Tsakure: Kimanin kashi goma sha biyar cikin ɗari na al’ummar duniya suna rayuwa da wani nau’i na nakasa. A Nijeriya kaɗai, sama da mutane miliyan goma sha tara (19) suke ɗauke da nau’o’in nakasa mabambanta, (Amamgbo, 2009). An lura cewa a wasu lokutan, ana ware nakasassu daga samun hakkokinsu da damammakinsu. Wannan wariya da ake nuna wa nakasassu ta samu ne ta hanyoyi da dama waɗanda suka haɗa da rashin ba su wani muhimmanci; rashin fifita al’amuran da suka shafi nakasassu daga fannin gwamnati a dukkan matakai da kuma rashin samar da wadatattun tsare-tsare da dokokin da za su bunƙasa tare da kare haƙƙoƙin nakasassun. Yawanci nakasa takan haɗu da wani nau’i na gazawa amma ba kowane nakasasshe ne yake zama kasasshe ba. Wannan tunani shi ne ya fito ƙarara a cikin littafin Daƙika Talatin, ɗaya daga cikin rubutattun wasannin kwaikwayon Hausa da aka samu a ƙarni na 21. Wannan maƙala ta ta’allaƙa ne kan fito da yadda marubucin littafin Daƙika Talatin wato Ado Ahmad Gidan Dabino ya kalli batun nan da ke nuni da babu nakasasshe sai kasasshe. An yi tsokaci kan rayuwar Ado Ahmad Gidan Dabino da kuma ɗaurayar littafin nasa na Daƙiƙa Talatin. Daga bisani an daddale bayanin yadda ake kallon nakasa ta fuskoki mabambanta, sai aka fayyace ma’aunin marubucin kan nakasa cikin waɗannan fuskoki huɗu da aka zayyano kamar yadda suka fito a littafin Daƙiƙa Talatin.
Rubutaccen Wasan Kwaikwayon Hausa a Ƙarni Na Ashirin
Da Ɗaya: Tsokaci Kan Ma’aunin Nakasa A Littafin Daƙiƙa Talatin Na Ado Ahmad Gidan Dabino
Na
Abdullahi Mujaheed
Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyar
Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna
I-mel:
mujaheedabdullahi@gmail.com
Waya:
+2348069299109, +2348156747550
Da
Abubakar
Hayatuddeen
Ɗalibi
a Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyar
Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna
Waya: +2348038220526
1.0 Gabatarwa
Rubutaccen wasan kwaikwayo na Hausa in an kwatanta shi
da aiwataccen wasannin kwaikwayo (irin su fina-finai da wasannin kwaikwayo na
talabijin da na rediyo), za a tarar cewa rubutaccen wasan kwaikwayon bai sami
wani isasshen tagomashi ba kamar sauran nau’o’in wasannin kwaikwayo a ƙasar
Hausa, ta fuskar samuwa da yawaita. Wannan ba ya rasa nasaba da yadda samuwar
rubutaccen adabi ya ginu cikin tarihin al’ummar Hausawa, daidai da al’ummomin
da Bahaushe ya koyi karatu da rubutu daga gare su (Larabawa da Turawa). Har ila
yau, ko da aka sami zaunuwar tadar rubuta wasan kwaikwayo cikin littafi bayan
zuwan Turawa, marubutan Hausa ba su mayar da hankali ga rubutaccen wasan
kwaikwayo ba kamar ƙagaggun labarai da rubutattun waƙoƙi. Shi ya sa batutuwan
da suka fito cikin jigogin rubutattun wasannin kwaikwayon ba su taka kara sun
karya ba; galibi sun fi karkata ga batun rayuwar aure da barkawanci da nishaɗantarwa
da ɗan abin da ba a rasa ba na zamantakewa.
Har ila yau, daga lokacin da
aka fara samun rubutaccen wasan kwaikwayo, wato 1902, har zuwa 1988, an sami
wasanni 27 ne kawai. Daga bisani kuma, sai akan sami wasu marubuta suna fitowa
da wasu jifa-jifa. Misali Barau Bambale ya rubuta wasan Kukan Kurciya. Sai kuma
wannan marubuci Ado Ahmad Gidan Dabino, wanda ya rubuta wasannin Malam
Zalimu da Ina Mafita? da kuma
wannan da aka nazarta, Daƙiƙa Talatin, (Hassan, 2017). Sai
kuma aka yi nasara wannan wasan ya zo da wani hoto (nakasa ba kasawa ba) wajen
isar da saƙonsa, wanda ba a saba da ganin irin sa ba cikin rubutattun wasannin kwaikwayon
Hausa. Kwanan nan kuma an sami ɓullar wani sabon littafin wasan kwaikwayo mai
suna Tarkon
Mut’a na Bashir Yahuza Malumfashi.
