamman magungunan cutukan da suke da nasaba da iskoki.
Sun haɗa da:
2.4.1 Bokaye
Sa’id,
(2006: 49) ya bayyana boka a matsayin “mai maganin gargajiya wanda ke ta’ammuli
da aljanu.” Kafin zuwan Musulunci ƙasar Hausa, boko na kan gaba wurin samar da
magunguna ga masu cutuka daban-daban. Yana amfani da iskoki domin gano cutar da
ke damun majinyaci tare da ba shi magani domin samun waraka. Za ta iya yiwuwa
ra’ayin da ya tafi kan cewa tushen magani shi ne iskoki ya yi la’akari ne da
al’amarin bokaye da bokanci. Bokaye na ba da magungunan cutuka da suka haɗa da
na jiki da na zuciya.
2.4.2 ‘Yan bori
‘Yan
bori su ma sanannu ne a ɓangaren ba da magungunan gargajiya. Akan kai majinyaci
wurin ‘yan bori, musamman idan an kasa gane nau’in cutar da ke damun sa. A mafi
yawan lokuta akan yi wa majinyacin girka, musamman idan cutar ta yi kama da
shafar iskoki. Dangane da lamarin ‘yan bori a ɓangaren ba da magani, ga abin da
Dr Mamman Shata ke cewa:
Yau wannan zamani,
Wannan lokaci,
Ko wani ke zazzaɓi,
Ka ga ana gai da
shi,
Yana amsawa
jika-jika,
Ku kai mai borin
Sule,
Sarkin Bori Sule.
Yanzu sai ka ga
sun warware,
Suna yawon duniya.
(Dr Mamman Shata: Waƙar Malam Babba na Ƙofar Gabas)
A
cikin ɗiyan waƙar da ke sama, Shata na bayyana ƙwarewa da ficen da ‘yan bori ke
da shi a ɓangaren ba da magunguna. Ya nuna cewa, duk tsananin ciwo da ke damun
majinyaci, nan take zai samu sauƙi da zarar an kai shi wurin ɗan bori.
2.4.3 Masu Sana’o’in Gargajiya
Wannan
wani rukuni ne na masu ba da magungunan gargajiya. Kusan kowane rukuni na masu
sana’o’in gargajiya na da nau’in magani da suke bayarwa. Da ma dai Bahaushe na
cewa: “Kowa a gida sarki ne.” A mafi yawan lokuta, shuwagabannin waɗannan
sana’o’i su suka fi ba da magani. A jadawalin da ke ƙasa, an kawo misalan
ire-iren magungunan da masu sana’o’in gargajiya ke bayarwa.
|
Masu Sana’o’i |
Shugaban Sana’a |
Nau’in Magani |
1.
|
Maharba
|
Sarkin
Baka |
1.
Maganin ciwon daji 2.
Maganin harbin kasko 3.
Maganin ciwon tsuntsu (Ƙyan-ƙyan) |
2.
|
Mahauta/RunDawa |
Sarkin
fawa |
1.
Maganin ƙaho |
3.
|
Maƙera
|
Sarkin
maƙera |
1.
Maganin ƙunan wuta |
4.
|
Masassaƙa |
Sarkin
ice/Sake |
1.
Maganin sanyi |
5.
|
Masunta/Sarkawa |
Sarkin
ruwa |
1.
Maganin sanyi 2.
Makwakkwafa[5] |
6.
|
Ɓarayi
|
Sarkin
ɓarayi |
1.
Maganin Jingina bango 2.
Maganin Baduhu 3.
Maganin sha-tiƙa |
7.
|
Wanzamai/Ma’aska[6] |
Sarkin
aska |
1.
Maganin mayu 2.
Maganin tsai da jini 3.
Maganin kaifi |
Madogara:
Sallau, (2009: 104); Gobir, (2012: 271)
2.4.4 Wasu Mutane na Musamman
Bahaushe
na kallon wasu mutane na musamman a matsayin masu ba da magani. A tunaninsa,
Ubangiji ya huwace musu damar ba da magani bisa yanayin halittarsu. Wasu daga
cikin mutane na musamman da ke ba da magani sun haɗa da:
a.
‘Yan-Biyu:
Yayin
da aka haifi jarirai biyu lokaci guda, ana ce musu ‘yan-biyu ko kuma tagwaye.