Da yake akwai hujjar da ta nuna cewa
bambancin da ake nuna wa nakasassu ba shi ne haƙiƙanin sakamakon da ya janyo
gazawarsu ba, illa ɗabi’ar nuna bambanci da wariya da mutane suka ƙirƙiro kuma
suka tasirantu da ita. Shi ya sa a wannan maƙala aka bi diddigin wasan Daƙiƙa
Talatin na Ado Ahmad Gidan Dabino, aka fayyace cewa su ma nakasassu a
matsayinsu na ‘yan Adam suna da haƙƙin su bayar da gudummawarsu tare da
amfanuwa da ayyukan cigaban al’umma.
2.0
Ado Gidan Dabino Cikin Tarihi
An haifi Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, a
shekarar 1964 a garin Ɗanbagina da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu.[1]
Ya girma a Unguwar Zangon Barebari a cikin birnin Kano. Bai sami yin karatun
boko da ƙuruciya ba, sai dai ya yi karatun allo da na Islamiyya daga shekarar
1968 zuwa 1974. Daga bisani ya yi
karatun yaƙi da jahilci a shekarar 1984 zuwa 1986, sannan ya shiga sakandare ta
dare a makarantar G.S.S Wurare Kano a shekarar 1987 zuwa 1990. Ya sami shaidar
diflomar ƙwarewa kan yaɗa labarai a Jami’ar Bayero daga shekarar 2004 zuwa 2005,
(Gidan Dabino, 2015: 112).
Shahararren marubucin littattafan Hausa
ne, sannan mai shiryawa da bayar da umarni a shirin fina-finan Hausa, kuma ɗan
jarida. Ya rubuta littattafai na ƙagaggun labarai da dama waɗanda suka haɗa da In Da So Da Ƙauna1-2 da Masoyan
Zamani 1-2 da Hattara Dai Masoya 1-2 da Wani Hani Ga Allah 1-2 da Duniya
Sai Sannu da Kaico!. A ɓangaren
wasan kwaikwayo kuma ya rubuta Malam
Zalimu da Daƙiƙa Talatin da Ina Mafita? Haka kuma ya yi wasu rubuce-rubucen a fannonin tarihi da
zamantakewa waɗanda suka haɗa da Mata Da
Shaye-Shayen Kayan Maye: Ina Mafita? da Sarkin
Ban Kano, Alhaji Dr. Mukhtar Adnan. Wasu daga cikin littattafan nasa an
fassara su zuwa harshen Ingilishi, (Gidan Dabino, 2015:112-113).
Bugu da ƙari, tare da shi aka kafa wasu ƙungiyoyi
kamar Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya Reshen Jihar Kano, (ANA) da Ƙungiyar Masu
Shirya Fina-finai ta Jihar Kano da kuma Ƙungiyar Marubuta ta Raina Kama. A taƙaice,
idan aka ce Ado Ahmad Gidan Dabino komai da ruwanka ne cikin harkar
rubuce-rubucen ƙagaggun labarai da wasan kwaikwayo da fina-finan Hausa, to, ba
a sharara ta ba. Wannan ya sa a ranar 29 ga watan Satumba na shekarar 2014
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta ƙasa mai taken,
Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama’a da yake yi cikin
ayyukansa, (Gidan Dabino, 2015: 114).
3.0
Ɗaurayar Littafin
Daƙiƙa Talatin
Daƙiƙa Talatin ɗaya ne daga cikin littattafan
wasan kwaikwayo da Ado Ahmad Gidan Dabino ya rubuta a shekarar 2015. Littafin
mai shafi 111 ya fito a daidai lokacin da ya dace, domin ko ba komai, ya
kashe wa ɗalibai da manazarta ƙishin da suke fama da shi na rashin isassun
littattafai kan wasan kwaikwayo na Hausa.
Wasan Daƙiƙa Talatin ya ginu ne a kan
babban jigon da ya mamaye jigogin adabin zamani na wannan ƙarni, wato soyayya
da kuma tsarin zamantakewa ta sha’anin zaman iyali. Soyayya ce ta ginu tsakanin
wani saurayi, Yassar, da kuma wata budurwa, gurguwa, mai suna Zannira. Daga ƙarshe
dai an yi aure, amma ango ya mutu kafin amarya ta tare, balle ma a mori zaman
auren, (Hassan, 2017).
A ranar biki, bayan an ɗaura aure, amarya
ta ziyarci ango, yana tare da abokansa, suka ɗan keɓe a ɗaki da amarya na wasu
mintuna, amarya da ƙawarta suka koma gida. Daga nan ango ya fita zuwa shago
domin ya yi wasu ‘yan saye-saye, bayan ya sallami baƙonsa da ya zo daga Legas.
A nan ya gamu da ajalinsa, inda mota ta buge shi, ya mutu.
Ashe a wannan ganawar da suka yi da amarya
ta ‘yan mintuna, alaƙa irin ta miji da mata ta shiga a tsakaninsu. Daga bisani
Zannira ta je asibiti tare da Aminu, abokin marigayi Yassar, mijinta, likita ya
tabbatar tana da juna biyu. Abin ya zama abin mamaki matuƙa har ya haifar da
zargi da cece-kuce tsakanin iyayen Zannira da iyayen Yassar da kuma sauran jama’ar
gari a kan ko dai Aminu (abokin Yassar ɗin) ne ya yi mata cikin? Da yake suna
aiki tare kuma kusan kodayaushe suna tare. Wannan muhallin shi ne ƙololuwar
rikicin da wasan yake ɗauke da shi:
Inna
Mai Koko: Ba zai yiwu ba, ina! Ta yaya
za a ce daga ɗaura aure ko awa biyu ba a yi ba
yaro ya mutu amma a ce wai
yarinya ta samu ciki da shi? A ina ta samu, a maganar da suka yi da shi
ko a numfashi ko yana lahirar ya yi mata cikin? Ina! Haram giya a gidan liman!
Kuma ba da mu ba gaɗa a maƙabarta (shafi na 71).
Wannan badaƙala ta sa har sai da aka tafi
kotu domin a yi shari’ar shin wa ke da wannan juna biyu na Zannira? Iyayenta
sun ce na Yassar ne domin ta shaida musu haka. Iyayen Yassar kuma suka ce ba su
yarda ba domin a iya saninsu babu wata haɗuwa ta aure da aka yi tsakanin Yassar
da Zannira har ya mutu.
A ƙarshen shari’ar, sai da alƙali ya buƙaci
likita ya zo ya yi wa jama’a bayanin sakamakon gwajinsa, da kuma abin da ya
gano cewa Zannira tana da ciki. Ya kuma yi dogon bayani a kan yadda ciki yake
shiga, har zuwa haihuwa, duk jama’a suna sauraronsa. Bayan ya gama bayani kowa
ya gamsu, kuma har iyayen Yassar, bisa jagorancin Inna Mai Koko, suka gamsu
cewa lallai ciki na Yassar ne:
Inna
Mai Koko: (Idanunta suna ƙwalla) Ranka
ya daɗe, na gamsu da bayanan da wannan
yaro likta ya yi. Ashe Yassar bai rasu ba tun da ga shi ya bar
wani abu a cikin matarsa. Allah ya
ji ƙan Yassar ya gafarta masa, ya sa ya huta, ya albarkaci cikin da ya bari
(shafi na 103).
Fitattun taurarin wannan wasa na Daƙiƙa
Talatin su ne Yassar da Zannira da Aminu da Amina da Samira da Inna Mai
Koko da Dr. Amir (likita) da Alƙali da Ka-Fi-Rediyo (maroƙi). Sauran taurarin sun
haɗa da Habu da Iro da Alhaji Abdullahi da Alawiyya da Mairo da Malam Isa da
Sadiya da Ladi da Alhaji Bashar da Tashare da sauransu.
Dangane da jigo, idan aka yi la’akari da yadda
likita ya warware abin da ya kusa ya gagari alƙali warwarewa, za a iya ɗaukar
amfanin ilimin kimiyya a matsayin wani jigo na wannan wasa. Domin kuwa wannan wasa ya yi ƙoƙarin nuna wa
Hausawa cewa ilimin zamani, musamman wanda ya shafi likitanci, zai iya warware
wasu matsaloli masu sarƙaƙiya na rayuwa, baya ga kula da lafiya da bayar da
magani, (Hassan, 2017).
Wani jigon da za a iya gani cikin wannan
wasa shi ne soyayya, musamman idan aka yi la’akari da karin maganar Hausawa da
suke cewa ‘shan koko, ɗaukar rai’. Wasu samari suna neman mata kyawawa masu
kyan diri da sauran wasu siffofi na mata da suke jan hankalin namiji, sai ga
shi Yassar duk waɗancan abubuwa ba su rufe masa ido ba. Gurguwa ya ji
yake so, yake kuma ƙauna (Hassan, 2017).