Bahaushe na ganin cewa, tagwaye na da baiwar bayar da magani.
b.
Mai
Ƙaton Kai: Bahaushe ya ɗauki mai ƙaton kai a matsayin wanda ke
da baiwa ta ba da magani. Ba mamaki ya yi la’akari da yanayin halittarsa ne
wanda ta saɓa wa ta al’ada. Da haka ne ya yanke wannan hukunci.
2.5 Mahaɗin Maganin Gargajiya
Wani
abin burgewa shi ne, haɗa maganin gargajiya na buƙatar ilimi na musamman. Sanin
mahaɗin magani wani ilimi ne mai zaman kansa. Masu shi suna amfani da shi a
matsayin baiwa ko wata huwacewar Ubangiji. Jadawalin da ke ƙasa ya kawo wasu
daga cikin mahaɗan magungunan gargajiya:
|
Rukunin Mahaɗin Magani |
Mahaɗin Magani |
||
1.
|
Bishiyoyi |
i.
|
Ganye
|
|
ii.
|
Kauci |
|||
iii.
|
Hure
|
|||
iv.
|
Sassaƙe
|
|||
v.
|
Ƙaro
|
|||
vi.
|
Saiwa
|
|||
vii.
|
Gawai
|
|||
viii.
|
Reshe
|
|||
ix.
|
Lingaɓi
|
|||
x.
|
Mai
|
|||
xi.
|
‘Ya’ya |
|||
2.
|
Tsirrai |
i.
|
Fure
|
|
ii.
|
‘Ya’ya |
|||
iii.
|
Ganye
|
|||
iv.
|
Ɓawo
|
|||
v.
|
Sansame
|
|||
vi.
|
Saiwa
|
|||
3.
|
Dabbobi
|
i.
|
Gaɓoɓi |
Jiki,
kai, wutsiya, ƙafa, ƙassa |
ii.
|
Sassan
jiki |
Fata,
harshe, haƙora, jijiya, gashi, ido, al’aura, kunne, kayan ciki |
||
iii.
|
Najasa
|
Kashi,
fitsari, maniyi |
||
iv.
|
Ruwa-Ruwa |
Kwantsa,
miyau, jini, majina, kitse, ɓargo |
||
4.
|
Ƙwari
|
i.
|
Gaɓoɓi |
Jiki,
kai, wutsiya, ƙafa, ƙassa |
ii.
|
Sassan
jiki |
Fata,
harshe, haƙora, jijiya, gashi, ido, al’aura, kunne, kayan ciki |
||
iii.
|
Najasa
|
Kashi
|
||
iv.
|
Ruwa-Ruwa |
Ƙwai,
saƙa, kishe |
||
5.
|
Tsuntsaye
|
i.
|
Gaɓoɓi |
Jiki,
kai, wutsiya, ƙafa, fukafuki |
ii.
|
Sassan
jiki |
Fata,
harshe, haƙora, jijiya, gashi, ido, al’aura, kunne, kayan ciki |
||
iii.
|
Najasa
|
Kashi
|
||
iv.
|
Ruwa-Ruwa |
Ƙwai,
kitse |
||
6.
|
Ɗan’adam |
i.
|
Gaɓoɓi |
Yatsa,
hannu, ƙafa, kai, tsara, dantse, ƙashi |
ii.
|
Sassan
jiki |
Zuciya,
tsoka, ido, al’aura, dubura, kunne, harshe, haƙora, gira, gashi, farce,
jijiya, haƙarƙari, fatar jiki, maraina |
||
iii.
|
Najasa
|
Boli,
kashi, maniyyi |
||
iv.
|
Ruwa-Ruwa |
Miyau,
jini, hawaye, majina, zufa, ɓargo |
||
7.
|
Abubuwan
da ke ƙarƙashin ƙasa |
i.
|
Farar
ƙasa |
|
ii.
|
Karmatako
|
|||
iii.
|
Ƙanƙara
da tama |
|||
iv.
|
Kanwa |
|||
v.
|
Balma
|
|||
vi.
|
Kowa
|
|||
8.
|
Ruwa
|
i.
|
Ruwan
kogi |
|
ii.