Amma a wannan maƙala, batun nan da Hausawa
kan ce ‘babu nakasasshe sai kasasshe’,
shi ne aka ɗauka a matsayin jigon da ya ratsa wasan na Daƙiƙa Talatin. An yi
la’akari da rayuwar Zannira a matsayin gurguwa amma duk da haka ba ta kasa ba
wajen ba da gudummawarta ga rayuwar al’umma, ta hanyar kafa da jogarantar ƙungiya
don taimaka wa mata da koya masu sana’o’in dogaro da kai. Haka kuma nakasarta
ba ta zamo mata ƙalubale ba wajen jajircewa ta ƙwato ‘yancinta a kotu game da
zargin da ake mata na cikin Yassar da take ɗauke da shi. A haka ta yi rayuwarta
har ta sami ɗaukaka da karramawar da wasu lafiyayyun ma ba su samu ba. Saboda
ba ta kasance kasasshiya ba, duk da tana da nakasa.
4.0
Yadda Ake Kallon Nakasa
Nazarin nakasa fage ne da ke ƙoƙarin
bayyana batutuwan da suke ɗamfare da zamantakewa da al’adu da siyasa waɗanda
suka jiɓanci yadda ake kallon nakasa da nakasassu. A
bisa yadda mutane suka fahimci nakasa, akwai hanyoyi guda huɗu da aka gano kuma
ake amfani da su don fuskantar al’amarin nakasa:
4.1 Hanyar Neman Magani
An ɗauki mutumin da yake da nakasa a matsayin mai wata
cuta wanda ke buƙatar ya warke domin samun dacewa da sauran jama’a cikin
al’umma. Wannan nakasasshe ana ganin sa a matsayin mara lafiyar da yake buƙatar
magani, kuma ana ware shi a matsayin wanda yake buƙatar taimakon magani. A
wannan tsari, duk da ana neman magance ko haɓaka lafiyar al’umma, ana ware
nakasassu daga cikin al’umma, ana ɗaukar su a matsayin marasa lafiyar da suke
buƙatar magani. Sa’annan ƙwararru za su shawarta irin kulawar da nakasassu ke
buƙata, su nakasassun ba su da ta cewa(IDDC, 2002).
4.2 Hanyar Ba Da Sadaka/Taimako
An ɗauki mutumin da yake da nakasa a matsayin mara
galihu, cima-zaune wanda ya cancanci a ji tausayinsa, kuma yake buƙatar a ba
shi sadaka. A wannan tsari, ana ɗaukar nakasassu a matsayin marasa daraja, masu
dogaro da wasu, waɗanda suke buƙatar a tausaya masu ko a taimake su. Hakan ya
sa ba a samar wa da nakasassu ayyukan yi, ana ɗaukar su a matsayin waɗanda ba
za su iya ba da wata gudummawa ga al’umma ba ko su taimaki kawunansu(IDDC,
2002).
4.3 Hanyar
Zamantakewa
An mayar da hankali ne kan al’umma, ba a ɗauki
nakasasshe a matsayin matsala ba. Sai dai an fi mayar da hankali ne kan kawar
da bambance-bambance da haɗin kai. A wannan tsari, an fi mayar da hankali ne a
kan ganowa tare da kawar da ɗabi’u munana da matsalolin muhalli da hukumomi waɗanda
suke zama tarnaƙi ga haɗuwar kai, don a samar da dama ga nakasassu da ma waɗanda
ba nakasassu ba, wajen samun muhimman abubuwan more rayuwa kamar ilimi da aikin
yi da sauransu. Haka kuma a shigar da nakasassu cikin al’umma ba tare da wariya
ba (IDDC, 2002).
4.4 Hanyar ‘Yanci
An ɗauki cewa nakasasshe cikakken ɗan ƙasa ne wanda
yake da ‘yanci. Masu wannan ra’ayi suna ƙarfafa nakasassu ne su shiga a fafata
da su wajen samar da cigaba, sannan su riƙe wasu muƙamai a wasu ma’aikatu, tare
da samar da tafarkin da za a bi a sami cim ma nasarar samun waɗannan haƙƙoƙi. A
wannan tsarin, ana bin dabarun samar da dokokin da suka dace don kawar da
shamakin da al’umma suka samar a tsakanin nakasassu da sauran al’umma. Sa’annan
a ƙarfafi nakasassu su sami damar bayar da gudummawa wajen cigaban al’umma,
gwamnati ta ɗauki alhakin samar da haƙƙoƙin nakasassun (IDDC, 2002)..
Abin lura a nan shi ne, hanyoyi guda biyu na bayar da
sadaka da hanyar tallafin magani sun mayar da hankali ne ga nakasasshe a
matsayin wata matsala da ake buƙatar a ga wasu ƙwararru sun shawo kanta. A ɗaya
ɓangaren kuma, hanyar zamantakewa da hanyar ‘yanci sun mayar da hankali ne ga
al’umma da hukumominta da tsare-tsarenta a matsayin ɓangarorin da suka gaza waɗanda
suke buƙatar gyara don samar da daidaito ga nakasassu a wurin cigaban al’umma.
5.0
Ma’aunin
Ado Gidan Dabino Kan Nakasa Cikin Littafin Daƙiƙa
Talatin[2]
Kamar
yadda aka bayyana a baya, cikin hanyoyi ko fuskokin da al’umma ke kallon
nakasa, hanyar zamantakewa da hanyar ‘yanci sun fi dacewa da batun da Bahaushe
kan ce ‘babu nakasasshe sai kasasshe’.
Domin kuwa hanyoyin sun mayar da hankali ne ga ƙarfafa nakasassu su shiga a fafata
da su wajen samar da cigaba, sannan su riƙe wasu muƙamai a wasu ma’aikatu, tare
da samar da tafarkin da za a bi domin su mori haƙƙoƙinsu na rayuwar yau da
kullum kamar kowane ɗan’Adam, ba tare da nuna wani bambanci ba. Wannan ita ce fuskar da Ado Ahmad Gidan Dabino
ya fayyace nakasa a littafin Daƙiƙa Talatin. Zannira ita ce fitacciyar
tauraruwar da aka gina wasan a kan ta. Kuma marubucin ya nuna ta a matsayin
‘nakasasshiya’, wato gurguwa mai tafiya a kan keken guragu, amma duk da haka ba
ta ɗauki wannan ƙalubale na gurgunta ta ƙwallafa wa ranta ba, ballantana ya
dame ta har nakasar ta zame mata kasawa. Maimakon haka, ta shiga an dama da ita
a fannonin rayuwa na zamantakewa da soyayya da neman ilimi da sana’a da sauransu.
5.1 Soyayya
A yawancin lokuta nakasassu na fuskantar wariya a
mu’amala ta soyayya, inda sai sun yi da gaske wajen kawar da kai ga irin ƙalubalen
da suke fuskanta. Amma ita Zannira ƙarfin
zuciyarta ya lulluɓe nakasar da take da shi a idon Yassar, ya ji duk duniya ba
wadda yake so sai ita. Shi ya sa ko da abokinsa Habu ya ƙalubalance shi a kan
me ya gani ga gurguwa (nakasasshiya) ya maƙale mata duk da akwai masu ƙaunarsa
da yawa? Ce masa ya yi:
Yassar: Duk na san da su, amma babu wadda ta kwanta
min a rai kamarta, kuma ita nake
so ba gudu babu ja da baya. Kuma
ka san masu iya magana suna cewa, ‘abin son rai
ne ƙawa da makauniya.’ Idan har mai ƙafa zai
tsani gurguwa, mene ne laifinta? Ai ba ita ta ɗora wa kanta ba, haka
Allah ya so ya gan ta, kai ma ba ka wuce haka ta same ka ba, don haka in wasu
suka ƙi ka za ka ji daɗi? Duk mutum
mutum ne, yana da darajarsa wadda Allah ya ajiye a tare da shi. (Shafi na
2)
A nan, marubucin ta bakin Yassar ya nuna cewa
nakasasshiya kamar kowace mace tana da ‘yancin a yi kowace irin mu’amala da ita
har da soyayya, ba tare da la’akari da nakasar ba, domin haka Allah ya so ya
gan ta, ba kuma don ba ya son ta ba. Sa’annan Allah zai iya jarabtar kowa da nakasar
idan ya ga dama. Har ila yau, wannan tunani na marubucin ya sake fitowa ƙarara
inda Alawiyya ƙawar Samira budurwar Yassar ta biyu ta yi furucin izgilanci ga
Zannira lokacin da suke hira a ofis ɗin Yassar tare da Aminu abokinsa, Yassar ɗin
ya yi caraf ya taka mata birki:
Yassar: (A fusace
ya nuna ta da yatsa). Ke Alawiyya, ba na
son cin mutunci da wulaƙanci,
kin
ji ko? Ku masu ƙafafun da me kuka fi gurguwar? Kuma kada ku manta abin son rai
ne mai mata uku ya auri jaka. (Shafi na 21)
5.2 Sana’a
Saɓanin yadda galibi ake kallon nakasassu a matsayin
waɗanda ba su da wata sana’a da za su iya yi da ta wuce bara, Ado Gidan Dabino