|
Ruwan
tafki ko gulbi |
|||
iii. |
Ruwan
sabuwar tukunya |
|||
iv. |
Raɓa
|
|||
v. |
Ruwan
mashaya |
|||
vi. |
Ruwan
tukunyar matar da ba ta taɓa yaji ba har na tsawon shekaru 30 |
|||
vii. |
Ruwan
marmaro |
|||
viiii. |
Ruwan
gidan makaho |
|||
ix. |
Ruwan
gidan sarki |
|||
9.
|
Wasu
abubuwa na musamman |
i. |
Sutura
|
|
ii. |
Surkulle
|
Kwaykwaya Daga: Bunza,
(2004: 2-10); Gobir, (2012: 242-248)
Dangane da amfani
da magani kuwa, akwai fitattun hanyoyi da suka haɗa da:
1. Sha
2. Shafawa
3. Hayaƙi
4. Turare
5. Suraci
6. Binnewa
7.
Ɗaurawa
2.6 Shigowar Musulunci da Sauye-Sauye
a Magungunan Bahaushe
Ba
a yi matsaya ba dangane da lokacin da Musulunci ya zo ƙasar Hausa. Hakan na da
nasaba ne da
ƙarancin ilimin rubutu da karatu a wancan lokacin. Rubuce-rubuce da suka gabata da dama sun waiwaici tarihin shigowar
Musulunci ƙasar Hausa. Akwai manyan abubuwa da kusan dukkani wani mai magana kan wannan batu ba zai
tsallake su ba. Sun shafi manyan abubuwan da suka faru cikin tasirin shigowar
Musulunci ƙasar Hausa. Yahaya, (2011: 8-14) ya kawo su daki-daki. Ra’ayoyin
malamai dangane da lokacin da Musulunci ya iso ƙasar Hausa sun haɗa da:
1. Akwai
ra’ayin da ke nuna cewa Musulunci ya iso Borno tun lokacin sarki Mai Dunama (1098-1150).
2. Limamin
Bauchi Alhaji Ahmadu Muhammad da Alhaji Nasiru Kabara Kano na da ra’ayin cewa
Musulunci ya iso Afirka ta Yamma,
musamman
Agadas da Borno sannan ya ƙaraso ƙasar Hausa tun a ƙarni na bakwai (7).
3. Ra’ayi
na uku shi ne wanda ke nuna cewa, Musulunci bai iso ƙasar Hausa ba sai a
wajajen ƙarni na goma sha ɗaya (11th
century).
Ko ma yaya abin yake, akwai yaƙinin cewa
Musulunci ya bunƙasa a ƙasar Hausa a ƙarni na goma sha biyar (15). Rukunan baƙin jama’a da suka taimaka wajen bunƙasar
addinin Musulunci a ƙasar Hausa a wancan lokaci sun haɗa da:
1. Fulani
Torankawa da Sulluɓawa daga Futa Toro ta ƙasar Malle da
2. Wangarawa
daga Senigal da kuma
3. Malami
mai suna Shehu Abdulkarim Almaghili daga Morocco (Yahaya, 2011: 11-12).
Magungunan
Musulunci na da alaƙa da Larabawa musamman idan ana magana ne daga mahangar
Bahaushe. A bisa wannan ne Ayad, (2008: 22) ya ce:
Islamic
medicine was definitely no part of divine revelation but was something
customarily practiced by the Arabs.
Fassara:
Haƙiƙa magungunan Musulunci ba su samu ta hanyar wahayi ba. Sun kasance wani ɓangare
ne na al’adun Larabawa.
Shigowar
Musulunci ƙasar Hausa ya samar da sauye-sauye da dama ga lamarin magani.
Sauye-sauyen sun shafi manyan ɓangarori da suka haɗa da (a) ƙaruwar rukunonin masu
ba da magungunan gargajiya da (b) sabbin kayan haɗin magunguna da kuma (c)
sauyi a hanyoyin ɗebo magani da sarrafa shi. A ƙasa an kawo tsokaci dangane da
kowane:
2.5.1 Ƙaruwar Rukunonin Masu ba da
Magungunan Gargajiya
Shigowar
Musulunci ƙasar Hausa ya samar da bunƙasa a ɓangaren rukunin jama’a da ke ba da
magungunan gargajiya. A sakamakon haka ne aka samu malamai masu ba da magani. Waɗannan malamai kuwa su ake kira da malaman tsibbu. Tasowar malaman tsibbu
ya kashe kasuwar bokaye da ‘yan bori matuƙa. Ga Abin da shata ke faɗi dangane
da Malam Babba:
Bugi ƙasa ka duba
musu,
Shidda shidda ka ɗauke
uku,
Ka ga idan ka haɗa
su sun zama tara,
Kowa aka gani
cikin tara ɗin nan,
Yai sha’ani nai
shi ta rufa …
Ka je Baba ya duba
maka.
Idan ya zana ƙasa
ya duba maka,
Ya ɗaga kai ya
shaida maka,
Ka ga kamar da shi
ne a kai.
(Dr Mamman Shata: Malam Baba na Ƙofar Gabas)
Yayin
da aka nazarci wannan ɗiyar waƙa da ke sama, za a tarar da cewa malaman tsibbu
da bokaye ko ‘yan bori ɗanjuma ne da kuma ɗanjummai. Ga dai Malam Babba yana
duba tamkar yadda bokaye ke yi! Wasu rukunan masu ba da magunguna da suka samu
sakamakon zuwan Musulunci su ne malaman
ruƙiyya. An samu bunƙasar ruƙiyya a ƙasar Hausa a wajen ƙarni na 21 (Gobir,
2012: 167).
2.5.2 Sabbin Kayan Haɗin Magunguna
Musulunci
ya zo da fannanin ilimi daban-daban. Daga cikinsu har da ilimin
magani. Ya taho da nau’ukan kayan haɗin magani da suka bambanta da na Hausawa.
Hausawa sun amfana da wannan dama ta hanyar aron ilimin. Daga cikin mahaɗan magani da suka riski Bahaushe a
sakamakon zuwam Musulunci akwai:
a. Ruwan
zam-zam
b. Habbatus
sauda
c. Man
zaitun
2.5.3 Ɗebo Magani da Sarrafa shi
Ta
fuskar ɗebo magani da sarrafa shi, Musulunci ya samar da sauye-sauye. Al’adun
Hausawa da dama ba su ci karo da koyarwar Musulunci ba. Wannan ne dalilin da ya
sa Musulunci ya bar su da ire-iren waɗannan al’adu. Hakan ya sa an karɓi addinin
cikin sauƙi. Ɗaya daga cikin al’amuran gargajiyar Bahaushe da ba su ci karo da addinin
ba shi ne neman waraka. Duk da haka, akwai sauye-sauye da Musulunci ya samar
dangane da abin da ya shafi ɗebo magungunan da kuma sarrafa su. Misalan sauye-sauye da aka samu a wannan ɓangare
sun haɗa da:
a. Hana
ɗebo magani tsirara
b. Hana
ɗebo magani ta baya ko idanu rufe
c. Hana
yin wasu surkulle kafin ɗibar magani
d. Ƙoƙarin
tabbatar da sahihancin magani daga koyarwar addinin Musulunci
e. Ƙoƙarin
tantance lokutan shan magani da kuma adadin da za a sha
f.
Yawaita amfani da zuma da ruwan zam-zam a
matsayin mahaɗan magunguna
Bayan
tafiya ta yi tafiya, an samu ɗakunan ba da magunguna da ake kira Islamic Chemist. Nau’ukan magunguna da
ake bayarwa a ire-iren waɗannan ɗakunan ba da magani su ake kira Islamic Medicine wato “magungunan
Musulunci.”
2.6 Tasirin Zamani a Kan Magungunan
Bahaushe
Zamani
ya yi gagarumin tasiri a ɓangaren magungunan gargajiya na Hausawa. Tasirin ya
kai matsayin da sai an yi da gaske a iya bambance wasu daga cikin nau’ukan
magungunan daga samfurin magani na zamani. Hakan na faruwa ne sakamakon
sauye-sauyen da zamani ya zo da su, wanda kuma suka yi tasiri kan yanayin
sarrafawa da sayarwa da kuma amfani da magungunan gargajiya. Za a iya kallon
wannan tasiri a ɓangarorin da suka haɗa da:
a.