ya nuna cikin wasan Daƙiƙa Talatin cewa
nakasassu za su iya sana’o’i da dama domin samun abin masarufi da dogaro da
kawunansu. Abin da kawai suke buƙata shi ne a ƙarfafa masu gwiwa cikin
al’amuransu, shi ya sa Yassar ya kasance mai ƙarfafa gwiwa ga Zannira wajen
neman ilimi musamman abin da ya shafi koyon sana’a kamar yadda ya shaida wa
Samira a tattaunawarsu kan Zannira:
Yassar: Sunanta
Zannira; Makarantar Koyon Sana’a ta gama bana, kuma bayan aurenmu za
ta cigaba da karatu, da yardar
Allah. (Shafi na 5)
Marubucin ya nuna ƙarara cewa ko da nakasa mutum ba zai
kasa koyon sana’a ba, musamman idan an ƙarfafa masa gwiwa. Shi ya sa Zannira ta
yi makarantar koyon sana’a kuma ta rayu a matsayin mai ƙarfafa gwiwa ga mata
domin su nemi hanyoyin sana’o’in dogaro da kawunansu. Ta cim ma gagarumar
nasara sakamakon ƙwarin gwiwa da goyon bayan da Yassar da Aminu da Amina suka
riƙa ba ta.
5.3 Daraja ta
Musamman
A wasan Daƙiƙa
Talatin, Ado Ahmad Gidan Dabino ya tabbatar da cewa nakasassu suna da wata
daraja ta musamman, domin haka bai dace a wulaƙanta su ba. Wannan ya fito ta
bakin Sadiya lokacin da suke tattaunawa da Yassar a kan buge Zannira da ƙawarta
Samira ta yi da motarta da gangan saboda tsabar kishi:
Sadiya: (Cikin
nuna damuwa) Kash! Ban ji daɗi ba da ba ka san inda take ba da har gida ma
sai
in je in duba ta, ai mutum daraja gare
shi, musamman ma wanda yake da wata lalura a tare da shi. Ba komai ni zan yi
wa Samira magana kan wannan rashin kirkin da ta yi, kuma zan nuna mata ba ta yi
daidai ba. (Shafi na 16)
A nan Samira cikin tausayawa ta nuna cewa ɗan’Adam
daraja gare shi, ko da kuwa yana ɗauke da wani nau’i na nakasa a jikinsa. Domin
haka, ya fi dacewa a kowace mu’amala a ba nakasasshe darajarsa kamar kowane ɗan’Adam.
5.4 Gudummawa ga
Al’umma
Wani abin burgewa marubucin ya jaddada cewa nakasassu
ma za su iya bayar da gudummawa ga rayuwar al’umma, ba tare da nakasar da suke ɗauke
da ita ta zame masu cikas ko ƙalubale ba. Har ila yau, ƙarfafawa da goyon baya
kawai suke buƙata, kamar yadda a wasan Daƙiƙa Talatin Zannira ta kafa kuma
ta shugabanci ƙungiyar Babu Nakasasshe
Sai Kasasshe domin yaƙar zaman banza da mutuwar zuciya da kuma wayar da kan
mata da matasa domin samar da hanyoyin dogaro da kai. An ga haka ƙarara a
lokacin da ƙungiyar Zannirar ta kira taro domin ƙaddamar da ƙungiyar da kuma gabatar
da jawabai a kan ‘Muhimmancin Sana’o’i ga Mata Ma’aurata da Sababbin Hanyoyin
Dogaro da Kai’:
Yassar: Ga waɗanda
suka san Zannira, sun san gurguwa ce, amma wannan bai hana ta neman
ilimi
da kuma dogaro da kanta ba, wanda wasu daga nan ne suke shiga bara da maula da
sace-sace saboda mutuwar zuciya. Saboda haka ne ma ya sa ta kafa wannan ƙungiya
ta yaƙi da zaman kashe wando ga maza da mata da kuma wayar da kan jama’a bisa
dogaro da kai. Yanzu zan gabatar da Zannira don ta gabatar da takardarta mai
taken Muhimmancin Sana’o’i ga Mata Ma’aurata da Sababbin Hanyoyin Dogaro da
Kai. Bayan ta gama duk masu tambaya suna iya yi mata tambaya game da abin da ta
gabatar. Malama Zannira Bissimilla. (Shafi na 32)
Wannan gabatarwa da Yassar ya yi wa Zannira ta dunƙule
dukkan bayanan da suke jaddada fahimtar marubucin wasan Daƙiƙa Talatin cewa
lallai nakasassu ma suna iya bayar da gudummawa ga rayuwar al’umma ta fuskoki
mabambanta kamar yadda kowane mutum mara nakasa zai iya, musamman in an ƙarfafa
masu gwiwa.