Naɗewa (Pacaging):
Wannan
ya shafi gyara magunguna
tare da sanya su
cikin leda ko fanko ko kwalba (da makamantansu) mai kyau. Haƙiƙa hakan tsari ne
da ya samu ga Hausawa bayan cuɗanyarsu da baƙin al’ummu.
b.
Sanya
Suna (Labelling): Yawanci wannan na samuwa ne bayan naɗewa. Akwai masu magungunan gargajiya a
yau da ke amfani da sunaye na musamman. Da zarar an ga irin wannan suna, kai
tsaye za a gane mai maganin. Suna kuwa ya shafi abubuwa guda biyu. Na farko
akwai sunan santa (wannan na zaman kamar kamfani). Na biyu shi ne
sunayen ɗaiɗaikun nau’ukan magunguna da ake da su. Ga misalai a jadawali da ke ƙasa:
|
Santocin Magunguna |
|
Sunayen Magunguna |
1.
|
Sangarib
Trado-Medical Centre (Kano) |
|
Hayaƙin
sheɗanu |
2.
|
|
|
Miski
|
3.
|
|
|
Bom
|
4.
|
|
|
Garlic
oil |
5.
|
|
|
Turaren
sheɗanu |
c.
Allon
Alama (Signboard): Akan samu allon alama ɗauke da sunan wata santa
ta maganin gargajiya. Hakan na mazaunin ishara ga masu neman santar da
kuma tallatawa ga sauran al’umma. Haƙiƙa wannan dabara ta samu ne a sakamakon
tasirin zamani.
d.
Gwaji/Awo/Awu
(Test): A yau akwai santocin ba da magungunan gargajiya da ke gwada majinyaci kafin ba shi magani. Sau
da dama sukan yi amfani da na’urorin zamani ne domin gudanar da gwajin.
e.
Ƙayyada
Lokaci da Adadin Shan Magani (Dose): An fara ƙayyade lokaci
da adadin shan magani tun bayan tasirin magungunan Musulunci a kan na
gargajiyar Bahaushe. Da tasirin zamani ya samu kuwa, sai lamarin ya ƙara bunƙasa.
f.
Talla:
A ɓangaren tallata magungunan gargajiya na Hausa a yau, akwai sauye-sauye da
dama. Misalan waɗannan sauye-sauye sun haɗa da:
i.
Amfani da mota ko mashin ko baro
ii.
Amfani da kafafen sadar da zumunta
iii.
Amfani da kakafen watsa labarai
iv.
Amfai da amsa kuwwa
3.1 Amfani da Illolin Magungunan
Gargajiya
Kamar
yadda Bahaushe ke cewa: “kowane allazi da nasa amanu,” magungunan gargajiya na
da nasu allazi da kuma amanu. Jadawali da ke ƙasa na ɗauke da wasu daga cikin amfanin
magungunan gargajiya da kuma illolinsu.
MAGUNGUNAN
GARGAJIYA |
|||
|
Amfani |
|
Illoli |
1.
|
A
mafi yawan lokuta, magungunan gargajiya na da araha. |
1.
|
A
wasu lokuta ba a amfani da ingantattun hanyoyin tantance cuta kafin ba da
magani. |
2.
|
Wasu
daga cikin magungunan gargajiya ba su buƙatar a saye su. Ana samun ire-iren
magungunan daga tsirrai da itatuwa (da makamantansu) da ke zagaye da muhallin
Bahaushe da dazukansa. |
2.
|
Babu
ingantacciyar hanyar auna adadi da yanayin amfani da magani. |
3.
|
Amfani
da magungunan gargajiya na taimakawa wajen yaɗa ilimin magani tsakanin
al’umma. Masu tasowa za su ci gaba da kallon nau’ukan magunguna daban-daban
da ake amfani da su. |
3. |
Babu
ingantacciyar hanyar tantance ko magani na ɗauke da sinadarai da ke da illa
ga lafiya. |
4.
|
Hanya
ce ta bunƙasa tattalin arziki da morar saukakkun albarkatu da ke zagaye da
muhalli da dazukan al’umma. |
4. |
Wasu
magungunan na cutarwa ne. Wato ana amfani ne da wasu dagacikin magungunan
domin cutarwa. |
5.