Har ila yau, a hirar Aminu da budurwarsa Amina sun sake
jaddada irin gudummawar da Zannira ke ba al’umma:
Amina: Ni na rasa
wane abu ne gurguwa take da shi da ya sa mu masu ƙafa kuke banzantar
da
mu kuna liƙe wa gurguwa? Ko dai akwai wani sirrin ne da ba mu sani ba?
Aminu: Sirrin
kawai na tsayawa tsayin daka wajen taimaka wa jama’a da gurguwa take yi,
shi ya sa take da farin jini. (Shafi
na 88)
Wannan ya nuna cewa irin gudummawar da Zannira take ba
al’umma ya sa ta yi zarra cikin tsara, har ma wasu suke kishi da ita. Kenan,
nakasarta ba ta zama tarnaƙi gare ta ba, wajen taimakon kanta har ma da
taimakon al’umma.
5.5 Babu
Nakasasshe Sai Kasasshe
Kamar yadda Bahaushe kan ce ‘nakasa ba kasawa ba ce’, Ado Ahmad Gidan Dabino ya nuna a wasan Daƙiƙa Talatin cewa nakasasshe zai iya
soyuwa a zukatan jama’a fiye ma da wanda ba shi da nakasar, har ya tabbatar wa
da duniya cewa babu nakasasshe sai kasasshe. Ga abin da Kwamishinar Mata ta ce
cikin jawabinta wajen taron karrama Zannira kan ayyukan da ƙungiyarta ke yi:
Kwamishinar Mata:
(Bayan ta gama yin gaishe-gaishen manyan baƙi sannan ta tsunduma
cikin
jawabinta). Babban abin farinciki ne a ce yau a jiharmu an sami mace wadda take
gurguwa amma tana koyar da mutane sana’o’i da kuma dogaro da kai. Wannan ya daɗa
tabbatar mana da sunan ƙungiyar tasu Babu Nakasasshe Sai Kasasshe. Muna fata a
sami irin Zannira da yawa a cikin jihar nan tamu, babu shakka za a ga abubuwan
al’ajabi nan da ‘yan shekaru. (Shafi na 107)
Mahalarta Taro:
(Suka kama tafi) Raf! Raf!! Raf!!!
Kwamishinar Mata:
Ya kamata matasanmu maza da mata su yi koyi da wannan ‘yar talika
Zannira, wajen yin tsayiwar daka da
jajircewa da sa kishin zuci a al’amuransu na rayuwa. Dukkanmu yanzu mun yarda
cewa, Babu Nakasasshe Sai Kasasshe. Allah ya cire mana nakasar zuciya da
kasawarta.(Shafi na 107)
A nan, Ado Gidan Dabino ta bakin Kwamishinar Mata ta
jaddada cewa nakasa a zuciya take, duk wata nakasa in ba a zuciya aka nakasa
ba, to tabbas ba za ta zamo naƙasu ko cikas ga rayuwar mai ɗauke da nakasar ba,
ba za ta hana a shiga a fafata a bayar da gudummawa a kowane ɓangare na
zamantakewa ba. Domin kuwa, babu nakasasshe sai kasasshe kamar yadda taken ƙungiyar
Zannira ya nuna.
6.0
Kammalawa
Ƙasar Nijeriya ta sa hannu a Taron Haɗa Kan Ƙasashen
Duniya kan haƙƙoƙin nakasassu (CRRD). Wannan taro ya samar da tsarin da za a bi
a haɓaka tare da samar da kariya ga haƙƙoƙin nakasassu tare da zayyano wajibcin
da ke kan ƙasashe irin su Nijeriya wajen tabbatar da nakasassu suna da
cikakkiyar dama wajen yanke shawara da bayar da gudummuwa a dukkanin ɓangarori
na rayuwa, waɗanda suka haɗa da samar da dokoki da tsare-tsare. Amma duk da
wannan sa hannu da Nijeriya ta yi, akwai babban giɓi a Nijeriya ta fuskar
cigaban nakasassu da kare haƙƙoƙinsu. Shi ya sa har yanzu a Nijeriya, yawancin
jama’a da ƙungiyoyi suna bayar da sadaka ko tallafin magani ne a matsayin aikin
da suka sa gaba game da ‘inganta’ rayuwar nakasassu.