|
Amfani
da magungunan gargajiya na sa a kauce wa wasi-wasi ko zulumin shunku ko
ha’inci da cuta da za a iya ɗura wa al’umma yayin da suke samun magungunansu
daga baƙin al’ummu. Ana iya ɓoye wata cuta cikin magani domin illatar da duk
wani wanda ya sha. |
5. |
Babu
kyakkyawar tanadin adanar magungunan gargajiya. |
6.
|
Hanya
ce ta samun abin masarufi ga wasu jama’a daga cikin al’umma. |
|
|
7.
|
Hanya
ce ta kyautata kiyon lafiya. |
|
|
3.2 Sakamakon Nazari
Lallai
an samu sauye-sauye da dama a ɓangaren magungunan gargajiyar Bahaushe. Ire-iren
waɗannan sauye-sauye sun fara tun lokacin da addinin Musulunci ya zo wa
Hausawa. A nan ne aka samu tasirin magungunan Musulunci. A lokacin ne Hausawa suka fara amfani da
nau’ukan magunguna da aka bayyana cikin Alkur’ani da hadisai. Sun kuma samu
wasu nau’ukan itatuwa daga Larabawa. A taƙaice dai, zuwan addinin Musulunci ya
samar da sauyi babba ga lamarin magungunan Bahaushe na gargajiya.
A
ɓangare guda kuwa, lamarin magungunan gargajiyan Bahaushe ya kasance tamkar hanjin jimina ne,
wato “akwai na ci akwai na zubarwa.” Abin nufi a nan shi ne, duk da ɗimbin
alfanun da ke tattare da magungunan na gargajiya, akan same su tattare da wasu
koma baya. Waɗannan koma baya sun fi shafar yadda ake ɗiba da adanawa da kuma
ba da maganin. Akan ajiye ire-iren magungunan a cikin ƙyalle ko tsumma ko
takarda ko leda mai datti. Dattin kansa na iya kasance cuta ta daban ga duk
wanda zai sha maganin. Dangane da ba da magani kuwa, ba a faye samun ƙa’ida ta
musamman ba da ta shafi adadin maganin da za a sha da lokutan shan.
3.3 Kammalawa da Shawarwari
Haƙiƙa
al’amarin magani babban fage ne mai
matuƙar muhimmanci a rayuwar kowace al’umma. Daga ciki har da Hausawa. Amfanin
magani ya sa manazarta da marubuta suka daɗe suna tururuwar leƙa ire-iren hikimomi da ɓangaren ya ƙunsa.
Magungunan gargajiyar Bahaushe sun daɗe suna taimakawa a ɓangaren waraka da
biyan buƙatun rayuwa tare kuma da kare kai. Bayan zuwan Musulunci, sai nau’ukan
magungunan suka ƙaru, inda kuma wasu suka dusashe, musamman waɗanda suka ci
karo da koyarwar Musulunci. Zamani kuwa ya kawo ci gaba a ɓangarori daban-daban.
Wannan ya shafi sarrafa magungunan da yadda ake tallata su da kuma yadda ake
amfani da su. A hasashen wannan bincike,
idan tafiya ta yi tafiya, magungunan gargajiyar Bahaushe za su samu ci gaba
wanda har sai an mance da kamannunsu da fasalinsu na gargajiya. Lura da ɗimbin
alfanun magungunan gargajiya na Bahaushe da kuma koma baya da yake da shi a
gefe guda, wannan takarda ta tanadi shawarwari da ke biye:
i.
Gwamnati ta samar da shiri na musamman
inda masu ba da magungunan gargajiya za su samu horo a zamanance. Horon ya
shafi:
a. Ilimin
binciken nau’in cuta da ke damun maras lafiya,
b. Ilimin
auna sinadaren magani domin cire waɗanda ke da illa,
c. Ilimin
adana magani a tsaftace da makamantansu.
ii.
Gwmnati ta tallafa wa masu ba da
magungunan gargajiya da na’urorin zamani da za su taimaka musu ga wannan
sana’ar. Wannan zai faru ne kawai bayan samun horo na musamman.
Manazarta
Ayad,
A. (2008). Healing Body and Soul. Saudi Arabia: International Islamic
Publishing House.
Bargery,
G.P. (1934). Hausa-English Dictionary,
English-Hausa Vocabulary. London: Oxford University Press.
Bunza,
A. M. (2004). Mahaɗin Magungunan Gargajiya. Takardar da aka
gabatar a taron ƙara wa juna sani, Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato
Bunza,
A. M. (1990). Hayaƙi Fid da na Kogo (Nazarin Siddabaru da Sihirin Hausawa).
Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano.
Gobir,
Y. A. & Sani, A-U. (2017). The Jinn, Women Vulnerabilities and The Act of
Healings in The Hausa Communities Of 21st Century. In IOSR Journal of Humanities and Social Science (IOSR-JHSS, Volume
23, Issue 1, ver. 5 (January. 2018) PP 67-73 e-ISSN: 2279-0837, p-ISSN:
2279-0845.
Gobir,
Y. A. & Sani, A-U. (2018). Traces of Supernatural in Hausa Oral Songs: A
Special Reference to Dr. Mamman Shata. In International Journal of Recent Advances
in Multidisciplinary Research, vol. 05, Issue 04, pp 3755-3760. ISSN:
2350-0743.
Gobir,
Y. A. (2002). Iskoki a Idon ‘Yan Bori da Masu Ruƙiyya. Kundin digiri na biyu
wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato
Gobir,
Y. A. (2012). Tasirin Iskoki ga Cutuka da Magungunan Hausawa. Kundin digiri na
uku wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato
Harold,
S. et al (1968). Family Processes and
Becoming a Mental Patient. In Stephan, P.S. et
al (eds). The Mental Patient: Studies
in the Sociology of Deviance. New York: MC Graw-Hill Book Company.
Sa’id,
B. (edita), (2006). Kamusun Hausa na
Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.
Sallau,
B.A.S. (2000). Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a Ƙasar Hausa. Kundin
digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Bayero, Kano.
Sallau,
B.A.S. (2009). Sana’ar Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani. Kundin digiri na uku
wanda aka gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Sarkin
Gulbi, A. (2014). Magani a Ma’auin Karin Magana. Kundin digiri na uku wanda aka
gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakwkato.
Tukur,
A. (1988). Nazari a Kna Cututtukan da Suka Shafi Fatar Jiki da Magungunansu a
Bahaushiyar Al’ada. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya, Jai’ar Bayero, Kano.
[1]
Masana da dama sun ba da
rabe-raben magungunan gargajiya. Daga cikinsu akwai Gobir, (2012: 237).
[2] Wasu daga cikin masana da suka
bayyana ma’anar magani sun haɗa da: Ahmad, (1984: 133) da Tukur,
(1988 134) da sauransu.
[3] Ɗaya daga cikin manyan hanyoyi da ake bi domin ɗan’adam ya fara cuɗanya
da iska shi ne “bori.” Akan yi wa mutum girka, a daidaita iskoki da ke kansa. Hakan
na ba da dama ga ɗan’adam domin ya fara mu’amala da
iskokin da ke tare da shi, (Gobir & Sani, 2018: 69-70).
[4] Takardar ta yi la’akari da cewa,
magungunan biyan buƙata ba su
tsaya kan “na alkairi” da “na sharri” kawi ba. Sun haɗa har da na “son kai.” A fassarar Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero,
alheri na nufin (i) Kirki ko aiki na gari, (ii) Kyauta ko baiwa, (iii) Buɗi ko riba ko albarka ko arziki ko amfani da falala. A
taƙaice kenan, alheri ya shafi farar
aniya da farin aiki. Su kuwa magungunan biyan buƙata, ko dai an yi su ne domin cutarwa ko kuma wani abu
da ke da dangantaka da Son kai. Misali, bi-ta-zai-zai da maganin neman mulki
duka son kai ne ƙarara. Wane
Son kai ne ya wuce mutum ya tilasta wa wani ya so shi? Wanne ne ya wuce mutum
ya nace ala tilas sai ya zama shugaba? Me zai hana shi aikata abin da za a ga
cancantarsa a ba shi shugabancin?
[5] Wannan cuta ce da ta shafi yawan
shan ruwa ba tare da an daina jin ƙishin
ruwan ba (Gobir, 2012: 273).
[6] Aikin Sallau (2000) da (2009) ya
kawo cikakken bayani dangane da sana’ar wanzanci da kuma ire-iren ayyukan da
wanzamai ke yi. A ciki ya kawo nau’ukan magungunan da wanzamai ke bayarwa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.