Ɓullar littafin Daƙiƙa
Talatin a wannan ƙarni na 21, ya zama tamkar susa a gurbin ƙaiƙayi. Domin
ko ba komai ya zo da wani saƙo da ba a saba da ganin irinsa a rubutattun
wasannin kwaikwayo na Hausa ba, sa’annan ya share wani sabon fage na nazarin
nakasa a adabin Hausa. Saboda haka wannan takarda ta nazarci ma’aunin nakasa a
littafin Daƙiƙa Talatin; Bayan shimfiɗa
game da rubutaccen wasan kwaikwayo, an kawo tarihin marubucin wasan wato Ado
Ahmad Gidan Dabino, daga bisani aka rattabo hanyoyin da ake kallon nakasa a
mu’amalance da kuma yadda marubucin ya sarrafa nakasa a cikin wasan, ta amfani
da ma’aunin da ke fayyace cewa ‘babu nakasasshe sai kasasshe’.
7.0
Manazarta
Abubakar,
Y.A (1972); The Political and Administratiɓe Implications of the Rehabilitation of
Beggers. Ibadan: University, Press.
Amamgbo,
O.C, (2009); Nigeria Planning for Golden Jubilee? Consider the Physically Challenged, http://www.iddconsortium.com
Bunguɗu, H. U. (2015);
“Nazarin Waƙoƙin Bara Na Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya A Zamfara.” Kundin Digiri Na
Uku. Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Coleridge, P.
(2001); Disability, Liberation and Deɓelopment. Chapter 1: Why This Book?. Oɗford:
An Oɗfam Publication.
Gidan Dabino, A.
A. (2015); Daƙiƙa Talatin. Kano:
Gidan Dabino Publishers.
Hassan, S. (2007);
“Sharhin Wasan Kwaikwayon Daƙiƙa Talatin Na Ado Ahmad Gidan
Dabino MON.” Cikin Jaridar Leadership
Hausa ta ranar, 9/11/2107.
IDDC, (2002);
“Making Inclusion a Reality in Deɓelopment Organisations”. International
Disability and Deɓelopment Consortium.
Malumfashi, A. (2014); “Adabin Hausa Jiya
Da Yau: Me Ke Faruwa Da Rubutun Waƙa Da Zube Da Kuma Wasan Kwaikwayo?” Jawabin
Da Aka Gabatar A Bikin Makarantar Malam Bambadiya (Facebook Group) Ranar
06/09/2014. Kaduna: Jami’ar Jihar Kaduna.
Muhammad, Ɗ.(1983);
“Ɓisual Imagery in Blind Poetry: Comments on Aliyu
Namangi’s Imfiraji and Audu Makaho’s Tabuka.” African Language Seminar Paper
presented in the Department of Nigerian and African Languages, Ahmadu Bello University,
Zaria.
Mujaheed, A.
(2017); “Adabin Bara: Nazarin Waƙoƙin Salisu Sa’in Makafin Zazzau.”Kundin
Digiri Na Biyu. Zariya: Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello.
Sarkin Gulbi,
A.(2007); “Nazari A Kan Al’adar Bara A Ƙasar Sakkwato.” Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato:
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Shehu, B. (2016);
“Sababbin Wasannin Kwaikwayon Hausa Nazari A Kan Littafin Malam Zalimu.” Kundin Digiri Na Ɗaya. Kaduna: Sashen Harsuna Da
Kimiyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna.
https://www.disabled-world.com/definitions/disability-models.php
http://www.nigeriaɓillagesƙuare.com/indeɗ2.php?option=content&dopdf=1&id=11938, Saturday, 04 April 2018.
[1] Hira da Ado Ahmad Gidan Dabino MON, a Dandalin Taurari Cikin Shirin Gari Ya Waye na Gidan Talabijin na Arewa 24
[2] A hirar da na yi da Gidan Dabino
ranar 18/02/2019 ya bayyana min cewa labarin Daƙiƙa Talatin ba labari ne da ya taɓa faruwa ba, ya ƙirƙira ne don nusar da mutane cewa kowane mutum yana da tasa darajar a
wajen al’umma. Burinsa shi ne mutane su ɗauka nakasa ba kasawa ba ce, ƙaddara ce daga Allah take samun mutum. Kuma wani
nakasasshen ma ya fi wani mai lafiyar amfani a cikin al’umma.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.